Showing 15001 words to 18000 words out of 36278 words
Chapter 6 - Zan Fasa Kwai Part 1 Complete by Hadiza Bara'u Gidan Iko.txt
tana mishi uzuri sai ta bar abin ya wuce ko aranta Bata aje shi ba taci gaba da rainon yaranta Wanda ke debe Mata kewa fiye da zato inda makocinta malam Ali ya shigo ya duba jikinta inda yake tambayar ta Kabir ya Zo kuwa? Tayi murmushi "Bai zo ba malam Ali , to Allah ya Kara lafiya da haka ya fice Yana mamakin wannan yaro da duniya ke rudu duk shaharar shi Amma abin haushi ya yasar da uwar shi sai tayi raino ta ke ciyar da kanta Amma shi Yana can cikin katon gida daga shi sai matar shi suke hutawa Anya kuwa Bai dauko hanyar lalacewa ba?
Uwafa? Uwar ma irin dungo wadda yasan yadda ta wahalta mishi har ya tako matsayin da ya tako? Babu wata riba ko nasara da ake samu ba ta silar uwaye ba koma an sameta to zata sulale saboda Babu albarkar iyayen sai yayi mishi adduar Allah ya shirye shi ya kuma shiryi Al ummar musulmi Baki Daya..........
[5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_
*Page 20*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
Yara suka taso cikin kulawa inda ummita iyaye da Yan uwan uwa da na uba ke nuna Mata so da kauna da Kuma kokarin dorata bisa bigiren tarbiya me kyau inda tayi matukar sabo da ubanta eng AK Wanda ko yaushe tana hannun shi Yana Mata wasa har tayi sabo me yawa dashi don in har Yana gida to Bata Rabuwa da shi tafi like mishi fiye da Uwar ta shima Kuma Yana janta jiki don wani irin so yake Mata jinta yake tamkar Ruhin shi lokacin da ta Kara wayo ma dakin shi take kwana in kaga sun Rabu to baya gari shima sai da hikima in ko ta na farke ya tafi ya barta to zata wuni kuka sai da kyar zata hakura in Kuma ya dawo kaf abinda ya Riko natane ba kuma zata yarda ya kubce Mata ba
Lokacin da ta Kai shekara biyu sabon ya Kara karfi da ta kula zai yi Mata wayo ya gudu sai tayi ca cumi rigar shi ta rike Taki saki sai anyi da gaske kafin akwace shi hannun ta
Sai da ta shekara biyar kafin lubabatu ta Kuma haihuwa inda ta haifo Mubarak bayan Mubarak sai Ahmed sai Fatima daga kansu haihuwa ta tsaya inda yaran ke samun kulawa Amma duk tsananin so da kulawar da ake Basu Bai Hana atarbiyan ce su bisa tsari ba don gaskiya lubabatu tana da kokarin tarbiya Bata kuma yarda da sakarci ba ko don ta tashi da tata tarbiyar ne? Sai yaran suka tashi cikin tarbiya da girmama mutane duk inda suka SHIGA sai sun zamo abin so da Sha awa
Sai dai soyayyar ummita da ban take azuciyar mahaifin su sai dai Yana kokarin saita Kan yaranshi ba tare da nuna wariya ba Amma duk da haka ummita na karbar girmama wa irin ta babban wa sai lamarin gidan eng AK ya zamo abin Sha awa akasin na gidan Kabir mashi
Daular da ake tanadawa humaira fulani ta zarce afadeta don akullum shaharar Kabir karuwa take kwagiloli Kai da Kai suke zuwa inda izzatu tace haihuwar fulani ne tazo da goshi Wai da ma ummul khairi aka samata inda kuma Kabir ya yarda da maganar ta
Kullum Kara shahara yake inda izzatu ke matukar kulawa da humaira wadda ta taso ba kwaba ba harara ko da ko zata yaga kudi
Yan magana sukace nono alkalin Da ai kuwa hakan ta na Shirin tabbata domin kuwa nonon da humaira ta tsotso ajikin uwar goyon ta na Shirin tabbata domin kuwa ta taso da wata irin sangarta da tabara bama wannan ne abin ji ba tun tana Yar shekara biyar ta iya tijara da wulakanci hakama idan ta na kuka Bata Jin rarrashi inda Kabir ke matukar so da kaunar ta Amma batayi sabo da shi ba sosai kamar izzatu Amma duk wani gata tana samun shi
Makaranta ma pravet aka saka ta me shegen tsada aka Kuma yi sa a tana da fahimta sai dai kullum sai tayi fada da yara Yan uwanta inda Kuma kaf din yaran da take fadan dasu Suma ya'yan wasu ne da yawan su ma sun fita matsayi da daraja shiyasa ake Zama lafiya Amma Wanda izzatu ta Raina ajawalin su yanzu ne zata fito ta wanke mutum soso da sabulu in ma taga Kai ba kowa bane to yanzu zata sa akulle ka
Lokacin da fulani ta shekara goma izzar ta ta fito fili duk wani wulakanci na izzatu fulani ta kwashe shi kaf har ma tacewa izzatu Bata iya ba inda Kuma tace waje take so akaita tayi karatu ai kuwa izzatu tasa Kabir ya sama Mata makaranta a America ta Kuma dage ta tafi inda acan ne Kuma ta Kara koyo izza da dagawa har da jijji da Kai har Allah da ikon shi ta kammala karatun ta dawo gida
Inda Kuma can ummita eng AK ya so fiddata waje tayo karatu Amma ita ummita tace Bata son abinda zai rabata da abban ta tafi son kullum ta ganshi
Yayi murmushi "to sai kinyi min alkawari Zakiyi karatu sosai don so nake kiyi karatu me zurfi......
