Showing 21001 words to 24000 words out of 36278 words

Chapter 8 - Zan Fasa Kwai Part 1 Complete by Hadiza Bara'u Gidan Iko.txt

shi tas inda Kuma motocin na Yan sanda suka faka har mota uku cike da Yan sanda tamkar zasu Kama Yan fashi


"Kunga shegen Nan ku Kama min shi cewar izzatu inda taga kaf din Yan sandan sun wuce wurin Wanda take cewa su Kama Amma me? Sai gani tayi suna kamewa da sarawa abinda ya bawa izzatu haushi.........


"Ku Kama min shege ku aje sai Naga ko uban waye yake daure mishi kugu..........


D P O ya dako Mata tsawa wadda Bata San ko ta wacece ba inda suke ta bawa Anwar hakuri suna sarawa abinda ya daurewa izzatu Kai Bata Sha mamaki ba sai da taji Anwar din na bada umarnin Kama ta ita da fulani kawai sai gani tayi suyo musu zummuwa


Aka garkama musu ankwa ana iza keyar su SHIGA motar Yan sandar........


"Kafin ku wuce dasu kusa yarinyar tazo ta janye motar can Kuma kar abada belin su sai in Ni Naga damar hakan Kuma don yanzu kar a kirani sai Nan da bayan wata uku don inaso uwar da Yar su koyi darasi. Ita Yar Ina so ta koyi tarbiya ita Kuma uwar don idan ta sake haifar wani dan Nan gaba ta San irin tarbiyar da zata bashi


Aka dakowa fulani tsawa ta fito jiki na rawa ta janye motar ta koma cikin motar Yan sanda akaja su aka wuce dasu inda izzatu ke kallon lamarin kamar wani mafarki ko Shirin film Wai ka dauko Dan sanda ya kama maka mutum Amma sai lamarin ya juye akanka waye wannan yaron da taga Yan sandan ma kamar tsoron shi sukeji? Da sauri ta jawo wayar ta ta Kira Kabir take fada mishi abinda ya faru inda isar su station din ko minti Sha biyar ba ayi ba Kabir mashi kashe arna ya iso don yayi belin iyalan nashi


Azaton shi ficen da yayi da sharar da kowa ya sanshi yasa yayi zaton da yazo ne za a bashi belin su izzatu Amma sai ya iske sabon Labari Wai babu batun beli sai Nan da wata uku


Yayi mamakin wannan yaro da izzatu ta fada mishi to waye? Da ya nemi sanin yaron da yayi wannan aikin D P O ya sanar dashi Anwar ne,


Mamaki ya Kama Kabir Jin Wai Anwar ne to Ina suka hadun da fulanin har sukayi wannan wautar? Da haka yayi sallama da caji ofis din ya nufi me bawa shugaban kasa shawara don ya zamo tsanin shi na ganin Mr President don ya San shi kadai ne zai saka Baki Anwar din ya fito mishi da iyalin shi don haka ya tunkari Alh uba Dan yaro Wanda ya sanar dashi abinda ya faru tsakanin yarshi da Anwar Wanda ya bada umarnin kulle su har sai bayan watannin uku shine yake son Isa wurin Mr President don asaka Baki Anwar ya hakura


Ai kuwa alh uba Dan yaro yayi mishi jagora har sukayi nasarar gani Mr President Kabir ya zayyane mishi komai inda yayi murmushi Yana cewa


"Yara ne su duka Kuma suna takama da zafin Kai kayi hakuri Kabir don Allah bansani ba Amma yanzu Nan zai zo Nan inji abinda yasa yayi hakan ya fada Yana dauko wayar shi ya latso lambar Anwar Kara biyu ya dauka inda uban yace yazo yanzu Yana son magana dashi ya amsa da gashi Nan zuwa ya aje wayar


Ya dubi Kabir "Kabir fatan ba zanyi maka shisshigi ba idan na tambaye ka bakayiwa Yar tamu miji ba? Ya amsa da baiyi Mata miji ba inda Mr President yace zaiso su hada Anwar da ita fulanin aure don wata Kil wannan tsamar tasu salon tasu soyayyar ne.


