Showing 12001 words to 15000 words out of 36278 words

Chapter 5 - Zan Fasa Kwai Part 1 Complete by Hadiza Bara'u Gidan Iko.txt

*Page 16*


*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








............ AK ya samu wayar hajiya Mama take sanar dashi haihuwar lubabatu inda ya yi murna ba kadan ba washe gari Bai ko gama aikin da ya kaishi sokoto ba ya juyo gida ya iso Yana tambayar lubabatu Babu inda ke Mata ciwo ko? Ta amsa da Babu ta Miko mishi yarinyar wadda ya kankame tamkar za a kwace mishi ita inda yayi Mata huduba da sunan hajiya Mama wato bilkisu inda za a kirata da ummita


Hidima sosai ak yayi tamkar Bai San zafin kudi ba tundaga Kan lubabatu har zuwa ummita inda akayi taro lafiya aka Kare lafiya lubabatu na kula da yarta wadda aka shiryawa gata da Jin Dadi ga Kuma kaunar Yan uwa da dangi na iyaye kasancewar an Dade ana jiran ganin ya'yan eng abdukarim din sai ummita ta zamo son kowa.


Acan Kuma gidan izzatu tamkar ba gidan haihuwa ba saboda ta Raina ajawalin mutane ba kowane take ganin ya cancanci tayi Hulda dashi ba shiyasa Babu wasu mutanen kirki sai Yan uwanta suma ba kowa ba don yanzu ne zatayi maka Gori koma ta nuna maka iyakarka


Ahaka dai akayi suna yarinya ta amsa sunan Aisha humaira inda izzatu ke kiranta fulani Wai alkunya ce irin ta Yar fari Sai dai abin haushi abin takaici Wai har akayi haihuwa har sai da aka kwana shida kafin Allah ya kawo dungo ba don ta San anyi haihuwar ba a a sai don ta duba izzatu don tunda tazo tayi mishi maganar zubewar katangar ta har yau din Nan Bai taka inda take ba Wai sai da tazo ta samu haihuwa har kwana shida gobe suna


Ta cika da mamaki yadda Kabir ke kokarin mantawa da ita arayuwar shi
Karin wani mamakin ma izzatu ta Hana dungon jaririya Wai bacci take yi
Tayi Mata barka da sauke Kaya lafiya tayi nufin komawa gida don ko Kabir din ba zata tsaya gani ba


Ta fito kenan motar shi ta faka inda yake ta shuga da fita akan hidimar sunan gobe sai kawai yayi karo da mahaifiyar tashi Wai sai yaji Bai kyauta Mata ba.


Yafito Yana fadin yaushe tazo? "Yanzu nazo Kuma har Zan koma....
"Baba ba suna kikazo ba da Zaki koma?.........
"Ina da wata martaba ne a idonka da zaka Fadi haka? Kuma ka fada min haihuwar ne da zaka zaci sunan ya kawoni? Atake ya Gane Yana Mata ba dai dai ba har ta Kai ga tankawa duk hakurin ta


Da sauri ya soma tuba da Bata hakuri akan Wai ya shafa a ne duk da ranta ya baci Amma sai da tayi mishi uziri Kai lallai abar uwa da danta


Da haka ya lallbota har ta yarda zata kwana ayi suna. Washe gari kuwa aka soma cin uban shagali Wanda Kabir ya Kashi kudi ba na wasa ba akayi taro aka Kare inda Kuma washe gari dungo tayi nufin wucewa birnin zazzau inda ya yi tsaye aka debar Mata nama me yawa acikin kattin Rigunan da ya yanka ya Kuma hadota da kudi masu dama ta wuto tana addua da sa albarka


Haka humaira fulani aka ci gaba da rainon ta itama da shirya Mata ALJANNAR DUNIYA komai ya tafi daidai
Sati biyun da sister mero ta diba Bata Kara ko awa da minti ba ta diro gidan izzatu wadda sai da akayi da gaske kafin a samo Mata maganin da zata Sha ruwan nononta ya Zo don ta gilla karyar Wai Bai zo ba ne inda cikin Yan aikinta wata ta sanar da ita agarin su da akwai me bada magsnin irin wannan matsalar a garin dutse ta jihar jigawa don haka ta hada Mata tafiya taje ta Kuma tako sa a har tayi amfani dashi Kuma ruwan nononta ya Zo don haka take shayar da fulani inda Kuma a yau sister mero ta diro gidan don karbar hakkinta


Ta shigo gidan ta samu izzatu na bawa fulanin nono inda ta dubeta a sheke ta watsar ta zauna akan kujera tana duban izzatu dake Mata kallon ke kadai Kika San sirri na


"Gani na biyo hakkina sati daya Kika bada Ni Kuma bayi biyu ai na daga kafa ko???.........
[5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_




*page 17*




*_insha Allah zamu koma muku posting a Rana so uku safe Rana da dare in hakan Bai samuba zamu koma so biyu a Rana in Allah ya Yar da_*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








.......... Izzatu ta dubi mero cikin Jin haushi da takaici . Mero ta dubeta yadda take Brest feeding din yarinyar tamkar itace asalin uwar ta ta gaskiya


"Uhum kinganki kamar dai ace da gaske kinji yadda akeji sai kokarin feeding ya akayi ma maman yazo? "Ba damuwar ki bace Ni bansan haka kike ba mero da ban hada tafiya ta dake ba Ina amfanin tafiya da matsiyaci?


