Showing 51001 words to 54000 words out of 80494 words

Chapter 18 - INSAF BOOK COMPLETE BY Amnah El Yaqoub.doc

12 Sep 2025

49

ba, amma besan dalili ba idan tayi fishi dashi yake Jin babu dadi a ransa, gashi koda yaushe cikin fada suke, amma idan tayi fishi taqi kula shi yana shiga cikin damuwa

Dan qaramin tsaki yaja a ransa, to mema ya kaishi kissing dinta? Wacce masifar ce ta kaishi? Karma tafara tunanin da niyya yayi mata hakan Dan yaji dadi kokuma wani abu makamancin haka, bayan Shima ba hakan ya soba, to Amma tayaya zai Hana ransa abinda yake so? =?3?=?J?


Yana wannan tunanin har suka qarasa, basu Sha wata wahala ba tunda tare suke da mamy aka bar Daddy yafuto, mamaki ya kama su ganinsa tare da Alhaji Umar, qanin mahaifin Lubna, wanda shi din abokin Daddy ne qut da qut

Jikin Amjad yayi sanyi, yakoma gefe daya Yatsaya kansa agefe, kwana daya kawai amma har kamar Daddy tafara sauyawa

Yana qaraso wa wajan su ya tsugunna yace "Hajiya Ussaina, kinmin komai a rayuwata, yanda kika riqemin dana ba kowacce macece zatayi hakan ba, Amma son abin duniya yarufemin ido naci amanar dan'uwana da muka futo ciki daya, naci amanar yaransa, haqiqa nabiyewa Rudin duniya, Amma inaso kisani ba laifi na bane hakan, asalima Alhaji Umar shine silar lalace war komai, shine mutumin dayake zigani daga gefe ina aikata komai, yasa na dauko takardun kadarorin ku nabashi a jiya, ashe yariga yagama siyar da komai yayi amfani da kudin, yar dan'uwansa taga Asim a makaranta ta nuna tana sonsa, yazo min da maganar auren banyi tunanin komai ba na amince, bayan yariga yasan yarinyar ba mutuniyar kirki bace, asali ma shida kansa yafadamin yasha neman yarinyar, amma rashin hankali yarufemin ido nayarda aka hadata da dan d'an'uwana, bayan zaluncin da yayiwa yarinyar yake ne manta a matsayin ta na yar dan'uwansa, hakan bai isa ba saida yafara yimata barazana Akan inde Bata kashe Asim ba, zaizo har gida yatona mata asiri, ita kuma hakan ne yasa take aikata komai
, abinda nasani shine na zalunci kaina da kaina, saboda nida kaina na aikowa da Lubna guba tazubawa Asim, amma Sai Allah ya kare shi Widad taci, saboda alokacin gani nake kin riga kin janye min dana Amjad daga jikina, kin rabani dashi, shiyasa Nima naso na rabaki da naki Yaron, amma banda wannan sauran kashe kashe da komai alhaji Umar ne yake kiran Lubna yake Bata umarni Akan komai, nariga na amshi laifi na tun a Daren jiya nayiwa hukuma Bayanin komai, ina fata hukuncin da za'a yanke min yazama Shine Sanadin shiryuwata, inaso Keda Asim da Amrah ku yafemin "

Yana gama wannan maganar yafara hawaye sosai, ita kanta mamy jikinta yayi wani iri, hawaye ya zubo mata tasa hannu ta share




Amjad kuwa yarufe Idonsa da tafukan hannunsa yana kuka wiwi, Asim ya goge kwallar Idonsa ya dubi d.p.o yace "babu yanda za'ai muyi belinsa yanzu?"

