Showing 21001 words to 24000 words out of 42899 words

Chapter 8 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt

da shi bin Allah, kaunar musulunci da kiyaye sallah, ko yana dauka ko baya dauka ita dai Nenne bata fasawa kuma bata fasa yi masa addu’a ta musaman a duk inda yake cikin duniya Allah ya kare mata shi daga rudin zamani dana kuruciya, kasancewarsa namiji daya tal a cikin mata uku da Allah ya bata.
A yadda Hajiya Sappa take rayuwa cikin yawan ibadah kullum, da kula da bautar aure da mijinta uban ‘ya’yanta, kai sai kayi tsammanin ita din wata waliyya ce. Shigarta kullum cikin hijabai (jilbabs) kala-kala kamar bata da alaqa da kowacce sarauta.
Duk shekara Hajj da umarah basa wuce Nenne Sappah, bata azumin Ramadhan a gidanta dake Lagos sai a birnin Makkah da Madinah duk shekara, wani abun burgewa da Nenne in zata je Hajji bata bin International saidai Pilgrims duk cikin halinta na (down to earthiness) da kaskantar da kai, wanda take bi duk shekara daga hukumar alhazai ta jihar Lagos zuwa Saudiyyah.
Shekarun Nenne Sappa a halin yanzu sun kai kusan sittin da biyar a duniya. Yayin da mahaifiyarta Nani tayi tsufa mai inganci saboda ibadah, har yanzu cikin koshin lafiya Nani Oummana take rayuwa a Gombe da jinta da kuma ganinta garau.
Tun Nene Sappa nada shekaru akalla sha biyar take gidan aure, kamar yadda na fada a baya mahaifinta Uban Kasar Gombe Ahmadu Umar Jallo, ya bada aurenta da hannunsa ga dan abokinsa kuma babban amininsa wanda ya kasance Bayeraben Ilorin (dan kabilar Yoruba).
Saida Prince AbdulRashid ya cika shekaru ashirin a duniya, bayan Nenne Sappa da Waziri Idrisu sun fidda rai da sake haihuwa, sannan kuma yaki kara auren kowa saboda son da yake ma Nennen Prince Hajiya Sappa, AbdulRasheed shi ya saka mata suna (Nenne). Kwatsam bayan fidda rai rana daya sai Allah ya kara baiwa Nenne Sappa haihuwa. Cikin ikon Allah wannan karon Nenne Sappa ‘yan biyu mata ta haifa kyawawa son kowa fara da baka, wato daya ta debo kalar dangin mahaifinsu Bayeraben usuli, dayar kuma ta debo Nenne, amma fa ko kusa ‘yan biyu basu kama kafar Yayansu Prince AbdulRasheed a kyau da farin jini gun iyaye da dangi ba, sabida shi nasa kyawun surki ne na ruwa biyu; wato duk uwar da kuma uban ya debo ya hada, don haka kamanninsa kamar na half-caste (ruwa biyu) suke. Aka kira su Princess Fatima da Princess Firdausi (Princess na nufin Gimbiya da harshen hausa).
Daga kan ‘yan biyunnan ba’a kara ko batan wata a gidan su AbdulRasheed ba. Har kawo recently, da Princess Fatima da Princess Firdausi sukayi bikin cikar shekarun haihuwarsu ashirin da hudu a duniya a gidan iyayensu dake yankin Banana Island a jihar Lagos.
Daga Princess Fatima har Princess Firdausi sun kammala karatun jami’a a Jami’ar Nsukka, kuma kowacce da zancen aurenta a kanta.
Gidan Engnr. Idris Akanni, yana nan a Banana Island wani bangare na (offshore) din Ikoyi, waje ne da masu arzikin kasar Najeriya da masu sarauta ke buya su zabga gininnuka na gidaje, su zauna suna cikin arzikin da suka tara ta yaki-halak yaki-haram tareda iyalansu tsakiyar a jihar Lagos. Banana Island, na nan a Ikoyi, inda acan aka haifi ‘yan biyun; Princess Firdausi da Princess Fatima.
