Showing 24001 words to 27000 words out of 42899 words

Chapter 9 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt

hawa ba, wato wani zubin yana hawa wasu Dawakan bayan Saheeb kuma lafiyayyu kamarsa, amma ya camfa cewa yafi jin kaimi da sakewa da nishadi idan ya hau shi don yin wasan Polo, kuma yafi samu nasara idan Saheeb ya hau. Ko babu komai ya fito ne daga hannu mai albarka, hannun Kakansa Sarki AbdulRasheed Akanni.
Playing Polo has been the hobby of his life. Ya sha cin kofin zinare a wasan ‘polo’ a ciki da waje, a garuruwa daban-daban na kasashen duniya.
Don haka wannan faduwar bazata da ta faru yau da Prince, ba ‘yan Africa kadai masoya Prince ta dagawa hankali ba, har dasu Turawan na Ajantina, wato (host country) na wasan da ake gudanarwa, da mahukunta gasar na kasar ta Argentina.
Wani hamshakin asibiti mai zaman kansa aka kai Prince AbdulRasheed yake zaman jinya a can ba nisa da gidansa.
Zaka yi mamaki in kaji cewa, duka raununnukan nan da yaji a jikin sa, har da karaya a kafa da hannu, sabida ba karamin faduwa yayi ba, domin Dokinnan sai da ya wulwula shi a sama sannan ya tika shi da kasa, amma raunukan nan basu dame shi ba, haka zugin ciwon su bai dami Prince Abdulrasheed ba, kamar subucewar kofin gasar nan, na ‘champion’ din duniya a POLO daga hannunsa.….
Wanda da wannan tsautsayin bai faru ba, ya saka ran zai kai shi ga attaining 10+ goal polo handicap (highest rank of the world’s polo player).
**** **** ****
BANANA ISLAND, LAGOS
P
rincess Fatima, ta shigo da dan saurinta tana cewa da mahaifiyarsu Hajiya Sappa.
“Ni me ya faru da kunnen Nenne na ne? Anata kiran ki a waya tun dazu kina kallonta ido hudu amma dagawa ta gagara, halan baki ji kiraye-kirayen bama Nenne?
Tun daga falo nake jiyo ringing din wayarki ba kakkautawa. Nenne meke damunki haka yau? Tun safe nake ganinki haka sukuku (moody) cikin tagumi da damuwarnan, duk kin birkice”.
Princess Fatima, ta karasa shigowa dakin na mahaifiyar su cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan manyan sarakuna, ta fadawa mahaifiyarta Nenne Sappa kalaman cikin taushin murya, Nenne dake gyangyadi akan dardumar data yi sallahr walha ta dago tana duban Fatima fuskarta fal damuwa.
A hankali ta bude ido sosai daga lumshewar data yi musu ta dubi doguwar diyarta Gimbiya Fatima, kyakkyawa ta karshe, wadda ke tsaye a kanta da wayar Nenne din a hannunta data sunkuya ta dauka a gabanta, har zuwa lokacin anata kira ba'a daina ba.
Da sauri Nenne tace “Miko min wayar, Allah yasa shine, bana cikin nutsuwa Fatima, saboda yau kwana biyu bai kira ni ba, gyangyadinnan da kika ga nake yi mafarkinsa nakeyi a cikinsa, wai bashi da lafiya, dadin dadawa tun shekaranjiya rabon da ya kira ni, abinda bai taba yi ba, jinkirta kira na a duk yanayin da yake ciki (koda kuwa ace yana kan Doki ne)”.
Fatima ta mika mata wayar, sannan ta zauna a gefe tana bata labarai. “Nenne jiya ne ‘Championship Tournament’ din su Hammah fa, a can Argentina, bashi da lokacin kansa kin sani. Na so inje kallo physically Dade (Baba) ya hanani, tun dazu kuma na kunna ‘PoloLine.TV’ ba’a nuno gasar ba.
“I am worried too”. Ta karasa fada da harshen yarbanci. Wato itama cikin damuwar take kwatankwacin ta mahaifiyarsu.
Ba tareda ta amsawa Fatima maganarta ba Nenne ta amsa wayar da ake tayi mata ba kakkautawa da sallama cikakkiya irin tata ta nutsuwa, ta hanyar nemawa wanda ya kirata amincin Ubangiji ba tare da ta san cewa katon Bayahude bane ke kiranta ba musulmi bane ba kuma Dan nata ba, duk kuwa da cewa da lambarsa aka kira ta.
A wayar aka shiga yiwa Nenne bayani da harshen da ba ganewa take yi ba, wato yaren “Araucano” na Argentina.
“Sunana Pareto Danny, ina magana daga wayar ubangidana, ya samu tsautsayi ne… muna asibiti, inason magana da Mother dinsa…”.
