Showing 3001 words to 6000 words out of 42899 words

Chapter 2 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt

idan ya samu dayansu.
A takaice tagwaitakarsu extraordinary tagwaitaka ce ta bada labari da bugawa a jarida. A wancan lokacin da na waiwaya na hasko muku su (flashback), Hassana Murjanatou da Hussaininta Prince, sun mallaki shekarun matasa ne talatin da haihuwa tana housemanship dinta a Lagos State Teaching Hospital.
Ta iso gida kenan tana kokarin sanya motarta a ma’adanarta, wayar ta dake aje gefe ta hau ruri kiran Hasinahn Prince ya shigo mata. Da far’a sosai Aunty Murjanatu ta daga kiran Hasinah, duk kuwa da gajiyar dake tare da ita, ta kwana biyu bata ji ta ba dama, don kusan kullum sai sunyi waya tun barinta gidanta da fara karatun Digirinta a kusa dashi a birnin Tokyo.
Taiwo ta daga wayar Hasinah (fiancée din Prince) tana tsokanarta da waka cikin yarbanci yadda ta saba koyaushe sukayi waya.
“Hasinah ta Prince, Hasinah kanwar Taiwo, Hasinan Taiwo & Kehinde, ta Abdulrasheed PRINCE bada kanki a sare kije gida kawai kice ya fadi!”.
A baya a duk lokacin da take mata irin wannan wakar mai kama da kirari kan Hasinah kumbura yake yi tayi ta blushing ita kadai kamar Aunty Taiwo na kallon ta, domin hakika tana jin dadin wakar gtana alfahari kwarai da son da Aunty Murja ke mata, amma a yau sabanin kullum sai tayi shiru tana kakarin magana amma maganar taki fita daga makogaronta tiryan-tiryan. Murjanatu ta fakamota ta kashe sai ta zauna a ciki ba tareda ta fito ba, ta ce.
“Yaya akayi ne kanwata nake jin muryar ki a shaqe kamar mai fama da mura? Kin fadar min da gaba. Kwana biyunnan ban jiki ba dama, Dear Haseenah in ce ko lafiya?”
Shiru Hasinah tayi bata ce komai ba ta daina kakarin maganar ma sai ciza lebe. Aunty Taiwo ta sake cewa “In ji dai lafiya kuke keda shi? I mean Prince din? Kuma yaya kuke coping da wheather din sanyinnan na winter da karatun naku ke da shi?”
Amma ga mamakinta sai taji kamar Hasinah sheshshekar kuka take yi. Kukan ma irin na fitar rai da ta kasa dannewa, irin mai cin zuciyar mai yinsa, da dugunzuma zuciyar wanda ake yimawa.
Murjanatu was shocked! Stunned daga zaunen da take a cikin mota, duk da ta kashe motar a ma’adaninta kukan Haseenah yasa ta kasa fitowa kuma.
Da kyar taji muryar Haseenah na fita zuwa cikin kunnenta, cikin sauti mai nuna matsananciyar nadama.
“Ki taimakeni ki bashi hakuri Aunty Taiwo, kaddara ce!!!”
Murjanatu ta zaro ido, kafin tace komai Haseenah ta sake cewa “kema kin san ba halina bane, kullum kina gargadina akan hakan, kuma na dade ina kiyayewa, kun sani lafiya kuka dauko ni a ‘virgin’ daga Ambursa, wallahi kafin na zo school ban taba yi ba, sau daya ne, sai wannan na biyu, shima kuma wallahi da kudi Tokumbo yake jan ra’ayi na, na dade ina kaucewa fitinarsa, wannnan din ma akasi aka samu, tsautsayi ne.
Nayi masa babban laifi Aunty Taiwo, kaddara ce ta fada mini.
Zina ba hali bace afkawar kaddara ce da karfin sha’awar da ya gagari dan adam.
Prince ya daina daga wayata yau kwana biyu kenan…. ya min iyaka da zuwa gidansa…. Ya ce kada in kara nuna masa mummunar fuskata ko a lahira!
