Showing 69001 words to 72000 words out of 80494 words

Chapter 24 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

12 Sep 2025

59

"yawwa Yaya"

Ishraqa ta matso tace "kintashi? Yajikin naki?"

"lafiya kalau Anty, banajin komai yanzu, dama kawai jiri nakeji"

Likita ne yashigo yasake dubata yace "zaku iya tafiya, babu abinda yake damunta kawai maleria ne da ciwon kai"

Katin Asi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????m ya karba sukaje akayi discharge dinsu sannan suka wuce gida

Suna zuwa gida taci gaba da harkokin ta, saida Asim din yahana ta yin komai, amma tanajin jikin nata dadan sauqi, batajin jirin komai,lafiya kalau suka kwanta, amma tana manne a jikinsa tana shaqar qamshin jikinsa

Cikin dare tatashi ta wata irin mahaukaciyar yunwa, Ahankali ta zare jikinta daga nasa tatafi kitchen, yan gidan da sauran yan biki duk suna bacci, indomie tadafa guda biyu tazauna a kitchen din tafara ci, zuciyarta ce tafara tashi, kafin tayi yunqurin tashi tafara sheqa amai awajan, Asim kuwa Yana juyi da yaji Bata kusa ya tashi ya duba toilet bai ganta ba, yafuto falo anan yaji motsinta a kitchen, Yana shiga yaganta ta dafe kanta da hannunta, cikin sauri ya qarasa wajan ta ya tare ta, mamy yakira ya sanar mata, cikin sauri tafuto tabiyosu zuwa d'akin, bayan ya kwantar da'ita mamy tace "Sannu Insaaf"


Bata iya amsawa ba Sai kanta data daga kawai

Mamy ta dubi Asim tace "meyake daamuntane?"

"mamy likita yace maleria ne, har qarin ruwa fa yayi mata, amma kuma yanzu ma Kinga jikin nata"

Tasake duban Insaaf tace "menene yake miki ciwo ne?"

Tace "mamy inaji kamar na mutu, ga jiri dayake dibana, kuma yunwa nakeji sosai, kuma amai nakeji gaba daya"

Mamy ta zaro idonta =?3?tace "Amai? A a, ba muga ta zama ba, Asim dauke ta mukoma asbitin nan"

Babu musu yace "to mamy"

Kayanta ya sauya mata, suka koma asbiti, wannan Karon likitan Yana ganinsu yace kawai ta'iyo fitsari a kawo masa, Asim ya sata tayi fitsari yakai musu, wani qarin ruwan suka saka mata, kafin Gari ya waye saida Tasha Leda hudu, daga nan fa Asim yakoma abin tausayi, gaba daya yashiga damuwa musanman idan ya kalleta yaga tasake yin wani irin fari, shi dama tun jiya dayaga yanayin ta yasan ba kalau take ba, amma saitace masa ita lafiyarta kalau, yanzu gashi daga jiya zuwa yau Tasha ledar ruwa har Tara, mamy ta kalleshi taji yabata tausayi, gakuma yarinya a kwance itama ba tasan inda kanta yake ba

Likitan ne yadawo zai dubata Asim yace "doctor result din bai futo bane?"

Kallansa yayi yace "yafuto, zamuyi mata scanning yanzu, sannan batada jini a jikinta, dole za'a qara mata"

"toku duba nawa idan yayi saiku saka mata"

"a a, akwai a asbitin ma, zamu saka mata yanzu, karku damu Yallabai" ya qarasa maganar murmushi Akan fuskarsa

Asim ya kalleshi wani irin haushi ya kamashi, su suna wannan halin amma dubi yanda doctor yake musu murmushi

Wata nurse ce tazo taturata sukaje akayi mata scanning, sannan suka dawo da ita suka daura mata qarin jini, idanun Asim yayi jajir damuwa tataru tayi masa yawa, Ajima ya kalleta yasake kallanta, gaba daya tausayin yarinyar yagama kamashi, ko menene yake damunta haka?

