Showing 15001 words to 18000 words out of 42899 words

Chapter 6 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt

kuma debe kewa kadai. Amma aikin da ya samu da (Qatar Petroleum Refinery) bayan kammala PhD dinsa akan (Oil and Gas Engineering) yasa dole ya bar kasar Polo ta Argentina ya tare a Qatar, sabida aikin refinery yafi cinye lokacinsa yanzu fiyeda wasan Polo.
A halin yanzu da yake da shekaru arba’in da biyu a duniya, Engnr. AbdulRasheed Idris Akanni, zamu iya cewa ya gama accomplishing komai na daukakar aiki akan Oil and Gas, tunda yana kan matsayin ‘Star Engineer’ na ‘Qatar Refinery’, AbdulRasheed ya gama cika duk wasu burika na rayuwarsa, saura kaiwa makura a gasar Polo wato (10+ goal handicap).
Kudi yake samu kawai daga kasashe daban-daban ta harkar Polo da kuma aikinsa, har bai san abinda zai yi dasu ba, babu Da, ba jika, balle matar da zata taya shi mora (babban tashin hankalin iyayensa kenan). Don haka AbdulRasheed ya himmatu wajen aikin alkhairi ga ‘yan uwansa mata guda uku musamman Taiwo, ya tsaya musu, ya tsayawa cigabansu, baya barin iyayensu su yi musu hidimar komai ta karatu kota yau da kullum, balle mijin Taiwo da yake da kankamo sai ya zamanto komai nata shine, har ila yau yana raba arzikinsa da iyaye da ‘yan uwansa na Uwa dana Uba (duk da kasancewarsu ba mabukata ba). A gefe kuma a boye, Prince Abdulrasheed ya dage wajen tallafawa gidajen marayu dana gajiyayyu a kasarshi Najeriya inda a irin haka ya samo HASEENAH.
A halin da ake ciki yanzu (he mainly consults for the refinery) fiye da zama a ofis yayi aiki. Don haka ne yake samun lokacin da yake fita ‘tournaments’ kadan-kadan, to really play his passion which is ‘Polo’. Amma dai rayuwarsa yanzu tafi yawa a birnin Qatar.
Wannan shine tarihinsu Prince AbdulRasheed da iyayensa, ‘yan uwansa, da komai da ya shafi rayuwarsa ta yau da kullum, rayuwar da kowa yake kallo masa a matsayin ‘incomplete’ wato wadda ba cikakkiya ba, mai wawakeken gibi, duk da tarin achievements din da ya cikata, da tarin arzikin dake cikinta musamman mahaifiyarsa, Kakarsa da mahaifinsa da ‘yan uwan haihuwarsa gabadaya suke cikin damuwa da rashin cikarta, domin kuwa har zuwa wannan lokacin da ya tasamma shiga shekaru 43 ba wanda ya san dalilin sa na kin yin aure ko yin budurwa in ka cire Murjanatu.
Wanda ya zamo na jikinsa sosai ne kadai zai iya gane cewa, duka lokutansa na yanzu ya mallakawa wasan ‘POLO’ ne, da kuma aikinsa na matatar man fetur, sannan Prince yana ibadah musamman ta yawan azumi a gidansa, ba abinda duniya ke zarginsa dashi ne a gabansa ba.
**** **** ****

HEARTBREAK
K
wanaki uku kenan da yin wayarsa da ‘yar uwarsa Murjanatu. Kwatanta halin da Abdulrasheed yake ciki a kwanaki ukunnan bazai yuwu ba, he is frustrated and heartbroken, kasancewar babu kowa a tare dashi shikadai ne a gidansa sai mai yi masa hidimar share-share da goge-goge da girkin abinci, daga shi sai zuciya da kwakwalwarsa suke aiki a kwanaki ukunnan, don haka suka taru suke ta kitsa masa duk abinda suka ga dama akan mata da al’amarinsu. Mai kyau da maras kyau. Shaidan ma yana taka rawarsa wajen gaya masa mata duka mazinata ne ya fita harkarsu. Babu wata soyayyar gaskiya in existence. Hakan yasa tunaninsa mafi rinjaye duk ya gurbace akan diya mace.
Abdulrasheed ya kullaci mata da soyayyarsu kowace iri ce, ta aure kota watsewa duk ya barranta kansa daga ciki, daga yau ya nesanta kansa da kowacce iri. Ya tsani taimako, duk da in tunanin hakan yazo masa yana cewa (astagfirullah). Ya zo ya tsani yarda da duk wata mace. Shaidan ya cigaba da ribatar sa yana gaya masa ai duk mata irin Hasinah ne marasa godiya, maciya amanar kauna, kuma marasa tsarki na jiki dana zuciya.
Saboda shi mahaifiyarsa ta dade tana cusa masa wani irin tsoron zina, tun sanda ya fara balaga, ta taso dashi da upbringing mai kyau cikin hikima da lallami take cusa masa kin zina, sau tari tana yawan gaya masa cewa ko mata nawa yake so kuma ko ‘ya’yan wa yake so a sarauta da arziki, haka kona talakawa ne yakeso zasu aura masa indai akwai nagarta da kykkyawar nasaba.
Amma ya taimaki kansa da su kada ya kusanci zina a rayuwarsa, sabida ita zina bashi ce wato dattinta naso yake yi a cikin zurri’a, da wannan belief din ya girma a ransa, duk da Haseenah taso ta wargaza wannan tufkar da Nenne ta dade tana yi a zuwanta Japan.
Amma yau Hasinah tasa abin ya shafi har mu’amalarshi da kowa, don gani yake duk ‘yan uwansa na wajen Uba ma irin Tokumbo ne wato mazinata ne (subhanallah), marasa la’akari da girman ‘yan uwantaka da abokantaka da yarda da aminci in dai akan mace ne, idan babu tsoron Allah ai ana barin halas don kunya.
Watakila

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login