Showing 36001 words to 39000 words out of 42899 words

Chapter 13 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt

nasa ba karfine dasu cancan ba. Maigidan nata Malam Yunus, tsohon malamin (federal government) ne da ya jima yana koyarwa a makarantar sakandiren ‘yammata ta Bajoga, shekaru biyu baya Allah ya tarfawa garinsa nono aka dauke shi aiki a Gombe State Pilgrims Board (ma’aikatar alhazai ta jihar Gombe).
Tun daga lokacin ne kuma suka samu damar da duk shekara yake samun kujerar hajji biyu, karkashin hukumar alhazai don su zo su kula da mahajjatan Gombe a Saudi. Shine yake baiwa maidakinnasa.
Da kyar ta samo Hemar ‘yan Lagos, bayan ta ci tafiya da zagaye a cikin Minna har ta gode Allah. Haka Haj. Zainab tayi ta bin fuskokin mata Yarabawa daya bayan daya tana dubawa amma ko mai kama da wannan kyakkyawar dattijiyar bafullatanar bata gani ba, ita gashi ko sunanta bata sani ba balle ta tambaya, amma tabbas ta rike kamannin fuskarta da kyau. Ita gani take ma fuskar na mata yanayi da wata popular fuska data sani ko a hoto ne ko a zahiri, amma ta kasa gane inda ta san fuskar Hajiyar Lagos. (A rashin saninta, fuskar Haj. Sappa na mata yanayin kama ne data Sarkinsu na Gombe, wato Uban Kasar Gombe na wannan lokacin, wanda suke kamar an tsaga kara da Nenne Sappa, don shi ya sha nono ya saki ta kama.
Allah bai tashi hada su ba sai ranar hawan Arfah a kan dutsen ARFAH. Bayan Haj. Zainab ta fidda ran ganin Nenne Sappa don damka mata dukiyarta. Har ta fara tunanin kaiwa hukumar kasar Najeriya ta Saudiyyah kudin tayi musu bayani. Haduwar tasu a filin Arfah ya zo ne indirectly ba tareda zaton kowaccensu ba.
Addu’ar data ji matar bayanta ta daga hannu sama tana yi a fili ne ya ja hankalinta gareta. Hannayenta biyu matar ta daga cikin kaskantar da kai ga Ubangiji da tsananin ikhlasi da tawali’u cikin addu’arta, sannan cikin zubar da hawaye mai yawa a kan dutse mai alfarma na Arfah, ranar da Ubangiji yayi alkawarin baya juyar da addu’ar bayinsa akan wannan tsarkakakken dutse, taji matar tana yin addu’a ga haularta (abinda ta haifa) a fili cikin harshen fulatancin Gombe ziryan.
“Ya Ubangiji ga Dana ABDURRASHEED dan IDRIS ABDURRASHEED (Kehinde), managarcin bawanka mai kyautatawa iyaye da kula dasu, mai tsantseni wajen ibadarka da kulawa ga ‘yan uwasa mata, mai yawan alheri ga danginsa da kyakkyawar zuciya ga kowa, mai tarin halayen kwarai na kyautata zumunci.
Na roke Ka, Ka dubi halin da Kehinde yake ciki na rashin aure. Ya Ubangiji ka yanke masa, kasa yana da rabon yin aure a rayuwarsa, ka kare min shi daga duk wani nau’I na aikin sabon ka a dalilin rashin aure, Ya Allah”.
Ta shafa addu’arta a daidai lokacin da take ji a zuciyarta Allah ya amsa mata, Mala’iku sun ce Ameen Abdurrasheed zai yi aure, kamar yadda Hajiya Zainab dake bayanta ma tace “Ameen” a fili, ta kuma tayata da shafa addu’ar itama zuwa tata fuskar cikin tausayawa, ganin yadda Nenne ke kuka tana addu’ar.
Sai Nenne taji an dafa kafadarta a hankali ta baya, anyi mata sallama cikin nema mata amincin Ubangiji.