Laifina bai kai haka ba. I didn’t deserve such a severe punishment, zan jure kowanne hukunci banda na rabuwa da Prince. Na shiga uku Aunty Taiwo, yau kwana biyu ban saka Prince a idanuna ba…
I am dying without him! Truly I am dying! Aunty Taiwo ki taimakeni! Ki cece ni ki ceci marainiya, ke kadai nake da yanzu, a duniya banda kamar ki, ki ceci soyayyar gaskiya da Prince yake yi mun, nasan Tokumbo ba aurena zai yi ba ya cuce ni ne kawai!”. (She screamed!!!). Irin ihunnan na girgiza zuciyar uwardaki. Har cikin kwakwalwar Murjanatu ihun nata ya ratsa ya kusa kurumta kunnuwan Murjanatu.
Ta shiga afi da hurwa, tana tumami a kasa cikin hawaye da majina, kamar Murjanatu na kallonta, kalamai take na tuba da nuna nadama, amsar kaicon kai, da kuma daukar alkawarin bazata sake ba. Begging for “one more last chance”.
Amma taki fadin hakikanin laifin nata, cikin matsanancin kuka na tashin hankali kawai take rokon Taiwo kamar itace Prince AbdulRasheed din da kansa.
Ta kwana da sanin idan Aunty Murjanatu ta yafe mata, tamkar Abdulrasheed da kansa ya yafe mata ne.
Kasancewar kowa dake tare dasu ya san Prince (AbdulRasheed) bai iya tsallake rarrashin Taiwo dinsa. Kamar yadda bai iya tsallake abinda ta umarceshi inta bullo masa da lallashi da banbaki ta bayan gida wanda ita kadai ta san lagonsa.
Amma itama Hasinah duk da wannan tabbacin data ke dashi, ita da kanta wannan karon tana shakka.
Ta yaya take da tabbacin laifin nata mai yafuwa ne ga Taiwo dinma? Since they sometimes share the same feelings itada kaninta Prince? Akan-karan kanta ta san laifinta ba mai yafuwa bane saboda girmansa. Musamman ga babban mutum, mai kishin kansa, dan babban gida da yasan ciwon kansa kamar PRINCE ABDULRASHEED.
Wannan shine babban tashin hankalin Hasinah Bello, idan ta tuna lokaci yazo da Prince da zai barta (lokacin rabuwa da gatanta Prince Abdulrasheed yazo) ko taki ko ta so, duka wannan ihu ne take yi bayan hari Abdulrasheed bazai taba mantawa ba balle ya yafe mata, wanda shine komai nata kuma masoyin da suka kulla alkawurran soyayyar da bazasu lissafu ba, soyayya mai tsabta wadda ikon Allah ce kadai ta wanzar da ita don ta san bata kai nan ba, bata is aba, bata kai matsayin ba. Haba! Wannan tunanin yasa sai ihunta ya ninka na baya.
Ta kuma kasa ambaton sunan Allah don tasan shima Ubangiji bata da uzuri a wurinsa don bata yi godiya da ni’imar da yayi mata ba ta bata sahihiyar soyayyar Abdulrasheed ba don isarta ba.
Bata taba tunanin akwai abinda zai iya yin sanadin da Prince zai ce mata “You! The bastard WHORE! Don’t dare show me your ugly face again!!!”.
Wadannan sune kalaman Prince na karshe a gareta, mafiya daga hankalinta, domin a sanda ya fadesu ta tabbata ya fadesu ne baka da zuci babu wata rana da zaiyi nadamar furtasu.
Tunda abinda yayi Kehinde shi yayi Taiwo. And they often share the same feelings, kowa nasu ya san hakan. To idan har Aunty Taiwo ta ji laifinnata ma, anya zata kara kallonta da idanun rahma? Ko dubanta da aminci da kaunar da take mata wanda duk sanadin Prince dinne???