Don haka sai kawai ta mikawa Princess Fatima wayar cikin yamutsa fuska tace “ungo nan Fatima, kiji me wannan yake fadi haka?”.
Ba don ma taga lambar ta Ajantina bace da bazata amsa kiran ba, a ka’idarta Nenne Sappa bata amsa bakuwar lamba, amma kasancewar ta san cewa AbdulRasheed yana can, kuma yau kwanaki biyu kenan tana alhinin rashin kiran wayarsa da bata samu ba kamar kullum, domin duk halin da yake ciki baya kasa kiranta kona minti uku ne, shine yasa ta amsa wannan kiran da gaggawa don jikinta ya bata ya shafe shi.
Maganar mintuna kusan uku Princess Fatima tayi da Pareto a wayar, ta fahimci me yake kokarin sanar dasu, wato Prince ya fado daga Doki, ya jikkata fiyeda koyaushe, yana asibiti a kwance da karaya a hannunsa, don haka Fatima sarkin raki sai kawai ta saki wayar a kasa ta dora hannuwa aka ta sakawa Nenne kuka.
Kasancewar Fatima mai tsananin so ga Yayan nata kuma mai saurin kuka. Suna son junansu suna kula da juna shigowar bare cikinsu ne dai karbarsa sai a hankali. Nenne nata tambayarta ta gaya mata me aka ce mata?
Da kyar, kafin Fatima tace cikin hawaye “Nenne Hammanmu wai, ya fado daga Doki yaji raunuka a jikinsa, yana asibiti can a kwance, an kira Dade a gaya masa ba’a sameshi ba shine aka kira ki”.
“Subhanallah!”
Inji Nenne, cikin kidimewa da mikewa tsaye, tana cewa “wannan DOKI!” Nan dai ta nemi fulatancin da take gwadawa akan AbdulRasheed sau tari yau ta rasa, Nenne bata jure rashin lafiyarsa ko kadan, duk da yana jimawa bai fadi a doki ba amma ko ya fadi baya jin wani ciwo na azo a gani, yaushe rabon ace yana kwance a asibiti ma ta manta koda ya fado daga Doki bai taba kwanciya asibiti ba sai dai ya sha maganin ciwon jiki yakwanat zuwa wayewar gari ya shiga harkokinsa, bait aba samun mummunan wani rauni ba.
Cikin damuwa ta ce da Fatima tayi mata ‘booking flight’ mafi kusa, tace da kanta zata tafi har can ta yi jinyarsa, tunda dama duk suna da Visa na shiga Argentina sun saba zuwar masa koyaushe suke so.
Kasancewar a kasar Argentina Prince AlbdulRasheed ya mallaki gidan kansa (Ranch House) mai ‘field’ na ‘Polo’ a cikinsa.
Iyayensa, Taiwo da danta na fari Hakeem (kafin a haifi Kiki) da kannensa mata ‘yan biyu Firdausi da Fatima, na yawan kai masa ziyara gidan, kafin ya samu aiki a Qatar refinery y araba rayuwarsa gida biyu tsakanin Qatar da Argentina. A Qatar Penthouse gareshi wanda bai kai girman gidansa na Argentina ba kuma babu Dawakansa acan.
Sai Princess Fatima tace itama don Allah zata bi Nenne gun Hamma suyi jinyar tasa tare, tace bazata iya zama a gida ba, alhalin bata san halin da Hamma ke ciki ba, damuwa zata isheta, don haka suka fara shirin tafiya itada Nenne.
Princess Firdausi kadai da masu aikinsu aka bari a gidan, don ta jira dawowar Dade ta kuma kula da gida wato ta jira mahaifinsu da zai dawo a satin, kada ya dawo gidan babu kowa kuma agidansa kawai yake cin abinci, wanda shima ya tafi nasa ‘medical check up’ din ne na lalurar sugar dinsa a Egypt.
Wani abun burgewa da wannan gidan nasu Prince Abdulrasheed shine tringualism dinsu; Babu irin yaren da bazaka ji anayi a gidan su AbdulRasheed ba cikin manyan yarukan nan uku su da iyayensu biyu da kannensa mata, tsakanin Hausa, Fulatanci da ‘native language’ na Babansu wato Yoruba, duk babu wanda basa ji, kuma babu wanda basa yi, wato babu wanda basa yarawa a junansu.
**** **** ****
THE PRINCE
N
enne Sappa da Princess Fatima sun sauka lafiya a kasar Argentina a wani marece na tsakiyar winter season, ana tsaka da tsuga yayyafin kankara. Nenne Sappa sanye da Hijab dinta ruwan kasa-kasa daga samanta har kasa, yayinda Princess Fatima ke sanye cikin wasu ‘Blue Royal Outfits’ masu kauri.