"mun riga mun tura case dinsu zuwa kotu Yallabai, laifin dasuka aikata ba qarami bane dazamu iya badashi yanzu, anrasa rayukan mutane ta sanadinsu, yanzu haka mun tura ataho da Lubna, zamu tattarasu mu turasu court gobe, amma idan bai Bawa kotu wahala ba kamar yanda muma yabamu hadin kai yafada mana komai tun kafin kuzo, to itama kotu zata iya masa sassauci Akan haka "

Al'amarin yawuce inda Asim yake tunani, haka suka dawo gida cike da damuwa, washe Gari kuwa kotu ta yanke musu hukunci, Alhaji Umar hukuncin kisa ta hanyar rataya,sannan kotu zata saida kadarorinsa abawa su Asim haqqinsu daya cinye, Daddy kuma an turashi Gidan kaso na tsawon shekara biyar, Lubna kuma Shekara biyu tare da aiki mai tsanani

Sosai take kuka tana kallon Asim, tanaso ta roqeshi yayafe mata amma babu hali


Bayan sun dawo daga katun Kasa gane kan Amjad sukayi, saida suka hadu gaba dayansu suka bashi hakuri tare da kalamai masu dadi sannan ne yad'an saaki ransa


Su Ishraqa ganin gidan babu lafiya suma basu nunawa Mamy suna son Insaaf tadawo wajan su ba kafin ayi maganar yanda zata tare agidan mijinta

Sai bayan sati daya suka shirya duk su ukun suka tafi Sudan domin taga dangi suma su ganta

Bayan sun sauka a qasar anan ne taga soyaiya sosai awajan dan'uwan mahaifinta Hammudi, Sai kuma wata cousin din Ishraqa mai suna Malaz, tunda sukaje awajan ta take zama, Ishraqa kam Bata zauna ba, kasuwa take shiga itada wata qawarta suna hado abubuwan gyaran jiki
, kwanan su hudu amma saboda yanayin Garin harta fara haske, kowacce Rana da abinda Malaz take koyawa Amina na kula da miji,kwanansu biyar Ishraqa ta turata wajan qawarta dake Shari Moya, acan ake mata gyaran jiki, turaren tsugunno kuwa wato (dukkan) tsallaken kwana daya sukeyi, yau idan akayi, gobe ba za'ayi ba, lokaci daya jiki ya murje, fata tafara sheqi, lungu da saqo nata ya dauki qamshi




Dazasu taho Nigeria sunje kasuwa, taga wani agogo mai kyau ta kalli mamanta tace "Anty Kinga wannan kamar zai yiwa Yaya Asim kyau"

Ishraqa tayi murmushi tace "zaiyi masa mana, ki dauka masa kihada masa da zobe ma, idan mun koma saiki saka masa"

Kunya ce ta kamata, tasa hannu tarufe idonta,

Haka suka bari qasar cikeda kewar yan'uwa

washe Gari suka dawo Nigeria, Kai tsaye agidan Ishraqa suka sauka, anan Amina taga wata sabuwar duniyar, kasancewar da daddare suka sauka basu nuna mata komai ba, bayan sun Gama cin abinci, tayi wanka tana saka kayan bacci Ishraqa tashigo d'akin

Zama tayi a gefen gadon ta tana kallon yar Tata, Amina ta juya ta kalleta tayi murmushi, turare ta fesa sannan tadawo kusa da ita zauna tace "Anty ina Abba na"

"Yana kwance adaki, yanzu zan tafi Nima, karbi ma ganinki Kisha, Antynki Malaz tace Karki yi wasa dashi"

Yatsina fuska tayi, idonta yayi rau rau Yana kawo ruwa tace "nifa Anty dama Dena bani wannan abun kukai"

Ishraqa ta kalleta da mamaki tace "saboda me?"

"Anty ni banaso Shima narasashi"

"waye bakya so ki rasa?me kike nufi?"

"shi Yaya Asim din,Kinga shine ya taimaka min, kuma ni...ni inajin tausayin sa"

Ishraqa tayi murmushi tace "Kinga Insaaf, kifadamin menene matsalar? Ba'iya uwa zaki daukeni ba, harda qawarki, kifadamin komai, kince kina Jin tausayin sa, hakan yana nufin kina sonsa ne?"