Likitan daya shigo dazu ne yadawo d'akin ya kalli Asim, ya miqa masa results din txt din yace "congratulations Yallabai, madam tana dauke da juna biyu na tsawon wata biyu, munyi mata scanning mungano 'yan biyu ne, shiyasa take wannan wahalar, but saide kuyi hakuri da wannan laulayin insha Allah Ahankali zata dinga Jin sauqi"




Zaro Idonsa yayi=?3? yace "yan biyu doctor"

Cikin murmushi likita yace "to, abinda muka gani kenan, bamu saniba mata ne ko maza ne, akwai magungunan cin abinci damuka rubuta mata dashi zata rage yawan amai tanacin abinci ko yaya ne, amma rashin lafiya saide Ahankali shine zata warke"

Mamy ta lumshe idonta tana yiwa Allah godia, cikin farin ciki tace "Alhamdulillahi, Asim kaga ikon Allah ko? Nida nake yan biyu ban haifi yan biyun ba, amma gashi kai Allah yabaka"

Wani irin farin-ciki yake ji sosai, ya kalli mahaifiyar tasa yace "mamy yan biyu fa" Sai hawaye =?-?

Murmushi tayi tace "godia zaka yiwa Allah Asim ba kuka ba, shine yabaka su alokacin daka rasa yarka qwaya daya jal, amfanin yarda da qaddara kenan"

Hawayen Idonsa yagoge ya kalli Insaaf datake kwance Ana mata qarin jini, cikin ransa yace I luv you so much Insaaf


Mamy ta kalli likita tace "doctor ai wannan albishir dole zan aikoma da goronsa"


Murmushi yayi yace "to hajiya godia nake" daga nan yafice daga d'akin

Mamy tace "To Asim, Bari inje gida na aiko muku da abinci, sannan in fadawa Ishraqa abinda yake faruwa, ga kuma Amrah anjima za'a kaita, ka zauna ka kula da'ita"


"to mamy, Allah yakiyaye"


Mamy na fita yakoma kan gadon ya rungume ta Yana kissing dinta ta ko'ina =?J?


Mamy tana zuwa gida taga Ishraqa ta tsaya Akan komai, komai Yana tafiya yanda ya kamata, lokacin data fada mata Insaaf tasamu ciki Sai tayi murmushi kawai, tana yiwa Allah godia, alokacin tayi gefe ta Kira El Hameed ta sanar dashi, cikin farin ciki yace "Alhamdulillahi, Habibty saiki shirya muje shopping a fara siyo mata kayaiyakin baby" =??

Ishraqa tace "Habiby mene?cikin wata biyu zamu fara yiwa siyaiyar kaya?"

Fada yafara yi mata "to zama zamuyi Sai haihuwar tazo sannan zamu siya? Wacce irin magana kike yi hakane? Yarinya zata haifi yan biyu idan Allah yabata dama, a a, jikokina ne fa nafarko, saina tsaya jira Sai ciki ya tsufa sannan zan siyo musu kaya? Toke idan bazaki ba, nikam zanje nasiyo musu "

Ishraqa tayi murmushi tace"to maida wuqar Yallabai, shikkenan Allah ya sauketa lafiya"

Da daddare su mamy suka hadu, aka yiwa Amrah fada tare da nasiha, Ishraqa takama hannunta suka shiga Mota Sai gidan Amjad, gidan ma babu Nisa sosai, acan suka Barta tare da qawayenta, bayan qawaye sun tafi, Amjad yashigo d'akin da sallama, Ahankali ta amsa masa, zama yayi agefenta tare da cire babbar rigarsa ya ajiye

Kallanta yayi yaga tayi wani mugun kyau, jikinta yayi wani irin fresh, qirjinta ya kalla yaga masha Allah komai acike, Ajiyar zuciya yayi yace "Anty Amrah kinyi kyau sosai"


Ahankali tace "thank you"

Tashi yayi yace "ki tashi muyi Sallah mana ko, saikici abinci ki kwanta ki huta"


