Showing 39001 words to 42000 words out of 42899 words

Chapter 14 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt

hawayenta ta zubar masa, hakan kuma bai sa ya amsa cewa ya yarda zai yi aure ba. Iyayensa maza ma sunyi iya bakin kokarinsu duk a banza, bai amsa musu da komaiba har gobe, bazata dorawa kanta ciwon da baida magani ba akan abinda bata da maganinsa. Duk da cewa tafi kowa damuwa da al’amarin idan ta tuna yawan shekarun Abdulrasheed na yanzu. Watakila baida rabon auren ne a gidan duniya, in haka ne tana masa fatan samun masu albarka a lahira, ba kowa ke samun rabon aure a rayuwarsa ba, ta yarda da danta dari bisa dari ba lalata ce ta hana shi aure ba. amma mafarkin data ke ta yi a ‘yan kwanakinnan fa?
Don haka Nenne ta taho Gombe ranar wata Lahadi da nufin zata yi kwana uku a gida, ta ga ‘yan uwa da dangi ta kuma gana da dan uwanta Uban kasa da ya kira ta officially, don ta jima rabonta da Gombe, ko bai kirata ba tayi niyyar zuwa a wannan watan.
Nenne na shigowa garin Gombe tana kwance a bayan mota ‘Ford’ direba na sharara gudu da ita, babu wanda ya fado mata a rai sai kawarta ta filin Arfah da Filin Munnah wato Haj. Zainab Yunus.
Don haka ta yunkura tun a cikin motar kafin su isa fadar Gombe, ta dubi direban Uban Kasa daya daukota dake ta aikin sa na tuki tace “tsaya a gefen titi!”, sannan ta ciro wayarta a jaka ta kira layin Haj. Zainab da tayi saving da (Zaynaba mai gaskiya).
Haj. Zainab na dagawa da sallama taji muryar Haj. Sappan Lagos kamar a mafarki, tana fadin “Zaynaba gani a Gombe, maza turomin adireshin ki, in fara tsayawa wajenku yanzu in ga Aisha-Siddiqah kafin na isa cikin gida in kasa samun lokacin sake fitowa kuma”. Ta kara da cewa “ina fatan na sameku lafiya cikin alkhairi keda malam Yunus da diyata Petel Siddiqah?”.
Haj. Zainab cikin ‘yar damuwa take amma kuma taji dadin ji daga Nenne Sappa ta ce “barka da zuwa Haj. Sappa, Jabbama-jabbama da Hajiyar Lagos maraba da isowa gida jewel in the savannah (Gombe kenan) inji ‘yan boko” duk suka yi dariya.
“Sai dai kash! Bama gida, kin ganmu nan a FMC tareda Petel din babu lafiya, asthma dinta ya tashi, tashin da ya jima bai yi irin sa ba.
Ina cikin damuwa da asmar nan tata Haj. Sappa domin Siddiqah itace ‘ya ta goma sha daya dana samu a duniya kafin Allah ya bar min, ban sani ba ko itama a shekarun girma Allah bazai bar min ita ba”.
“Ashsha Zaynaba, daina fadin haka, da yardarm Allah Petel zata ji sauki, kada ki girgiza imaninki akan ciwon ’ya’ya, ciwo ba mutuwa bane kin ji? Diyata Firdausi ma tana da (brittle asthma) haka muke ta fama. Allah zai bata lafiya da yardarSa”.
“Nagode da karfafawa Hajiya Sappa kuma ma dai yau din alhamdulillahi tana warwarewa ba kamar jiya ba, don har ta karbi shayi ta sha sosai”.
Nenne ta ce “to bari kawai in karaso asibitin in sameku can, ai bani ita zakiyi in tafi da ita Lagos kawai ko na sati biyu ne taga likitan Firdausi, tunda an yi hutun makaranta, Dr. Femi ya kware sosai akan treating asthma”. Umman Siddiqah ta kwatanta mata inda zata same su a female ward. Tana fadi aranta “ba inda zata iya bari Petel taje inba cikin dakinta ba, in ka san soyayya ta rabin rai ta Aisha-Siddiqah da Ummanta ne”.
