Showing 12001 words to 15000 words out of 42899 words
Chapter 5 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt
mashahurin so, kamar babu wata mace a fadin duniya bayan ita. Banbancin harshe da yare bai zamo musu barrier ga soyayya ba.
Da fari Nenne ta samu kanta cikin bakunta, kasancewar ta shigo cikin wata kabila da ba tata ba, al’adu da dabi’u sun banbanta, amma gradually tayi hobbasa ta koyi yarensa duk da wahalarsa cikin dan lokaci, shima kuma dama ya iya fulatanci, wannan ne ya taimaka mata sosai wajen zama a cikinsu.
Sai ya zamanto Idris tun daga kanta bai kara marmarin auren kowacce mace ba har zuwa inda yau ke motsi da suka cimma shekarun girma shi da Nenne Sappa, da zaratan tagwayen ‘ya’yansu saiti biyu.
Bayan aurenshi da Sappa da kadan ya samu aiki da wata masana’antar safarar jiragen ruwa a kasar Japan (Japanese shipping authority), sai ya dauketa da karamin ciki ya tafi da ita Japan, ya saka ta a makaranta tayi ilmin zamani mai zurfi a fannin aikin jinya (Nursing) ba don tayi aiki ba sai don ta samu ilmin kula masa da lafiyar yaransu a gida.
Sappa ta fara da haihuwar ‘yan biyu mace da namiji a haihuwarta ta fari. Yaran da al’adar Yoruba ta riga ta basu suna “Taiwo” da “Kehinde” watau Hassana da Hussaini. Taiwo sunan Kakarsu ta wajen uba mai rasuwa taci wato “Olori Murjanatu”, Kehinde kuma kai tsaye ya samu sunan Kakansa Emir (Abdulrasheed) ake kiransa “Prince”, kenan Sarki aka yiwa takwara.
Taiwo da Kehinde sun taso cikin koshin lafiya da samun kulawar iyaye wanda ya haifar musu da saurin girma, saidai kowannensu da irin halinsa da irin dabi’unsa.
Kowa ya shaida Taiwo nada fitina, korafi, da mita tun tana karama, duk wani hali na matan yarbawa Taiwo nada shi musamma daukan tsegumi daga kannenta. Nenne Sappa bata shiri da Taiwo saboda kiriniyarta da wadannan halayen nata, gata da tsokanar yara ‘yan uwanta, Abdulrasheed kuwa gashi dai bas hi da aboki na jiki kamar Taiwo to kwatakwata halinsu ba daya bane, mahaifinsa na kiransa “Prince” Emir kuma yace masa “Kehinde”, a zahiri shi irin yaran nan ne kamammu, salihai, introvert, wadanda magana ma wuya take musu a zahiri saidai suyi action a gani, wato Abdulrasheed lumbu-lumbu ne da ake cema wutar kaikayi saidai yanada temper, babu mai sanin abinda ke zuciyarsa don fuskarsa bata bada expression na abinda yake ransa, wato kwarai ya iya waskewa da shanye expression, Nenne Sappa kadai ke iya karantarsa tana ganewa in abu yayi masa a fuskarsa ko bai masa ba. Babansu da suke kira “DADE” sanda suka fara budar baki shi da Taiwo, yaga yadda Prince yake saka Taiwo kuka ta ruwan sanyi, ba tareda iyayensu sun san me yayi mata ba, ya kance “Prince GREEN SNAKE ne”.
Sun rayu tsayin shekaru kusan goma sha biyar shi da Sappa da ‘ya’yansu na fari a kasar Japan, domin saukar su a Japan da watanni kadan suka haifi ‘Prince Kehinde’ da ‘Princess Taiwo’.
Abdulrasheed ya shiga ran Kakansa matuka, kasancewarsa namiji kuma jika na farko a gareshi, ya zama (favourite jika) ga Kakansa Emir of Ilorin, kuma babban aboki na jiki ga Kakansa Sarki Abdulrasheed.