Kamar yadda aka riga aka tsara hakan ce ta kasance; yaronsa Pareto shi yazo ya daukesu da wata kankanuwar motar Abdulrasheed din (Alfa Romeo), daga filin jirgi zuwa asibitin da yake, Pareto yayi musu jagora har dakin da Prince yake a kwance yana jinya a asibitin kashi.
Sanda suka shiga dakin barci yake yi sadidan, don zugin hadewar kashi ya ishe shi, hakan yasa aka yi masa allurar barci don ya samu sa’ida ya kuma huta azabar.
Nenne da Princess Fatima, suka taka suka isa gareshi suka tsaya a kansa suka kura masa ido, suna kallon kyakkyawar fuskarsa (with great affection) da alhini cikin idanunsu, daga bisani duk suka aje mayafansu akan kujera don yin alwallah su sauke sallolin da suka riskesu a hanya.
Har suka yi sallah suka idar duk AbdulRasheed yana barci na karfin allura baima san da zuwan nasu ba.
Pareto wanda shi yake kula dashi a asibitin kafin isowar ‘yan gidansu, shi ya kawo musu abinci na alfarma daga ‘restaurant’ din asibitin, daga cikin provisions din da aka yiwa Engnr. AbdulRasheed, duk irin abincin da yake so shi asibitin zai bashi, haka wadanda ke tare dashi don kula dashi.
Sai magriba ya farka, yana bude ido a hankali, ya yi tozali da Nenne a gefensa tana sallah, Nennensa, daidai lokacin data sallame sallahr, wani kyakkyawan murmushi Prince ya saki yana fadin,
“welcome my Nenne, saukar yaushe haka babu zato? What a surprise!”
Sannan ya yunkura ya tashi zaune da kyar, ta mike daga kan dardumar ta gyara masa filo a bayansa yadda zaiji dadin jingina sannan taja kujera daidai kansa ta zauna, shikuma ya gaisheta cikin harshen Yoruba. Ita kuma sai ta mayar masa cikin fulatanci, haka sukeyi daman, in sun yi mata tana ji amma bata mayarwa, don har gobe Nenne jefi-jefi take yin yaren mijinta da ‘ya’yanta, tafi rike nata da kyau. Bata son yadda yaranta suka fi yin na Babansu suke kin yin nata, ba kuma don basu iya ba saidon sun fi girmama nasu.
Nenne ta koma kujerar daidai kanshi ta zauna, ta dubi yadda ya sha daurin bandeji waje-waje, hannu da kafa duk karaya, tayi kwafa cikin damuwa da takaici ta ce.
“Isn’t this enough Hammansu? Ni na tabbata yadda ka dauki hawa Dokinnan da muhimmanci bana jin ko aikinka kana maida hankali haka a kansa.
Balle kuma sallah da ibadar Allah, na tabbatar suna wuceka, alhalin kana bisa sabgar Dawakai, wadanda su kadai zasu tserar da dan adam ranar lahira ba wasan tseren Doki ba”.
Sai kuma Nenne ta dakata kadan sannan ta sassauta murya ta koma yin magana wannan karon cikin lallashi da lumana, ganin yadda Prince ke wani irin yamutsa fuska akan zantukanta, baya so take cewa baya ibadah sai hawa Doki.
A ganinsa yana baiwa kowanne lokacinsa yana kokari kwarai wajen kiyaye sallah a duk inda ya samu kansa. In akayi la’akari da irin schedules dinsa. Yana irin nasa kokarin a ganinsa.
“Magana ta domin Allah, Hammansu, ka maida kan ka kamar wani tsuntsu mai tashi sama kan fiffike, yau baka nan gobe baka can duk don hawa Doki?? Ni menene a cikin hawa doki ne? Ka ki tsugunnawa a wuri guda ka fuskanci rayuwa ta reality. Saboda Allah yaushe rabon ka da zuwa aikin Hajj don sauke farali balle umarah da take sunnah?
A tunanina duk wata daukaka, ko suna da kake nema cikin wannan sana’ar ina ganin zuwa yanzu daka mallaki kofunan Zinare sau ba adadi a sanadinta, in ban yi kuskure ba kofunanka sun kai biyar, ko shidda, ina ganin ai ka gama samun daukakar Polo kuma Hammansu.
Ko tunanin aure da aje iyali baka yi wanda shine wajibinka a rayuwa ta hakika kuma mai ma’ana ga dan adam, ba don komai ba sai don saboda hawa doki ne kadai a ranka, ka manta cewa harka fita shekarun kuruciya da jimawa ka shiga na girma, don ma dai bakayi kama da shekarun ka ba; you are still looking fit and healthy”.