Mintuna ashirin ta kawo su har kofar dakin da Aisha Siddiqah take kwance, sai Nenne ta kira Haj. Zainab ta sanar da ita suna bakin kofa.
Hajiya Zainab ta fito ta yiwa Nenne jagora zuwa cikin dakin har gaban gadon Aisha-Siddiqah. Wanda daki ne na mutum daya (sideroom) a sashen kwanciya na bangaren mata. Nenne ta sa kai a dakin bakita dauke da sallama.
Kallo daya Nenne Sappah ta yiwa “AISHA-SIDDIQAH YUNUS” dake kishingide a gadon marassa lafiya da karin ruwa a hannun ta taji wani bakon yanayi a tare da ita.
Idanun Nenne basu sauka a ko’ina ba sai akan warawaran zinaren dake hannun ta wadanda suka kawata halittar fatar hannunta fara sol. Ga yarinyar ‘yar karama da ita (mai karamin ruwa) wato irin amsu karamin jikin nan ce siririya sosai kamar in ta sunkuya karyewa zata yi. Idanunta kamar na kwan zabo, masu haske da kyau. Nenne tayi birki a gaban gadon Siddiqah ta kama hannunta mara allurar a jiki tana kallonta da murmushi, Siddiqah wadda ke kishingide akan filo, rike da dan littafin addu’o’I na hisnul muslim a hannunta ta daga fararen idanunta a hankali tana kallon Nenne Sappa.
Umma bata lura da yanayin kallon kaunar uwa da Haj. Sappa ta fada akan Siddiqah ba, tana ta faman lale-maraba da Hajiyar Lagos, (jabbama-jabbama), ta bata farar kujerar roba ta ‘yan dubiya don ta zauna amma ina! Hankalin Nenne Sappa ya tafi ga wani tunani daban. Ya bar jikin ta gabadaya.
Domin dai yau ji take a jikin ta ga uwar jikokin ta, wato ga matar Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni, yau Allah ya nuna mata da sauran numfashinta, wadda ta dade tana ganin surarta a cikin mafarki duk ranar data yi istikhara akan sha’anin auren Prince Kehinde.
Ta dade, ta jima tana ganin wannan kyakkyawar fuskar a cikin barcin ta, bata taba sanin alaqar yarinyar da mafarkan istikhararta ba. Taji a ranta bata iya barin Gombe ba tareda Aisha-Siddiqah ba.
Lokacin da Aisha-Siddiqah ta bude baki tana gaida Nenne da sassanyar muryarta ta mai jinya Nenne kasa amasawa tayi, domin Aisha da komai nata ya shiga ran Nenne farat daya (daga gani na farko). Ji tayi kamar ta sace ta kawai ta gudu da ita Ikko, in yaso ta aurawa Prince Abdulrasheed Kehinde. Ta san dai ko zaiki kowacce mace banda wannan kyakkyawar halittar dake gabanta.
Da kyar ta iya amsa gaisuwar Siddiqah da wani kyakkyawan (maternal feeling) akan fuskarta. Kafin su zauna su bude babin hirar Saudiyyah tsakanin Hajiyar Lagos da kawarta Hajiya Zainab irinta wadanda suka aminta da juna, tabbas kawancensu hadin Allah ne kawai, domin ajin rayuwarsu ko kusa ba daya bane. Allah shi yake hada mutum da mutum su kaunaci juna saboda Allah.
Nenne tace da Haj. Zainab ta nema mata iznin Baban Aisha tana so ta tafi da ita Lagos taga likitansu Firdausi, kwararre ne sosai akan lalurar huhu da numfashi, wanda shi yake duba Princess Firdausi (itama asthmatic ce), daga nan tana so Aisha ta karasa hutun wannan zangon a hannun ta.
