Showing 18001 words to 21000 words out of 36278 words
Chapter 7 - Zan Fasa Kwai Part 1 Complete by Hadiza Bara'u Gidan Iko.txt
garin Abuja sai dai zaman mota ya jigatata don haka da kyar da gano gidan Kabir inda take ta shessheka numfashi na neman daukewa tamkar me ciwon asma
Fulani ta tarbota don wani ikon Allah jinin su ya hadu
Ta rungumota tana fadin
"Ya Kaka Baki da lafiya ne?
Da kyar dungo take magana
"Bani da lafiya Aisha ina mutanen gidan ne?
Izzatu ta fito ta aunowa fulani harara don Bata so take shiga sabgar tsohuwar
"Tashi ki bace min da gani kilbabbiya, ta fada tana hararen humairar
Ta tashi ta nufi dakin ta tana tausayin kakarta
Izzatu ta dubeta tana dafe da gefen cikinta alamar ciwo yake Mata
"Baki da lafiya ne dungo?
"Wallahi kuwa izzatu jiki yaki Dadi Allah yasa Kabir Yana gari ? Yana Nan sai dai inma kudi Kika zo nema bashi dasu don kwanan Nan lamarin sai godiyar Allah
"To Allah ya rufa asiri dama cikon kudine so yayi min don Zan siyar da Yan awakina in nemi magani ........
"Ai da kin bugo waya ba ki wahalar da kanki ba yanzu irin haka ke Dadi kinzo kin Bata kudinki Kuma ba lallai ki samu kudin ba
Sai izzatu ta SHIGA sababi tana fada Wai ba a haka sanar da mutum ake in za a zo wurin shi ba Wai azo ayi mishi tashi na kamaka ba in turawa ne in baka sanar dasu zuwanka ba ko ruwa ba zasu baka ba
Haka Kabir ya dawo ya samu tsohuwar shi cikin halin ciwo Kuma ko ruwa ba a Bata ba bare abinci. Kafin ma ta sanar dashi matsalar ta izzatu ta rigata inda ta Dora da Wai Babu kudi yanzu
Shima sai yabi bayan matar tashi akan dai Babu kudin don ya Gane izzatu batayi na am da bayar da kudin ba
Dungo tayi murmushi "Babu komai Kabir ko aro ne anemo min ciwona Yana bukatar gaggawa.......
"Gaggawa Kuma ? Yo dungo ko mutuwa ta shiga gidan da Babu ai dolenta ta fita
Kabir ya dubi izzatu Yana mikewa inda ya nufi daki ta bishi
"Gaskiya baba Bata da lafiya izzatu Bata taba tambayar kudi wurina ba So Zan Bata duk abinda take bukata........
"To kudin da zaka bani na bikin Barth day din fulani fa ? Shiyasa kaji tun farko na ce baka da kudi ka Bata kudin mota kawai ta koma gida zuwa wata me kamawa idan sun samu sai abata don hidimar zatayi maka yawa
Haka kuwa akayi ya dawo ya sanar da ita ya buga waya ko rancen ya samu Amma abin ya gagara da haka ya aje Mata dubu biyar yayi Mata fatan samun lafiya
Ta Dade zaune tana Kore sauro inda kuma har yanzu ba a Bata ruwa ba bare abinci
Fulani ta fito ta dauko Mata robar madarar laban da abinci Wanda ta zubo Mata naman kaji zuku zuku ta dire gabanta
"Ya Kaka Baki Jin yunwa kikayi shiru Baki Sha ko ruwa ba?
Ta karbi madarar ta soma Sha kafin ta soma cin Naman inda wani ikon Allah sai taji kamar ana rage Mata ciwon Ni Kam gidan iko nace ko ciwo Yana son abinci me kyau
Adakin humaira ta kwana cikin gidan sauro inda dungo ke ta saka Mata albarka washe gari ta hado kayan ta fulani ta kawo ta Tasha inda izzatu ke taksicin wannan kawa zuci na fulani ga jemammiyar tsohuwar
Ai kuwa da ta dawo daga Kai dungo Tasha sai da taja kunnen ta kamar ta cire shi tana fadin Wai Babu ruwanta da tsohuwar
"Haba momy kakata ce Kuma ace Babu ruwana da ita? ......
