Showing 9001 words to 12000 words out of 36278 words

Chapter 4 - Zan Fasa Kwai Part 1 Complete by Hadiza Bara'u Gidan Iko.txt

Miki?
"Hakan nake nufi.
"To tashi ki Kai kudin ki gaban da Kika San fin dubu zasu yi Miki Ni dai Kam albarka ban siyar ba.
"Haba wannan ma ai Rainin hankali ne da son ki wulakanta min aiki kija akore Ni
Haka kawai wata zatayi wahalar daukar ciki da rainon shi ta Kuma ketare hadarin na kuda ta haifa saboda son zuciya sai in sato in kawo Miki don Allah meye sunana idan nayi Miki hakan? Yaya zakiji idan ke akayiwa hakan? To mu rufe wannan maganar muyi wata


Izzatu ta dubeta asheke
"Dama fa ALHERI bai Faye karbar bakin mutum ba Amma ki sani kudin da kike kokarin yiwa arziki kullin da zai tarwatse har ki mutu ba Zaki taba mallakar su ba tunda Kuma ba Zaki iya ba zanje birnin gaba inda za ayi min
Tana gama fadin haka ta Suri Jakarta ta fice tamkar kububuwa inda sister mero ta bita da kallo inda Kuma take Jin wani lissafin me kama da na dokin Rano ya sauko Mata akan bukatunta na son ta mallaki mota da son ta siyi gida Amma ta Yaya zata mallaki gidan da motar alhalin albashin ta ma kafin ta karbe shi bukatu sun targada shi? Amma Kuma ta Yaya zata iya wannan aiki me matukar hadari akanta da aikinta? Sannan Kuma Yaya zatayi da hakki da alhakin wadda zata sibarewa Dan?


Ance mugun tunani shi ke abotakar shaidan sai sister mero ta ture wancen kalubalen ta hango bukatar ta inda tayi na am da aikin da zai mallaka Mata milyon goma wannan ai shine yiwa arziki kulli yaushe ne? Yaushe ne zata hada Kan wadan can kudin a wannan Nigeriar me jiya tafi yau gobe tafi jibi.


Don haka tana tashi aiki sai ta Kira wayar izzatu ta nemi kwatancen gidanta......


"Me ye na neman kwatancen gidana Kuma? In ma shawara Kika sauya kin makara don Ni magana guda nake bana maimaici.....
"Yi hakuri fada min inzo muyi magana
Izzatu taja tsaki kafin ta Bata kwatancen
Mero ta iso gidan Wanda ita da kanta ta San lallai Dole izzatu ke rudewa da son samun mafita


Ta dubeta awatse
"Meye Kuma na biyoni gida?
"Kiyi hakuri shawara nayi Naga Bai kamata ace kizo da bukatar ki wurina ba in watsa Miki kasa a ido haka na yarda sai mu tsara yadda abun zai kasance.


"Me yasa shi matsiyaci ko ya shiga tandun Mai yake fitowa kandas?
Yaushe ne mero Zaki Tara milyon goma?
Meye abin wuya acikin aikina?
Wannan magana tayiwa mero zafi Amma ta hadiye


"Ni dai yanzu muyi magana Yaya abin zai kasance?
"Zan sanar da Kabir nazo Asibiti ance inada ciki Zan dauki acting din masu ciki ke Kuma ba ki Nan da wata bakwai ko takwas kiyi kokarin kawo min abinda yasamu namiji ko mace duk Wanda ya samu Ina so


"To shikenan zanyi kokarin hakan in Sha Allah sai dai maganar kudin Zaki fara bani wani Abu ne kafin cikar aikin ?


"Kare ya cijeni ne mero da zan Baki kudi Baki gama aiki ba?
Ranar da duk Kika gama aikin ki Ina me tabbatar Miki da ko minti ba za a Kara ba Zan biya ki kudin ki cash


Da haka sukayi sallama da mero ta fice daga gidan inda Kuma a wannan Rana lamarin ya soma Wanda ya kunshi wani KWAI da fasuwar shi zai tafi da Ruhin Al umma da yawa.


Kabir ya dawo inda izzatu ke sanar dashi taje Asibiti an sanar da ita cikine da ita inda yayi murna tamkar ya mayar da ita cikin shi inda ita Kuma ta soma fito da salo kala kala inda Kuma izzatu ke baza izza inda Kuma akayi sa a Kabir Bai Faye bawa uwarshi muhimmanci ba inda izzatu ta Kara baza komar wulakanta uwar Kabir din wadda Allah ya zubawa tsananin hakuri da alkunya inda a yau ta nuko gari tundaga birnin Zaria ta iso gidan Dan nata don ta ga shi saboda shi dai yakan iya share shekara Bai lekota ba bare ya agaza Mata duk kudin shi da shaharar shi Bai bada Kai ga lamarin mahaifiyar shi ba inda Ni Kam gidan iko nace anyi asara kuwa indai haka ne...........
[5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 12*