Hajiya Zainab tayi dan jimmm! Kafin tace “Babanta yana wajen aikinsa amma na san ba zai ki baki Petel ba, don ba tun yau yake da labarinki ba, zan masa bayani idan ya dawo kafin ki gama abinda ya kawo ki Gombe, kwarai nice dai zanyi kewarta, don bama raba gari tun haihuwarta sai da ta fara makaranta a Billiri.
Akwai yaron da ke rikon neman aurenta Ishaqa dan makwabtanmu, yana jami’a a Ibadan, yanada da hakki shima a sanar dashi kafin ku tafi din”.
Nenne tace cikin jin faduwar gaban ta sameta a take “an yi musu baiko ne?” Kafin Haj. Zainab ta bata amsa Nenne ta kira sunan Allah sau ba adadi tana neman daukinsa akan Allah yasa Aisha rabon su ce. Wani ikon Allah sai Haj. Zaina tace “A’ah tukunna, Ishaqa dalibi ne a jami’a, mahaifinsa yace sai ya kammala ya fara aiki koda zai masa aure, suna dai matukar kaunar juna shi da Petel kowa ya sani, sabida shi Aisha bata sauraron kowa.
Gida biyu ne a tsakanin mu dasu, tare suka taso tun suna kanana soyayyar ba ta yau bace, kuma dai Ishaq yana da hankali da nasaba mai kyau, ya dade yana hidima da ita don haka dukkanmu mun yi na’am da shi tuntuni sai fatan Allah ya nuna mana lokacin”.
Aisha na jin su, kunya kamar tayi yaya! Sai ‘yan mutsu-mutsu take kamar tace kasar ta tsage ta shige.
A karshe Haj. Zainab da Haj. Sappa sunyi sallama kan sai jibi zata zo ta gana da Baban Aisha, in ya amince ta wuce da ita Lagos ganin kwararren likitan numfashi da huhu. Da Nenne zata tafi ne ta matsa gaban gadon Siddiqah.
Tana murmushi tasa hannu ta shafa gashin kanta cike da damuwar ganin yadda take ta kokawa da inhaler ita kadai, tace “get well soon my dear, Allah ya baki lafiya kinji ko Siddiqah? Sai na dawo”.
Har bakin mota Haj. Zainab ta raka Nenne. Suka sake kafa sabuwar hira kafin suyi sallama da kyar.
Nenne Sappa ta samu dan uwanta Uban kasar Gombe da iyalinsa lafiya, suka sha hirar zumunci irin wadda suka dade basu sha ba. Kafin ya gaya mata maqasudin abinda yasa shi kiran da yayi mata, wanda dama ta tsammace shi tun ma kafin ta ji shi. Maganar dai guda day ace. Gabadaya danginta da iyayenta da dangin mahaifinsa da nasa mahaifin basu da damuwa yanzu sai ta auren Prince.
“Ki turo AbdulRasheed ya zo ya ga ‘yar uwarsa Naziha, malaman fada sun gayamin idan har ba auren muka yi masa da kanmu ba, a haka zai kare rayuwarsa bazai taba kawo mace yace yana so ba don sunce aljana ta aure shi.
Sannan ance dani akwai aguminsu na maketan Yarbawa makiya Kakansa, akwai kuma sihiri irinna magauta gidansu duk a jikin sa, bazai taba ganin mace yace yana so ya aura ba”.
Nenne tayi ajiyar zuciya cikin damuwa, bata son irin wannan false beliefs din ita sam, gasgata malaman tsubbu da Yayanta Uban kasa ke yi a rayuwarsa yana damunta, ita tafi yarda da cewa auren Abdulrasheed LOKACI ne bai yi ba, kuma koda yayi din, duk da za’a kira shi ‘LATE MARRIAGE’ tofa ba zai wanke masa tarihin cewa ya jima bai yi aure ba, don haka ba kowacce mace zata yarda ya aura ba musamman cikin ‘ya’yan ‘yan uwa don kada abata zumunci in ya jingine musu ‘ya’ya saboda Polo.
