Showing 3001 words to 6000 words out of 36278 words

Chapter 2 - Zan Fasa Kwai Part 1 Complete by Hadiza Bara'u Gidan Iko.txt

ki Fara don Zan iya jure komai akaran kaina Amma ba Zan jure ko kallon banza ga hajiya ba bare ki nuna Mata yatsa.......


"Ohooo sai nice za a iske gida azageni in Kuma shiga sabgarsu su zageni saboda Ni ban San yanci ba ko kuma shago aka bude na fito ko Kuma daga sama na fado? "To na rantse maka Babu shegen da Zan Kuma yarda ya taka Ni in zuba ido in kyale shi don yanzu Kai nakewa Alfarma ba kamar Ni da suke zaton kayi min Alfarmar ba sai Kuma ka shirya sanar dasu Kaine da matsala ba Ni ba.


Ya dubeta "Ina fatan cikin shegun da ba Zaki yarda su taka ki ba Babu hajiya? Kiji ki Kuma kiyaye Babu wani Abu da hajiya zata so ko ta sani Wanda ba zanyi shi ba don bani da wani fata ko buri sai na in rabu da ita lafiya. Ko auren take so nayi zanyi don zanyi biyayya agareta sai ki kiyaye.


Tayi wata kwafa ta shige daki ta barshi da yi Mata rakiya da ido kafin yayi murmushi kishi manya kowace mace da kalar nata abinda ma yake tambaya shine shi kishi dabi a ce ko hali ne?


Tunda sukayi haka sai izzatu ta fito da sabbin salo tamkar wadda ake zugawa Amma dayake Allah yayi mishi hakuri sai yayi Mata uzuri akan cewa maganar hajiya ce ta sa ta daukar Kai


Sati biyu Yana gida Yana kallon idon mikiya a tashar farin wata shafa ta shigo ita da wata budurwa me shegen kyau ya tashi zaune inda izzatu ke kallon su awatse
Suka zauna suna gaishe da shi inda ko kallon izzatu Basuyi ba
Bayan sun gaisa shafa tace
"Dama hajiya ce tace na kawo maka lubabatu gata nan kanwar mijin asiya ce idan Allah ya yi sai ku dai dai ta".


Lubabatu ta sunnar da kanta kasa cikin Jin kunya inda yaji wani Abu marar Dadi in Banda hajiya yaushe zata turo mishi yarinyar har gida Mai makon ma ace yaje ya ganta.
Izzatu da take kallon su cikin kaskanci ta tofa albarka cin bakinta.


"Wane irin aure ne haka marar daraja da sanin kimar Kai? In ba lalacewa ba lubabatu yaushe za a turoki gidan mutum maimakon shi ya iskeki gidan ku in dai ba zubarwa Kai daraja ba?
Shafa ta dubeta
"Ai Rashin daraja ya Kare ga ci kasayas? Babu komai indai ta samu shigowa ai tayi daraja.....
Ya dago Mata hannu cikin fusata
"Ashe kema kin iya wannan iskancin irin na su Samira da asmau? Akan idona kike fada Mata haka?


"To Yaya bakaji abinda tace ba? ....
"Tashi kuje Zan zo in samu hajiyar muyi magana....
Shafa ta finciki hannun lubabatu suka fice daga gidan


"Gaskiya ba Zan boye maka ba ak indai aure ake Shirin Yi maka Ni Kam sai dai ka sauwake min aurenka don ba Zan iya zaman hakuri biyu ba, ba zanyi hakuri da Rashin haihuwa ba Kuma inzo inyi da kishiya da dangin miji abarni inji da Abu daya


Bai tankawa maganar ta ba ya ci gaba da kallon shi inda wayar shi tayi Kara ya duba ya dauka da sauri inda ake sanar dashi batun kwangilar da aka bawa wani Dan kwangila ne wato Kabir mashi Wanda aka karbo aka bashi don anfi yarda da aikin shi fiye da Kabir mashi din don haka ake son ya fara cikin watan Nan kwangilar shimfida tituna ce a wasu kauyuka wadda za a samu ALHERI sai dai baiji dadin karbewa daga hannun Kabir mashi ba don Babu me son ayi mishi haka Amma dai ya amsa sukayi sallama


Washe gari sai ga hajiya Mama ta diro gidan ak na Shirin ficewa
Ya zube gaban ta Yana kwasar gaisuwa
"Jiya na turo shafa da lubabatu akace matarka tayi Mata wulakanci? A a hajiya Babu abinda tayi Mata dama Ina Shirin zuwa ne Kika zo.