AbdulRashid (Kehinde) da Murjanatu (Taiwo) sunyi primary da secondary duk a Tokyo/Japan, ba tareda an yi masu kanwa ko kani ba, Taiwo na gama sakandire akayi mata aure da Toufeeq Adam Adebayo, wanda aure ne na (family friends) tsakanin iyayen su, Toufeeq Bayarabe ne dan abokin Engnr. Idrees ne, sun zauna a Ilorin da farko inda ta shiga Unilorin ta fara karatu, Taiwo ta jima tana karatu kafin ta fara haihuwa.
Sau da yawa mahaifin Idris Akanni wato (Emir) yana yin tattaki har Japan in yana son ganawa da babban dan nasa Engnr. Idris Akanni, ko kuma in yana son ganin jikansa mafi soyuwa a ransa wato ‘Prince AdulRasheed’, sai da ya soma tsufa sosai ne ya daina yawon bin Idrisu kasar Japan inda yake zaune, don sauran ‘ya’yansa maza sun kawo karfi, sun taru sun hanashi fita daga Najeriya kwata-kwata, ko don kula da lafiyar sa data fara samun tasgaro da maida hankali ga hakkin talakawansa dake rataye a wuyansa.
Daga baya Idrisu din yayi ritaya daga kamfanin safarar jiragen ruwan da yakewa aiki ya dawo gida Najeriya gabadaya da iyalinsa, amma still yaki zama a Ilorin, don gudun sarautar yake, baida sha’awar sarautar gidansu ko kadan, don ma kada watarana a kwadaita masa ita a matsayinsa na babban Da ga Emir, sai yai nesa da gida Ilorin. Inda ya zabi Jihar Lagos don zama na dindindin tareda iyalinsa bayan barinsa aiki da ‘Japanese Shipping Authority’.
Kowannen su cikin ‘ya’yan Sarkin Ilorin (wadanda duk maza ne) su goma dinnan nada ‘title’ na sarauta da mahaifinsu ya nada musu da hannunsa. Suna kuma rike da ‘chieftaincy’ kala-kala na kasar Ilorin.
Idris Akanni, a matsayinsa na babban Da, yanada ‘title’ na Waziri of Ilorin, sai mai bi masa Abdulyaqeen Akanni shine Turaki of Ilorin, sai Zanan of Ilorin mai binsa. Abdulganiyu Akanni ya biyo Zanan, sai Dan Iyan of Ilorin mai suna Abdulfatahi Akanni, sai Abdullateef Akanni wanda shine GrandMufti of Ilorin, sai Malami Ubandoma wato Abdulrazak Akanni.
Biye dasu sune Madawaki, Tafida da Shettima da Mutawalli of Ilorin, duka kannensu ne dake binsu a haihuwa daga iyaye mata daban-daban guda hudu da sarki ke aure bayan rasuwar Olori Murjanatu wato matarsa ta lelle da suka rayu tare tun yana karatun jami’a, kowanne cikin ‘ya’yan sarkin sunansa ya fara da ‘Abdul’ wane (sunaye dai na manyan musulman Yarbawa).
Wadannan gawurtattun ‘ya’yan na sarkin Ilorin, duk da ba dukkansu ne ciki daya ba zaka samu biyu a daki daya ‘ya’ya biyu ko uku dakinsu daya. Anyi sa’a dattijon mahaifinsu mai tsayuwar daka ne akan hadin kan ‘ya’yansa, ya dade da hade kawunansu wuri guda, duk da ba duka suke ciki daya ba suna kaunar juna da kula da zumuncin da mahaifinsu ya dorasu akai. Haka Idrisu da ya taso a shikadai a dakinsu baida dan uwa na ciki daya a cikinsu basa taba nuna ba uwa daya ta haifesu ba.