*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








..........Ta faka motar me kololuwar daraja a farfajiyar Asibitin national hospital dake babban birnin tarayya Abuja inda ta fito fuskarta sanye da Derk spes ta soma takawa sannu ahankali tamkar me tausayin kasa hannunta sabe da jakar LV kafar ta sanye da takalmin LV mahadin jakar sai wani matsiyacin leshe Wanda ya lashe kudi ba kadan ba kamshin turaren ta ya bulale wurin ta kara daukar kanta yayin da ta ga wasu manyan Mata suna binta da kallo don gaskiyar magana shigarta Babu karya don ta samu Kabir mashi yadda take so Kuma ya rike Mata Kan macijin inda har take Jin kanta ame jinin arziki
Ta iso ofis din sister mero wadda aiki yayiwa sauki suka gaisa inda meron ke kallon ta cikin Sha awa


"Jiya kin Kira bana Asibiti naje gwarunfa duba wata abokiyar aikina da bataji Dadi ba Ina fatan dai ba kwayar pills din da Kika Saba karba Zaki karba don gaskiya lokaci yayi da ya kamata ace kin haihu ai kin Sha Miya haka Nan,


"Uhum mero ai ba Zan kuma yarda insha wani Abu yanzu da sunan Hana daukar ciki don nayi nadama ba kadan ba......


"Gara dai Kam don abin in ya kazanta Babu kyau. To yanzu me za ayi Miki?
Ta sauke ajiyar zuciya


"Mero na rabu da mijina sanadin Rashin haihuwa inda ayanzu nayi wani auren Wanda bana fatan sake gamuwa da wani tarnakin irin na gidan AK shine nake son samun mafita daga gareki.....
Mero ta tareta
"Kin samu matsala ne halan?
"Na samu matsala kuwa gagaruma wadda silar Shan maganin Hana daukar ciki ya haifar min har na samu bakin sakamakon ba Zan haihu ba shine nake gudun haduwa da irin waccan matsalar ta gidan AK shine nake so ki taimakeni da mafita.


Sister mero ta sauke ajiyar zuciya
"Gaskiya izzatu Babu wani taimakon da Zan iya yi Miki illa ki rungumi kaddara Kuma hakan ya zamo izna da Jan kunne gareki da masu irin abinda kikayi
Shi Allah ba ayi mishi Dole ana yin tsari Amma sai an fara haihuwa anga yadda haihuwar ta faro misali yinta Kai da Kai ko Kuma inke da mijinki zaku iya haifar me cutar sikila idan kunyi tsari ba laifi bane don ku hutar da yaran daga wahala Amma da yawan ku Kuna SHIGA hurumin Ubangiji da son kuci gyaran wahayi........


"Kinga mero ban baro gida don inzo kiyi min wa azi ba in wa azi nake sonji zanje ne in siyi kaset ko in bude Sunnah TV ban kumayo wanka don inzo ki shaki kamshin turarena ba, A a nayo kwalliya ne don ina so ta biyani kudin sabulu......


"To naji hajiya izzatu me kike so nayi Miki yanzu?
"Shine abinda ya kamata kiyi ba Wai ki saki baki kina neman shiga rigar malunta ba.
"Ina so ne na mallaki Da ko Diya ta yadda Zan fita daga matsalar bana haihuwa shine kawai nake so ki taimakeni


"Wannan me sauki ne inaga gidan marayu kawai ya kamata kije ki darzo duk kalar Wanda yayi Miki mace ko namiji sai kin zaba....


"Idan naje gidan marayu na dauko ai kowa yasan ba nawa bane Kuma bana son na gidan marayu gaskiya Kuma ai kowa zai kalle shi da sanin asalin sa,


"To yanzu ya kike so ayi ?
"Mijina na yanzu baisan bana haihuwa ba shiyasa nake so yin kauda bara da hankalin shi abinda nake so mero ke Nike so muyi magana ta fahimta don Zan biyaki kudi tundaga naira milyan daya zuwa goma akan bukatata idan har Zaki iya shiyasa ma na taho gareki don nasan aikin da Zan Baki akwai mutane fin dubu da in na Kai musu da gudu zasuyi min


Sister mero da taji yawan kudin da izzatu ta ambato zata Bata akan aikin da bataji komeye ba sai ta rude ta kidime har take Jin ita ko ma Arayuwar ta ta taba Kama milyon guda ahannun ta? Yau sai ace za ta samu goma me take jira?..............
[5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 14*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








..........Matar ta shigo da buhun bakco Wanda ta zubo kayan kadi dangin su kukar Miya daddawar kalwa da kubewa da karkashi ta shigo da sallama inda izzatu ke kwance akan kujera tree seater a Dole laulayi take
Ta amsawa matar aciki ta zauna tana kallon ta ganin kamar Bata da lafiya