Cikin sauri tace "a a Anty, ni Bana sonsa, nide kawai inajin tausayin sa, kuma banaso narabu dashi"

Ajiyar zuciya ta sauke, takamo hannun yarinyar Tata tariqe, tace "Insaaf kinason Asim, wannan shine maganar gaskiya"

"A a Anty, ni tausayinsa nakeji kawai, sannan Kuma Ina tsoron wani abu yafaru atsakanin mu, zai mutu,kamar yanda sauran mazajan dana aura suke mutuwa, ni kuma Bazan iya jure rashin sa ba"


Mamaki yakama Ishraqa, tace "mazaje kuma?"

Idonta ne yacika da qwalla, tabbas akwai abinda yake damun yar tasu, wacce irin damuwa ce wannan? Muryarta na rawa tace "kintaba yin aure ne Insaaf?"


Kanta ta daga mata, sannan tace "Aurena shida Anty"

Hawaye ya sakko wa Ishraqa, akwai wata aqasa kenan, tasa hannu ta share tace "meyasa baki fadamin ba? Haba Insaaf? Nifa mahaifiyar kice, ta wani Fannin kuma qawarki, tunda kina auren abokina ai kema kinzama qawata, meyasa tun kafin muje Sudan baki sanar dani ba, Dan nasan irin gyaran dazasu miki? Wacce irin rayuwa kikai Abaya Insaaf? "

Kallan mahaifiyar Tata tayi tace" Anty nifa... ni... ni babu abinda yake hadani dasu, kowa na aura mutuwa yake, inde sunzo wajena da daddare to shikkenan saisu mutu, bansan meyasa ba Nima, Yaya Ammar ma Dana aure shi kwanan sa daya yarasu, shine su Inna suka koreni daga wajan su, Shima me garin yace dama yafadamin inde wani yasake mutuwa ta dalilina to zan bar masa garinsa, shine Yaya Asim yace nazo mutafi, dana biyoshi wani malami yayi mana aure dashi, Shima washegarin daya daura mana aure yamutu, Kinga Shima Yaya Asim zai mutu ko? Shima tafiya zaiyi yabarni, shiyasa nakeso Shima yasake ni, banaso yamutu Anty...."















Sharhi,Anda Share please =?O?


Amnah El yaqoub
' [2/24, 1:08 PM] El~Yaqoub: INSAAF

Writing by:Amnah El yaqoub

37&38


Like my page on Facebook =?G?
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493




Kasa magana Ishraqa tayi, Sai kuka data fashe dashi, kawai Girgiza kanta take takasa cewa komai, itama 'yar dataga haka saita fara hawaye, cikin kuka tace "Anty kiyi Shiru"

Cikeda kuka tace "saboda me zanyi Shiru Insaaf?, nadade na sanin akwai abinda kika boyemin, ina nan ina Addu'ah Allah yasa kinfada cikin hannu nagari, ina tunanin mutane zasu soki ashe gudunki suke, hasbinallahu wa ni'imal wakeel, wacce irin masifa ce wannan? Aurenki bakwai Insaaf meyasa kikeso kiyi na takwas? Idan Asim ya sakeki wakike tunanin zai aureki ya 6oye miki sirrin ki kamar yanda Asim yayi? Duk yanda nake dashi betaba fadamin labarinki ba tun kafin nasan ke 'yata ce, Insaaf Ada kenan ma dabaisan akwai wata alaqa a tsakanin muba, tayaya kike tunanin yanzu zai fadamin wannan matsalar?
Asim mutum ne Insaaf, abun so awajan kowa, bazan taba yarda kirabu da Asim ba, Insaaf tun kafin na haifeki nake tare da Asim, tun kafin yasan ke wacece yake kula da dukiyar ki, idan kika rabu dashi kwata kwata ni baki kyauta minba, zan samu babanki nayi masa magana gobe, amma kidena cewa kinaso yasakeki kinji, Allah bayason haka "

Ahankali ta daga mata kai, sannan tace"to Anty"

"yauwa karbi maganin ki Kisha, ki kwanta kihuta"

Babu musu ta karba ta shanye Sannan ta kwanta, Ishraqa taja mata Bargo sannan takashe mata wutar d'akin tatafi d'akin El Hameed itama ta kwanta

Qasa qasa yake jin kukan ta Yana ratso cikin kunnansa
Ahankali ya karanta Addu'ar tashi daga bacci, ya kalleta yace "Habibty lafiya kuwa?"

