Showing 6001 words to 9000 words out of 42899 words
Chapter 3 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt
wuya.
Hausawa suka ce wai sabo akewa kuka ba mutuwa ba! sabon da yayi da Haseenah shi zai fi wahalar dashi fiyeda soyayyarta, wadda dama tausayi ne jigonta da wasu hujjoji nasu. Don haka ta bar dakinsu Kiki ta soma takawa zuwa dakin ta don kaucema kunnen Bunmi.
Sai da ta zauna a gefen gado ta tattaro nutsuwarta sannan ta sake koro masa tambaya, (wannan karon sounding absolutely serious with seniority domin kuwa da sunansa na yanka ta kira shi, wanda da wuya kaji Taiwo tayi hakan. Itada Kakansu Emir (Kehinde) kawai suke kiransa wato sunan shi na al’ada wato (Hassan).
“I said what’s happening ABDULRASHEED? Tell me! Nace me ya faru? Ko me ke faruwa tsakaninka da baiwar Allah Hasinah haka?”
A shaqare (kamar wanda aka shaqe maganar a makogaronsa AbdulRasheed yace da ita.
“Babu komai! Ki yarda babu komai! Amma ki sani KARYA ce kuma ALADE ce!!!”
“Naji na kuma yarda, amma yanzunnan ta kira ni tana kuka, kuka fa as in screaming any how, tace ka daina daga wayarta yau kwana biyu kenan, kuma kayi mata iyaka da zuwa inda kake…. Kace kada ta kara nuna maka mummunar fuskarta.
Me tayi maka haka da zafi? Bansan yaushe ka koyi wannan halin na saurin yanke hukunci da daukarsa a hannunka ba.
Anya Kehinde, ba zaka dinga hakuri kana sassauta fushinka akan kananan abubuwa ba ga na kasa da kai alhalin kaida ita kuna shirin zama abu daya???
Mu fa mata duk inda muke sunanmu mata, daga lankwasashshen kashin hakarkarin kirjinku aka halicce mu, dole ayita hakuri damu, balle Hasinah da har gobe yarinya ce da bata kai ashirin da biyar ba, kuma marainiya… sannan…. sannan…kasan batada ko….”.
Cikin karaji da nashi screaming din da ya firgita Murja. Wanda ya dame na Haseenah AbdulRasheed ya katse Taiwo, da iyakacin muryarsa yace.
“Maraici nasa mace zama Alade ko dabba mai iya saduwa da shaqiqin mijin da zata aura, saduwar ma irin ta dabbobi? Irin…irin…”. Ya kasa karasawa sakamakon wani makoko da yazo ya tokare a makoshinsa, image din nasu ya kara gilma masa.
“Hasbunallawu wani’imal wakeel”. Inji Taiwo “ko dai ka sha kwaya ne Kehinde?”
Ya rintse ido da karfi. “Don Allah don Annabi daga yau sai yau…. Maman Kiki, na rokeki da darajar iyayenmu, ki manta da mun taba saninta, kada ki kara yi min maganar wata Hasinah daga yau na rufe babinta a rayuwata.
Nenne ta fimu gaskiya, tsintacciyar mage bata mage, matsiyaci matsiyaci ne ko a tandun mai ka saka shi kandas dinsa zai fito ya nuna asalinsa na zina da halinsa na kwadayi, kada ki kara tuna min ita!
I AM PURE AND I LOVE PURITY. Ni dan Sunnah ne cikin Uwa da Ubana, daga tsafta na fito ba najasa a jikina. Ki manta kin taba sanina da wata halitta wai ita Hasinah saboda Dabba ce…. karya ce!
In dai a sanadina kika santa, kike kuma alaqar uwardaki da abota da ita, to daga yau na raba ku nasa almakashi na datse duk wata alaqa tsakanin ku, from thousand milestones.
I hate them, I repeat I hate them!
Har abada bani ba su!!!”.