"Babu lafiya ne halan?
"Eh wallahi dungo cikine ke ta bani wahala , ta fada tana gatsina fuska tamkar dai ace cikin ne na gaske
"Allah ya Raba lafiya ai haka laulayi yake Dole ne ake jinjinawa uwa akan wahalar samuwar danta Allah kayi Rahama ga iyayen mu ke kuma ya Raba ku lafiya ke da duk wata me dauke da Kaya irin naki. Ta amsa kamar ana Mata Dole.
Amma abin mamaki ko ruwa ba ayi karar bawa ladidi ba me amsa sunan dungo ita da gidan danta bare abincin tarba Amma dayake Allah ya zuba Mata ruwan hakuri Bata damu ba daga karshe ma izzatu Nan ta barta yashe afalo ita Kuma ta shige daki tabi gado Wai ita me ciki
Sai biyar na yamma me gidan ya shigo inda yayi arba da uwarshi yashe a falo ya zube suna gaisawa inda yake tambayar Wai lafiya tazo?


"Eh lafiya Amma ba Lau ba ruwan da akayi kwana uku da ya wuce bango na ya Fadi Allah ya kiyaye Babu abinda ya taba sai Yar akuyata itama ba sosai taji jiki ba don na barota ma tana yawon ta.


"To Allah ya kiyaye gaba zansa agyara shi ko zuwa Nan da wata me kamawa in Sha Allah.
"To Allah ya bada iko Kuna lafiya dai ko?
Nazo na samu izzatu ba lafiya inda take sanar Dani cikine Allah ya Raba lafiya
Ya amsa Yana murmushi don shi kanshi Yana muradin yaran
Kishin ruwa ya isheta har ta kauda alkunya ta tambaya ya dauko gorar ruwan ya Bata ya Kuma lariya ta kawo Mata abinci Amma tace ta koshi inda ta Miko mishi kayan kadin dai dai da fitowar izzatu tana shake hanci Wai wani wari wari take ji inda ya nuna Mata kayan da babar ta kawo inda ta toshe hanci
"Haba Ashe buhunki ne baba yake wannan doyin don Allah jeki dasu zasu sakani amai bana ma amfani da irin su
Wani Abu marar Dadi ya daki zuciyar dattijuwar Amma ta matse inda ta amsa da fadin ba komai Bata San basa amfani da su bane ta Mike da Shirin tahowa inda takewa izzatu fatan samun lafiya abin takaici Wai dubu biyu tayi kudin mota daga hamshakin Dan nata ta karba tayi godiya ta taho tanemo tashar mota kafin ta jirayi cikar motar da zata zo birnin zazzau inda sai dare sosai kafin ta iso gidan nata Wanda ta gada daga marigayin mijinta uban Kabir Wanda ta haifa shi kadai saboda yawan wabin da tayi sai da kyar ta sameshi inda ta zamo jajirtacciya wurin neman kwabo inda ayanzu ma hada rainon yara takeyi Wanda duk wata uwayen yaran Kan biyata dubu biyar inda take rainon yaran idan iyaye su zasu fita aiki su kawo Mata idan ta dawo Kuma su karbi abinsu yara biyar take raino inda suke biyanta dubu ashirin da biyar kenan shiyasa Kabir Bai damu da ya Bata kulawa ba Wai ai tana samun kudi sai Kuma akayi sa a ita din ba me son roko bace bare matsawa shiyasa idan taga ya Sharari lokaci Bai zo ba sai ita tazo ta ganshi ta koma
Haka Kuma katangar da ta sanar dashi ta Fadi yace zai sa agyara Bai gyara ba sai dai itace ta siyi zana aka killaceta


Izzatu ta bude fejin salo da firirita Wai ita adole ga me ciki inda shi Kuma yake biye Mata da tace uhum zai ce meye ko me take so? Tabara iri iri inda Kuma Yan aikinta suka SHIGA UKU da yawan aiki ta yi ta tofar da yawu da Aman karya suna faman wankewa da gogewa
Inda Kuma kadan zasu kuskure tayi ta Danna musu ashariya sai dai su kauda Kai suyi hakuri


Wata biyar dai dai da yin maganar su ta kwangila da sister mero lubabatu matar eng AK ta tashi da nakudar haihuwa ta biyu don wancan da ta haifa Bai zo da Rai ba kasancewar ta Sha wahala shiyasa wannan karon aka kawota asibitin national inda Kuma cikin sa a sister mero ce ke night duty inda tayi hikimar sakawa lubabatu ruwan nakuda dama tayi hakan don cimma kudirinta na son cika burinta ta kumayi sa a lubabatu tafita hayyacinta har Bata San lokacin da ta haife abinda ke cikinta ba...........
[5/16, 6:07 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