"Habiby nayi magana da Insaaf ne yanzu"

"magana kuma? Dama baki Barta ta kwanta tahuta ba?"

"A a Habiby, maganar tanada muhimnci sosai, Insaaf tana tare da matsala Habiby, tacemin tanaso Asim ya saketa"

Yanajin haka ya tashi zaune da sauri "saki kuma? Meyake faruwa to?"

"Habiby Insaaf fa aurenta shida kafin Asim...." tsaf ta zayyana masa komai kamar yanda Minal ta sanar da'ita

"innalillahi...yanzu Ina Insaaf din take?"

"ta kwanta, tana dakinta"

"wanne irin tana dakinta Ishraqa, tayaya yarinya zata fada miki wannan maganar kitaso ki Barta cikin damuwa?" =??

"to ai Naga dare yayi, kuma daga tafiya me nisa muke, kaima bansan dagama hankali"

Dan qaramin tsaki yaja yace "Kinga, tashi muje dan Allah, to Ishraqa kodaga bangon duniya muke ya dace mubar ta cikin damuwa ne? Muje idan na tabbatar tayi bacci saimu dawo"


Daga masa kai tayi, sannan suka nufi d'akin Minal, suna zuwa ya kunna wutar d'akin, harta fara bacci Alokacin, wutar dasuka kunna ne yasa tatashi, zama Sukai Akan gadon, El Hameed ya shafa dogon gashin ta yace "bakya tare da damuwa Insaaf?"

Cikin mamaki tace "Abba damuwa kuma?"

"mamanki tayi min Bayani yanzu, kiyi hakuri karkisa damuwa aranki harta ta6a lafiyarki"

Murmushi tayi tace "babu komai, ai harna fara bacci ma"

"to Allah ya yi miki albarka yata, kwanta kiyi baccinki"

Komawa tayi ta kwanta, ya sunkuya yadora ba kinsa a kanta yayi kissing sannan yaja mata bargon

Fira suka fara yi shida Ishraqa kadan kadan, basusan yaushe bacci ya dauke suba, haka suka kwana duka su ukun a dakinta



*** ****** ***



Zaune yake a falon su, yayi kyau sosai cikin shigar sa ta kullum wato suit, breakfast yagama amma yana zaune afalon baitafi wajan aiki ba, mamy tana gefensa da Carbi a hannun ta,idan bai manta ba rabonsa da Insaaf tun kafin sutafi Sudan, ta nemeshi awaya ma ya gagara, wajan contact din kan wayar sa yashiga yafara duba numbers din ciki, saida yagama gani sannan ya yatsina fuskarsa, Sai yanzu yatuna batada waya , ya kamata ace yakira ta ya nuna mata kuskuren ta Akan rashin kiranshi, to Amma kuma ta'ina zai kirata? Ishraqa zai Kira ko El Hameed? >??

Amrah ce tafuto daga d'akin su kai tsaye wajansa ta nufa ta zauna aqasansa ta gaida shi

A taqaice ya amsa mata,zuciyarsa ce ta bashi shawara yanemo number Ishraqa.


Number yakamo yayi dialling saiya katse, yasake yi a Karo na biyu nanma ya katse

Wayar ya ajiye agefe, to yanzu idan ya Kira Ishraqa ma meze cemata?
Wata zuciyar ce tace dashi kakirata, kasan Yara da San wasa da waya, yanzu haka wayar tana hannun Minal din tana yin game da'ita

Haka yasake dialling number, tana shiga kuwa aka daga, muryar Ishraqa yaji tace "Salamu Alaikum Asim katashi lafiya?"

Wayar ya kalla, cikin sauri ya kashe, anata bangaren tace "kode network ne?, Bari nasake Kira"
Tana Kira yad'auka yace "Sorry akwai number dazan Kira ne sainayi mistek" =??