Murjanatu Taiwo, taji hankalin ta yafi nada matukar tashi, maganganun da yake yi are very dirty. Daga inda ya dauko Hasinah kadai, ya kawo ta kusa dashi, cikin rayuwarsa, zaka shaida girman son sa gareta.
Tabbas ruwa baya tsami a banza inji Murjanatu, kalamansa kadai sun gama bayyana komai duk da cewa indirect ya fadesu.
Taiwo sai nan da nan ta soma kuka don tana tsoron kada yayiwa kansa lahani. Gashi babu kowa a tare da shi a inda yake.
“Abdulrasheed, my Kehinde, I am your only twin sister TAIWO! Gaya min me ya faru daku, ka ji Kehinde dina?
As always, ka sani, zan rufe sirrinka, kuma ni zan fahimceka in karbi uzurinka, koda duk duniya bata fahimceka ba ni zan fahimta, zan kuma kasance a bayanka kamar kodayaushe, koda duk duniya bata bayan ka, be rest assured that your Taiwo will stand by you!”.
Da irin wannan lallashi da ban bakin Taiwo take shawo kan Abdulrasheed, to yau ma da irin sa ta dage don ya gaya mata abinda ya faru tsakaninsa da Hasinah Ambursa exactly, ita da wa yake cewa ya tsane su haka babu ko sakayawa?
Kalamansa dai, da wasu daga na Hasinah sun gama tona komai na kazantar da Hasinah din ta aikata, amma so take ya gaya mata abinda ya faru da bakinsa don tana shakka tana kuma tabaab Hasinan zata iya aikata hakan. Tunda dai a sanin ta da Abdulrasheed baida abokin fada balle masoyiyarsa, matar da yake burin zai aura yana kammala project na masters dinsa wanda Polo ya dauke masa hankali da tun shekaru biyun baya ya kammalashi?
Inda wanda bazai taba boyewa damuwarsa a duniya ba komai girmanta ko muninta to Taiwo ce, abokiyar tagwaitakarsa, his very own twin, his confidant Murjanatu-Taiwo, duk abinda yake ciki a rayuwa ita yake fara fadamawa kafin kowa, komai zafinsa.
Taiwo da Abdulrasheed sunada wani irin (twin bond) ga junansu da ko mahaifiyarsu Nenne Sappa, wani sa’in bata sanin girman sirrin amanar dake tsakaninsu.
Itama kuma Taiwo hakan yake a gareta, Abdulrasheed shine confidant dinta, har sirrinta na mata wanda a matsayinsa na namiji bai kamata ya sani ba, amma Adulrasheed ya san komai na mata akan ‘yar uwarsa Taiwo, kamar lokacin da Taiwo ta samu girma wato lokacin data fara jinin al’ada lokacin suna ‘yan shekaru sha biyu shi ta fara sanarwa cikin tashin hankali da tsoron ko wani mummunar abu ta aikata, Abdulrasheed shi yaje chemist aka hado shi da always pad ba tare da Nenne ta sani ba, sai daga baya ne Nenne ta sani, bayan tuni Murjanatu ta iya kula da kanta da taimakon kaninta, akan Taiwo zai iya batawa da kowa itama haka, in yace kowa yana nufin KOWA!
Itama din kuma haka yake a gareta, idan Taofeeq ya bata mata rai Abdulrasheed kadai take iya kira ta gayawa, domin a wurinsa ne kadai zata samu duk wani lallashi da shawarwari da kwarin guiwa da kuma goyon bayan da duk take nema cikin kowanne yanayi duk da kasancewarsa namiji.
Abdulrasheed ne ya fara sani lokacin da ta samu cikin Hakeem, ko Toufeeq din bai sani ba yana can yawon duniyarsa, saida cikin ya girma. Abdulrasheed shi yayi ta kula da ita har ta haihu don gidanta ya koma da zama yana kaita asibiti da makaranta, don cikinta nata na Hakeem irin mai masifar laulayi ne kamar bazata kai ba, ga miji baya kusa. Taiwo da Kehinde kaunar ‘yan uwantaka sukewa juna irin wadda ba duk ‘yan biyu ba.