Kallansa tayi, itade tasan cewa wannan aure dama yarjejeniya sukai, menene yakawo zancen sallah kuma? Ba amaren da sukai auren gaskiya ne suke wannan abun ba?, wata zuciyar tace to ai ba neman ki yayi ba, ibada ce zakuyi, Ahankali tasauko daga gadon, yanda ta sunkuya wajan saukowar shiya Bawa Amjad Damar ganin qirjinta sosai, wani irin murmushi yayi wanda ake Kira zaki raina kanki yarinya




Bayan sun idar da sallar saita ga Yana kokarin cire mata hijabi, tace "bari mana Amjad, zan cire idan zan kwanta"

Ledar kazar daya shigo da'ita ya dauko yace "to kici kazarki saiki kwanta ki huta, kinsan akwai gajiya"

Cikin sauri tace "ka zata kuma?"

"emana, ta kice, siyo miki nayi, saboda nasan kina sonta"

Jikinta ne yayi sanyi, cikin ranta tace Allah sarki Amjad, yayi kokari, to Amma kuma menene abin siyo mata wata kaza? Kaza ai ta amare ce kuma duk amaryar dataci saita biya

afili saitace "a a, Kaci abarka kawai, meyakaini cin wata kaza nida ba za mane yakawo ni ba?"

"a a, kici wallahi, menene aciki?"

Qinci tayi, duk da ranta yanason kazar, shi kuwa saiya dauko guda daya yabata a baki, babu musu tabude bakin tafara Ci, wasa wasa saida sukaci sosai shida ita, kayan wajan ya dauke bayan sun Gama, yadawo yazauna agefenta yazauna, cikin shagwaba yace" Anty Amrah.... tah "

Kallansa tayi ta kawar da kanta, jikinta ya matso yacire mata hijabin, batayi aune ba taji ya kwanta agadon bayan ta, yazubo hannunsa saman qirjinta ya matse ta a jikinsa, hancinsa yafara gogawa a saman wuyanta, cikin muryar rada yace" Antyyynaaaah...... "


Wani irin abu taji yafara yawo a jikinta,Amjad kuwa hannunsa daya dora aqirjinta yafara yawo dashi Sai qamshin datake ne yake sake fizgar jikinsa

Wani irin haushi ya kamata, cikin sauri takwace jikinta tatashi tsaye tace"Amjad pls tashi kafita"

"tayaya zan barki ke kadai Anty Amrah"

Hannunta ta hade waje daya =?O?

Yace "Ok" yafuto yaja mata kofar d'akin, compound din gidan yaje ya tsaya yakira wayar Yaya Asim

Bayan ya a dauka yace "Yaya"

Asim yace "ya akayi Amjad?"

Muryarsa ce take rawa kamar zaiyi kuka yace "Yaya Anty Amrah ce, kaga yanzu ma daga d'akin ta koroni"



Asim yayi Shiru, takaici yataru yayi masa yawa, yanzu dare ne, idan yace zaizo gidan nasu zai Iya kwakwkwada mata mari ne, tayaya zata bar masa dan'uwa a waje ita tazauna adakin? Tanaso tace ita yarinya ce ba tasan me ake nufi da aure ba?
To yanzu bazaije gidan ba, idan yaje a kanta zai huce dama akusa yake matarsa babu lafiya =??=??

Ajiyar zuciya yayi yace "
"Kora kuma? Kai kuma shine kafuto kabar mata d'akin? Amjad kana Jina ko? Babu wata Anty Amrah, Amrah zaka ce, itace aqasanka yanzu, kadena mata shagwaba kafuto mata a namiji, karka sake tsaya wa ta rainaka kana Jina ko?"


Shima Amjad din Ajiyar zuciya yayi yace"nagane, angama yaya"

Daga nan yakashe wayar yajuya cikin gida



Washe Gari dasafe likita ya sallamesu, jikin nata dadan dama dama, tana zaune a gaban motar Asim Yana ja, tafiya kadan Saiya kalleta yace "baby babu komai de ko?"