**** **** ****
BAYAN SHEKARU GOMA SHA HUDU
Y
a zama cewa a halin yanzu Engnr. AbdulRasheed (Prince) ya cika shekaru 44 na rayuwarsa, shekaru ne da suka zo suka wuce kamar kiftawar ido cikin tarin nasarori masu dimbin yawa da budi da falala a gareshi da bazasu lissafu ba. Wace duniya Haseenah take bai sani ba, don bayan kammala Masters dinsa sai ya bar Japan kwatakwata. Ya koma Argentina yayi PhD a jami’ar da ayayi karatun digiri na farko. Daga baya ya koma Qatar inda ya samu aiki da ‘Qatar Refinery’.
Bayan wancan incidence din da ya faru dashi shekaru goma sha hudu a baya still yana nan akan ra’ayinsa na tafiyar da rayuwarsa yadda yake yinta ba tare da tunanin aje iyali ba, sannan ba wani aikin ashsha ne a gabansa ba sabida hardly Prince ya zauna baya komai in ba lokacin barci ba, bashi ma da lokacin kansa kona tunanin abinda ya dace a gareshi don koyaushe baka raba shi da yawon fita tournaments kasashen duniya da ake ji da wasan Polo.
Polo a kasashen da ta karbu babbar sana’a ce mai matukar farin jini kuma ta manyan ‘ya’ya, Prince Abdulrasheed ya samu duk abinda ake nema a cikin Polo zuwa yanzu saura taki daya ya rage masa.
Polo na jika shi yadda ba’a zato har fiye da aikinsa na matatar mai, domin yana cigaba da dauko kofin zinare a yawancin tournaments dinsa, sunansa da shararsa na kara harbawa yana shawagi a sararin samaniyar duniyar wasan Polo na duniya.
Saidai kuma duk dan adam mai lafiya ai baka raba shi da feelings. Ya yarda shi dan adam ne ajizi kamar kowa, amma kuma mai iya controlling feelings dinsa, by making himself always busy da harkar Dawakansa a cikin gida, da aikinsa na matatar man fetur idan yana birnin Qatar, da kuma tseren doki idan ya fita tournaments sauran kasashe. Yafi rayuwarsa a kasar Argentina inda acan yafi yin wasan Polo, kasar data zame masa uwardaki bayan kasar haihuwarsa, Argentina.
A yau tana zaune a ranch house dinsa cikin wata kujera sakar kaba ta hannu, yana kallon ingarman dokinsa da ya kira da suna ‘SEHEEB` wato ‘ABOKI’ daga can nesa dashi.
A tsaya fadin cewa Dokinsa Saheeb mai muhimmanci ne da tsohon tarihi a cikin rayuwarsa bata baki ne, kasancewar shine dokin da ya fara mallaka a rayuwarsa, kuma wanda yafi so cikin duka sababbin Dawakansa.
Dokin na cin korran ciyayin da suka mamaye gidan daga korran shuke-shuke masu ban sha’awa da kayatar da idanun wanda duk ya kusanto su. Daga can gefe yana iya hangen duk wani motsi na hadiminsa Pareto wanda ya dukufa aiki, saurayin dake kula masa da Doki Saheeb da sauran Dawakan dake cikin stable din gidansa.
Saurayin yana rage tsayin ciyayin gidan ne da inji, yana daidaita tsayinsu da cutlass, yadda zasu fi bada sha’awa. Sannan yana kwashe kashin Doki a abin shara na musamman.
A sa’ilin ba komai Prince Abdulrasheed ke yi ba sai kurbar sassanyar ruwan Inibi a tambulan na glass mai garai-garai, yana cikin tunanin yadda tournament dinsa na gobe zai kasance. Wani wasan tseren Doki ne wanda ya jima yana jiran zuwan lokacinsa, da yi masa kyakkyawan shiri.