Da far’a ta juya ta amsa tana share ido, kuma nan da nan suka gane juna. Suka rungume juna suka sauko daga kan dutsen Arfah tare rike da hannun juna.
Hajiya Zainab ta kwanto lalitarta daga cikin jikinta, ta damkawa Nenne Jakarta hannu da hannu.
“ga nan kudinki ne masu yawa da kika manta nake ta nemanki in baki. A bandakin da muka shiga a Munna kika mantasu, na nemeki kamar ba gobe, har Hemar ku ta ‘yan Lagos naje nemanki Allah baiyi haduwarmu ba, inata addu’a dai da rokon Allah ya hada mu cikin sauki in baki, don in aka shiga Makkah bansan halin da zaki fada wajen sayen abinci ba idan babu guzuri a tare dake, don kamar dukkan guzurinki yana cikin jakar nan.”
Baki Nenne ta saki tana mamaki. Ta tuna zunzurutun dalolin dake cikin jakar. Sai ta kara rike hannun Haj. Zainab gam. Tare suka zauna akan kananun katifunnan na filin Arfah Haj. Sappa ta rasa da bakin da zata godewa wannan baiwar Allah.
Abinda ya bata mamaki shine na farko da ganin matar ba wata wadata ce irin tasu a tareda ita ba, amma ta iya wannan halin na mutanen kwarai, mai wuyar samu a wannan zamanin.
Dala na gugar dala da har dala dubu biyar ne a cikin battar, data kirga suna nan cif yadda ta lankwasasu ta ajiye a cikin zip ko guda daya bata yi ciwon kai ba.
Ashe dama har yanzu akwai mutane masu wadatar zuci da gudun abun duniya irin haka? Nenne Sappa, ta tambayi kanta domin kwarai Haj. Zainab ta burgeta. Kudine da Abdulrasheed Kehinde ya bata domin tayi guzurin aikin Hajjinta dasu kamar yadda ya saba bata duk shekara. Da ta tabbatar ta yar da su taji babu dadi amma bata yi mamaki ba sabida irin gajiyar datayi da tafiya a lokacin a Munna, ji take kamar ta yanke kafafunta bakidaya ta yar, don suma sun mata nauyi da kyar take iya cirasu, balle jakar guzuri.
Nenne da Hajiya Zainab basu rabu ba daga filin arfah ba sai da suka karbi adireshin junansu na hotel din da kowacce take zaune a cikin Makkah.
Bayan sun koma Makkah Nenne ta soma tunanin me zata baiwa wannan matar a matsayin kyauta ta jinjinawa, sabida taji dadin wannan halin kwarai data gwada mata har fiye da kudin data maido mata. Nenne Sappa na matukar son mutum mai tsoron gamuwa da Allah, mai gudun duniya mai cin halal.
Don haka da taje sayawa Princess Fatima warawaran zinaren data bata sautu a kasuwar Jiddah, sai ta sayi wasu warawaran (bracelet) again, sak irin na ‘yan biyunta Firdausi da Fatima wadanda kudinsu mai kima ne da daraja sosai.
Data dawo daga Jiddah shagon zinaren kai tsaye ta wuce gidan ‘yan Gombe wato masaukin ‘yan jihar Gombe a Makkah.
Da yake ta rike lambar dakin da haj. Zainab ta gaya mata, sai ta hau lifta (elevator) ta isa har kofar dakin, ta danna ‘door-bell’ daga ciki akayi mata iznin shiga sannan tasa kai ta shiga dakin da sallama abakinta.
Nan ta tadda Haj. Zainab ita kadai a dakin dawowarta kenan daga Dawafi. Haj. Zainab tana ganinta nan da nan ta shaidata, ta kuwa shiga lale marhabin da hidima da ita da duk abinda take dashi a dakin na sakawa a baka, itace kawo Laban(Al-mara’i) itace kawo ‘Aseer’ wato jus mai sanyi. Kai har Gahwah data koyi sha a kasar ta hada mata wadda ake kira (Gahwah Al-Arabiyyah) ta zuba musu a kananan kofunan karau suka zauna a gefen gadon Haj. Zainab suna sha sai suka balle da hira.