Tace "to shikkenan, jiya mun sauka da daddare, ko zaka shigo ne kafin kawuce office?"

"no, akwai ayyukan da zanyi"

Mamy dake gefe ta daga kai ta kalleshi, Yana cewa akwai ayyukan da zaiyi amma kuma Yana zaune bashida alamar tafiya office dinma, tarasa meyake jira?

Daga dayan bangaren Ishraqa tace "Ok, Allah yakiyaye hanya"

Shima yace "Amin" sannan yakashe wayar

Ishraqa tayi Murmushi, kode Asim yana neman Insaaf ne? Ikon Allah, aure me Hana wani abun,aure mesa ayi wani abun, jidai yanda Asim yake magana da'ita kamar ba Ishraqa tasa ba, kamar ba aminiyarsa Ishraqa ba, Ahankali tatashi tashiga d'akin Insaaf, tana zaune da breakfast agabanta, El ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Hameed Yana karanta mata Jarida, zama tayi ta kalleta tace "idan kingama break din kishirya muje kizabi wayar da kikeso, yanzu mijin ki yanason magana dake, kikirashi"
Ta ajiye mata wayar agefenta

El-Hameed yace "saide kuje Keda ita, ni akwai inda zani, nayi waya da wani malami Akan issue dinta, zanje musan abinda ya kamata ayi"

Tace "to zamuje insha Allah"

Kallan Minal yayi yace "Insaaf idan kingama wayar, ki same mu adaki"

Ahankali tace "to Abba"

Suna fita takirashi, yayi mamakin ganin kiran Ishraqa bayan sunyi sallama ita dashi, dauka yayi tare da sallama, itama anata bangaren ta amsa masa, tace "Yaya ina kwana"

Wata irin Ajiyar zuciya yasauke, har ita kanta Minal din taji shi, Kallan gefen mamy yayi, ya kalli Amrah data zauna agabansa, lokaci daya ya tsinci kansa da qaramar murya =?J?

Cikin qasa-qasa da murya yace "bakya kira kiji lafiyar mutane ko?"

Cikin shagwaba tace "to Yaya ni banda waya fa..."


Yasalam!
Yafurta hakan a ransa

"Alright, kishirya Amjad yakaiki saiki za6i wadda ta miki, Amrah tanason magana Dake"

"Yaya Anty tace zasu siyamin, ka cewa Anty Amrah ina missing dinta"

Idanunsa ya runtse =?#?
Iya Amrah take missing, Ahankali yace "Bye" qit yakashe wayar

Mamaki ya kamata, Ana magana rimi-rimi kuma Sai abun yaqare a haka?

Tashi tayi ta nufi wajan Iyayen nata, anan suka fara nuna mata kayaiyakin ta, da wasu daga cikin kadarorinta,da kayanta tana qarama, Abin saiya dinga Bata mamaki yanda suka iya Adana kayan har zuwa wannan lokacin, anan El Hameed yabar su, yafice zuwa wajan Malamin da sukai magana



*** ****** ***




Amjad ne yafuto daga dakinsa, kana ganin fuskarsa zaka tabbatar Yana cikin damuwa, bayan ya gaisa da Mamy yazauna kusa da Asim, yace "Yaya ina kwana"

Kallansa yayi yace "lafiya, yaushe zaka tafi Adamawa ne?"

"inata shiri Yaya, zan koma insha Allah, Bana Jina yanda ya kamata ne shiyasa"

Asim ya jinjina kansa, yasan cewa damuwar Amjad Bata wuce Akan Daddy bane.

Amjad ya kalli Amrah yace "Anty Amrah ina kwana"

Tanaji tayi banza dashi, yayi Dan qaramin murmushi yace "bazaki amsa ba?"

Nanma batace masa komai ba tayi Shiru, Asim ya kalleta, yaga alama kamar Amjad Yana son Amrah, amma ba zaice komai ba tunda Shima Amjad din be furta ba, inda hakan ta kasance kuwa zaifi kowa farin-ciki, ko banza Amjad dinsa zai zama cikakken namiji, yadena wannan shagwa6ar,yanda yakejin Amjad a ransa zai Iya bashi kowanne irin goyon baya Akan hakan, ajiyar zuciya yayi yace "ba dake yake magana bane?"