"Nayi maka alkawari Abba in Sha Allah ba Zan baka kunya ba kuma sai kayi alfahari Dani",
Hakan kuwa akayi itama tayi nata karatun anan cikin garin Abuja har ta Kare inda ita Kuma ta taso cikin nuna irin nata alkalin da ta tsotso
Babu hayaniya sai tsantsar irin tarbiyar da ta samu ita da kowa sai mutunci da mutuntawa da Kuma sanyin hali inda shima eng ya soma shahara akan kwagiloli Kan na kamfuna da Kuma na gwamnati komai dai cikin rufin asiri Rayuwa Kuma na tafiya cikin godiya da Kuma wadata.....................
[5/16, 9:33 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_
*Page 22*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
[
...........Mutane suka soma fusata da wannan wulakanci da humaira ke yi kowa Yana son ya wuce gida amma saboda iskanci ta saka kida ta ware Kara ta bar mutane da danno horn Wanda ya cika kunnuwan mutane inda gayen da tayi hakan domin shi ya Gane tayi hakan ne domin ta Kona ranshi ai kuwa Yan ta wagarshi dake bayan shi suka fito daga motar dake bayan shi katti ne majiya karfi da ita da motar sukayi Mata dibar Karan mahaukaciya suka aje gefe
Sai jinta tayi an fizgi motar an kaita gefe inda ashar din da mutane ke ta dura mata Kan Bata musu lokaci da tayi ya Kara Bata haushi inda ta fito taga yadda bayani motar ya bandare saboda dibar Rashin albarka da akayi Mata motar da ko sati batayi da kawowa ba haushi ya isheta ga Kuma zagin da ake ta sheko Mata abinka da Yar gata haihuwar Asibiti sai kawai ta bare da kuka shabe shabe ganin Babu Wanda ya kula ta sai ma kallon banza da ake jifar ta dashi ya sa ta shigo motar ta taho inda taji gaba daya motar ta sauya saboda bandarewar da tayi haka ta iso gidan Yana kuka inda izzatu ta fito da sauri tana tambayar ta me ya faru?
"Momy dubi yadda ya mayar min da mota wallahi ba zan yarda ba...... ....
"Waye da wannan aikin?
"Wani dan iska ne momy bayan yayi min Bari Kuma yasa Yan iska sukayi min haka da mota wallahi sai ya biyani......
"Muje ki nuna min shi don ubanshi ko waye uban shi sai na saka an daure min shi Bai San ke ko wacece bane? Hana suka SHIGA mota suka fice izzatu na ta zuba sababi har inda abib ya faru sai dai ko me kama dashi Basu gani inda izzatu ta SHIGA sababi da dai ta Gane harara cikin duhu take sai tace su koma gida kawai
"Dan iska Allah ya kure shi da ya Kare Rayuwar shi gidan sarka matsiyacin banza bai San ke din zaune kike da kuturinki ba?
Haka suka dawo fulani na kukan ita motar ta ya zatayi? Izzatu ta rungume ta tana Bata hakuri tana fada Mata Wai za a gyara Mata motar ta......
"Ni momy sai dai asauya min wata wallahi bana sonta bama Zan sake hawanta ba..........