Kowa bai ishi Murjanatu kallo ba, in dai baida sarauta, mulki ko dukiya, itama din albarkacin Prince ta ci hawa-hawa a wurinta tunda har ta riketa na shekaru a hannunta, sai kuma jininsu yazo ya hadu daga bisani saboda dukkansu halayensu yazo daya masu son rayuwa ne sosai.
Wannan tunani ya kara dugunzuma zuciyar Hasinah, ta kara kururuta kukan da take yima Dr. Taiwo a waya kamar zata fasa dodon kunnenta, fatan ta dai Murjanatu taji tausayinta. Ta kuma tuna ita marainiya ce, da bata da kowa sai su.
Murja ta kasa gane komai akan kukan Hasinah da maganganunta, wadanda bata san ina suka dosa ba, ta bata su ne a lullube, a kudundune, amma hakika ta daga mata hankali fiyeda yadda Hasinan tayi zato, kasancewar Taiwo a very cool and reserved person, wadda ko kusa bata son iface-iface da hayaniya yasa ta sa hannu ta toshe kan wayar da hannunta, ita dai ta san daga ita Hasinah har ubandakinta AbdulRasheed son juna suke kamar su hadiye juna don soyayyah, AbdulRasheed na takun-saka da mahaifiyarsu Nenne akan taki yarda ya auri zabinsa Haseenah, wani cikinsu bai taba kawo karar dan uwansa gareta ba sai yau da Haseenah ta kawo karar Prince, don haka Taiwo ta kasance a uku, ta rasa bayan wa zata bi a cikinsu. Da kyar ta nisa tace da Hasinah cikin lallashi, da gajiyawa da jin kukan da ihun nata na marassa tawakkali, cikin nuna matukar concern ga damuwarta tace.
“Hold on Hasinah, kina ji na ko? Ki bar kukannan haka take it easy Hasinahty, ki tsaya har in yi magana da shi yanzu, idan na samu ya daga kirana, I will get back to you ASAP.
Nima yau kwana uku kenan ban ji shi ba, bai kira ni ba, nima kuma ban samu na kira shi ba, abin yana raina matuka amma yawan karatun dake gabana kuma bai barni na bi ba’asin long unusual silence dinnasa ba”.
Irin kukan da Hasinah ke yi har zuwa lokacin yayi matukar daga hankalin Murja, duk kuwa da cewa Hasinah ta rage karfinsa sai sheshsheka da jan majina, maraicinta da rashin gatanta in babu su a tare da ita, ya fito karara ta cikinsa.
Kamar ance karshenta yazo ne, idan Prince AbdulRasheed ya juya mata baya. Kamar zautatta sabon kamu haka sai ta hau sakin zance a kunnen Taiwo.
Ni Hasinah da ba Uwa ba Uba ba dangi, ba asali ba nasaba ba tushe, sai Abdulrasheed da Taiwo dinsa, da suka karbeni a hakana, duk da rashin asalin nawa.
I was ungrateful, selfish and greedy.
Shine komai nawa, my life support and also a guardian, idan ya bar ni a dalilin kuskurena ina zan koma yanzu a karbeni banda GIDAN MARAYUN AMBURSA?
Zancen zucinta kenan da har bata san yaushe ya fito ya subuce daga bakinta yake shiga kunnen Taiwo ba.
Taiwo ta tabbatar al’amarin da ya saka Hasinah mai soyayyen idanu kuka da nadama irin haka akan AbdulRasheed, harta zauce haka, wanda kusan a baya sai abinda tace masa yake yi, saurayin kan-tace ne Abdul. Abdulrasheed din da ransa ne kawai bai fitar ya baima Hasinah ba don SO na gaskiya, ko meye wannan laifin zai kasance ba karamin laifi bane tayi masa da bazai iya yafewa ba.
A takaice zamu ce Taiwo tafi kowa sanin irin son da Abdulrasheed ke yiwa Hasinah sabida itace confidant dinsa.