Ta gwabje Mata Baki
"Baki hada komai da ita ba hanya ko ta rafi nono ko na gora meye hadan kifi da kaska?
Fulani ta shige daki tana gunin Jan kunnen ta da akayi inda Kuma sister mero ta shigo gidan da sallamar ta me kwari.
Arude izzatu ke kallon ta
"Me ya kawoki gidan Nan mero? Me kikazo yi ?
"Haba irin wannan tambayoyi tamkar na SHIGA kabari ko Dan ruwa ba za a bani ba ? Bakonka Annabin ka fa......
"Baki cikin layin bakon ka Annabin ka donke kallon tauraruwa me wutsiya nake Miki don haka Fadi abinda ya kawo ki kiyi ki bar min gidana..........
"Kai hajjaju makkatul mukarramina wannan dogon sharhin tamkar Baki San daga ina nafito ba?
To dama matsalar kudi ce ta kamanni shine na tuna dake don haka milyon biyu kurum nake so ba yawa.......
"Agidan ubanwa za a samo milyon biyun? Wace irin jaka ce ke ne? Kina bina bashi ne Zaki wanko tsantsaman jikinki kice na Baki kudi?
"Karki Kuma zagin ubana izzatu arziki ya hadamu ba tsiya ba ke komai sai an biyo Miki ta bayan gida ake daidaita wa dake? Meye don nace ki bani milyon biyu Ina ce farin cikin da na Samar Miki ya zarta milyon dari? To bani in wuce don bana son ta kaimu ga cacar Baki in kuwa ba haka ba wallahi yanzu ne Zan fasa kwai .........
"Allah ya tsine Miki idan Baki fasa dangin kaji da tsuntsaye ba. Bari in gaya Miki mero na fiki tashanci da iya lalata ban San haka kike ba wallahi da ban yarda na hada hanya dake ba Amma ki sani duk Ranar da Kika kaini karshe na rantse Miki da Allah sai dai ki tsinci kanki kushewa Zan Baki milyon biyu Amma ki kaddara daga kanta ko a mafarki kar ki yarda kice kin sanni don sani na zai zo Miki da matsala..........
"To naji hajiya izzatu dauko min in wuce don sauri nake.
Izztu ta rubuto mata cek ta Bata ta karba tana godiya inda izzatu ke Mata kashedi da idonta
Sister mero ta Mike tana fadin Wai sai gani na biyu.......
"To a gani na biyun ki tabbatar kin taho da likkafanin ki don Zaki zo inda Zaki gama yawo. Mero ta kyalkyale da dariya ta fice daga gidan inda izzatu tayi shiru tana tunanin mero da irin salon da take nufin kawo Mata
Itama sai tayi murmushi"mero kenan muje zuwa Ni dake za agane waye gaba.........
[5/17, 10:10 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_
*Page 24*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
........Bai Kara tunawa da batun wata halitta Wai ita dungo ba asalima tun da ta tafi ya share da lamarin ta inda aka kashe kudi sosai wurin yiwa fulani bikin murnar cikar ta Sha bakwai da haihuwa akayi taro na manyan Yara ta Kuma samu kyaututtuka daga kawayen ta na karatu
Kana biyu da yin bikin yake sanar da izzatu anyi mishi alkawarin bashi kwangilar gyaran wutar lantarki wadda zai samu manyan kudin na tashin zance inda ta cika da murna don duniyar su zata Kara haskawa
Sai dai me ? Maimakon yaji Kiran daga fadar me bawa shugaban kasa shawara Kan abinda ya shafi aikin. Sai ji yayi Wai har anyi kwangilar an gama har ma an Dora da wasu manya har uku Kuma Babu wadda ta fito da sunan shi sai sunan eng AK Wanda a yanzu shike Kan gaba na karbar kwangila daga gwamnatin tarayya abinda ya girguza Kabir mashi har ya gurfana agaban me bawa shugaban kasa shawara
"Ranka ya Dade na tuba don Allah a gafarce Ni idan har da kuskure a cikin aikina to asanar Dani Zan gyara ban San abinda nayi ba aka mayar Dani gefe anyi mini alkawarin bani kwangilar gyaran wutar lantarki Amma sai ji nayi har anyi ta angama menene laifina?