*Page 15*


*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








..........Wani ikon Allah da ya Saukar shine lubabatu ta haifo Yan biyu duk Mata batare da ta San tayi hakan inda Kuma sister mero take kallon lamarin tamkar cikin shirin film ko wani shiryayyen Abu inda kuma tayi maza ta aiwatar da wani shiri tamkar walkiya ko ibilishiya ta shirya yarinyar guda ta turo ta zuwa dakin hutu inda ta fito take sanar da wadanda suka kawo lubabatun ta haihu wato hajiya Mama da tsohuwa talai don AK baya gari inda Kuma mero ta sada su hajiya Mama da talai dakin da lubabatu ke ta sharar bacci saboda allurar bacci da ta zurkuda Mata da sauri mero ta zagaya bayan tagar dakin da lubabatu ta haihu ta Suri Jakarta wadda aciki ta saka jinjirar ta fice da sauri tana duba yarinyar dake tsotsar yatsun hannunta
Ta jawo wayar ta ta Kira izzatu ta daga tana fadin ya akayi Kuma kike isata da Kiran waya...


"Aikina Yana dab da cika ga kyakkyawar yarinya ahannu na ya za ayi kenan?.....


"Ki Bari don Allah? Taho kawai gani Nan Zan bude Miki gida tunda Kabir na can Yana bacci Kinga sai mu kashe mu binne ba tare da ya sani ba Kinga asiri rufe kenan. To fito ki bude min don gani Nan daf da gidan don Ina so in koma Bakin aikina..


Duk dare ne kusan Sha Daya da mintuna haka izzatu ta taso tazo ta bude gate din inda napep ya sauke mero inda tace ya jira ya mayar da ita Asibiti


Suka shigo da izzatu inda mero ta fito da yarinyar daga katuwar Jakarta ta mikawa izzatu dai dai da ta tsanyara kuka inda izzatu ta doka daki Kabir tana Kiran sunan shi ya taso Jin kukan jaririya ya fito da sauri inda yayi arba da sister mero cikin kayan aikinta


"Kar dai Ina can Ina bacci har akayi haihuwar ban sani ba?,
"Ai dayake ma ta samu nakuda me sauki shiyasa ta kirani na garzayo. Ya karbi yarinyar Yana kallonta kyawu Kam tamkar Hindu inda atake yayi Mata huduba Aisha humaira ya mikata ga mero Yana kallon izzatu Yana Mata barka.


Mero ta Mike da Shirin komawa Asibiti inda Kabir ya debo kudi masu dama ya Bata tafito tana godiya ta shige napep ta koma Asibiti inda ta iske dakin da lubabatu take cike da Yan uwa suna ta yaba kyawun Yar inda mero ke musu kallon na Sha da ku. Talai ita tace zata kwana wurin uwar dakinta lubabatu don lubabatu Kam ta dauketa tamkar uwa ga kyautatawa da take Mata Kai kaf din ma aikatan lubabatu na kyautata musu shiyasa ma talai tace ita zata kwana hajiya Mama ta tafi gida ta huta
Haka hajiyar ta taho kafin asubahi lubabatu ta farko inda mero ta tabbatar Babu matsala ta sallame su itama ta harlanta aiki ga Wanda zai canjeta ta taho gida tana fatan tayi baccinta zuwa Sha biyun Rana taje gidan izzatu ta karbo kudinta


Sai karfe biyu na Rana ta nufi gidan izzatu inda Koda izzatu ta ganta sai ta hade fuska tana masifa
"Me Kuma kikazo yi mero ? In don kudin kine ai Kya Bari ayi suna ko?......
"Bamuyi haka da ke ba indai ba Saba min alkawarin Zakiyi ba nayi cinikin mota kuma yau nace Zan bada don haka dauko min hakki na in wuce...
"Bafa Zan Baki ko sisi yanzu ba wallahi sai bayan suna don haka karki tada min hankali, mero ta dubeta cikin sikewa da son ta nuna Mata halin Dan Adam na butulci


"Bamuyi haka dake ba indai ba Saba min alkawari Zakiyi ba........
"Kije dai bayan suna ki zo ki karbi kudin ki don ai kin San nafi karfin kudin ki matsalar matsiyaci kenan Bai iya samun wuri ba....


"Karki Kuma zagina akan hakki na, na Baki kwana Sha hudu ma ba bakwai ba Zan dawo karbar kudina ina me tabbatar Miki idan nadawo wata magana me kamar irin haka ta sake faruwa tsakanina dake na rantse Miki da Allah ZAN FASA KWAI !


Mero tafice afusace inda izzatu ta bita da kallo tana tunanin lallai mero zata zamo Mata katon kalubale kuwa in ba sakin hannun juna suka yi ba




To Bari mugani sati biyu ya wuce me zai faru?....................
[5/16, 6:07 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login