"Na ma fi da haka matukar kikce Zaki dawo min da bara bana akan hakki na don haka tashi ki dauko min in wuce me motar da na siya ya isheni da na kawo mishi kudin shi


Izzatu ta Mike tana Saba fulani akafada tana fadin Banga amfanin tarayya dake ba tunda Baki da mutunci
Ta shige daki ta rubuto check na milyon biyar ta Miko Mata
"Sai abi wani sarkin ba na garin mu ba
Mero ta dubeta tana kallon ceck din da take Miko Mata
"Ai bamuyi dake Zaki bani takarda banki ba cash kikace Zaki don haka koma ki dauko min kudi na daidai.
"Banda su ajiye sai dai kije banki ki karba ta fada tana cillo Mata ceck din afuskar ta


Mero ta dauki cack din tana duba inda tayi arba da rubutun milyon biyar
Ta dubeta
"Ya Naga kin rubuta min milyon biyar amaimakon goma?


"Biyar din Naga damar Baki don ko ke Kika yi cikin Kika haife iyakar ta kenan


Mero ta Mike tsaye tana kwabe gyalenta ta na cin damara a kugun ta
"Bari kiji in fada Miki izzatu bafiki iskanci don ni har takardar shaida sai da na Kama don haka bini sannu ko yanzu in fasa kwai rubuto min cikon kudina in wuce in ko Kuma yanzu in iske Kabir mashi in fasa mishi Kwan kigani idan Baki kwana gidan ku ba


Da gaske kuwa ta Kada hantar cikin izzatu inda har ta rubuto mata cikon kudin ta tabata . "Ai kuwa godiya ma ya kamata in Miki don kuwa kin yi min silar farin cikin da ba Zan iya manta shi ba na gode sosai Allah ya Kara daukaka


"To ameen in da gaske kike in ma ba gaske ba ne Allah ya biye bakinki Nima na gode da samun abinda ban taba zaton samu ba sai gani na biyu.....


"Bana bukatar ganin ki a gidana don Zaki iya Zama barazana ga Rayuwa ta mu hadu Nan mu Rabu Nan
Sister mero tayi murmushi ta fice inda ta shige mota ta nufi banki don ta fito da kudi ta biya me mota kudin shi.


Fitar sister mero ya bawa izzatu damar kamo bakin zaren wani mugun qulli da tayi nufin zargawa mero
Da sauri ta jawo wayar ta ta Kira wani Dan ta Adda da ta sani Wanda ya taba yiwa wata kawarta aiki har ta zarga nata mugun qullin
Don haka ta Kira wayar gambo mafiyas Wanda ya kware a iya Sara suka da ta addsnci


Kara biyu gambo mafiyas ya daga "Allah ya taimaki hajjyata ta samu ne? Kwarai kuwa gambo maza kazo Ina son ganinka....


"An gama hajiya dama Babu komai ahannu na..........
"To maza garzayo kasamu kudi yanzu


Minti Sha biyar ya iso inda take fada mishi abinda take so yayi Mata
"Ka Gane ko gambo wata ce nake so ka bi min bayanta zuwa first Bank zata fiddo wasu manyan kudi shine nake son ka karbo min su ka dawo min dasu zaka ganta cikin mota 206 jar kala me lambar katsina yi maza gambo ka karbo min kudin Nan kar ka yarda asamu akasi ko sabani.........


"Babu kuskure acikin aikina hajiya Ina me tabbatar Miki da awa uku tayi yawa kisaka Ranki inuwa kudin ki sun dawo Miki sun gama
Ya fice Yana fiyto izzatu ta zauna tana dariyar mugunta
"Uhum mero kenan yaro yaro ne yaro Bai San wuta ba sai ya taka mero kinci karya kin kwana da yunwa


Gambo mafiyas ya iso bakin ya labe a gefe Yana kallon mutane me SHIGA da me fita ba inda ya hango motar sister mero wadda aka kwatanta mishi Sai ya soma dakon jiran fitowar mero