Ko daga yadda Nenne Sappa take magana kadai cikin yanayi na kasaita Haj. Zainab ta alakantata da Sarauta mai girma cikin zuciyarta, in kuma ba sarauta ba to da arzikin da ya zauna a muhallinsa, komai na jikinta kadai dake walwali cikin zobban zinare ya fallasa hakan. Sun dade suna hira kafin Nenne ta ce zata koma hotel dinta, don ta baro autarta Firdausi a daki kwance bata jin dadi tun dawowarsu Arfah a nasu Fundaq (hotel) din. Ta ciro warwaron data zo dasu a cikin battarsu ta damkawa Haj. Zainab a cikin hannunta.
Ta ce kyauta ce tayi mata don su rinka tuna juna in su koma garuruwansu mabanbanta. Tana son mutane masu irin halinta na gaskiya da rikon amana. Sama da komai tsoron abin duniya.
Haj Zainab ta ce “ba’a maida hannun kyauta baya, don hakata gode”. Kuma duk da bata san darajar wadannan warawaran ba, amma ko ba komai aka ce ido ba mudu ba ya san kima.
Tayi godiya mai yawa sosai ga Nenne, tanakokarin gwada warawaran, cikin ‘yar dariyar jin dadin alkhairin da aka yi mata Haj. Zainab tace da Nenne.
“Yo ni wannan ai bazasu shiga hannu na ba, sun min kankanta na yara ne, sai dai in kaiwa PETEL (AISHAH-SIDDIQAH), yafi kama da na ‘yan mata”. Nenne ta ce “har nawa kike da bazakiyi kwalliya da awarwaro ba?” Nan ta daga nata hannun tana nuna mata nata warwaron guda shidda tace “bana rabo dasu a hannayena don su din adon diya mace ne. suna karawa kwalliyar mace kima su da zobuna, wacece Petel-Aisha-Siddiqah kuma? Halan kinada ‘ya budurwa ne kema kamar su Fatima?
‘Yan biyuna (Firdausi da Fatima) na sayawa, shine kema nayi miki sha’awarsu”.
Cike da far’a Haj. Zainab tace “eh, inada Petel-Siddiqah a gida, itama ‘yan biyu ce, su biyu aka haifa tun lokacin Hassanar ta rasu a wurin haihuwa, ita kadai ta saura mana.
Allah ya dora min iftila’in WABI, domin kuwa haihuwata goma amma AISHA-SIDDIQAH ce kadai Allah ya bar mana a raye”.
“Allahu akbar!” Inji Nenne, “lallai dole ki so AISHAH-SIDDIQAH. Har nima yanzu zan tayaki son nata, naji a raina ina son SIDDIQAH. Ajinta nawa yanzun?”
Murmushi sosai Haj. Zainab tayi tace “Petel na ajinta na biyar a makarantar gwamnatin tarayya ta Billiri Gombe”. Sun dade a bakin kofar suna hirar Aishah, kafin Nenne ta karbi lambar wayar Haj. Zainab ta gida Najeriya, da alkawarin duk ranar da Allah yayi mata shigowa Gombe (kasancewar tana yin shekaru kusan biyu bata zo ganin gida ba), zata nemi Haj. Zainab har unguwarsu su gaisa. Kafin dan lokaci kakkarfan kawance ya kullu tsakanin matan biyu a aikin Hajjin bana.
Sati daya bayan nan Alhazai suka soma shirin komawa gida.
Ranar Asabar Nenne da Princess Firdausi suka koma gida Lagos. Yayinda Haj. Zainab jirgin kusan karshe suka bi suka koma gida Gombe don saida aka gama kwashe ‘yan jihar su kaf.
**** **** ****
Tunda Haj Zainab ta koma Gombe Kusan kullum sai ta baiwa Maigidanta Mal. Yunus labarin kawarta mai karamci Hajiya Sappa ta Lagos da suka hadu a Minnah, kawar da tayiwa Petel dinta kyautar warawaran zinare ta yaya zata manta ta?