Tace "babu komai Yaya"


Sunci gaba da tafiya taga wata mata a gefen hanya tana saida dambu, cikin sauri tace "tsaya Yaya, tsaya tsaya kasiya min dambu, yaban sha'awa"


Kallanta yayi cikin mamaki yace "dambu kuma baby?"


Batare data kalleshi ba tace "Eh, shi nake so"


Kansa ya Girgiza yace "yanzu baby kirasa abinda zakici Sai abincin bakin hanya? kan titi?"

Cikin shagwaba ta daga masa kanta alamun eh

Jinjina kansa yayi, yafita yasiyo mata, yabata sannan yaja motar suka tafi, suna zuwa gida tabaje a falon tasa dambu agaba tana Ci, sosai take wata irin Loma kamar mayunwaciya, Asim yayi Shiru Yana kallanta


Mamy kuwa da tasan halin mace mai ciki murmushi kawai tayi


Saida taci dayawa sannan tafara jin amai, cikin gudu tayi daki tashige toilet tana amai, Dasauri ya tashi zai bita mamy tace "ina zaka?"

"mamy Kinga gudu takefa, kuma likita yace ta dinga tafiya ma Ahankali, saboda lafiyar abinda yake cikinta"

Mamy tace "oh ni Hussaina, Dan Allah Asim ka sararawa ranka" =??

Dawowa yayi yazauna badan yaso ba, itama Insaaf din Bata Dade ba tafuto tana goge bakinta, ta kalli mamy tace "mamy zo6o nakeso Nasha"

Mamy tace "to Insaaf, zauna ki huta zan hada miki shi yanzu yanzu"


Tace "to mamy" sannan ta maida kan TV


Acikin TV din ne aka nuno wata mata tana cin alale da manja, lokaci daya taji a duniya babu abinda takeso inba alale ba, Asim Yana kallonta qasa-qasa, Yana jira yaji me kuma zata tace tanaso 9&?

itama Juyawa tayi ta kalleshi tace "Yaya"

Cikin sauri ya kawar da kansa Yana Addu'ah Allah yasa ba alalen siyarwa zata sake cewa tanaso ba =??

Mamy ta kalleshi taga yanda yake kawar da kai, dariya ta kamata, ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah, Insaaf tasake juyowa ta kalleshi da kyau tace" Yaya kaje ka samomin Alale irin wannan, shi nakeso naci"
















Amnah El yaqoub
' [3/3, 11:02 PM] El~Yaqoub: INSAAF

Writing by:Amnah El yaqoub

51&52


Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493



Sarai yaji abinda tace, amma saiya sake kallanta yace "mekikace? Mekikeso kici?"

Cikin shagwaba tace "Bana fadama ba"

Qeyarsa ya Sosa ya tashi yace "to bari naje na nemo miki"

Mamy tace "A a, kayi zamanka, Bari naje nayi mata saina hado mata zo6on ma"

Komawa yayi yazauna Yana Kallan Insaaf, tosu masu cikin dama haka suke? daga wannan abu Sai wannan? Lokacin da Lubna Takeda ciki babu abinda Yasani, saide ya Kade rigarsa yafice office =??

Bazai dawo gidanba Sai dare, yanzu kuma gashi yanayi Dan dolensa

mamy tatashi tawuce kitchen, ta hada mata komai yanda ya dace, sannan tadawo falon, har zuwa lokacin suna nan zaune yanda ta barsu,abincin ta dauka tafara Ci amma ko guda daya bataci ba taji amai, haka, da gudu tasake tafiya taje tadawo, Asim ya runtse Idonsa =??gaba daya abin duniya yataru yayi masa yawa

Bayan tadawo mamy tayi mata sannu, ta kalli mamy tace "nagaji da Aman nan mamy, kuma yunwa nakeji, na gaji wallahi, bansan meyake damu naba"

Mamy tayi murmushi ta kalli Asim tace "baka fada mata ba?"