‘Ya’yan Sarki su goma maza sun zama tsintsiya madaurinki daya a jihar Ilorin, sunansu ya shahara yayi tambari, kowanne cikin ‘ya’yan Sarki ya rigada ya kama kasa yadda ya kamata, mahaifinsu ya wadatasu da ilmi daidai gwargwado na addini dana zamani, kowannensu yana bin rayuwar da addini ya tsara irin wadda ya zabawa kansa da iyalinsa babu mai shiga rayuwar dan uwansa da sunan hassada, suna kokarin hada kan ‘ya’yanu kuma maza da mata, sannan wasu daga cikin ‘ya’yan Sarkin suna auren mata fiye da daya, basa takurawa junansu da kyashi da ‘yan ubanci don ilmi da wayewa da alfarmomin rayuwa ya wadacesu, sannan babu rikicin gadar sarauta a tsakaninsu sai na competition na rayuwa, wato wannan na son ace ya kere wannan a cigaban rayuwa, musamman da Allah yayiwa tsohonsu tsahon rai, hakan ya rage rikicin neman gadon sarauta a tsakaninsu, sannan babban Yayansu Idrees Akanni da akewa ganin shi zai gaji gidan ya barranta kansa daga Sarautar gidansu kwatakwata, ta hanyar ficewa daga gida zuwa kasar Japan kusan shekaru ashirin acan ya zauna, inda yayi rabin rayuwarsa kacokam, har gobe Sarki Abdurrasheed Abdullateeef Akanni yana nan daram da ransa da lafiyarsa, yana gudanar da sha’anin mulkinsa cikin adalci ga talakawansa yana kuma kara hada kan mazan ‘ya’yansa da jikokinsa maza da mata da kullum suke karuwa.
Mafi yawansu basa Ilorin yanzu, suna rayuwa ne a garuruwa daban daban a cikin kasar Najeriya, duk ayyuka da sana’o’I sun sun raba musu jihohin zama, kadan ne suke a Ilorin kusa da mahaifinsu.
Sannan duk cikinsu, babbansu, wato Engnr. Idrees Akanni, shikadai ne ya taba ficewa daga gida, wato ya bar gida Ilorin tunda kuruciyarsa zuwa ketare ya jima sosai, shi da maidakinsa Hajiya Sappa da ‘ya’yanta ke kira “Nenne”.
Saida Prince AbdulRashid da ‘yar uwarsa Taiwo suka cika shekaru sha tara a duniya, bayan Nenne Sappa da Waziri Idrisu sun fidda rai da sake haihuwa, sannan kuma yaki kara auren kowa bayan Nenne, AbdulRasheed shi ya saka mata suna (Nenne) har sauran kannensu suka kama.
Kwatsam bayan fidda rai da sake haihuwa rana daya sai Allah ya kara baiwa Nenne Sappa haihuwa. Cikin ikon Allah wannan karonma Nenne Sappa ‘yan biyu mata ta sake haifa kyawawa son kowa, daya ta debo kalar dangin mahaifinsu Bayaraben usuli, dayar kuma ta debo kalar Nenne, fulanin usuli, sai suka cakuda, kamar yadda su Kehinde suke masu hasken kala amma bakake ne, amma fa ko kusa ‘yan biyu basu kama kafar Yayyunsu Prince AbdulRasheed da ‘yar uwar haihuwarsa Taiwo a kyau da farin jini gun iyaye da dangi ba.
Sabida sunzo daga baya, bayan an fiddawa Nenne rai da sake haihuwa, su nasu kyawun ina nufin (Taiwo&Kehinde) surki ne na uwa da uba (Fulani da Yorubas); wato uwar da kuma uban suka debo duka suka hada gabadaya, don haka kamanninsu kamar na half-caste (ruwa biyu) suke don kyau da ban sha’awa wato Princess Taiwo da Prince Kehinde.
Ranar suna aka kira jariran Nenne da suna Princess Fatima da Princess Firdausi.
Daga kan ‘yan biyunnan ba’a kara ko batan wata a gidan su AbdulRasheed ba. Har kawo recently, da Princess Fatima da Princess Firdausi sukayi bikin cikar shekarun haihuwarsu ashirin da hudu a duniya a gidan iyayensu dake yankin Banana Island a jihar Lagos.
Princess Fatima da Princess Firdausi sun kammala karatun jami’a a Jami’ar Nsukka, kuma kowacce da zancen aure a kanta wanda za’ayi shekara mai zuwa.
Gidan Engnr. Idris Akanni, yana nan a Banana Island wani bangare na Ikoyi, waje ne da masu arzikin kasar Najeriya da masu sarauta ke buya su zabga gininnuka na hutu da garari, gidaje na gani na fada, su zauna suna cin arzikin da suka tara a ketare ta yaki-halak yaki-haram duk, tareda iyalansu a tsakiyar jihar Lagos.