Wani Dadi da ya rufe Kabir tamkar ya shide don Yana ganin auren fulani zai zamo mishi auren jari da yadda zai dawo da kwangilolin shi da ake son yi mishi fin karfi don haka jiki na rawa ya amsa da Babu matsala duk yadda Mr President ke so hakan za ayi daga karshe ma yace ya bawa Anwar din auren fulanin idan an shirya azo ayi magana


Mr President yaji Dadi sosai dama Yana neman Yar da zai hada da Anwar tunda shi har yanzu cewa yake Wai baiga wadda tayi mishi ba don haka ya zabi yi mishi haka don baya son yaron nashi ya bude Tasha shiyasa yake son yi mishi aure


Mr President ya kawo kyautar girma ya bada yace akaiwa fulani ta siyi kayan kwalliya abind ya gigita Kabir mashi shi Kam zai iya cewa gara da akayi da haka Anwar yayi sallama ya shigo ya zube Yana gaishe da Kabir mashi don ya sanshi sosai Yana ganinshi agidan nasu sai dai har ga Allah Bai zaci shine uban yarinyar da tayi mishi gatsali ba. Mr President ya tambayeshi
"Su waye kasa aka kulle a station? Ya fada mishi duk yadda abin ya faro har zuwan izzatu da irin tozarcin da tayi mishi duk ya fada musu inda Mr President yayi murmushi


"To kanwar ka da uwarka kasa aka kulle don iyalan Kabir ne sai kaje maza kasa asake su............


Yazube gaban Kabir Yana bashi hakuri
"Kayi hakuri Abba ban sani ba ne ka gafarce Ni yanzu ne zansa akansu har gida.............
[5/19, 4:36 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 27*


*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








.........Abinn tausayi abin kuka da zubar hawaye ciwon dungo duk me tsoron Allah Dole yaji zuciyar shi ta raunan bisa Dole ta aje raino don Bata iyawa ciwo yaci karfinta


Makotan ta malam Ali da Jamila sun Mata karah matuka gaya inda malam Ali ke tur da Allah wadai da Kabir da duniyar dake Rudin shi
Jamila Bata San dungon nada wani da da har ya shahara ba kallon da take Mata Bata taba haihuwa ba Amma da dungon ta fada Mata tana da Da Yana zaune garin Abuja......


"Kuma ke Kika haifeshi dungo? Kwarai kuwa Jamila baya son dai rabata Koko Yana ganin ya wuce akalli fakiriya Irina ace nice na haifeshiba? Oho


"Amma gaskiya kiyi hakuri dungo indai ke Kika haife shi gaskiya Bai maida biki ba Kuma Bai zamo da abin alfahari ba tunda Bai damu da damuwar ki ba shi kuwa me yake nema cikin duniya da har take Rudin shi yake Miki hakan? Allah ya shirye shi yasa ya Gane Amma fa Yana da tarin kalubale gaban shi Wanda alhakin kadai zai iya tadeshi


Shi kuwa malam Ali da ya shigo yaga dungon cikin halin ciwo ya tausaya Mata
Ya dubeta
"Dungo kabiru kuwa yasan Baki da lafiya haka?
"Ya sani malam Ali tunda har gida na taka naje na sanar dashi
"Ya Zama Dole akirashi yanzu don Dole Dole ce. Ya a karbi wayar ta ya lalubo lambar shi ya kirashi
Wayar ta shiga tayi ta burari kamar ba zai daga ba sai da aka jera mishi Kira kusan bakwai kafin ya daga Kuma Yana gani ya kuma san me lambar Yana ganin dai idan ya dauka aiki zata Sara mishi shiyasa ya watsar da Kiran sai da yaga ba za a hakura da Kiran ba ne ya dauka akule