Alh uba Dan yaro ya dubeshi
"Agaskiya Kabir sunyi bincike ne akanka inda suka gano kana bada rata da yawa har aikin ya zamo Babu nagarta inda sukace aikin eng AK yafi naka nesa ba kusa ba shiyasa suka juya akalar Kan shi Amma idan zaka gyara ba damuwa bace sai nayi maka request wata ta gaba abaka don nasan wata Kil waccan akasi aka samu
Ya zube Yana godiya da alkawarin zai gyara da haka ya taso ya taho Yana mamakin yadda eng AK ya samu SHIGA fiye dashi matukar kuwa hakan yake nufi to zai ware kwanji sai ya dawo da bara bana Akan harkar shi da ake son yi mishi fin karfi
Izzatu ma tamkar zata fasa kuka Amma tace itama ba zata taba yarda wani ak can da tagama rufe babin shi ya ce zai Kuma sake shiga Rayuwar ta da mijinta ba da sakel wallahi
Aguje fulani take gudu akan hanyar don dama haka take Bata tafiya sannu sai dai tamkar zata tashi sama
Cikin sa a ta shawo kwana daidai da wata katuwar mota itama ta shawo kwana Kuma hanyar Dole sai daya ya kauce kafin dayan ya samu zarafin wucewa
Su duka suka sunno hancinan motocin su alokaci daya sukayi kallon kuda Atare inda atake ta ganeshi gayen Nan ne da yayi Mata Rashin mutunci har sau biyu dama neman shi take sai gashi sun Kuma haduwa inda zai Gane itama Yar zafin Kai ce Tama fi shi zafin Kai don haka sai ta kashe motar Taki fitowa shima ya kalle ta Yana mamakin kaddarar dake hadosu
Suka Kuma yin kallon kuda inda yaga har da harara take Aiko mishi inda yayi murmushi Wanda ya kular da ita shi yaki yin baya itama Taki yin baya kowa na takama da zafin kanshi sai akayi sa a itace akan hanya shi in za a kwana bashi da damuwa ta Gane hakan ne ganin yadda ya tada kida amotar ya bawa banza ajiyarta inda ita Kuma aka fara Kiran wayarta don tana Kan hanyar zuwa bikin kawar tane Kuma itace babbar kawa shiyasa ma ta fito aguje gashi Kuma akwai tazarar da zata iya takawa kasa ba don haka kawai sai ta fito don ganin ya Dora kanshi akan sitiyarin motar Yana lumshe ido tamkar me bacci
Kawai sai ji yayi gilas din motar tashi yayi Kara tatssss
Ya dago da sauri inda yaga ta sauke katon dutsin akan gilas din motar shi wadda ita da kanta ta Gane tafi karfin yaro shiyasa ma ta ke ganin Yana ji da kanshi
Abin ya Bata mishi Rai matuka gaya har Bai San lokacin da ya sauke Mata Marika biyu afuska ba abinda ya haddasa Mata daukewar gani na wucin gadi
Lokacin da ta dawo duniyar mutane ne ta soma wanke shi da manyan asharai kafin ta fasa kuka ta Kira wayar izzatu take fada Mata ga Wanda ke Mata wulakancin Nan ya mareta har idonta ya fice........