Don haka ta katse wayarta da Hasinah ta dauko komatsanta ta fito daga motar zuwa ciki, tana shiga gida bata nemi su Kiki ba, da mai rainonta Bunmi, ta tadda babban danta Hakeem yayi dai-dai yana barci a falo, da alama ya kwaso gajiyar makaranta ne, a gigice take sosai da lamarin nasu, don haka sai ta wuce dakin barcinta kai tsaye ta rufo kofa jikake bamm! Kafin daga bisani ta zauna a bakin gado, tana warware mayafin laffayar jikinta, sannan ta ciro wayarta da gaggawa ta kira dan uwan nata.
Wayar ta jima tana ringing har saida ta katse kanta, akalla Murjanatu ta kira ta kara kira ya kai sau uku kafin tayi sa’ar samun Prince ya daga, shima kuma ba tare da yace da ita komai ba.
In da sabo ta saba da sarautarsa da ginshirarsa. Amma yau bayan jan aji na sarauta da ginshirar ma tabbas akwai wani abun. Tunda akalla duk jan ajinsa shi zai fara gaisheta.
An dauki lokaci tana maimaita masa sallama cikin kwantar da murya da nema masa sassauci, tareda nema masa amincin Ubangiji ta hanyar cikakkiyar sallama, har saida ta kai ga jawo masa Hadisin daya yi umarni da wajabcin amsa sallama ga musulmi da mafi kyawunta ko mayar da martini da makamanciyarta.
Kafin ta samu Engnr. AbdulRasheed (Kehinde) Idris Akanni, ya amsa mata da kyar. Kuma ciki-ciki. Ta hanyar cewa;
“Wa’alaykumussalam-warahmatullah”.
Bayan haka sai bai kara cewa ko uffan ba.
Wannan wani abu ne weird daga Abdulrasheed zuwa gareta a wurin Murjanatu-Taiwo. Ko Prince zai ma kowa kyaliya irin wadda ya saba yiwa wanda ya bashi haushi banda ita Taiwo dinsa, amma me? He has his reason. Wato tuni ya riga ya san zancen da Taiwo tazo zata yi masa, bana komai bane na ‘yar dakinta Hasinah ne, ya riga ya san yadda soyayyarsa da Hasinah ta assasa aminci mai girma tsakaninta da ‘yar uwar tagwaitakarsa, Taiwo, sanadin zamanta tare da ita na wasu shekaru tana karatu a hannunta.
Ya riga ya kwana da sanin cewa ta kanta Hasinah zata fara bi, da sunan a sulhuntasu, a bashi hakuri ko a lallashe shi. Yau ba Taiwo ba ko lallashin Nenne ne bazai ji ba, in dai akan matsiyaciya Hasinah ne.
“Let her GO please! I will take her back to where I adopted her!”.
Cikin murya ta lallashi da nuna kauna, irin tasu ta ‘yan biyun Nenne Sappa da kowa ya sani, wadanda ko a cikin tagwayen duniya bakidaya su twins ne na musamman ta fannin fahimtar juna da kaunarsu da juna, haka kulawarsu ga damuwar kowannensu mai girma ce, don ta zarta ta common Yaya da kaninta, saidai ace ta wadanda suka fito duniya daga mahaifa daya, sannan a lokaci guda.
Ubangiji Subhana da kansa yaga damar ya dunkulesu ya haliccesu tare a mahaifa guda, don haka zukatansu sau tari suna aiki da bugawa tare ne.
Taiwo ke yiwa (twin brother) din nata Prince Abdulrasheed magana cikin lallashi na hikima da taushin murya.
“Kehinde, me ke faruwa tsakaninka da Hasinah haka? How can I let her back to orphanage a shekarun girmanta don kawai ta bata maka rai?
A kowanne relationship, na soyayya ko mu’amala, dama ai akan samu sabani which is normal, amma a wannan lokacin hankali bata yake yi bat, sai ayi kokari asa hankali ya nemo shi.