Banana Island, na nan a offshore din Ikoyi, inda acan aka haifi Princess Firdausi da Princess Fatima
**** **** ****
THE HORSE RIDER
“
PRINCE” Ya taso da azabar son hawa Doki wanda ya budi ido yaga ana yi a gidan Kakansa Emir of Ilorin.
Dadin abun shine, ko muce ludufin da Allah yayima iyayen Prince AbdulRasheed shine; duk sonsa da hawa Doki wanda ya kasance masa ‘hobby’ a tasowarsa, ya kuma zamar masa azababben ‘passion’ na rayuwa tun yana matashi, hakan bai hanashi tsayawa yayi karatun makaranta mai inganci ba.
Ya kai cewa a yanzu ya taka mataki har na digirin digirgir, a fannin injiniyan mai (Petrochemical Engineering).
Duk da haka Polo Sport ya zame masa hobby din da ya kasa bari tun tashen balagarsa.
A can baya Prince yana yin wasan Polo ne (for fun) kadai, a matsayinsa na jinin Sarauta gaba da baya, ba don neman kudi ko neman suna ba, haka ba tareda tsammanin zai kawo mataki irin wanda yake kai a yanzu, a wasan tseren Dawakai ba.
A kan karan-kansa ya san yana yin wasan Polo ne kawai don ransa yana so, yana yi ne don biyan bukatar sha’awarsa ga wasan, da nishadin da yake samu a cikinsa.
Polo ne kadai ke mantar dashi damuwarsa, wanda ya fara koyo tun yana sakandire idan sunzo hutu Ilorin tareda yaran Baffanninsa su Adetokumbo.
Later on in life, ya koma hawa Dawakan turawa da yara sa’anninsa a kasar Japan, wato kafin Dade yayi ritaya.
Sai kuma Allah ya kaddareshi da samun duka abubuwan guda biyu dake cikin nasarar wasan Polo lokacin da ya soma girma, wato ya samu “kudi” ya kuma suna “suna” (wealth and reputation) a sanadin Polo Sport. Wadanda bai shigo wasan Polo domin nemansu ba, amma dare daya ya wayi gari dasu dumu-dumu a harkar Polo.
A sa’ilin da ya cika shekaru talatin ya zama gawurtaccen dan Polo, wato ya zama ‘Polo Legend’ na Africa da Turai, don tun yana da shekaru ashirin da biyar ya fara fita (Polo Tournaments) a manyan kasashen da ake yin Polo a duniya.
Kakansa ne ya fara saya masa Dokinsa na farko, kasancewar shikadai yake mara masa baya akan wannan ‘hobby’ din nasa na Polo, iyayensa duka biyu Uwa da Uba da Kakarsa ta wajen uwa Nani Ummana basa sonsa da Polo, sabida yadda yasa wasan a gaba ya mamaye lokutan rayuwarsa masu muhimmanci gabadaya, suna tunanin Polo ne ya hana shi maida hankali ga wajibinsa (yin aure) a lokacin da ya isa aure. Bayan kuma a wurinsa ba Polo bane, yana da dalilinsa, dalilin da su har yau basu sani ba banda aminiyarsa Taiwo.
A can baya lokacin da mahaifin shi zai kai shi jami’a, sai Prince ya zabi tafiya kasar ‘Argentina’ yace ba inda zai je yin karatu sai acan. Hankalin Uban wato Waziri of Ilorin ya tashi kwarai, yaji tsoron kada ya kaishi can yaki yin karatu sai Polo, don haka ya kafe kan cewa bai yarda ba shima, zai saka shi a gaba ne su koma Lagos yayi acan tunda yayi ritaya a lokacin, kuma ba zai taba yarda Polo ya zame masa sana’a ba, saidai yayi karatun a gabansu, a lokacin basu kai ga dawowa Lagos ba.
AbdulRasheed fafur yaki zabin Dade dinsa, na yin karatu a kusa dasu, ba don komai ba sai don tun a lokacin ya kwadaitu da komawa Argentina, yanada masaniyar cewa kasar Argentina itace kan gaba (lamba daya) a kan wasan Polo a duniya.