Ba don komai ba sai don kasancewar wasa ne da zai gama daga darajar sa a duniyar wasan tseren Doki, da shahararsa a Polo a kasar da yake yiwa Polo tana biyansa (Argentina). A wannan wasan ne yake saka ran kaiwa sauran taki kadan din daya rage masa…. In Allah yasa yayi nasara, zai samu ya kai matakin karshe na kwarewa a wasan Polo da ya dade yana harin kaiwa wato (10+ goal Polo Handicap).
Shi kansa Saheeb kamar ya san shirin da ubangidansa keyi akan fitarsu ta gobe, da burinsa akan tournament din gobe, don haka in ka ganshi sai kayi mamakin yadda yake annashuwa, sai harbin iska yake da haniniya cikin sabo da yanayin da koshin lafiya a tare dashi.
Hausawa suka ce wai rana bata karya saidai uwar diya ta ji kunya, kome aka sawa rana cikin yardar Allah zai iso kamar kiftawar ido, gobe ne wannan ranar da Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni ke ta dakon zuwanta wadda yake yiwa wannan babban shirin da kyakkyawan fatan, wato ranar tseren Dawaki na duniya da Argentina ta shirya tsakaninta da sauran kasashen Polo na duniya.
Amma shin ba masu azancin magana ta tsinkaye sunce mafarkai kamar dan da ba’a haifa bane? Wani a haife shi a raye, wani kuwa a mace ake haifarsa.
Ba kowanne fata, ba kowanne buri ne yake tabbatuwa a lokacin da mukeso, ko muka tsara yuwuwar tabbatuwarsa ba! Sai lokacin da Allah ya so, ko ya ga damar tabbatuwarsa.
**** **** ****
RANAR GASAR KOFIN TSEREN DAWAKI NA DUNIYA A KASAR AJANTINA (ARGENTINIAN INTERNATIONAL OPEN POLO TOURNAMENT)
S
ahu biyu ne na mahaya Dawakai zaka iya hange, suna masu kallon juna sashe-sashe sun jeru reras akan layi. Duka Dawakai goma ne a kawanne sahu, nashi dokin yana tsakiyar sahun farko, Dawakan sun tsaya car da kafafuwansu, suna kartar kasa da kofatonsu gwanin ban sha’awa cikin koshin lafiya sai faman ragaji da harbin iska suke tsabar koshi, sai sheki suke kamar zasu fashe sabida tsaftar da suke samu, ‘Polo Riders’ din (mahayan) sun yi irin tsayuwar nan ta jiran umarni daga ‘umpire’ bisa ingarmomin Dawakan tseren Doki na musamman wadanda ake kira (Polo Horses).
Dawakan duka murdaddu ne kuma kosassu, sannan dogaye sambal, kalolinsu sun hada da farare, bakake da ruwan kasa, ga gashi yala-yala a kansu, da ka gansu kaga lafiyayyun Dawakai rainon gidan gona saboda koshinsu da cikar tsokar naman jikkunansu.
Wadannan Dawakai ana rainonsu ne musamman don wasan tseren doki (Polo Tournament) na kwatankwacin irin wannan da ake yi yau, ko kuma don mallakar manyan Sarakuna da masu kudin gaske, dake da sha’awar wasan tseren Doki a matsayin ‘hobby’ dinsu ko ‘sport’ dinsu.
Irin wadannan Dawakan zaka samu ba’a ko’ina ake kiwata su ba, kuma ba’a sayar dasu a ko’ina kamar yadda ake sayar da sauran normal Dawakai na kasar Hausa. Su din Dawakai ne na musamman, da sai a wannan babbar kasa kuma hamshakiya a sha’anin wasan Polo (Argentina) kadai ake kiwata su, wadda sanin kowa ne ta shahara fiyeda kowacce kasa a duniya in dai akan sha’anin wasan Polo ne, wato birnin Buenos Aires (Capital of Argentina).
Ana kiran wadannan Dawakan da suna;
‘Thoroughbred Argentinian Horses’.