In ana haddace labarin mutanen kirki Malam Yunus ya dade da haddace wannan labarin na Haj. Sappa daga bakin matarsa. Shima kuma ya yaba da kirkin nata duk da bai ganta ba. Domin ya san matarsa sarai shishshigi gun masu kudi ko dukiya ba halinta bane, sannan ya shaideta kan ita din ba mai kwadayi bace, kuma mai wadatar zuci ce. Allah – Allah take Aisha-Siddiqah wadda take kira (Petel) dinta tazo hutu, ta gwada mata warawarannan da suka fito daga hannun Haj. Sappah, Baban Petel ya tabbatar mata na danyen farin zinare ne (white gold) kirar kasar Saudiyyah.
Ta san Patel da son warwaro, kusan kullum baka raba hannunta da awarwaro, kamar wata ba’indiya haka zata yi ta rawa ita kadai tana juyasu tana kadasu idan tana cikin farin cikin wani abu, an sha ‘seezing’ dinsu a makaranta amma hakan bazai hana gobe ta sake rokon Ummanta ta sai mata wasu ta sake sakawa ba.
Ranar hutun 'yan makaranta Aisha - Siddiqa Yunus, siririyar budurwa ‘yar shekaru goma sha shidda, Aisha mai sassanyan kyau, ma’abociyar yalwar suma (gargasa) a gira da saman idonta, wadda kaurinsu ya fallasa adadin yawan wadda zaka tarar a gashin kanta, da tsakar rana ta dawo gidan su daga Billiri. Motar haya ta biyo yadda ta saba ta dawo gida, ba tareda anje daukota ba.
Data shigo dakin ta wata irin mika Aisha tayi ta gajiya da farin cikin dawawo gida, tana fadin "Oh no place like home!". Sannan ta ajiye jakar goyonta da bacconta ta fada wanka.
Bata samu Ummanta a gida ba ta shiga makwabta gidansu Umman Abdul dubiya, don haka Aisha take ta kissima kome da me Ummanta ta sayo mata daga Saudiyyah a hajjin bana? Ta san dai tsarabarta tafi ta kowa yawa a wurin Umma. Allah dai yasa bata manta da sakonninta na Abaya da dogayen riguna ba.
Umman Siddiqah (yadda ake kiranta a unguwar su ta Jeka da Fari) ta dawo gida gefen la’asar daga dubiyar data shiga a makwabtansu, ta tadda Aisha-Siddiqah ta fito daga wanka kenan har ta saka kayan sallahrta koren jilbaab ta tada sallah. Don haka ta wuce ta hada mata abinci, sannan ta koma dakinta ta janyo jakar tsarabarta ta soma fidda tsarabar Aisha din a gefe. Musamman (bracelet) din wajen Nenne, ta san sai Aisha tafi murna da shi fiye da duk tarkacen abayoyin data kwaso mata.
Aisha na idar da sallah ta ma kasa tsayawa ta shafa addu’a tsabar dokin ganin Umma, sai ta wuce dakin Umma da gudu ta fada jikinta cike da farin cikin dawowarta lafiya, rabon ta da Umma yau wata uku kwarara tun komawarta hutun farkon zango. Lokacin visiting dinsu duk tana Saudiyyah. Umma ta rungume ta itama tana dariya tana fadin.
“Petel am miyelwi ma (Petel dina nayi kewarki)”.
Bada bata lokaci ba ta shiga fiddo warawaran na na wajen Haj. Sappa, guda shidda rus ta shiga zurasu a hannun Aishah daya bayan daya. Kasancewar Petel ‘yar karama mai karamin jiki kuma ‘yar siririya, komai na halittar Siddiqah karami ne, hanci ido da baki, sai suka shige hannun nata sukuf babu gargada, kuma basa zamewa sun zauna cif-cif kamar saida ta gwadasu tun farko.