"Kabiru kana lafiya? Cewar malam Ali ya amsa da lafiya
"Dama don in sanar dakai tsohuwa fa ba lafiya har ana bukatar ganin ka da gaggawa in ma Babu wani uzuri me nauyi akanka to ko zuwa gobe ne sai ka Zo.
'to Babu matsala ya fada Yana aje wayar ba tare da yajira sallamar malam Ali ba
Washe gari kuwa sai gashi ya iso da safe inda ya iske dungon cikin halin ciwo ta rame ta Kare abin tausayi ga me raunannar zuciya ma sai ya koka Amma dayake akwai karfin hali sai kwarara kanta take.


Ya zube Yana gaishe ta Yana Mata sannu da jiki ta amsa tana tambayar shi iyali ya amsa da kowa lafiya


Malam Ali ya shigo suka gaisa inda yake mishi bayanin ciwon da ya ke damun tsohuwar tashi
Ya kadu ba kadan ba Jin Wai ciwon Koda ne matsalar ta


Ya sauke ajiyar zuciya
"Aikin gaskiya babba ne kudi ake kashewa ba kadan ba yayin dashen Koda Kuma Ni gaskiya yanzu bani da kudin da Zan iya biyan aikin. Sai dai ko a saurara zuwa gaba.......


"Haba kabiru irin wannan halin da take ciki kake maganar a saurara? Idan har baka da kudin biyan aikin sai kuje a ciri taka a dasa Mata don duk Wanda zaiyi hakan bayanka yake


"Nima fa ba lafiyar Nan gareni ba malam Ali a dai saurara din har zuwa gaba shi ciwo shi ke shiga da garaje Amma lafiya sai ahankali.


Malam Ali ya bishi da kallon takaici da hasara da dai haihuwar irin wannan yaron gara abarar dashi a zauna Babu haihuwa don haihuwar irinsu in ba damuwa da bakin ciki ba Babu abinda suke gadarwa


Kabir ya zura hannu acikin aljihun shi ya debo kudi dubu goma ya dire agabanta
"Gashi inna a rike wannan Zan dawo bayan kwana biyu inga yadda jikin ya zamo.........


"A a kabiru kaje da kudinka na gode Amma Zan so ka tsaya in FASA MAKA wani KWAI don kaji idan na cancanci irin wannan sakayyar a gareka.........


"Inna yanzu sauri nake don akwai wata kwangila da aka bani yau Zan soma ta ki aje duk wata magana gefe sai na dawo.....


Wayar shi ta dauki tsuwwa inda ya ga sunan alh uba Dan yaro ya dauka da sauri inda ake sanar dashi ana neman shi Kan kwangilar da zai Fara
Da sauri ya fice daga gidan Basuyi cikakkiyar sallama da uwar tashi ba bare Mal Ali


Hawaye ya zubowa malam Ali ya share Yana duban dungo
"Anya kuwa ke Kika haifi kabiru dungo? "Uhum Ni na haife shi Mal Ali...... To ki tuna indai har a Asibiti Kika haife shi sauya Miki shi akayi
Baba zaton Dan halak zaiyi abinda yayi Miki, mu da muka hada makotaka kawai dake muna Jin tausayin ki Amma ace da ya kasa Jin Kan uwar da ta wahalta maka? Dungo ta Mike cikin layi da jigatar ciwo ta hankado kar Kashin gadonta ta jawo wata katuwar mantimoti ta jawo wani kunshi kulle cikin tsumma ta kuma jawo wata tsohuwar takarda ta nufo malam Ali dake kallon ta da mamakin abinda take nema.