Gabadaya mahayan nan suna sanye da kaya iri daya, wanda ya zame musu (uniform) na wasan tseren dawaki wato; fararen riguna masu kwala da farin wando (Polo t-shirts and white Trousers).
Kamar yadda na fada a sama ‘team’ din mahaya Dawakan guda biyu ne, sukayi sahu-sahu suna masu fuskantar juna cikin jiran a kada kararrawa, su fara.
Kawunansu sanye da ‘polo helmets’ wadda itama fara ce kal da ratsin shudi kamar kalar kayan jikin su. Yayinda kafafunsu ke sunke cikin fararen takalmannan tsadaddu da ake kira ‘Brogues’ da 'Chukka boots' da kuma ‘loafers’.
Umarnin ‘umpire’ kawai suke jira ya kada kararrawar bada umarnin farawa, su kuma su fafari dawakansu ta hanyar baiwa Dawakan umarnin tafiya, wato daga nan za’a fara ‘match’ din.
‘Umpire’ (mai bada umarni/alkalin wasa) ya duba lokaci a agogonsa, yaga lallai lokacin da aka saka domin farawa ya cika, karfe hudu na yamma ta cika daidai (agogon kasar Argentina).
Sai kawai ya kada kararrawa… and the match begins marvellously (wasan ya fara da matukar ban sha’awa, da burge idanun dubban masu kallo matuka gaya), masu gani physically cikin ‘yan kallo da masu gani virtually.
Abin takaici Dokin kowa ya tafi, amma nasa Dokin bai ko motsa ba, sai ya tsaya yana kartar kasa cikin ‘yan mutsu-mutsu da alamu na kin son tafiya, babu gaira babu dalili kuma, hasali ma dai Doki Saheeb bai taba yin irin haka ga ubangidansa ba tunda ya mallakeshi.
Wanda hakan ya bashi mamaki, at the same time ya kuma fusata shi matuka. Da kakkausar muryarsa ta ‘yan Polo, wadda ta fito very harsh and unpleasant (raspy voice) yace da dokin nasa;
“SAHEEB!!!”
Saheeb din yayi haniniya cikin amsawa, amma bai tafi ba. Ya kara cewa da sauti mai karfi fiyeda na farko “SAHEEB, Go!”. Wanda hakan ya zama fusataccen umarni na biyu ga Dokin da aka kira da suna “SAHEEB” abinda bai taba faruwa ga Dokin ba (ubangidansa yayi masa umarni sau biyu). Shi kansa dokin sai ya rikice. (Thoroughbred Horse) ne wato haihuwar Argentina kuma acan aka raine shi har ya girma, mamallakin nasa ya kwashe shekaru yana kiwata shi cikin gata da kula da lafiyarsa da tsaftar jikinsa da akaifarsa, kasancewarsa (favourite horse) dinsa cikin duka Dawakan da ya mallaka a (stable) din dake Ranch House dinsa (wajen kiwon Dawakai a jere cikin gidan gona).
Ba Saheeb ne kadai Dokinsa ba, Dawakan hawansa sun kai shida, amma shine na gaban goshinsa, babu mai ganin soyayya da gatan da Saheeb ke samu.
A ka’ida duk bayan shekaru biyu sai ya sake lafiyayyen Doki, amma shi wannan da ya kira “Saheeb” abokinsa ne da bai taba sake shi ba, kula yake da shi kamar dan cikinsa, kasacewar ya fito daga hannun daraja, wato hannun Kakansa da yake matukar so (dattijo mai ran karfe), tun lokacin da Kakan nasa yayi masa kyautar sa har kawo yau yake son Dokin sosai.
Kakansa ya saya masa Dokin ne a wani zuwa da yayi musamman har kasar Argentina da kansa, don ganewa idonsa yadda babban jikan nasa yake gudanar da wasan nasa na Polo, a lokacin gasar ‘World Polo Championship’, wanda shima an gudanar dashi ne anan kasar Argentina. Haka yake bata lokacinsa da aljihunsa wajen kula dashi da lafiyarsa, kamar yadda yake kula da tasa lafiyar.