A hankali Murjanatu taji numfarfashin Abdulrasheed a kunnenta, wani abu da bazata iya tuna (when last) ta ji shi ba, watakila tun farkon balagar su, lokacin da suna sakandire a kasar Japan idan Dade dinsu (mahaifinsu) ya hana shi hawa Doki ya janye shi daga bargar Dawakan Polo ya rankwasheshi yace ya tafi makaranta.
Haka zai yi ta furzar da numfarfashin bacin rai kamar mai nakuda, don baya iya kuka a rayuwarsa. Wannan numfarfashin (is a replica) na kuka a wurin Prince AbdulRasheed, “her very own Kehinde”.
Don haka lamarin ya daga hankalin Murjanatu fiyeda tsammaninsa.
Kiris ya rage Taiwo ma ta fashe da nata kukan na zallar kaico, da taya dan uwanta bakin ciki da kishi da Allah wadai, he is totally heartbroken a baka da zuci, lokacin da yake yi mata bayanin abinda ya faru dasu kwana biyu da suka wuce tsakanin sa da fiancée dinnasa Hasinah, da dan uwansu cousin dinsu kuma amininsa guda daya a family da ya janyo jikinsa yake amfana dashi wato (Adetokumbo).
Cewa yayi ya gansu suna irin sex din dabbobi akan gadonsa.
“What a betrayal!” Taiwo kanta a karshe (could not control her own tears), ta barsu suka zubo a kundukukinta. Sabida feeling din Prince nata ne. And she feels the pain din har fiye da shi, don ita da hannunta ta rike masa Hasinah ba da sanin maahifiyarsu ba da farko, don sun san bazata amince ba, har sai bayan ta fara nisa sosai da karatun sakandire ma a hannun Murjanatu sannan Nenne ta san da zamanta wurinta.
Zuciyar Murjanatu ta hau tafarfasa. Data tuna wacece Hasinah, da irin gatanta rayuwarta da Abdulrasheed yayi, kirjinta ya hau tururi kamar wuta ake hurawa.
Ta tuna wanene kaninta Prince Abdulrasheed, gatan da yake dashi da girman nasaba da matakin rayuwar da yake kai, amma duk bai duba su ba, sabida halin tawali’unsa irin na Nenne, ya zabi Hasinah a matsayin life-partner din da yake burin mallaka, against the wishes na mahaifiyarsu, ita kuma a matsayinta na mai son duk abinda Kehinde dinta yake so sai ta mara masa baya, ta taya shi son Hasinah a haka da zuciyarta daya.
Yau shekaru biyu kenan da suke ta takun saka da mahaifiyarsu a kan neman yardarta da amincewarta da aurensa da Haseenah, don Nenne ta kafa ta tsare bata boye ba, duk kirki irin nata da yawan taimakonta ga kowa kiri-kiri tace bata yarda Abdulrasheed ya aure ta ba, ba don komai ba sai don NASABA wani abu ce mai girma da muhimmanci a Aure. Amma a wannan lokacin, a wannan gabar, Taiwo ta san Prince support dinta kadai yake nema ba ingiza mai kantu da rura wuta ba.
Idan bata karfafeshi ba yau, waye zai zama karfinsa???
Nenne me zata ce in taji? Banda Allah ya kara? Ta dade tana cewa dasu bata kin Hasinah, amma tsintacciyar mage bata mage. Shi garin banza duk kyawunsa a farau-farau din banza ne.
Abin nufi wato mara tsarkin asali da kyawun nasaba ba duka keda tsarki ba. Shiyasa har gobe ba’a yi auren ba, ake ta jan lokaci. Don neman yarda da albarkar Nenne.