Hajiya ayi hakuri da maganar auren Nan don Allah. Auren ne kawai zamu iya hajiya Amma Babu me iya bani haihuwa sai Allah da yaso bani zai bani inko Bai zano ba to Matan kawai Zan Tara don haka hajiya na rokeki kiyi min addua abarwa Ubangiji komai Yana sane da Ni da matsala ta


Hajiya ta sauke ajiyar zuciya, "To shikenan abdulkarim na fahimce ka Kuma maganar ka itace gaskiya na janye maganar lubabatu Ubangiji yasa kana da Rabon ganin naka diyan Amma gaskiya sai kajawa matarka kunne......


"A a hajiya tunda dai kin janye Taki maganar Ni Kuma yanzu ne zanyi tawa maganar
"Wai hajiya Baki San shine da matsala ba kike kokarin yi mishi aure ? To Nima ba Zan iya auren Wanda baya haihuwa ba tunda ya Zama juya Nima Ina da muradin karawa gaba tsawon shekaru goma Sha inda haihuwa nayi yanzu da na kusa aurarwa tunda kun gama naku wulakanci Nima yanzu ne zanyi nawa




Shekaru biyu kenan da suka wuce mukaje Asibiti akayi Mana gwaji Ni da shi inda likitan ya nemi in Basu wuri suyi ganawar sirri ban San me ya fada mishi ba Kuma har yanzu Bai sanar Dani ba inda ba gano an samu matsala daga gareshi shine ya boye min don kar in ce ba Zan iya ba inda kuka Dora min jakar tsaba to hajiya abdulkarim ne me matsala ba izzatu ba sai ku gaji ku hutas ku Kuma sakar min Mara inyi fitsari


Hajiya ta dubeshi ta dubi izzatu cikin tashin hankali..........
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_




*Page 5*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








........ Hajiya ta dube shi da mamakin wannan magana ta izzatu.
"Da gaske ne abdulkarim"?
Yayi murmushi Yana mamakin izzatu akan yadda take kokarin butulce mishi
"Hajiya mu rufe maganar Nan don Allah babu amfanin da tado ta zaiyi Mana mu barwa Allah ikon shi kawai sai mu zauna lafiya.....
"A a abdulkarim idan har kasan kana da matasala kar ka rufeni fada min sai anema maka magani tunda Ubangiji Bai Saukar da cuta ba sai da ya Saukar da maganin ta.


"Haka ne hajiya to anema Mana sai muyi amfani dashi Ni da izzatu........


"Adalilin me da Kare zai dauki Dame? Ai ba a taba karan ta min akan komai ba sai sai akan magani? Kuma Ni meye hadina da Shan maganin ka na matsala? Kai ne nasu Kuma Kaine da matsalar Nan meye nawa? Ni fa kasani wallahi na gaji da wannan zaman cutar don nazo karshe wallahi da zaka sauwake min zanfi farin ciki don yanzu Babu wani amfanin Zama da Kai


Hajiya ta Mike da Shirin komawa
"Zansa mas udu ya karbo min maganin sai kuyi amfani dashi mugani Allah ya sa mu dace
Ya Mike shima suka fito don yiwa hajiya rakiya inda direban ta ya ke


Izzatu ta rako hajiyar da harara tana Jin kadan ya rage ta make tsohuwar komai zai faru ya Dade Bai faru ba.
Hajiya ta wuce shi Kuma ya dawo inda ya isketa sai cika da batsewa takeyi
Ya soma rarrashin ta Akan tayi hakuri su barwa Allah ikon shi akan maganar haihuwa......


"Saboda ka Gane Kai ke cutata shiyasa zakace inyi hakuri Mana Amma ai ka Dade da sanin irin wulakacin da danginka harma da hajiyar ka suke min suna zaton nice da matsala har suka kasa yi min uzuri sai yanzu da Allah ya haska min na gano ka shine Nima za a cuceni? To kasani Kai namiji ne komai Daren dadewa zaka iya samun haihuwa Amma Ni da lokaci na ya wuce to yafa wuce kenan so abinda yafi kawai mu hakurewa juna don Allah ka sahale min aurenka tun lokaci Bai kure min ba.
"Ni dai nasan duk kokarin me kokari Bai Isa ya samo abinda ba Rabon shi ko ya samo din kuwa zai sulale ya barshi don ba Rabo bane don haka Zan Baki shawara ki roki Allah abu mafi ALHERI a Rayuwar ki sai kiga ALHERI Yana samunki a ko ina Amma son zuciya Babu abinda yake haifarwa sai bacin zuciyar don haka don Allah don Annabin sa ina so daga yau ke daga yanzu ma mu rufe babin maganar haihuwa Ubangiji yayi Mana baiwa me yawa don Bai bamu haihuwa ba sai mu butulce mishi? Ina rokon Allah yasa Rashin haihuwar da Bai bamu ba ya zamo sanadin SHIGA ALJANNAH shi kenan magana ta Kare daga yau.