Rigima shi da Babansa har gaban Emir Sarki Abdulrasheed. Shikuma kuma Kakannasa Sarkin Ilorin ya bi bayansa, yace akai shi duk inda yake so yayi karatu a duniya, a kuma barshi ya hau Doki son ransa har sai ranar da ya bari don radin kansa.
A bashi freedom ya shiga ko’ina yake so a duniya yayi wasan Polo, da yarda da amincewa da albarkarsa da yawun bakinsa.
Sannan ya zaunar da mahaifin yaron, wato dansa Engnr. Waziri Idrisu Akanni, yana masa nasiha mai shiga jiki irin ta manya inda ya nusar dashi cewa, duk abinda danka ke da ‘giftedness’ a kai, na karatu ko na sana’a ko ‘sport’, kada kayi ‘opposing’ dinsa, indai har ba sabon Allah bane.
Yace dashi da harshen Yoruba “rather encourage him, support him and uplift him on it, baka san inda Allah zai kai shi akai ba, baka tunanin Allah ya sakama Kehinde nasibinsa da baiwarsa a cikin wasan Polo ne? Don haka kada ka tauyeshi akan nasibinsa.
Barshi yayi tayi, shi da kansa watarana in girma ya haushi zai bari, kaidai ka bi shi da addu’ar kariya, fatan nasara da fatan alkhairi”.
Wannan ne yasa Engnr. Edrees Akanni ya kyale AbdulRasheed ya tafi yin degree na farko a kasar Argentina, ya zagaya ya hade karatun da zuwa koyon Polo.
Domin koda ya sauka a makaranta domin yin karatun digiri akan (Petrochemical Engineering) kwas din da mahaifinsa ya zabar masa a jami’a kenan, cikin babban birnin kasar wato ‘Buenos Aires’, tofa duk da cewa yana karatun amma sama-sama, rabin rayuwar Prince Abdulrasheed (Kehinde) a filin tseren Dawaki na kasar wato (Argentina Polo Ground) wanda akafi sani da (Cathedral of Polo), a can yake gudanar da rabin rayuwarsa.
Ya gama first degree a Petroleum Engineering da matsakaicin sakamako (2.2) wanda hakan ya dan faranta ran Dade, sai ya wuce masters a Japan tsayin shekara daya ya dakatar da rubutun masters din na lokaci mai tsaho saboda Polo, kullum yanaso ya gama ko don ya farantawa Dade.
Yadda wasan Polo ya rinjayeshi ne yasa Abulrasheed bai samu kammala masters da wuri ba har ya shiga cikin shekaru na talatin, bayan ya kammala at 33 da kyar da sudin ludayi, sai ya ajiye kwalayen a kasan gado ya rungumi Polo again, baya ko tunanin saurarawa Polo ko makamancin bari, har inda yau ke motsi.
A daidai wannan lokacin fitar sunan AbdulRasheed Idris Akanni a wasan Polo, zamu iya kwatanta shi da hada kafada dana manyan ‘yan wasan Polo na duniya irin su Nacho Figueras, Mariano Aguerre, da Lia Salvo. A kasashen Africa kuma irin su Adolfo Cambiaso na South Africa, Bello Buba na kasar Najeriya, da matashin dan Polo mai tasowa a arewacin Najeriya wato Khalil Halilu, wanda bai kai su shuhura ba.
A shekarun da suka gabata Abdulrasheed ya sha ciyowa Africa kofi a USPA Gold Cup, haka ya ci kofin World Polo Championship, Concacaf Gold Cup, Dubai Gold Cup, U.S Polo Championship, da Cartier Queen’s Cup.
Duka wadanan siraran kofuna suna nan a jere akan makeken tebirin ofishinsa dake cikin (Qatar Petroleum Refinery) a birni mai tashen arziki (Qatar), inda ya samu muhimmin aikin yi irin wanda mahaifinsa yafi na’am dashi.
Har zuwa lokacin cikarsa shekaru arba’in a duniya Prince bai kara sha’awar soyayya ba, bai kara sakawa ransa son yin aure ba, ya tattara maganar aure da mata ya tura su can wani gefe mara amfani na shafin rayuwarsa, ya zamo yana cigaba da playing Polo for fun and pleasure da