Ashe da rabon zancen Nenne zai tabbata gaskiya tun tana raye kuma tun gabanin cikar alkawarin dake tsakaninshi da Haseenah?
Taiwo ta kara fada a fili cikin girgiza kai “lallai tsintacciyar mage bata mage”. Kuma “Garin banza a farau-farau din banza yake karewa!”.
A tunanin ta Hasinah zata dubi maraicinta da daga darajarta da Abdulrasheed yayi a tsakanin mata tsararrakinta, musamman fiddota da yayi daga gidan marayu na garin Ambursa ya dauketa cikin mutunci ya kaiwa ‘yar uwarsa, ta yi sakandire ta ‘ya’yan gata, kafin daga nan ya kawota kasar Japan, yasa a makaranta, cikin ire-iren marayun da yake ponsoring scholarship dinsu a kasashen waje ba wanda ya kawo jikinsa wato inda yake zaune sai Haseenah, a tunaninta ko wannan ya isa yasa Haseenah ta tsayar da soyayyarta da sha’awarta da hankalinta akan sa shikadai, ta zame masa matar rufin asiri, ba kamar sauran ‘yammatan da ke haukar son shi don wasu kyale-kyale nasa ba, kamar kasancewarsa “basarake” kuma “celebrity”. Sannan gashi “Handsome Yoruba Demon” da shaidanun matan Africa dake kasashen ketare ke rububi don son sheke aya dashi kawai ba.
Ta dauka Hasinah zata barranta kanta daga masu neman soyayya ta watsewa bayan shigarta Jami’a, ta dauka Haseenah zata zama mai kamewa data iyawa maraicinta, ta dauka zata tsaya ga matsayin da Allah ya bata na fiancée din da Abdulrasheed ya yarda zai aura da zuciya daya cikin dimbin matan dake son shi da suka fita gata da kyawun nasaba, ko don kasancewarta musulma kuma bahaushiya, ashe kame kai ba daga yare ko kabila yake ba, saboda kyawun surar dan uwanta ma kadai ya ishi duk wata mace mai lafiya da dogon buri akan samun miji na nunawa sa’a tinkahon duk da zata yi a kan kowanne da namiji.
Taiwo ta zabi su bar maganar nan a tsakaninsu. Suka binneta a ranar, ya zama wani sirri ne da ko iyayensu bazasu iya fadawa ba.
Taji ta tsani Hasinah daga yau, da shima Toks din, wato dan uwansu (Tokumbo) fiye ma da yadda Abdulrasheed ke ikirarin ya tsanesu. Bata taba tsammanin akwai dan akuya cikin zuri’rsu ba sai yau.
Shi ya san cewa (he has someone on his corner), all the time he need (a kowanne lokaci ya bukata), wata wadda zai iya kira (his own person) wato tashi, a duk sanda ya bida, wadda ba kowa bace sai ‘yar uwar tagwaitakarsa “Dr. Murjanatu-Taiwo Akanni”. Kafadar da zai jingina akai yayi kuka ko dariya a lokuta na bacin rai irin wadannan.
***** **** ****
WAIWAYE ADON TAFIYA (2)
(AMBURSA ORPHANAGE)
A
mbursa karamin gari ne a jihar Birnin Kebbi. Prince ya saba da irin wadannan tafiye-tafiyen cikin garuruwa da kauyukan Arewa a duk lokacin da yazo kasarshi ta haihuwa, kasancewar rayuwarshi tafi yawa a yankin Tokyo ta (Japan).
Dabi’arsa ce kaunar marayu, don haka duk inda ya samu labarin akwai gidan marayu ya kan ziyarta, komai nisan garin daga inda yake, baya kasa a gwiwa zai je don kai tallafi. Idan yaje din kuma sai ya zaga ciki ya gansu, ya gaisa dasu, ya shafa kawunnansu, yana mai godewa Allah cikin zuciyarsa dashi yayi masa ni’imar iyaye, masu kykkyawan asali daga tsatso mai albarka, iyayen ma jajirtattu irin ‘Nenne’ da ‘Dade’ da ba duk duniya ake da irin su ba.