Kallan Asim din tayi tace "naji shi Yaya, kafada masa ni yafita harkata, kowa yayi abinda ya shafeshi" =? ?

Asim ya dafe kansa da hannunsa yace "meyake damun kune? Ku qananun Yara ne? Koda yaushe bakuda aiki daga fada Sai fada?"

Mamy dake gefe ta kalli yaran nata "doke-doke zaka ce Asim,Abin ai yafi qarfin fada, ninariga na zare hannu na daga Al'amarin su, saide Kai in zaka iya"

Amjad ya shafa sumar kansa yayi murmushi, ya tashi yace "Bari in dauko wayata akwai inda zani, Anty Amrah ko zakije?"

Yaqarasa maganar Yana kallonta =?
?

Kanta ta girgiza tace "A a"
Daga nanma tatashi tashige dakinsu, tunani take a ranta tayaya ma zata bishi? Agidama ya matse ta yayi kissing dinta idan tabishi waje tasan mezai faru?

Shima murmushi yayi kawai yawuce dakinsa, Asim yabishi da kallon mamaki, baiyi tunanin Amjad zai share Amrah ba,yayi tunanin zai biyeta suyi cacar baki ne kamar yanda suka saba, amma abin mamakin saiyaga murmushi ma yayi, kode tunanin sane yake shirin tabbata?

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Mamy


"zantafi office mamy, saina dawo"

"inason magana dakai"

Dawowa yayi ya zauna, ta kalleshi da kyau, tanaso ta tambayeshi menene damuwar sa? dawa yake waya haka Sai kashe murya yake kamar yasamu budurwar sa, duk da tasan ba lalle ne yabata amsa ba, ya kamata ace taji da wadda yake wannan maganar, kartaje haqilon banza kawai take akansa


tace "dawa kake waya ne?"

Kai tsaye yace "Mami Minal ce..."

Murmushi tayi tace "lafiya dai ko?"

"gashinan de" =??

"meyake faruwa to?"

"mamy tunda sukai tafiyar nan Bata ta6a nemana ba, sannan memakon ta sauka anan shine tabisu Takoma can gidan, nakirata ina mata maganar Bata kirana, shine tacemin tayi missed din Amrah" yaqarasa maganar Yana hade rai

Mamy tayi Shiru tana Kallan tsantsan karfin hali dakuma rashin gaskiya irin na Asim, da kunnanta taji yana cewa Amrah tana son magana da ita, amma yanzu Wai qiri-qiri yake cewa yayi mata magana Bata kiransa

Kallansa tasake tace "Asim"

"na'am mamy"

Tace " kafita daga cikin Idona na rufe Asim,kafadamin kana son wannan yarinyar kokuma baka sonta?"

Cikin sauri ya kalleta yace "Mamy daga maganar kiran waya meya kawo zancen soyaiya kuma?"

Mamy tace "ikon Allah,toka sauwaqe mata, ina amfanin zama da mutumin da baya qaunarka?"

"to mamy waye yace Bana qaunarta?, itace Bata sona, Nima shiyasa ban nuna mata ba"=?J?=??=??

"waye yafadama Insaaf Bata qaunarka?"

"mamy Muhsin ne yacemin ranar dasuka hadu a hanya yadauke ta suka tafi gidansa ita da kanta take roqonsa yakai ta court Araba auren mu"

"Subhanallah..., to Amma kasan yarinya ce, sannan may be da rashin kulawar da kuke Bawa juna shiyasa tafadi haka, Asim baka kula ta, itama Bata kulaka, tayaya zaku Fahimci juna?"

"Nima bansan ina sonta ba, saida Muhsin ya fadamin, daga baya sainayi tunani Naga hakanne, sannan mamy akwai abinda nake tsoro, duk mazajen da Minal ta aura mutuwa suke mamy,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login