"Sha kuruminki Yar lele za a sauya Miki ko jirgin sama kike so ubanki na da kudin siya Miki bare wata mota can da kudinta ba zasu wuce milyon goma ba
Haka kuwa akayi Bata Kuma hawan motar ba sai da Kabir ya sauya Mata wata wadda tace tagani ana talla a aljazira ai kuwa akayi Mata oder ta soma burkar gari
Wata Ranar asabar ta nufi park don ta huta bayan tayi order abinda take so ta shimfida darduma ta zauna tana chat awayarta har uku na maraice inda ta nade dardumar tayi nufin tafiya gida tana tsaye zata bude mota ta SHIGA taji saukar bawon ayaba afuskar ta
Ta dago da sauri don taga daga inda ya fito sai kawai idonta ya hasko Mata gayen da yayi Mata wulakanci har hawa biyu
Har ga Allah baiyi da niya ba asalima Bai San ya watso inda take ba
Ta tafi afusace Kan ta sauke mishi lodi abin haushi kafin ta Isa har yaja motar yayi gaba abinshi
Haka ta juyo tana kuka izzatu ta tarbeta tana tambayar ta
"Momy sai na wulakanta gayen can me na yi mishi yake min haka? "Ba dai Wanda ya lalata Miki mota ba?
Shine momy yau ma sai da ya watsa min bawon ayaba afuska.......
"Wai Dan gidan uban waye ne? Dame yake takama? To koma uban waye ubanshi duk Ranar da ya sake na Kama shi ga hannu sai na saka an daure shi ya Kare Rayuwar shi a kurkuku.
Nan ma haka izzatu tayi ta masifa har dai suka Gane ba mafita sai yazo hannu.
Ciwo ya dawo wa dungo sabo gal inda wannan karon ta nufi Asibiti inda aka yi Mata awo aka gano matsalar ta
Abin ya firgita likitan Amma ita dungon Bata firgita ba don tuni ta soma hasashen hakan
Likitan ya dubeta cikin rudani da tashin hankali don Yana tausayin ta tun wancen zuwan da tayi yake tausaya Mata
"Baba matsalar kwada ce tare dake Kuma mun duba munga saura guda daya Tak shin kin taba bada kodarki ga wani ne? Ta amsa da eh kwarai kuwa nasan anyi hakan......
"To baba sauran gudar da tayi saura tana da matsala don haka ana bukatar sake dasa Miki wata kafin wannan gudar ta tsaya da aikinta don ko za a dawo kanta sai anyi aikin dashen
Ta dubeshi cikin zafin ciwo
'to yanzu kamar nawa ake bukata wurin aikin likita? Yawan kudin da ya ambato Mata ya kusa sakata faduwa inda ta tabbatar da lallai sai ta nemi daukin danta Kabir don wurin shi ne kawai zata iya samun wannan kudin don haka tacew likitan zata yi iyakar kokarin ta har ta samo kudin kome kenan zata dawo da haka sukayi sallama da likitan ta dawo gida
Ta sanar da malam Ali abinda akace ta Kuma ce zataje Abuja wurin Kabir ta sanar dashi abinda kenan......
"Inaga ki Bari naje tunda Baki da lafiya dungo ko Zaki iya zuwa?
"Eh Zan iya malam gobe zanje in Sha Allah sai afadawa su Jamila naje abuja don yau lahadi na San gobe litinin zasu kawo yaran su
"To Babu matsala Allah ya kaiki lafiya ya dawo dake lafiya yasa kuma adace ya tashi kafadunki..
Ta amsa da Allahumma ameen
Washe gari ta bugi hanyar abuja...............
[5/16, 9:33 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_
*Page 21*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
.........A yanayin tsarin halitta humaira fulani farace Amma ba irin farin Nan me haske sosai ba da kadan tafi wankan tarwada sai dai akwai wani Abu Wai shi kyau ga Kuma diri me tsari don dirarriyace me daukar hankali Bata Faye son yawan kwalliya ba Amma duk shigar da tayi zata karbeta Kuma ta zamo Zara cikin taurari akwai yauki da yanga da Kuma nuna matanci sai dai tsabar dagawa da izgili har da izza to dama yaushe barewa ke gudu danta ya rarrafa?
