Showing 6001 words to 9000 words out of 36278 words

Chapter 3 - Zan Fasa Kwai Part 1 Complete by Hadiza Bara'u Gidan Iko.txt

ta.
Tayi murmushi kafin tace
"Ga maganin Nan ki ajewa abdukarim da Zuma ake Sha safe da maraice. Bata karba ba kamar yadda Bata nuna ta San da zaman hajiyar a wurin ba
Talai da taji zuwan hajiyar ta karaso tana gaishe ta


"Yauwa talai ga magani Nan ki ajewa abdukarim kice mishi sau biyu ake Sha safe da maraice Kuma da Zuma ake Sha
Talai ta karba tana fadin insha Allah ba Zan manta ba hajiya


Hajiyar ta Mike da Shirin ficewa inda talai tace
"Hajiya ki tsaya ko ruwa Kisha Mana bare ki huta.....
"Tunda gidan gyatumin tazo sai ki Bata ruwa gwana yar ka iya , cewar izzatu wadda ke wurgo musu harara


"Ni in nagane mutum munafiki ne me zai hada Ni dashi da munafurcin sa? Wallahi a yanzu dai dai nake da anuna min yatsa na karya tunda tafiyar Babu mutunci


Hajiya Mama ta Kada kanta "Allah ya shiryeki ya dawo dake hanya.....
"Ameen in dagaske kike duk da kema kina bukatar shiriyar tsohuwar banza me bibiyar Matan ya'yan ta......


Kalmar tsohuwar banza ta fado akunne AK dake shigowa gidan wani Abu ya naushi kahon zuciyar shi ya dubi hajiya ya Kuma dubi talai da ta soke Kai kasa Yana son ya gano wadda izzatu ke jifa da kalmar tsohuwar banza amma ya kasa ganowa


"Yanzu kike tafe hajiya? Yayi karfin halin tambaya
"Yanzu nazo har Zan wuce dama magani na kawo maka gashi Nan wurin talai tayi maka bayani.
Wannan saurin na hajiya shi ya alam ta mishi zagin tsohuwar banza da izzatu tayi ba da kowa take ba sai hajiya mama.


Ya riko hannun hajiyar Yana fadin "hajiya don Allah me ya faru kike sauri haka?
"Babu abinda ya faru ak Zan koma gida ne kawai ka tabbatar kayi amfani da maganin da na kawo maka....
"Ina fatan hajiya ba ke ko talai take Kira da tsohuwar banza ba?
"To wacece Ni da ba za a zageni ba ......


Kafin ma hajiya ta dire zancen ta ya Cabo izzatu ya soma wanketa da maruka
"Ayau Zan nuna Miki hajiya tafi karfin komai agareni Ina tausaya Miki Amma da yake jaka ce Baki San ana tausayin ki kije na sakek........


"Kar ka fara abdulkarim !
Hajiya ta katse shi da tsawa.
"Ka rabu da ita Kai dai kayi ta hakuri.....


"Ai dama da wannan manufar kikazo bakar munafuka annamimiya kin Kuma ci nasara don Ina me tabbatar Miki da yau wallahi aurena da abdulkarim ba zai Kuma kwana a duniya ba sai ya sakeni don in Kara gaba ko Zan haihu.


Ta dubi ak "Idan dai Kai din Dan halak ne cikin wannan tsohuwar banzar da wancen tsohon banzan na kushewa ka sakeni saki uku....


Kafin ma ta dire zancen ya furta Mata kalmar sakin
"Idan akwai sakin da ya wuce a lissafa shi fiye da uku to nayi Miki shi kije kije kije bana bukatar ganin bakar fuskar ki Arayuwa ta Ina fatan hakan zai tabbatar Miki Ni din Dan halak......


Ta dubeshi ta watsar
"Sai ka auro hajiya Mama kasaka dakin da Zan bari.......
Bata rufe Baki ba ya rufeta da duka sai da hajiya ta yi mishi tsawa kafin ya saurara Mata inda tafice aguje don ta tabbatar ba cikin hankalin shi yake ba


"Baka kyauta min ba abdulkarim me zaisa ka biye Mata ?
Zagi ai baya Kari don ta zageni sai menene?
Naso ka lallaba matar ka kuyi zaman ku har Allah ya warware maka lalurar ka don ba kowace mace bace zata hakura da Rashin haihuwa shi yasa kaga Nima nake lallabata


"Hajiya na gaji da halin matar Nan Kuma ba ayi wata mace da zata zageki ba in kyale ta ko Ruhin mu hade yake wallahi na gwammace in mutu da dai in Bari wani ya muzanta min ke bare izzatu dake home da barazana cikin rizgar arzina. Kuma Bari in fada Miki gaskiya hajiya da dai nayi nufin yin shiru har muddin Rayuwa akan matsalar Rashin haihuwa hajiya Ni lafiya ta kalau itace me matsalar ba Ni ba.............
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 9*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








........Hajiya Mama ta dubeshi azabure Jin Yana fadin ba shine me matsalar ba izzatu ce.
"Dama lafiyar ka kalau abdulkarim Amma kaja Baki ka tsuke? Lallai na sarawa hakurin ka ka Kuma yi halacci Amma anyi maka butulci.
"Tun tsawon wane lokaci ne kasan hakan?