Ta rasa abinda zata ce da Uban kasa, a karshe ta samu bakinta yana bashi hakuri, tana fadin ta yi wa AbdulRasheed mata, kuma anan Gombe, sannan cikakkar bafullatana diyar dattijai. In sha Allahu data koma Lagos zata gabatar da maganar ga mahaifinsa.
Uban kasa bai ce a’a ba, duk da yafi matukar son Abdulrasheed yayi aure a cikin gidansa, saidai ya nemi jin su waye iyayen yarinyar data ke ikirarin ta samar masa ta kuma fada masa, yace zai yi bincike akan Malam Yunus din da sana’arsa da gaggawa.
Ba’a kwana ba, ba’a yini ba saida komai na Malam Yunus ma’aikacin hukumar Alhazai tsohon malamin federal government na jihar Gombe ya zo kunnen Uban kasa har asalinsa, duk wata shaidar arziki da kyakkyawar nasaba malam Yunus Hamza da maidakinsa Haj. Zainab Hamza sun gama samun ta a unguwarsu Jeka da fari.
Sunyi waya da Haj. Zainab a ranar da zata wuce Lagos bayan an sallamesu daga FMC cewa tana tafe a hanya zuwa gidan Malam Yunus.
Yau ko fita Abba bai yi ba, yana jiran zuwan Haj. Zainab. Bakuwar da matarsa take ambata da alkhairi kamar tafi kowa kirki da darajta dan adam a duniya.
Nenne ta iso wajejen karfe goma na safe don taredasu ma ta karya kumallo da kunun gyada da kosai mai zafi a falon Haj. Zainab.
Aisha na daki tana ta kumburi, Ummah tace wai zata bi kawarta Lagos tayi hutu kuma taga likita.
Tunda Aisha take a duniya bata taba barin garin Gombe ba, kai ko Azare bata taba shiga ba banda Billiri makaranta, balle akai ga kwana da wani wuri da ba makaranta ko dakin ta ko na Ummanta ba.
Aisha akwai makon UWA, irin yaran nan ne da gasu dai sun girma, amma kamar yaran goye suke agaban iyayensu mata, ko kusa bata son gusawa daga jikin Ummanta.
Amma yanzu maganar zata je tayi sati biyu a Lagos ake yi. Tun jiya da taki hada kayanta Umma da kanta ta hada mata. Tana ta lallashin ta da cewa Haj. Zainab bazata roki alfarma ta kasa yi mata ba. Kuma dai lafiyarta ake son ingantawa.
Budar bakin Aisha sai cewa tayi (cikin alamu na karyewar zuciya da damuwar cewa yau Umma tace zata tafi wani gari ta kwana ba tare da ita ba).
“Amma dai Umma kinsan ba yau na fara ciwona ba ko, wane irin likita ne ban gani ba? Kuma Umma kin dai san Asthma bata da wani magani bayan inhaler ta da wadanda nake sha yanzu ko?”
Umma ta girgiza kai itama ranta a dame da damuwar Aisha tace “babu ciwon da bashi da magani sai tsufa sai mutuwa kinji ko Petel, shi magani dace ne, shin Siddiqah in baki koyi shiga mutane yanzu ba sai yaushe ne?
Ko wajen yan uwana ko na Abban ki ba kya yarda ki je ki kwana, kada ki manta watarana aure ne zai raba mu gabadaya”.
Ai kuwa Aisha ta balle da kuka tana fadin “Umma in kika sake cewa zamu rabu in nayi aure to bazan yi auren ba har abada”.
Umma na dariya tace “to ai Ishaq din bazai yarda ya daukemu mu biyu ba, mun yi yawa a gidan Ishaqa”.
Aisha ta hau rantsuwa, kan cewa sun dade suna kulla alkawari itada Ishaq cewa in yayi kudi ya tashi ginin gida zai ginawa Umma daki a gidan sa, in ba haka ba bazata yi auren ba”.