Rashin kumari irin na Petel yana matukar damun mahaifiyarta, don sam bata da jiki kuma bata da kauri hakanan bata da cika ido, wasu lokutan Aisha bata da kuzari idan Asma dinta ya motsa. Tana da Asma kadan (Mild Asthma), a gida ne ko a makaranta koyaushe baka rabata da inhaler a tare da ita.
Bakin Aisha ya fadada har kunne, don murna, warawaran sun burgeta wadanda bata san ina Ummanta ta samo su ba, ta san dai Umma ko tana da kudin sayensu bazata saye su haka kawai ba, Petel (Siddiqah) ta kasa boye mamakinta da farin cikinta, don ta san ko guzurin Ummanta gabadaya aka hada bazai sayi bracelet dinnan ba, in dai na danyen zinare ne kamar yadda suke zagin idonta. (Bayeraben mutum nada son ajiye kadarar zinare, don haka shine kadara abin ajiyewa a wurin Nenne Sappa da ‘ya’yan ta mata, Taiwo, Firdaus da Fatima).
Aisha-Siddiqah tace da Umma cikin mamaki “Umma ina kika samo awarwaro mai kyau da tsada haka?”
Nan Umma kamar jira take don har zuwa lokacin shaukin haduwarta da Hajiya Sappa da karamcinta na makale a ranta, kullum da tunanin sake haduwa da ita take kwana take tashi, nan ta kwashe labarin haduwarsu da Haj. Sappa a filin Muna ta labartawa Aisha, yadda ta tsinci jakar kudinta da yadda ta maida mata, irin amincin da ya shiga tsakanin su sanadin hakan. Ta ce ta dai lura matar Basarakiya ce ko matar Basarake. Sannan kuma bafullatanar Gombe ce itama.
Aisha ta koyi wasu abubuwa guda biyu cikin labarinnan da Ummanta ta gama bata yanzu, wato “gaskiya da amana su ke sawa a so mutum!” tace a ranta “na shaida Ummana mai gaskiyace, amana da rashin kwadayi halin Umma na ne, nima daga yau zan koye su don kowa ya so ni.
A karshe hirarsu Aisha ta yarda idan ka rike gaskiya, amana da rashin kwadayi suka zama symbol dinka watarana zasu samo maka abinda baka taba zaton samu a rayuwarka ba, da kauna da amincewar mutanen da kake zagaye dasu”.
A yinin ranar bakidaya har dare labarin da suke yi kenan itada Umma wato na Hajiyar Lagos, tsakanin Aisha da Ummanta aka rasa wanda yafi wani dokin son sake haduwa da Nenne Sappa, Aisha ta ji itama tana son matar har cikin ranta duk da kuwa labarin kirkinta kawai Umma ta bata.
Kwanan Aisha-Siddiqah uku da dawowa hutu Asthma dinta ya tashi haikan, tun asali (she’s asthmatic) wato mai fama da ciwon Asthma ce (mild asthma) da sai ta dade bata motsa ba. Wannan karon tashin da yayi yafi karfin a kwantar dashi da (inhaler) dinta don a karshe har sai da ta kai su ga kwanciya hajaran majaran a babban asibitin Gombe wato (FMC Gombe) ake ta treating Aisha.
**** **** ****
Maimartaba Uban Kasar Gombe wato Yayan Nenne (Sarkin Gombe na lokacin) ya aika mata sammacin kira yana son ganawa da ita a gida Gombe, ido da ido, ba maganar waya bace. A ganin Uban kasa har da daurin gindinta a rashin auren da Prince Abdulrasheed ya ki yi har shekarun kuruciya suka fice masa, domin in tayi masa umarni a matsayin ta na uwa in har yana son albarka dole yayi ko yana so ko baya so. Ya gaji da maganganu akan Abdulrasheed, ko’ina ka shiga sunan Abdulrasheed Idrees Akanni ne a bakin samari ‘yan bana bakwai a kasar Najeriya, har wani lakabi suke binsa da shi “The Latest Yoruba Demon (Prince). Ita kuwa Nenne ta fannin ta Allah ya gani bata san ya zata yi da Abdulrasheed ba kuma, tunda har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login