"Izzatu ta matsa min da son lallai sai munyi gwaji idan ma magani zamu soma karba sai mu karba inda na Gane manufar ta ta son agano me matsala ce.
Munje Asibiti inda akayi gwajin sai dai akanta aka samu matsala don likitan ya fada min tayi shaye shayen magunguna na Hana daukar ciki Wanda suka haifar Mata da matsala a mahaifar ta inda ya bada magani don ta Sha
Munyi ganawar sirri ne da likitan Wanda ya ce ta bamu wuri zamu gana inda ta fito ta dawo mota Ni Kuma ya sanar Dani matata ba zata taba haihuwa ba saboda illar da maganin Hana daukar ciki yayi Mata a mahaifar
Ni Kuma nayi alkawarin Zama da ita da lalurar ta inda take min kallon nine me matsalar ba ita ba inda maganin da aka Bata ma Bata yi amfani da shi ba tace ita ta San lafiyar ta kalau Kuma tunda bataji nayi Mata wata magana ba to matsalar tawace Ni Kuma nayi nufin rufa wannan asirin don Ina tausayin ta gidan su ba komai bane bare Kuma duk ta wanke dangin da Rashin mutunci
Kuma ma Bata San mijin da zata aura ba Wanda kalubalen dake tare da ita yafi na Nan shiyasa Kika da Ina hakuri da ita Amma tunda har lamarin ya soma shafarki Dole ne inyiwa tufkar hanci dama kwanaki ta Mari talai to ko akan Marin zanyi Mata hukunci sai gashi ta jawo abinda na gudar Mata na Kuma San zata gano hakan da kanta musamman idan ta Kuma yin wani auren


Hajiya Mama ta sauke ajiyar zuciya
"Allah ya shirye ta yasa ta Gane ko Babu komai dagawa da izgili aikin shaidan ne duk yadda kake tausaya Mata ita Bata tausayin kanta....


"Hajiya na yarda ki nema min auren lubabatu Amma ki Fara Jin Ra ayin ta idan nayi Mata sai ayi magana kawai...


"To ko kaje da kanka kawai sai ku fahimci juna dama wancan zuwan shafa ce ta zanzame Ni akan ta kawo maka lubabatu don ita yarinyar cewa tayi kunya take ji Allah ya zaba abinda yake shine ALHERI ina fatan auren ku da lubabatu ya zamo silar farin ciki Kai da ita damu gaba Daya


"Abu kamar was karamar magana ta Zama babba inda lubabatu ta amsa tayi na am da batun tuni aka tsayar da Rana cikin wata biyu aka Sha biki amarya ta tare inda Kuma can izzatu ta soma fuskantar kalubalen gidan su don tuni ta Gane Bata da uwa agidan sai dai Matan uba Wanda take wuni bauta musu Babu gode bare bare godiya ga Rashin abinci bare Kuma dare yayi sauraye su cika Mata kunne da guda har ta kasa barci


Dawowar ta gida ko wata ba ayi ba taji shelar bikin AK da lubabatu Wanda acewar ta take barka da rabuwa da shi Amma sai da ta tsinci wata damuwa wadda ta rasa ko ta mecece
Damuwar da Bata da maraba da kishi Amma sai ta maze taci gaba da harkokinta har ta fita daga idda inda Kuma zawarawa sukayo Mata sallama inda tayi nufin yin aure ko don ta nunawa ak ita din ba irin matar dake bandaro bace Wai don an saketa.


Kayanta da ta baro gidan ak yasa aka kwaso Mata mota har gida ya kawo Mata inda ya Kuma Bata wata takarda yace taje ga likita Usman Wanda ya zamo musu family doctor Ada can wai zaiyi Mata bayani.....


"Yo bayanin me zaiyi min tunda dai Allah ya Raba Ni da wahalar auren ka Wanda Babu komai acikin shi sai asara? Yayi murmushi
"Kar kice haka don akwai wani Al amari da Usman din zai sanar dake Wanda zai haska Miki abinda ke cikin duhu


Da haka ya juyo abinshi ya barota da yi mishi rakiya da ido tana hasaso wani Abu me kama da nadama


Amma haka ta cije washe gari ta nufi Asibiti inda ta zarce office din doctor Usman.............
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*page 10*


*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






....... Doctor Usman ya tarbeta cikin mutunci don Bai zaci sun rabu da AK ba bayan sun gaisa yake Mata fatan alkhairi akan auren AK din
"Ashe eng ya angwa ce madam ? To Allah ya baku zaman hakuri da haka Mata ke goyawa mazajen su baya ai da ko Ni Nan na karo wata to Amma abin ne ba duka Kai ba sunan wata hula


Izzatu ta kwabe Baki kafin tace
"Shi dai Kam ai aikin banza ne yake Wai jefa agwagwa ruwa Wanda Bai ko Kai ga harara cikin duhu ba .