Abinda ta kawowa ranta shine kawai Yana son taci gaba da Zama dashi Yana cutar ta tunda yasan shine bashi haihuwa
Bata tanka mishi ba Amma fa tana Jin ba zata yarda da wannan cutar ba.


Tundaga wannan Ranar sai zaman lafiya ya wanzu tsakanin ta da dangin miji su shafa duk da ba SHIGA sabgar su take ba haka ma hajiya Bata Kuma zuwa gidan ta ba inda Kuma ak yayi kwangilar shi ya gama ya samu ALHERI me yawa yayiwa hajiya da danginshi hidima itama izzatu ya Bata kasonta Wanda me yawa Wanda duk in yayi kwangila ya gama dama ka Ida ne sai ya Bata sai dai awannan karon Bata amsa ba tace ta gode ba zai siyi Ra ayin ta ba idan dai har son burgeta yakeyi to ya sauwake Mata auren shi ta Kara gaba inda itama zata haihu
Yayi murmushi Nan ma rarrashin ta yayi Yana Bata hakuri shima tayi shiru ba don ta yarda ko ta aminta ba.


Ranar wata alhamis ta kwanta barci inda tayi wani mafarki Wanda shine silar zamowa karshen auren su da AK .......
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_




*Page 6*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






.....Wani mutum tagani a matsayyin mijin aurenta Wanda ba AK ba kawai Kuma ta ganta da jaririya ahannu amatsayin yarta sai dai wani hayaki dake biye da ita ta rasa Gane hayakin meye akarshe ma sai hayakin Nan ya rikide ya koma wuta wadda ke biye da ita tana Shirin lasota aguje take gudu kankame da jaririyar inda ta hango ak Yana tafiya hankali kwance akan wani Abu me kama da jirgin kasa inda ta sheka aguje tana son ya taimaketa kar wutar Nan dake biye da ita ta lasota Amma ga mamakinta sai sai taga ko kallon ta baiyi ba ya wuce abinshi.
Tabishi da kallo har ya kusa kurewa ganin ta inda ta hangi wata yarinya me kyau tana rungume da jaririya ta mikawa ak din ya karba Yana murmushi ya rungume yarinyar Yana murna inda ta ke kallon yarinyar da tabawa ak jaririya kamar lubabatu tana kallo Kuma ya dauketa cikin abin hawan shi me kama da jirgin kasa suka wuce suka barta ta shagala da kallon matar me kama da lubabatu har taji wani mugun radadi Yana binta ajiki kafin ta kwallara Kara inda Kuma taji an fizge jaririyar dake hannunta tana kallo akayi sama da ita
Ta kuma kwallara Kara kafin ta farka....


Ta farka inda take jiyo hucin wutar na bin jikinta
Babu batun ADDU A irin ta Wanda yayi mugun mafarki don gaskiya Bata iya ta ba sai ta shiga laluben fassara mafarkin ta
Da taso gaskiya koma ace da Dan guntun sani akanta to zata Gane wa azi ne da izna akayi Mata tunda tagani ta samu yarinya Amma hayaki da wuta sun biyota akwai kura kenan


Kuma lubabatu da tagani da ak in batayi sannu ba zata barwa lubabatun ak da filin gidan ta Amma sai batayi wannan hasashen ba sai kawai ta kalli mijin da tagani amatsayin Wanda zata haihu dashi sai ta haukace ta Kuma tada bular lallai sai ak ya sauwake Mata auren shi


Ta nufi dakin shi don tuni suka Raba makwanci don tace bataga amfanin zuwa dakin nashi ba sai ta fito da tsiya taku kala kala inda Kuma tafi sauke tsiyar ta Akan tsohuwa talai.
Ta shiga dakin ak din Yana tsaka da bacci yaji ta antayo mishi ruwan sanyi ajiki gashi lokacin sanyi ya farka afirgice Yana shissheka ya dubeta tana Kada jiki da son ta fashe


Ya dubeta cikin sanyin murya "me ya farune izzatu",?
"So nake ka tashi ka sallame Ni don na gaji gaskiya ba Zan Kare a auren da Babu tsiyar da zai tsinana min ba........
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_




*Page 7*


*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








......... Ya share ruwan dake yarari akan fuskar shi Yana murmushi Yana kallonta


"Izzatu Allah ya sani Ina Jin tausayin ki Zan Kuma Kara hadaki da Allah da manzon sa ki bar maganar Nan haka......