Abincin da ake masa cusa dashi daban dana sauran Dawakai ‘yan uwansa, haka yanada kwararren Vetrenary Doctor dinsa (likitan dabbobi), wurin kwanan Saheeb na musamman ne cikin duka Dawakansa.
Saheeb yana kwana ne a cikin korran ciyayi masu taushi (pitch grass) dake cikin (stable) dinsa.
Mai kula da taje gashinsa da rage shi da gyara shi da yankan kumbarsa zaman Dokin yake a gidansa dindindin, ma’aikaci ne specialist akan raino da kula da Dawakai yake zaman albashi domin kula da Doki “SAHEEB” a (ranch house) din mamallakinsa shine Pareto.
Albashi na musamman Pareto yake lamushewa daga aljihun maigidansa don kula da hamshakin Dokin nan nasa (Saheeb).
Shi wannan saurayin Ba’ajantine (Pareto) wani kwararren ‘Horse Breeder’ ne, wanda yayi karatunsa da kwarewa musamman akan kiwon Dawakai da kula dasu.
**** **** ****
Umarni na biyu wanda ya fito cikin matukar fusata daga Ubangidansa, da dukan da yayi masa da sandar Polon dake hannunsa (polo mallet), shi ya sanya Doki SAHEEB yin fitar kibiya don bin umarnin ubangidansa, ya daddage ya taka a guje, yabi bayan sauran Dawakan har nan da nan kamar kiftawar ido ya cimmasu.
Daganan mahayan suka saki ragamar Dawakan a guje, da wani irin gudu mai gigitarwa. ‘Helmet’ din dake kan kowannensu, wadda ta rufe rabin fuskokinsu ta bar rabi a waje, shi zai sa ka gane cewa Abdulrasheed (Kehinde) shikadai ne bakar fata dan Africa a cikin su, kuma dan kasarmu ta “Najeriya” mai wakiltar hadakar kasashen Africa ta yamma a ‘tournament’ din.
Baka jin komai na tashi daga bangaren ‘yan kallo (sashen ‘yan Africa) sai ‘applause’ na kiran sunansa da fito da usur, cikin ambaton “…. PRINCE!!! PRINCE! PRINCE!” Suna masu daga masa hannu cikin tarin kauna da bada karfin guiwa…. As he started to lead the match now…. wato ya zamo shine akan gaba, dokinsa ya yiwa sauran fintinkau, duk da kasancewar dokinsa yayi jinkiri da farko, amma daga bisani dokin gudu yake baya ko sassautawa kamar ma ya fita a hayyacinsa sabida sabo da yayi jinkiri, gudu kawai SAHEEB yake zubawa kamar zai tashi sama dashi, har shi da kansa ya sha jinin jikinsa cewa gudun da Saheeb yake yi yau ya zarta kima.
Gab da zasu isa ‘goal’ ne mummunan tsautsayin mara dadin ji da gani mai muni sosai ya afku.
Taki kadan kafin isar su ga ‘goal’, PRINCE ya fado kasa daga dokinsa ji kake timmm! Sakamakon faduwar bazata da dokin nasa Saheeb yayi, alhalin yana gab da isa ‘goal’.
Nan da nan hankula suka tashi, ‘yan kallo suka mike tsaye cikin alhini, Alkalan gasa ma haka suka dakata, aka kawo gado nan da nan aka dauke shi daga wajen zuwa asibiti, bayan an fara bashi duk wani taimakon gaggawa tun a hanya kafin a isa asibitin dashi.
Karo na sau ba adadi da faduwarsa a Doki, a duka tarihin hawa dokinsa tun na kuruciya, bai taba faduwa yaji rauni irin na wannan karon ba, Saheeb ya raunata shi sosai, bayan kwashe kusan shekaru masa dan dama yana wasan Polo dashi a wurare daban daban cikin kasar Argentina.
Duk da bashi kadai yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login