Doctor Usman yayi murmushi
"To madam na Gane karatun sai ayi ta hakuri dama shi zaman haka ya gada Amma da anyi hakuri sai komai ya zamo ba komai ba duniyar ma guda nawa ce?


"Likita bama tare fa da AK ahalin yanzu don Allah ya sani ba Zan jure zaman asara agidan shi ba shekaru goma Sha biyu Babu haihuwa haka Zan Kare saboda Allah? Yanzu ma zuwa nayi ka fasa min wancen KWAN na gwajin da kayi Mana don har yanzu Bai fuskance Ni da sakamakon gwajin ba Wanda Ni da kaina na gano matsala daga gareshi don yadda dangin shi ke son saka min ciwon Kai da nice da matsala da tuni sun mishi aure shine kawai na zabi ya sauwake min auren shi in Kara gaba don kasar Allah me yalwa ce in kaji matsatsi ka Kara gaba shine nake son sanin sakamakon don in har da bukatar Nima adora Ni Kam magani ko ya sakar min wata cutar sai na Tara kusa.
Doctor Usman ya zuba Mata ido Yana Mata kallon kinyi wauta.
Ya tambayeta
"Yanzu shi eng yasan Zaki zo Nan wuri na?
"Eh yasani ta bashi amsa Amma duk da haka sai da ya Kira wayar shi don sunyi dashi shima zai Taya shi rufe sirrin


Kara biyu ya daga bayan sun gaisa yake sanar dashi madam ce tazo da wata magana wadda muka Dade da haka Rami muka binne na Kuma yi maka alkawarin sai dai ta fito ta bakin ka ba dai Baki na ba.


"Kar ka damu Usman baba tare da ita a yanzu ta nemi saki ne gareni don tana ganin nine me matsala bayan ta gama cinye fuskar hajiya ta tas inda na sauwake Mata Kuma tunda tazo gareka na yarda ka fada Mata gaskiyar magana don ta Gane kalmar tausayin ta da nake yawan nanata Mata Amma Bata taba daga kalmar tayi Mata duban fahimta ba
So kar ka damu na yarda na amince ba ita ba duk wani ma me min kallon da take min ka sanar dashi na gode ya fada Yana tsinke wayar shi


Radam tajiyo maganar da AK yayi inda taji wani ruwa na bin jikinta inda ta Gane zufa ce don ko Usman Bai fada Mata ba ta gano bakin zaren.


Usman ya soma da yi Mata tambayoyi akan Shan kwayar Hana daukar ciki
Kai tsaye ta amsa mishi da eh kwarai ta yi su.


Inda shi Kuma ya Dora yi Mata bayani
"Wadan Nan magunguna da Kika Sha sune sukayiwa mahaifar ki muguwar illah wadda ta kassara ta har kikaji babu batun ciki ko haihuwa
Ranar da kukazo gwaji eng ya nemi sanin dalilin matsalar ku inda ta bangaren shi ba a samu matsala ba sai ta bangaren ki inda bincike ya gano illar da maganin yayi Miki
Dalilin da yasa na ce ki bamu wuri kenan don ban San ya me gidanki zai fahimci zancen ba inda nayi mishi bayanin komai Amma ga mamaki na sai Naga ya tausaya Miki har ma yace mu haka mu binne Ni da shi baya son kowa yaji shine dalilin da Bai fuskance ki da maganar ba ya dai karba Miki magunguna Wanda ya sanar Dani Wai kinki amfani dasu wannan shine dalilin da kikji Bai sanar dake komai ba
Amma banji Dadin abinda Kika sanar Dani ba gaskiya Kuma kin tafka kuskure ba karami ba


Ta dafe kanta hawaye na zuba inda take Jin wani Abu me kama da nadama duk da Bata taba yin nadamar wani Abu da tayi a Rayuwar ta ba sai yau da taji inda ake halacci ba tare da an duba Kai waye Wanda akewa halaccin ba


Bata cewa Usman komai ba ta taso ta taho Kai tsaye ta zarce gidan abdulkarim duk da ita Kanta Bata San me zai kaita gidan ba bare abinda zata yo.............
[5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 11*