"Kar ka Kuma Jin tausayi na Kai ne abin tausayi ba Ni ba don Ni na hango mafitata a mafarki don haka sallame Ni kawai in Kama gabana.
Yayi murmushi "Abinda Kika gani a mafarki ba lallai ya zamo gaske ba sai dai nuni ko izna don Allah kiyi hakuri ki barni nayi barci na kaina ciwo yake,


Ya kwanta ya barta tana jijjigar jiki idonta fal masifa ta fito tana sababi inda ta iske tsohuwa talai zaune tana Gyan gyadi sai kawai ta shara Mata Mari
Abin tausayi tsohuwar ta farka afirgice
"Wane irin dabban cine ki share wuri ki zauna kina min bacci da tsakar Rana?
Ke Bari fa kiji in fada Miki idan kinji kin gaji da aikin Nan babu lallai Babu tilas na gaji da gayyar hakora in kin gaji sai na sallame ki
Ta shiga zubar da ruwan tijara inda tsohuwa talai hawaye ya tararo Mata tana ta ahi da neman afuwa


Jin Marin da izzatu tayi wa talai yasa ak fitowa ya na kallon yadda take Mata tijara ranshi ya baci matuka gaya don Allah yasaka mishi son tsohuwa talai don asali talai wurin hajiya Mama take aiki shine ya matsa da sai tsohuwa talai ta dawo gidan shi don ya Saba da abincin ta tun da sauran karfinta tayi aiki a gidan su shine mafarin tsanar da izzatu tayi Mata saboda tana ganin an turo tsohuwar ne don ta saka Mata ido ko da take wulakanta masu aiki tafi wulakanta Talai


Ya karaso wurin ya kamo hannunta ya tada ita inda yaga hawaye na bin idonta
"Kiyi hakuri talai Ni naji Miki Amma ban San haka kike muskanta ba .
Ya dubi izzatu cikin wani irin fushi da Bata taba gani afuskar shi ba


"Baki ji kunyar cire hannu ki Mari tsohuwa irin haka kamar talai ba? To ya zamo na karshe da Zaki Kuma yiwa wani ma aikaci a gidan Nan bare talai. Talai kamar Uwata ce daga yau kar ki Kuma sakata ko shara bare wani aiki na soke Mata duk wani aiki sai dai agirka abata......


"Wannan ne Kuma baka Isa ba wallahi muddin Ina gidan Nan to Dole ne tayi aiki ba tsufa ba ko mu kwana lafiya ce . Dama na Dade da ganota tsohuwar muna fukace wadda aka turo don tazo ta saka min ido to aiki ya Zama Dole tayi shi ko Kuma jikinta ya Bata Labari wallahi salon kasa ta kalli kanta a wata tsiya kace sai dai agirka abata ita a way?


Bai San lokacin da ya faska Mata Marin ba karon farko a tarihin Rayuwar auren su da ya taba Kai hannu jikinta da sunan duka abinda bai taba yi ba.


"Ba Zan taba Bari ki wulakanta tsohuwar da Ni ne na kawo ta gida na ba
Akan talai ba sai kin roki saki ba Zan Baki shi jahilar banza wadda Bata San kimar tsoho ba. Idan har ka girmama tsohon wani to naka ka martaba don hak sai ki kiyaye ba Zan lamunci wulakanta mutanen dake kasanki ba......


Ta cakumo kwalar rigar shi ta tattare ahannun ta "Tunda har ka mareni akan wannan tsohuwar banzar ai kasan ta ballowa kanka aikin da ba zaka iya dashi in yaso sai ka auri talai ko hajiya mama.......


Ya Kuma Bata kyakkyawan marika guda biyu ajere Wanda yasa taga wata koriyar walkiya
Ya Kira duka ma aikatan gidan inda yace kar akuma saka tsohuwa talai aikin komai Koda dibar ruwa ne wankin kayan ta ma arika hadawa ana kaiwa shago a wanko
Haka Kuma duk Wanda izzatu ta Kuma ciwa fuska ko wulakanci to ya fada mishi tunda ga wannan Rana tsohuwa talai ta samu cikakken yanci inda Kuma izzatu ta fice daga gida ta nufi nasu da sunan tagama auren dama sanadi take nema ta Kuma samu sai dai acan gidan Basu Bata samu goyon baya ba inda aka tuso keyar ta aka dawo da ita aka Kuma bawa ak hakuri inda ita Kuma take Jin ta gama auren shi Koda shi Daya yayi saura aduniya sai sun rabu inda Kuma ta fito da sabon salo na aunawa hajiya Mama da duk wani nashi zagi abinda yake Jin ba zai daukaba


Tsawon sati biyu tana gurza mishi Rashin mutunci Yana dauke Kai inda washe gari sai ga hajiya mama da tarin magunguna ta diro gidan..........
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_




*Page 8*


*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*






...........Hajiya Mama ta shigo gidan tana sallama inda izzatu ke zaune tana chatt a wayarta ta dago kanta ta dubi hajiyar ba tare da ta amsa sallamar ta ba ta maida kanta ga wayarta taci gaba da chat dinta
Hajiyar ta karaso ta zauna tana kallon izzatu da ta baiwa banza ajiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login