Umma abin ya bata dariya sosai, da yake lallabata take don ta yarda ta bi Hajiya Sappa sai tace toh ya isa haka ta ji, ta kuma amince ita din itace ‘yar zaman dakin Petel (Siddiqah)”.
Suna daki suna dambarwa ita da Aishah Haj. Zainab na can gaban Malam Yunus a falonsa tana gabatar masa da uzurinta na nemawa tilon dan ta wanda a cewarta ya manyanta auren Aisha-Siddiqah daga mahaifin ta Malam Yunusa Hamza.
Tace masa in ya amince da ta koma Lagos zata sanar da mahaifin Abdulrasheed, cewa tayi masa matar aure a Gombe, ba jimawa iyayen Abdulrasheed maza zasu zo da komai na dukiyar aure, basa bukatar komai, amarya kawai za’a basu su dauka.
Malam Yunus ya hau zufa nan take, sabida kwarjinin da Nenne Sappa tayi masa sai ya kasa cewa kai tsaye bazai bayar ba, yasa habar taguwarsa yana share zufa daga goshin sa daya tuno irin soyayya da shaquwar dake tsakanin Ishaq da Aisha, ya kauda idonsa daga kwarjinin Nenne yana fadin “akwai wanda ke neman aurenta tun tana kankanuwa, amma ban tari hanzarin ki ba inna tambayi cewa shi Abdulrasheed dinne ya ga Aisha yace yana so?
Ko kuwa shi Abdulrasheed ne yace a nemo masa matar aure? Ke kuma hakannan kika ga dacewar zaba masa Aisha-Siddiqarmu?
Nenne Sappa ta saka habar mayafinta tana share hawayen da suka kawo mata a idon ta, ta kwashe labarin su kaf ta baiwa Malam Yunus, da yawan shekarun AbdulRasheed a duniya amma bai taba aure ba.
A karshe ta gaya masa halin tsangwamar da take fuskanta daga dangin mijinta akan rashin auren Prince, kowa ya bude baki laifinta yake gani, sabida mijinta baya son laifinta, da yadda take raba dare bata barci saboda damuwa da addu’ar Allah ya yanke masa, in yana da rabon aure a rayuwarsa Allah ya nuna mata, don ita bata yarda da wai aljana ta aure shi ba, tafi yarda in za’a ce yawan sabgogin Polo da ya saka a gabansa ne suka cire masa tunani da sha’awar aure kwatakwata.
Har mafarkin fuskar Petel data sha yi sai da ta gaya masa a duk ranar data yi istikhara, Malam Yunus ya tausaya ma damuwar da Nenne ke ciki akan dan nata, ya kuma dan tsorata duk da bai gaya mata ba, shima fa yanata mafarkin mutum akan doki a ‘yan kwanakinnan, gashi tace dan nata mai hawa Doki ne.
Nenne Sappa ta katse masa tunani da cewa, “na yarda Ubangiji ya aiko ni Gombe ne wannan karon don lokacin da nake ta addu’ar zuwan sa ya zo ga AbdulRasheed, kada ka juyawa wannan alkhairin da nake nufin mu kulla nida ku baya.
Ka yiwa Allah malam Yunus mu taru mu taimaki juna ta hanyar kulla aure mai albarka tsakanin ‘ya’yanmu. Wanda zai mikar da zumunci na daku har illa ma sha Allahu.
Na amince daku dari bisa dari ba tun yau ba, haka na amince da Siddiqah ce kadai zata zama surukata a cikin duk matan dake garinnan, da wadanda ke garinsu mijina (Ilorin) dama kasar Najeriya gabadaya Siddiqah nake fata da addu’ar ta zame min suruka.
Malam Yunus ya nisa, duk da yayi na’am da komai da Haj. Sappa ke furtawa amma yace tayi hakuri, ba zai yi gaggawar amsawa ba sai yayi shawara da na gaba da shi, kuma sai ya san hakikanin abinda ya hana Abdulrasheed yin aure har zuwa wannan lokacin sannan zai yarda ya bashi Aisha, shima kuma sai idan Ishaq bai tashi aure yanzu ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login