"ban fada mata ba mamy, naga Bata gama warwarewa bane"

Mamy tace "A a Asim"

Ta kalli Insaaf tace "Insaaf Allah ne ya azurta ku da samun baby, ciki ne dake, laulayi ne yasa bakya iya cin abinci dayawa, Sai kiyiwa Allah godia da kyautar daya miki"

Maganar taji wani iri, cikin ranta tace ciki kuma? Haka ake cikin? Yanzu ahakan itace zata haihu? Kallan mamy tayi tace "mamy ciki kuma? Ina tsoron haihuwa zan'iya mutuwa"

Cikin sauri Asim yajuyo ya kalleta, yace "wacce irin magana kike hakane?"

Kafin ta bashi amsa ya dauko zo6on da mamy ta hada mata yakai mata gaban ta yace "Kinga, ba zaki mutu ba, Sha abinki, ga zo6on Kisha"

Kanta ta daga masa sannan ta karba tafara Sha, yayi mata dadi sosai kuwa, cikin ikon Allah datasha batayi Aman ba, tana gama Sha ta kwanta Akan kujera


Mamy tace "to ai bakici komai ba zaki kwanta, me kike so sai adafa miki"

Kallan mamy tayi tace "mamy alale kawai nakeso, amma bazan iya cin wannan dinba"

Mamy tace "Ok bari na fadawa Ishraqa tayi miki ko zaki iyacin nata"

Wayarta ta dauko adaki takira Ishraqa, ta nayi mata Bayani Ishraqa tace zatayi, aikuwa ko awa biyu ba'ayi ba tabawa maigadinta yakawo, zama tayi tafaraci amma daya Kasa zaune yakasa tsaye Addu'ah yake a ransa Allah yasa ta'iya Ci, kalau kuwa taci, ta tura masa flaks din tace "Yaya ajiye min sauran, anjima shi zan qaraci"

Babu musu yace "to" sannan ya tashi yayi kitchen da sauran abincin, Yana tafiya Yana waigenta, wacce irin fitina ce wannan ace bazaka iya cin abincin gidanku ba saina maqota 9&?>?#?



Da daddare suna cikin bacci tafarka, wata irin hamma tayi tashafa cikinta taji babu komai kamar anyi mata yasa, kallan Asim taga Yana bacci, Ahankali takai hannunta tashafa sajensa, Bude Idonsa yayi ya kalleta "Baby lafiya? Meyafaru?"

Shiru tayi tana darurar fada masa yunwa takeji

Janyota yayi jikinsa yace "fadamin, meyake faruwa?"

"Yaya yunwa nakeji"

"tome zakici? Sai naje kitchen din da kaina nagani ko zan iya hada miki" =?J?

"Yaya nifa dabino nakeso"

Zaro Idonsa yayi =?3?yace "Dabino baby? Dare yayi fa"

Tace "ai Yaya idan banci dabinon nan ba akwai matsala, bazan iya bacci ba"

Tashi yayi zaune yace "Subhanallah...meyakawo wannan maganar kuma?"

Tsaye ya miqe yazura jallabiya, sannan yasake Kallan agogo, ya dauki key din Mota yafuto, Dasauri tabiyoshi tace "Yaya muje"

Babu musu yace "to sako hijabi mutafi"


Maigadi ma yariga yayi bacci, saida suka tasoshi yabude musu get din sannan suka futo, haka suka dinga bulayi suna neman dabino amma basu samu ba, wani mai kayan fruit suka gani Yana tattare kayansa da alama Shima yayi dare ne bai tafi gida ba, tambayar sa sukayi yace maqocinsa dai Yana siyarwa, haka suka daukeshi Amota suka tafi gidan, aka taso maqoci, yakawo musu dabinon kusan Rabin kwano

Asim ya kalleshi yace "Bata kwano biyar, idan yaqare saina dawo aqara mata wani"

Jikin me dabino na rawa ya auna musu sannan suka tafi gida, suna zuwa yacire rigarsa ya kwanta, ita kuwa zama tayi Akan gadon tafara cin danon, saida taci yakai Rabin kwano Sanna tature sauran, Shima gajiya tayi taci, amma ba qoshi tayi ba, juyi yayi yaganta azaune tana hada qwallon dabino waje daya, cikin muryar bacci yace "Wai baki kwanta ba?"