Nenne ta kara kwantar da murya yadda dole dan nata ya tausaya mata, tace “Abdulrasheed ko tausayina baka ji, duk faccalolina sun ajiye jikokin ‘ya’yansu maza ni ko daya babu, ba don Taiwo ta bani ba, jikoki ba da saidai kowa ya riga ni tarawa, har wadanda sukazo a bayana, ga maganganun nan marassa dadi da duniya ke yi akan ka suna dawowa kunnenmu, haka ‘yan uwan ubanka suma suke yimin irin tasu tijarar a kanka, suna ganin ni na hana Ubanka kara aure har tsufansa, haka zai mutu da mace daya kamar rai sai kace auren zobe, kai kuma dana haifa mun daure maka gindi kana yawon tambada da lalata a duniya ka ki cika Sunnah, kana gudun aure wanda yake sunnar Annabi SAW.
Ka ki ko tsayawa kayi tunanin ya kamata ace a wannan matakin na rayuwarka kana da yara lafiyayyu har guda uku ko hudu.
Yau dai tunda Doki ya kusa hallaka ka kana ji kana gani, ina ganin ya kamata ka hakura dashi haka Kehinde! Babu sauran alfanu kuma a cikin hawansa”.
Prince AbdulRasheed ya muskuta ya gyara kwanciyar sa cikin jin azabar zafin ciwo irin na hadewar kashi, yace.
“Nenne bana so ko kadan kike sakawa kanki damuwa akan abinda at least kin riga kin san bazan iya bari da sauki ba.
Polo ya zama wani bangare na jikina Nenne, ina yi ne kawai don jin dadina da biyan bukatar sha’awata ga wasan Polo, amma ba don tara kofuna ba, yana debe min kewa yana hanani tunani yana kuma hana ni damuwa da komai, ba don neman wani abu kuma nake Polo ba ko da can balle yanzu da nake da aikin yi kwakkwara, don haka banaso kina damuwa da ance-ance din mutane wadanda basu da gadonka. Su mutane ai al’adarsu ne damuwa da abinda bai shafesu ba.
Abinda ka kwashe rabin shekarun rayuwarka kana yi yana da wuyar bari a dare daya kuma farat daya Nenne. Kimin addu’a, idan inada rabon barin hawa Doki in bari a hankali.
Nenne nifa zan iya ajiye aikina na refinery dungurungum! In rungumi wasan Polo shikadai.
Idan Doki shine ajalina haka Allah ya kaddara min Nenne”.
Yayi dan shiru yana dan haki, na zafi da zogin ciwon karaya, kafin yace “Nenne tun shigowarki bakiyi duba da halin ciwo da nake ciki ba, sannan ko jajen raunin da SAHEEB yaji baki yimin ba kin hau ni da fadan rashin aure anya Nenne?
Ki godewa Allah da ban zarce ba, na barki da ciwon rashina bana rashin aurena ba.
Kimin addu’ar samun sauki da gaggawa kinji Nenne na, ki daina damun kanki akan abinda banida rabo a cikinsa, ki roka min tsahon rai da lafiya mai amfani mu rayu tare, yafi min rayuwa da wata mace, tunda ba wani abun kunya na ke yi a yawon hawa Dokin nawa ba, sha’awa ce kawai, hobby na ne kawai yin wasan Polo.
Amma ba haka kawai rana daya kice lallai in bar abinda nafi so a rayuwata ba, wai don tsautsayi ya gitta min wand aba yau farau ba, kuma mutane suna maganar banza a kaina da ke, ina ruwana da maganar mutane?
Ko an gaya musu inada business da mutane su yabe ni ko su zage ni?
Aure ra’ayi ne, kuma banida ra’ayin yinsa a yanzu, tunda dai auren nan Sunnah ne ba farillah ba”.
Nanne sai ta zama speechless, ta rasa me zata ce masa kuma, duk ta inda tabi don Kehinde ya gane damuwarta da ciwon ranta akan rashin aurensa bazai gane ba, ta yarda kuma babu abinda zai sa AbdulRasheed barin Polo, idan wannan karairayewar da ta sameshi yanzu, basu saka ya barta hakannan ba.
Ta kuma yarda bashi da niyyar yin aure nan kusa, aure baya ransa kwata-kwata, baya cikin burikansa da fatansa na gaba, burinta na samun jikoki daga jikinsa, bata san ranar da Allah zai dubeta ya cika mata shi ba.
Wayar Murjanatu ce ta katse tunanin Nenne, ta boye dan guntun hawayen da ya tsatstsafo mata. Hankalin sa kacokam ya koma kan waya da Aunty Taiwo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login