Agefe Daya Kuma tsarin halittar ummita ya zamo Fara ce tas har tana yellow yellow ita kuwa macece me son ado da kwalliya Kuma idan tayi kwalliya Kai kace Yar tsanace
Bakinta dauke da siririn hakorin makka Wanda shekarar da ta wuce ne abban nata ya biya musu kujera su duka hada haj mama sukaje suka sauke farali dama hakorin makka na burgeta sai Kuma akayi sa a ta sanyo shi inda ya Kara fito da martabar ta inda samari ke ta kawo mata Hari Amma Allah Bai sa taji tana son tsayawa da su ba inda Kuma abbanta yace ba yanzu ne zata soma magana da samari ba sai dokar tayi Mata Dadi ta kulle su ta jefar da makullin
Ta kwashi su Mubarak a motarta da abban ya siya Mata elements suka nufi sahad don Allah yayi ta me son kayan makulashe dangin Zaki shiyasa Bata sati Bata zo sahad ba yadda take son chocolate da biscuits Bata damu da abinci haka ba shiyasa take kwaso kannenta suzo sahad ko jifatu su kwashi abinda suke so
Ta faka motar a parking space dai dai da da fakawar wata katuwar mota kusa da inda tayi parking cikin Rashin sa a kyauren motar ya gogi motar da ta faka kusa da ita. Fulani ta fito tana kallon yadda kyauren ya Dan gogi motar ta ta lailayo wata ashar marar tsarki ta antakawa ummita ta fito tana Bata hakuri.....Kafin ta cire hannu ta tsinkawa ummita mari
"Ubawaye ubanki agarin Nan da Zaki gogae min mota.? Wannan shegiyar motar Taki me kama da amalanken shanu ita kike kokarin lalata min tawa motar da sai ta siyi Taki hudu ko biyar?
Ummita ta dubeta tana dafe da inda ta mareta dayake ba me son tashin hankali bace sai ta kuma Bata hakuri tana fadin ba da gangan tayi Mata kuskure ba
Haka fulani ta wuce tana sababi inda ummita ta sauke ajiyar zuciya taja kannenta suka shiga cikin sahad din inda Mubarak ke fadin shi fa sai yaci ubanta idan ta kuma zagin ummitan.......
"Rabu da ita Mubarak Allah ya hada ta da daidai ita Ni bana neman tashin hankali. Haka suka SHIGA suka judo kayan kwalam din su fal ledoji inda itama fulani ta siyo ice cream da da wasu abubuwan inda suka fito kusan Atare ummita na mamakin ta Akan zafin Kai da zuciya
Adaidai kofar fita fulani ke gaba su ummita na bayanta inda sukayi taho mu gama da shi, shi zai shigo ita Kuma zata fita suka gwabza wani irin karo Wanda har kayan hannunta suka tarwatse ice cream din ya watse ajikinta ga Kuma goshinta da suka gwabza karo ya daku sosai
"Ya subhallah ya fada Yana dafe goshin sa da yaji Yana mishi radadi ya duka Yana tattaro Mata kayanta da suka zube kasa ya kwaso su Yana Miko Mata inda zuciya ta ciyota maimakon ta karba sai kawai ta gaura mishi Mari tana sababi
"Dabba da Kai zakayi min Bari salon kayi min sata banza matsiyaci".
Ya dubeta Yana shafa inda yaji tafin hannun ta kamar shi namiji me jini ajika ace mace kamar wannan ta cire hannu ta tsinka mishi Mari ? Sai yaga ai shi yayi Mata laifi
Don haka yace ta Bari ya SHIGA ya amso Mata kayan da yayi Mata asara....
"Kaine matsiyaci kaje da sauran ma na bar maka tunda dama kazo kayi min sata ne...
Ta wuce fuuu ta bar shi da yi Mata rakiya da ido , Amma lallai yarinyar can ta sameshi da yawa yadda yake da zafin Kai Amma ace har amare shi Amma bai dauki mataki ba?
Yana kallonta ta fice aguje ta bar sahad din inda su ummita da kannenta suka fito Mubarak nacewa
"Kinga Allah ya saka Miki anty . "Uhm na gani Mubarak Kai dai bi duniya a sannu don Bata da tabbas itama Ina rokon Allah ya shiryeta don wallahi naji Ina son ta duk da abinda tayi min......
"Wallahi Ni bana sonta anty tunda Bata da kirki. Ummita tayi murmushi tajawo mota suka dawo gida
Inda Mubarak ke fadawa ummansu abinda ya faru asahad ummita tayi mata bayanin komai haj lubabatu yace Allah ya kyauta sai ki kula .
Ita kuwa fulani ko da ta fito daga sahad sai ta zarce jifatu ta siyo abinda take muradi tana tafe tana sababi da tijara ita kadai inda tazo dai dai traffic light ta tsaida su. Nan ma said masifa take Akan jiran traffic din inda ta waiwayo bayanta taga dogon go slow din da aka hada inda motar dake bayan ta ta hango gayen da yayi Mata Bari abakin sahad
Taja tsaki tana Jin tamkar ta fito ta shake shi inda kuma traffic ta Basu hannu Amma tayi kunnen uwar shegu Taki matsawa saboda Wai ta Rama abinda yayi Mata.
Aka ci gaba da danno Mata horn Akan ta matsa gaba Amma ta share sai ma latsa kida a CD ta Kuma Ware kidan..............
[5/17, 10:10 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_
*Page 23*
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
.........Cikin ikon Ubangiji ta iso