Mero da ta gabatar da cek din da zata fitar su kansu sun girgiza Anna da suka duba asusun izzatu sai Basuyi mamaki ba atake suka Bata takardar da zata cike ta cike aka fitar Mata da kudin duka sai ta raba su ta saka milyon biyar cikin asusun ta ta fito da milyon biyar don taje ta biya bashi sau Kuma ta aje don bukatu


Ta SHIGA motar ta ta nufi gida don ta Kira me mota yazo gida ya amshi kudin shi saboda zai fi sirri
Sai dai wani Al amari dake Shirin faruwa ya gigita sister mero inda wata mota ta Sha gabanta cikin azama ta taka burki don kadan ya rage ta banki motar da ta Sha gabanta


Atake gambo mafiyas ya fito ya na bude motar mero Yana kanga Mata bindiga agoshi Yana tambayar ta kudi
Bataja ba ta jawo buhun kudin ta Miko mishi ya amsa ya koma motar sukaja motar aguje suka bacewa ganinta inda mero take sauke ajiyar zuciya ta iso gida tana tunanin waye ya San zataje banki? Babu ko shakka izzatu na da hannu akan wannan abin da akayi Mata koma ita ta turo Mata bakaken mabiya sai Kuma ta tuna da yadda izzatun taso yi Mata dungu akan kudinta sai kawai ta gano mugun kulli ne izzatu ta kullo Mata inda Kuma wata zuciya ke Bata shawarar tashi kije kuyi ta ta Kare Babu Wanda yasan zakije banki sai ita to komai zai iya faruwa


Aikuwa ta fice zuwa gidan izzatu inda ta badda sawu da saka nikabi ta tari napep ya kawota kofar gidan izzatu inda Kuma cikin sa a ta ga motar da tayi Mata fashi ta faka har katon basamuden da ya yi Mata atakin da bindiga ya fito Yana rike da buhun kudinta inda ta tabbatar dai izzatu ce me alhakin yi Mata hakan, to yanzu meye abin yi? Anya kuwa idan tace SHIGA zatayi gidan izzatu ba zata saka katon ya illatata ba????............
[5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_




*page 18*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








.........Wata zuciyar tace Mata shiga kawai ki karbo hakkin ki tunda ma gashi kin gani ya kawowa wadda ta sakashi
Har ta cire kafa zata tunkari kofar shiga gidan sai Kuma wata zuciyar ta kwabeta
Akul Kika SHIGA gidan can yadda Dan ta addar can ya nuna Miki bindiga komai zai iya faruwa gara dai ki koma gida ki sako sabon lale Amma SHIGA gidan can ayanzu akwai matsala
Sai Kuma ta karbi wannan shawarar da fuskar fahimta ta juya gida


Gambo mafiyas ya direwa izzatu kudin a gabanta inda inda ta Gane kudin ba duka bane Amma dai an rage ta Zaria rafar dubu dari ta bashi ya karba Yana godiya inda yace da wani aikin ya samu ta kirashi
Da haka ya fice Yana zukar tabar iblis din shi


Abinda izzatu bats sani ba shine shima gambo mafiyas sai da ya wari wasu kudin ya boye don harkar duka Babu Amana Amma izzatu Bata Gane ba ta dauki kudin ta mayar daki


Komawar sister mero gida ta doko wa izzatu waya inda tana ganin Kiran meron gabanta ya Sara dass ! Amma sai ta maze ta daga da salon bagararwa


"Sister mero ya kike ya aikine?
"Lafiya Amma abinda Zan fada Miki izzatu karki yarda kice irin wannan wasan zamuyi dake don na rantse Miki da Allah sai na kaiki kasa warwas..........


"Me akayi Kuma mero?....... .
"Karki yaudare Ni don Ni ba yarinyar goye bace idan kudin ki kike so ai ba sai kin turo min babbakun mabiya ba sai in maido Miki in karbi Yar mutane.........


"Nifa bangane Abinda kike nufi ba mero wani Abu ya faru ne?
"Kin fini sanin abinda ya faru saboda Babu Wanda ya San zanje banki karbar kudi sai ke to Akan me Zaki turo min Dan fashi bayan Ni da ke taimakon juna mukayi? Kuma magana Kare nazo dazu na tarar da shi Wanda Kika sa yayi min fashin ya Zo gidan ki da buhun kudina to saurareni da kyau na rantse Miki da sarkin da ya huran numfashi da tassarufin lamurana sai kin biyani kudina Baki Nan da awa ashirin da hudu ki turo min kudina ga lambar asusuna Nan Zan turo Miki idan Kuma kina bukatar sauran kudinki Zan maido Miki in karbi Yar mutane duk shawarar da Kika yanke Ina jiran kiranki.........
Dit ta yanke wayar tabar izzatu da kyalkyala dariya