Ta zube kunshin da takardar agaban shi
"Malam Ali Bari yau in fada maka wata magana da ta zamo sirrina saboda Kai din ka zamo Dan uwana Kuma wannan sakon Ina so ka isar dashi ga kabiru don inaji ajikina ba zai dawo ya riske Ni da Rai ba don nasan zai wuce shekara Bai dawo ba.....................
[5/19, 4:36 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_




*Page 28*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








...........Malam Ali ya bita da kallo inda ta kwance kunshin tsumman sai ga kudi dumus Yan naira dubu dubu sabbi gal a daure da takardar banki malam Ali mamaki ya kashe shi daga zaune har dai yayi kokarin tankawa


"Kina da kudin Nan dungo Amma Kika zauna da ciwo har Kika Sha wahala haka? ........
"Ba kudi na bane malam Ali wannan kudin kabiru ne na abinda ya gada kuma shine KWAN da nake cewa dashi ya tsaya in fasa mishi ya ki don haka ga Amana Nan dukiyar maraya ce ka isar gareshi dukiyar da mahaifin shi ya mutu ya bar mishi ce ba Zan taba mishi abinshi ba saboda Nima an bani nawa Ina Kuma Ina tsoron taba mishi dukiyar shi don nasan hadarin dake tare da cin dukiyar maraya aka Kuma sanar dashi na yafe mishi Amma yayi sannu da wannan Rayuwar.


Ta Miko mishi tsohuwar takardar
"Wannan Kuma sadaukarwar da nayi mishi ce wadda shi ya kasa yi min irinta itace rubuce aciki ya karanta ko don ya Gane Ni naso shi tun kafin ya shigo duniya Amma shi duniyar ta rudeshi ya watsar da lamarina . Ta fada da hawaye na bin idonta


Malam Ali ya karbi kudin da takardar Yana dubanta
"Lallai uwa da Da sai Allah dungo kina aje da kudi kina fama da rainon yaran da ake biyanki ki cida kanki kina tanadawa Dan da yake can Yana more Rayuwar shi baya ma sakoki a lissafi. Zan cika Miki wannan alkawarin Zan Kuma kiyaye da ko duba takardar ba Zan Bari wani yayi ba bare ataba mishi kudin shi ke Kuma Allah ya Baki lafiya


Ta amsa da ameen
"Nayi maka izini ka duba takardar Nan malam Ali ko don kaima ka San abinda nayiwa kabiru Amma shi ya kasa yi min irin shi na yarda ka duba ai Ni da Kai mun Zama Daya


Malam Ali yaji Yana son duba takardar ko don ya fita daga zato
Ya bude takardar ya soma bin rubutun cikin ta Yana karantawa dogon rubutu ne har ya gama karance shi tsab inda hawaye ya kece mishi Banda Yana da karfin hali da Babu abinda zai Hana shi kokawa


Dungo ta dubeshi
"Ban San lamarin zai motsa zuciyar ka ba da bance ka karanta ba.........


"Dungo Anya kuwa kabiru na son gamawa lafiya? Anya kuwa Yana son DUNIYA da Rayuwa su barshi Zama cikin salama? Kinyi kokari Allah ya biyaki da ALJANNAH kin Kuma fita hakkin shi shine ya kasa fita naki


Ya Mike ya fice tun Bai durawa kabiru ashar ba. Haka ya wuni Yana mamakin yadda wannan yaro da abinda ke Rudin shi


Haka Jamila ta wuni zaryar dubata da girka Mata Dan abin tabawa inda da Rana ta girka Mata wake da Yar anta ta kawo Mata inda ta isketa ciwon ya taso abin sai da yasaka Jamila hawaye ta tallabota ta Dora kanta bisa cinyarta inda taga kamar tana Suma ta soma shafa Mata ruwa afuska har ta kawo numfashi ta farko cikin wani irin yanayi me kama da son wucewa kiyama inda Jamila ta tashi don ta taro mota su wuce Asibiti


Ta samo me napep da kyar saboda wahalar da napep din keyi ta iso gidan inda ta iske wani bakon Al amari me kama da mafarki


"Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Ina dungon ta shige ? Ta duba gidan kaf Amma Babu dungo Babu dalilin ta
Ta ci gaba da karade lungu da sako na gidan Amma maganar guda ce Babu dungo Babu dalilin ta


Malam Ali ya shigo shima Yana son duba dungon Amma ya riski lamarin me kama da almara Jamila kuka take tana karawa inda malam Ali ke tunanin ko dai rijiya dungo ta fada saboda bakin cikin abinda danta ke Mata? Don haka yayi maza ya bude rijiya Yana dubawa Amma Babu ita


Sai aka shiga nema da Jaje da duba asibitoci Amma Babu labarin dungo har dai daga karshe aka barwa Allah lamarin inda aka rufe gidan dungon Wanda hatta wayarta Bata dauka ba komai Yana Nan abinda ke Kara saka baba Ali zubar hawaye shine abinda ya dauki dungo shin wani ne ya dauketa Koko ita ta gudu da kanta ? Idan ita ta gudu ina ta tafi to? Idan Kuma wani ya dauketa meye hikimar daukarta?


Haka malam Ali ya rufe gidan ya na tunanin Ranar da zai iske Kabir ya isar mishi da sakon uwarshi..................
[5/21, 5:47 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_




*Page 29*


*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








......... Aguje fulani ta sheko akan titin tamkar zata tashi sama inda ta wuce wata hamshakiyar mota wadda ta rasa gano inda ta santa. Atake ta gano motar gayen Nan ce da yayi Mata Rashin mutunci


Ai kuwa da sauri tayo rubos ta dawo inda taga ya faka motar shi zai siyi tuffa da inubi
Ta fito tana sanye katon gilashin ido Wanda ya mamaye fiye da Rabin fuskar ta tana sanye da doguwar Riga ta yadin material lemon green anyi mishi adon fulawowi ja da Baki tayi kyau sosai ta yafa mayafi Dan karami Wanda Bai rufe Mata dogon goshinta ba Wanda iska ke kadawa tamkar kwallo


Kai tsaye ta tunkar me kayan fruit din tana takawa tamkar me tafiya akan kwai.
"Malam bani aybar Nan ta dari biyar ta fada tana Mika mishi gudar naira dubu
Ya karba Yana saka Mata aleda ta Ciro guda biyu tana barewa inda Anwar ke kallonta Yana mamakin yadda take mishi kallon da wa ka shigo garin Abuja? In har ya fahimta dai dai ma sai da yaga bakinta na motsi duk da baiji abinda take fada ba Amma yayi sa ar jiyo tsakin da tayi


Me fruit din ya Miko Mata cikon dari biyar dinta ta dubeshi ba tare da ta karba ba.
Ta Nuno Anwar dake zaune cikin mota Yana kallon ta
"Ka bawa wancan matsiyacin sadaka don nasan irinmu irinmu ya ke jira yayi maula ta fada dai dai da ta jefa mishi bawon ayabar afuskar shi


Daya daga cikin masu biye dashi don bashi kulawa wato body guard dinshi da ya kula da abinda tayiwa uban gidan su ya daga hannu zai sharara Mata Mari Amma da sauri Anwar ya dakatar dashi.


"Da dai ka barshi ya mareni ya Maro ajalin shi jaki da shi Yana biye da jaki Dan uwanshi,


Ta bude motar ta tashige ta figeta aguje ta hau titi inda wani hamshaki da abin ya faru akan idon shi yaji ya mutu da son fulani don shi Allah yayi shi da son mace me tsiwa tana burgeshi don haka da sauri ya shiga tashi motar ya rufa Mata baya inda suka bar Anwar Yana mamakin wannan yarinya daga karshe dai yayi murmushi ya siyi abinda ya kawoshi ya wuce gida


Sister mero tayi sallama gidan izzatu tana murmushi inda izzatu ta fito tana nunata da yatsa , "Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login