Tace "yanzu de zan kwanta Yaya"

Murmushi yayi yakoma yaci gaba da bacci


*** ****** ***



Tunda safe dasuka tashi yake da daure fuska, Yana kallanta tanata zirga-zirga saide ya kalleta ya dauke kansa, babu alamun wasa ko kadan a fuskarsa, singlet ce a jikinsa Sai dogon wando na jeans, tunani yake ina zaije yahuta tunda ya dauki hutu awajan aikinsa?


Yasake kallanta Sai abin gaban ta takeyi ko kallo ma be ishetaba, mezai sa yazauna ma a gidan suna wannan Zaman ko in kula din?>??

Kallanta yayi yahadiye wani irin saliva saboda yanda kayan jikinta suka gama tafiya da Imaninsa, yace "Amrah dauko min rigata adaki inaso nafita"

Kallansa tayi, cikin ranta tace Amrah! Ta kalli jikinsa Sai wani shining yake kasancewar sa fari tas, tasake Kallan dantsan hannunsa taga kamar bashi ba, tunani take kode taje ta dauko masa? Gida da gashi Sai ita Gara ta lallaba shi surabu lafiya =??


Afili tace "da meyasa kafuto babu rigar"

Fuskarsa a daure yace "to ko bazan samu bane inyi abinda Naga ya dace?"

Dasauri tace "menene abinda ya dace din?"

Tashi yayi yafara nufarta yace "bari inzo in nuna miki"

Tana ganin ya nufota tayi sauri tashige dakinsa ta dauko rigar ta kawo masa

Murmushi yayi yace "thank you, sweet Anty"

Itade Amrah tayi Shiru ta qyaleshi, rigar yagama sakawa Idonsa ya sauka Akan qirjinta yayi wani irin murmushi yace "Suger Anty...."

Juyawa tayi zata bar wajan, taga alama Jan magana kawai yakeji, tana tafiya taji ya rungumota tabaya, tace "Amjad bari mana"


Kafin yayi magana sukaji wani irin qara mai firgitarwa sakamakon tayar wata babbar Mota data fashe, gaba dayansu suka kwasa aguje zuwa daki, Amrah gudu Amjad gudu =??



Suna shiga daki suka Amjad yafara kokarin rufe wa, Amrah kuwa jikinta ne yake rawa takama hannunsa Tariqe tana fadin "Amjad yi sauri karufe kofar"

Yana rufewa tashige cikin jikinsa, tana jiyo yanda bugun zuciyarsa ya sauya, kallanta yayi yaga tashige cikin jikinsa gaba daya Sai yanzu ne yaji wata irin kunya ta kamashi, Yaya akai wannan qaran yasa shi ya tsorata harya biye mata suka shigo daki aguje? Anya kuwa wannan abun ba zaisa Amrah tasake raina shi ba?

Murmushi yayi yasaka hannu yasake rungume ta sosai a jikinsa, yayi qasa da kansa cikin muryar rada yace "Amrah abin yatafi fa"

Qin dago fuskarta tayi daga qirjinsa tace "tsoro nakeji Amjad"

Wani irin dadi yaji, yasake rungume ta,yayi qasa da kansa dede fuskarta, cikin shagwa6ar daya saba yace "Allah yatafi fa"

Bakinta tabude zatayi magana yayi sauri yahade bakin su, zaro idonta tayi ka kalleshi, suna hada ido ya lumshe mata Idonsa, yasaka hannu yariqe kanta Yana yi mata wani irin kiss, kokarin tureshi take amma yayi mata wani irin ruqo, dukansa tafara amma maimakon yasake ta saiya sake riqeta yakai hannunsa bayan rigarta yayi qasa da zip din


Lokacin da yayi arba da qirjinta rasa nutsuwar sa yayi, Amrah tafashe dawani irin kuka, takaici ya kamata, cikin kuka ta qwace bakinta tace "haka mukai dakai?, dama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login