"Kina Ina yanzu? Ta kwatanta Mata aikuwa izzatu ta Figo mayafi ta fice tamkar zata tashi sama inda ta Miki hanya sai gata agaban su fulani nata rera kuka
Aguje izzatu ta fito ta soma wanka mishi Mari hagu da dama tanayi tana antaka mishi ashariya amma da yake namijin duniya ne Bai ko motsa ba Yana kallon yadda izzatu ke sauke mishi lodin zagi kala kala................
[5/19, 7:15 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_
*Page 26*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
........."Babu komai Anwar Rashin sani ne Kuma itama ai tayi maka Rashin mutunci Zan Kuma ja kunnen ta kaima kayi hakuri. Atake Anwar ya Kira wayar yasa aka saki su fulani inda Kabir yayiwa Mr President sallama ya wuce station ya kwaso su izzatu Wanda sukayi firgai firgai inda fulani ke ta kuka izzatu na Bata hakuri
"Wallahi momy ba Zan taba kyale gayen can ba yayi min wulakanci Kuma yasa an kulle ki saboda Rashin mutunci ? Ko Zan kyale shi Akan abinda yayi min wallahi ba Zan kyale shi Akan kulleki da yayi cikin zarnin fitsari ba ko waye ubanshi kuwa duk Ranar da muka sake haduwa dashi Wallahi sai ya Raina kanshi da haka suka iso gida ta wuce ban daki don tayi wanka acewar ta duk zaurin fitsari take
Shigar ta bandaki izzatu ke tambayar Kabir waye wannan yaron da yasa akayi musu wulakanci? "Anwar ne Dan gidan Mr President.......
"Koda naji gadarar yaron ta nuna ya Taki wani Abu Amma Yana da hakuri gaskiya don inda yace sai yabi kadin ashar din da nayi ta banka mishi Babu shakka da fitowar mu ba yanzu ba.........
"Ai albishirin ki ma kiji wani Abu da yasa nace gara da akayi Wai Mr President din ke nemawa Anwar din auren fulani Wai salon soyayyar sune haka...........
Izzatu ta rangado guda me karfi inda take Jin tafi Kabir farin ciki yau ace yarta na auren Dan gidan shugaban kasa ita me yafi wannan farin ciki?
"Kace gara da akayi Kabir ko ba komai lamarin zai zamo Mana tamkar jari don Dole ma abaka kwangila tunda ka zamo surukin masu Abu da kansu .......
"Ashe dai kin Gane Nima hakan nagani Zan dawo da martabata da ake son yi min fin karfi...
"To Amma wani hanzarin ba gudu ba ta Yaya kake ganin yuwar lamarin alhalin fulani ta kullaci yaron ba kadan ba Kuma shima Ni Banga wani Abu da zai nuna zasuyiwa juna uzuri ba?
Wannan me sauki ne idan akayi auren can zasu shirya kansu shima namiji yayi biyayya bare ita mace? Ai Dole ne ma tayi biyayya ke dai kar ki sanar da ita ayanzu sai lamarin ya tunkaro sai ta San komai da haka suka aje magana
Dungo baiwar Allah ciwo yaki Jin magani duk Yan dabarunta na Shan magani Amma ciwo yaki inda ta siyar da Yan awakinta ta hada kudin da Basu Kai ko Rabin abinda ake nema ba ta nufi likitan ta Yi mishi bayani ya tausaya Mata matuka inda tace ya ajiye kudin hannunshi idan ta Nemo cikon zata zo ayi Mata aikin
Ya karbi kudin sukayi rubutu ya Kuma nemi address dinta ta kawo shi har gidanta inda yake ganin kokarin ta na son ta taimaki kanta da kaucewa roko da tumasanci sai yake Jin ko da cikon ne ma zaiyi Mata in ta kama don haka sai ya saurareta
Zaman gidan yayiwa ummita yawa inda ta nemi shiga makarantar koyon computer Kuma eng ya Goya Mata baya ta shiga inda take Jin ta rage kadaici
Sai ya zamo ta fannin shaharar aikin kwangila ya zarta Kabir mashi kashe arna don gudar da akace za a rokar mishi ma ba a bashi ba eng AK aka bawa ita , idan har baiyi kuskure ba kusan wata goma Sha daya kenan Rabon da ace mishi ga aikin kwangila don haka yake ganin eng ne yayi mishi shigar sauri abinda kuwa ba zai yarda dashi kenan ba
Izzatu da take ta durawa ak din ashar tace ya zamo Dole yaje ya samu ak ya yayi gargadin shi Akan ya Daina karbar kwangila sai dai ya Bari idan anyi a Yan mishi wani Abu
Ai kuwa ya sallamawa eng Wanda ya fito ya tarbeshi suka gaisa inda ya fito mishi ta hanyar siyasa
"Eng nazo ne inji adadin kwangilar da akace za a bani Amma shiru har yanzu sai ji nayi Wai an baka kayi ta harma ka Dora da wasu shine abin ya bani mamaki.