Shi ba attajiri bane a lokacin dalibi ne, amma yanada attajirar zuciya, ‘philanthrophy’ musamman ga marayu a cikin jininsu ne na iyaye da kakanni.
Kusan zamu iya cewa ya gaji wannan (positive attitude) din na son marayu da son inganta rayuwarsu ne daga Kakansa. Sarki Akanni mai ran karfe. A zuciyarsa yana tausayin maraya a duk inda ya ganshi, yana kuma jin maraicin da suke ji a ransa, ba don shi din maraya bane.
Yana yawan kwatantawa a ransa inda ace shine su, yake rayuwar da suke yi a kange, babu Nenne da Dade a gefensa, a samansa da kasansa, ko yaya rayuwa zata kasance masa?
Yana kan hanyarsa ta isa gidan marayun Ambursa ne daga Birni Kebbi, inda yaje halartar daurin auren abokin karatunsa Bello Dasuki. Bello D. abokinsa ne tuntuni da sukayi karatun sakandire tare a Japan a lokacin Baban Bello Jakada ne acan, dan asalin Birnin Kebbi. Don haka ne bai ji kiwar yin tattaki tun daga Lagos ya halarci daurin aurensa ba.
Hira ce tayi hira tsakanin shi da Bello Dasuki bayan kammala reception na daurin aure, Dasukin na tsokanarsa da UBAN MARAYU! Inda sabo ya saba da wannan sunan daga bakin Dasukin, tun daga lokacin da ya nemi rakiyarsa zuwa wani gidan marayu a Bauchi. Dasuki yace dashi cikin hira ai kwanannan suma an bude musu sabon gidan marayu a garin iyayensa wato Ambursa.
Zancen ya wuce, kamar bai ji ba ma, suka shiga wata hirar ta abubuwan da suka shafesu na POLO.
Har sukayi sallama da Bello Dasuki zai wuce Airport, inda daga nan zai tashi zuwa gida Lagos, bai gaya masa zai ziyarci gidan marayun nan da ya bashi labari ba. Kawai tunaninsa na alkhairi ya gaya masa akwai bukatar yaje sabon gidan marayunnan ya gani, domin akwai wasu kudade tare dashi masu dan dama da yayi niyyar kaiwa gidan marayu na jihar Gombe, kuma ya tuna bazai samu zuwa Gombe ganin Kakarsa Oummana kafin ya wuce Japan ba lokaci zaya kure masa, tunda kuma daga Birnin Kebbin zuwa Ambursa babu nisa bari kawai ya karasa can, ya basu tallafin sannan su wuce Airport din Sokoto.
Umarni yayiwa direban Bello Dasuki wanda ya dauko shi a motar Dasukin, da ya karkata kan motar ya juya dashi zuwa Ambursa. Ya ce dashi ko basu san wajen ba suyi ta tambaya.
Don haka suka tasarma kauyen Ambursa, kuma koda suka shiga garin basu sha wahalar tambaya ba kasancewarsa kwararren direba kuma dan gari, suka samu sabon gidan marayun, wanda ba’a dade da kafashi a jihar Kebbi ba, sakamakon yawaitar tsintar ‘ya’ya da walagigin marayu a jihar. A saman gidan manyan rubutu ne da shudiyar kala an rubuta AMBURSA ORPHANAGE.
Shugabar gidan marayun Mrs. Taibat ta karbeshi sosai, domin da gani babu tambaya; irin bakin da suke maraba-lale dasu ne, wato ‘ya’yan manyan kasa masu zuciyar taimako. Wato masu kawo tallafin kudi, ko na karatu ko na suttura ko abinci ga yaran, duk da bata san waye shi ba, amma ko daga yanayin tafiyarsa da kasaitarsa da maganarsa tasan dan manya ne,