*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








..........Ta shigo gidan cikin wani irin sanyin jiki da nadama tana tafe tana kunga kafa da son lalubo yadda zata dawo da bara bana
Ta shiga gidan inda ta iske Lubabatu na aikin matsa katafun ak Wanda ke kwance akan kujera tree seater lubabatu ta amsa sallamar izzatu tana yi Mata sannu da zuwa inda ak ya tashi zaune Yana kallon ta


Ta zube gaban shi tana sharar hawaye kafin ta kece da kuka tamkar wadda akayiwa mutuwa idan baka San ta ba sai ta baka tausayi


"Me yasa baka fada min halaccin da kake min ba AK? Nayi nadama fiye da yawan shekaru na a yau na gano tausayin da kake fadar kana min a lokacin da damata ta barni
Don Allah ka gafarce Ni abdulkarim yau Ni NA SHIGA UKU ina Zan sa kaina?
Tsam ya tashi ya bar Mata gidan don Yana ganin Rainin hankali ne ma ya tsaya sauraren ta inda ta gama kukanta ta fito inda lubabatu ke Bata hakuri da haka ta fice tana tafe tana zancen zuci babu abinda yafi damunta irin yadda taga lubabatu ta murje har cikin ta ya bayyana ita kuwa har yanzu ba ta samu nasarar da take fadin asarace zaman gidan shi


Mutumin da ta tsayar me abin hannun shi ne irin Yan bokon Nan Wanda duniya ke fadawa karya Wanda suke dadewa Basuyi aure ba saboda tsara Rayuwa da suke ai kuwa aka daura auren ta tare agidan shi


Babu abinda ya sauya daga halinta sai ma abinda yayi gaba na wulakanta ma aikata da son dagawa da fangima . daular dake gidan Kabir mashi ta zarce ta gidan ak don shima Dan kwangila ne me zaman kanshi don shima Yana da communication da fadar shugaban kasa wurin karbar kwangila


Hakan yasa ta ga ya Zama dole ta dakushe kaifin irin wancan garnakakin irin na gidan ak don ba zata yarda tarihi ya maimaita kanshi ba Dole ne ta samawa kanta mafita akan samun magaji agidan Kabir don haka ta lalubo lambar sister mero wata malamar Asibiti dake taimakon ta a lokacin da ta nemi maganin Hana daukar ciki


Kara biyu sister mero ta daga wayar bayan sun gaisa take tambayar tana Asibiti? Ta amsa Bata Asibiti yanzu sai dai ko zuwa gobe su hadu a asibitin kawai don azaton sister mero maganin da ta Saba karba ne zata karba da haka sukayi sallama ta aje wayar inda take tunanin idan Bata yi kokarin samun Wanda zai gaji dukiyar Kabir ba idan ya kauce ai ta tabbata me asara to ba ma zata yarda tarihi ya maimaita kanshi ba daga gidan Kabir ta gama matsawa wani wurin don ta hadu da matsalar dangin miji ba Kuma zata yarda Rashin haihuwa ya Kara kawo Mata wani tarnaki ba don haka ta Matsu garin ya waye ta iske mero don taji yadda zasu faro da yadda zasu Kare


Washe gari kuwa ta gillawa Kabir karyar cewa Bata da lafiya zata je Asibiti inda ya cika Mata Jakarta da kudi ta ja motar da Kabir ya siya Mata ta wuce Asibitin national hospital dake garin Abuja don ganawa da sister mero.....




Bari muji yadda wannan ganawa zata Kaya tsakanin izzatu da sister mero
[5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 13*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








...........Sister mero ta zakuda tamkar wadda kunama ta sakarwa harbi jin izzatu na ambato Mata milyon goma


"Banji me kikace ba izzatu
"Yadda kikaji hakan nake nufi milyon goma na ce Zan Baki idan har aikinki ya tafi daidai.....


"Wane irin aikine zanyi Miki ki bani wannan kudin? Don Allah karki yaudare Ni izzatu ko cikin mafarki ban taba ganin milyon goma ba ......
"Zaki gansu ido biyu harma su zamo naki idan kinyi nasarar kammala aikin ki Babu kuskure ko sabani........
"To naji wane irin aikine kike ta fada haka? Fada min don Allah tun zuciya ta Bata buga ba.


Izzatu ta dubeta tayi shiru kafin tace
"So nake mu hada wata kwangila dake kwangilar da zata danka Miki milyon goma ahannu.....


"Wace irin kwangila Ni ki fito amutum kiyi min magana ba alaye da kwane kwane ba.


"Da ko Diya nake so ki samo min acikin karbar haihuwar da kike Ni Kuma Zan sanar inada ciki Wanda Dan da Zaki kawo min shine Zan batar da hankalin mutane Kan cewa nice na haifa.........


"Dakata Allah idan na fahimce ki wata ta dauki cikin ta haife sai in dauko in kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login