"Kwarai kuwa me gida nayi ta har ma na dora da wasu guda biyu Wanda nakeyi yanzu. Amma banji Dadin tada maka alkawari da akayi ba. Sai dai Zan baka shawara ka nemi dalili idan na kuskure ne sai agyara shi don gaba don yanzu haka akarshen shekara za a gabatar da wasu manyan kwangilolin har biyar kaga idan ka nuna bakaji dadin alkawarin da aka tada maka ba to Ina me tabbatar maka da acikin wadan can biyar din za a baka wasu inaga hakan ya dace kayi.
"Kwarai kuwa eng ka kawo shawara na Kuma gode da haka sukayi sallama ya dawo gida Yana fadawa izzatu yadda sukayi........
"Rainin hankali ne kawai yake son shigo maka dashi ta Yaya zakaja kunnen gwamnati indai ba salon Dan sauran girmanka ya zubeba?
Idan har irin wannan ta Kuma faruwa nagane shi ke son talauta ka to Zan sako gambo mafiyas atafiyar don in ba koya mishi hankali akayi ba to munaji muna gani sai ruwa ma ya gagare mu
Kabir yayi na am da hakan inda suka ci gaba da zaman jiran saurare Amma shiru tamkar bawa ya leka garin su..............
[5/19, 7:15 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_
*page 25*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
.........."Kai Nan har Dan iska ne Kai da zaka saka shimfideden hannunka ka marar min yariya? Dama ina jiranka akan wulakancin da kayi Mata har sau uku saboda Kai Dan iska ne? Waye ubanka a duk fadin Nigeria? To zaka Gane karyar iskanci kake don sai ka Kare Rayuwar ka agidan maza. Kasan ko wacece ita da irin gatan dake gareta ? To bude kunnen ka kaji da ranta ya baci gara gara amaimsita yakin badar da tabuka ita kadai ce gayya zakuma ka Gane gatanta ya zarce ayi Mata ko harara bare kallon banza
Izzatu tayi ta sababi da masifa tana wanke shi soso da sabulu Amma ko daga Kai baiyi ba bare ya tanka inda izzatu ta fiddo wayar ta ta Kira D P O na yankin ta sanar dashi tana son aturo Mata motar Yan sanda biyu suzo su wuce Mata da wani Dan iska da take son abatar dashi gaba daya
Ta gama wayar tana mishi kallon banza inda ta dubi motar shi ta dora da sababi
"Dan iska da Kai ka aro mota ka shigo gari shine zaka nemi shiga hurumin yarinyata shege da ganinka ma kayi Kama da masu wankin mota wata Kil wanki aka kawo maka shine ka shigo gari don kayi bagu da barazana da motar mutane don da ganinka matsiyacine Kai zaka Gane ka tabo abinda yafi karfin ka har iyayen ka sai an kulle min su tunda Basu iya tarbiya ba......
Baice Mata komai ba har tagama cinye fuskar