Dama ka daukota da niyyar watarana in ta bata maka rai zaka maidata ne? Ko kuwa ka daukota ne don ka aureta ba don tun asali ka taimaketa ba?”
(Daga ita sai Kakansu Emir da Babansu Dade suke kiransa Kehinde, kowa PRINCE yake cewa) kannensu kuma suce masa HAMMA.
Maimakon ya bata amsar tambayarta kamar yadda ta bukata sai taji muryarsa (in despair) cikin wani yanayi yana fadin.
“Taiwo Please! Let that PIG go I said! (Ki bar wannan Aladen ta tafi nace), in kuma kin ki toh, ya rage naki. For now, ki hada ni da Kiki!”.
A yadda Murjanatu taji muryarsa kadai ta fahimci yana cikin matsananciyar damuwa da kunar zuciya, kuma da gaske yake muryar Kiki kadai yake son ji da shirmen zantukanta ya fiye masa zacennan da take masa na wadda ya kira “karya” kuma “alade” Hasinah.
Kiki kadai yake bukatar saurare a wannan lokacin, baya son wani zance bayan nata, koda ABCD dinta zata yi masa ya fiye masa wannan wa’azin na Taiwo mai kama da a kafa mata drum ta hau kai tayi ta yiwa wasu amma bas hi ba.
Jiki sanyaye Murjanatu tabi umarninsa, ta fito da wayar a hannunta zuwa dakin da Kiki-Ruqayyat take wasa da mai rainonta.
“Uncle AK wants to speak with you Kiki!”
Taiwo ta fadama Kiki, tana mika mata kan wayar. Da zumudi mai yawa yarinyar ta dirgo daga dan gadonta ta amsa, tana dokin jin muryar Kawun nata, wanda koda take yarinya karama ta san girman kaunarsa gareta ko Daddynta Toufeeq albarka.
Sabida yadda yake janta a jiki har ta saba dashi a waya. Balle kuma in ya zo gidansu, tayi ta sukuwa a jikinsa kenan. Taiwo ta koma gefen gado ta zauna cikin damuwa ta zuba tagumi tana kallon shirmen da Kiki ke masa a waya na sunayen dabbobi da suka fara da harafin “A” fuskarta fal annashuwa, shi kuma Uncle din ya dage yana biye mata cooly. Dama tone na muryarsa kullum is cool amma na yau is more than cool is despair.
A tunaninsa a wannan yanayin da yake ciki muryar Kiki-Ruqayyat kadai da shirmenta ne zai mantar dashi ya debe masa kewa, ya rage masa zogin zuciya da radadinta kan abinda ya gani, wato ya mantar dashi abinda Hasinah tayi masa. Kiki his beloved little niece, amma ina! Ko Kiki ta gaza yau, domin ta kasa mantar da shi bacin ran Haseenah dake kasan ransa, still yana nan yana sakadar ruhinsa har zuwa lokacin. Kiki ‘yar lukuta yarinyar data shiga ran Engnr. Abdulrasheed matuka, itace diyar Taiwo ta biyu bayan Hakeem.
Ganin sun ki gama shirmensu shi da Kiki, ita kuma an barta cikin ci da zuci, yaki ma ya saurareta balle ya gaya mata hakikanin abinda ya faru, sai Murjanatu ta karbi wayar daga hannun Kiki ta bar dakin, don ita tafi kowa sanin yanayin da Abdulrasheed zai iya kasancewa a wannan lokacin in har da gaske ya yanke shawarar rabuwa da Hasinah kwatakwata.
Ta san Abdulrasheed bai iya sabo ba, sabo yana wahalar dashi, wholeheartedlhy yake sabawa da mutumin da ya kwanta masa, balle sabonsa da Haseenah na kusan shekaru biyar, kasancewar ta san ba karamin so yakewa Hasinan ba, kafin ya iya yakiceta daga ransa zai sha matukar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login