"Uhum mero kenan na kula in ba kwanji na na motsa ba Zaki zame min kadangaren bakin tulu to duk Zan hada in kashe da tulun da kadangaren don Banga amfanin su ba


Akarshe dai ta yanke shawarar turawa sister mero kudinta don suna game wayar sakon lambar account din ta shigo wayar izzatu a take kuma tayi Mata transfer ta wsyar kudinta suka SHIGA inda sister mero tayi murmushi


"Uhum izzatu kenan tunda wannan turbar kike son mubi to Zan nuna Miki Ni har gobe takadarci Yana min Rana Baki sanni bane Amma Zan nuna Miki kece karamar Yar iskace Nasha gabanki har abada ke gaba da abada ma na wuce da iyawar ki Zan Kuma waiwaye ki don wasan mu Bai ma fara ba karamar marar kunya dake bileja


Itama izzatu anata bangaren Tasha mugun Alwashin akan mero saboda ta kula itace zata zamo Mata matsala to su zuba shege NE zai fasa Bata santa bane nata iskancin kawai ta sani Bata San nata ba Allah yasa tsautsayi ko azal ya sa mero Kiran wayarta ko ma zuwa gidanta taga yadda ake kera Rashin mutunci




Tom Bari muga yadda Za ayi haduwa ta gaba da sister mero da izzatu waye zai FASA KWAI.............
[5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*




*NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_




*Page 19*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








.........Wata irin Rashin lafiya ta Kama dungo uwar Kabir mashi ciwo irin Wanda Bata taba yin irin taba Amma da yake ta iya jarumta da hakuri haka take ta jaganiya da Yan yaran rainon ta yaran Babu Wanda ya shekara biyu ga Yar banzar rigima wancan yayi kuka ta rurruga wancan yayi fitsari ta wanke wancan yayi Kashi ta wanke ba zata taba samun sauki ba sai sunyi bacci ko iyayen su sun karbesu Amma Duk da haka ciwon da takeji Bai sa ta kwanta ba duk da kallo Daya zakayi Mata ka Gane Bata da lafiya matukar dai kana Gane lamarin Rayuwa sai dai Rashin kudi ya Hana Mata zuwa Asibiti inda ta Bari sai ta karbi kudin rainon ta idan anyi albashi sun karbi kudin su


Sai dai kafin albashin ciwo yaci karfin ta har ta Fadi kwance ciwo riris inda har rainon ma ya gagara
Wata daga cikin masu kawo yaranta me suna Jamila ta shigo gidan inda ta iske dungon kwance abin tausayi


"Subhallah ladidi Baki da lafiya ne? Wallahi kuwa Jamila Ina Dan gidana fahat? Yaron da take raino ya SHIGA dago Mata hannu Yana son ta dauke shi saboda sunyi sabo me karfi da yaran
Ta Mika hannu ya taho ta rungume shi inda Jamila ke kallon ta cikin tausayawa


"Amma ladidi kinje Asibiti kuwa? A a Jamila banje ba saboda Babu kudi hannu na..........
"Karki damu taso muje in kaiki ai lafiya tafi komai


Jamila ta kaita Asibiti aka dubata aka Bata magun guna suka juyo gida inda jamilar ta kashe kudi masu dama sama da dubu goma Sha biyar duka dawo gida gungo nata zuba godiya don gaskiya Jamila na mutunta ta ko abinci me Dadi tayi sai ta Aiko Mata bare ta dafa nama


"Karki damu ladidi ai mun Zama Daya Babu komai ke dai Allah ya Baki lafiya
Ta amsa da ameen ya Allah
Haka Tasha magani har sauki ya samu
Inda wata ya cika Jamila ta dauki albashinta ta kawowa dungo hakkinta Amma dungo tace Allah ya sauwake wallahi ba zata karba ba Amma Jamila tace wallahi sai ta karba.....


"Haba Jamila don dai nice uwar marasa mutunci sai na karbi kudinki ?......
"A a sai kin amshe su wallahi banyi don komai ba sai don Allah da zaman tare Allah ya Kara Miki lafiya ta aje Mata kudin ta dauko danta ta fito inda ta bar dungo da zubar hawaye Wai yau Dan da ta haifa ta wahaltawa shi ke gudunta yayin da can wasu da Basu hada komai ba sai musulunci da mutunci suke wahala Mata har suyi Mata abinda danta Bai yi Mata ba


Babu abinda yafi Kona ranta irin yadda ta taka har gida ta sanar dashi zubar bangon ta Amma har yau Bai tada Mata ba asalima an kusa shekara Amma har yau zuwan shi guda Kuma yaga yadda aka saka zana amma bai Kuma zuwa ba Kuma yanzu da mutuwa tayi ba lallai ya sani ba to in ta mutu ma Yana da asara ne?


Amma dayake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login