Showing 42001 words to 42899 words out of 42899 words
Chapter 15 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt
Yace ya gaji da yawan maneman auren Aisha, kullum masu zuwa yau daban dana gobe, yace gara ya aurar da ita haka ya huta, kowa ya huta, dama bai mata alkawarin samun ilmin gaba da sakandire ba. Amma shi baya ra’ayin karatun boko mai zurfi sam a gareta.
Burinsa shine tayi aure da wuri ta haifa masa jikokin da zai kalla a matsayin ‘ya’yan da shi Allah bai yi nasa sun zauna a raye ba, don mahaifiyarta ma iyakacin ta firamare ya aure ta.
A karshe yace ya ji bukatar ta na son tafiya da Aisha taga likitan Asthma, sai kuma yace bai yarda ta zauna a Lagos har sai hutu ya kare ba, saboda tana zuwa Tahfiz yin haddar Al’qur’ani a kowanne hutu anan kusa dasu a unguwar Dawaki, da ta gama ganin likitan don Allah a dawo da ita gida ta karasa hutunta tare da su don suma sun jima basa tare da ita tun tafiyarsu aikin Hajji.
Nenne Sappa tayi ta mamakin wannan soyayya ta iyayen Aisha ga diyarsu Aisha, ta dauka Haj. Zainab ce kawai ke mummuken Siddiqah ahe har baban nata, ta amince da yadda Malam Yunus ya zaba cewa Aisha zata yi sati daya a Lagos ta dawo musu da ita gida.
Malam Yunus ya bukaci sanin waye mahaifin AbdulRasheed da kuma asalin ita Nenne anan Gombe. Nenne ta bashi damar yayi duk wani bincike da addini ya bashi dama akan Prince AbdulRasheed dasu iyayensa.
Sun rabu akan cewa zai yi bincike zai kuma yi shawara da maidakinsa da Yayansa, sannan zai sa Zainaba ta sanar da ita abinda suka hadu suka yanke.
An samu shawo kan Aisha da kyar da sudin ludayi ta yarda zata bi Hajiya Sappa Lagos bayan ta ci kuka ta koshi ta gode Allah a toilet don kada Hajiya Sappa ta ga kukanta, wai sati guda! Sati guda babu Umma yaya rayuwa zata yi dadi ga PETEL?! Sati gudan da a cikinsa dukkkan kundin kaddarar rayuwar Aisha take, tareda dan kabilar Yarbawa.
Nenne da Aisha suka kama hanyar Lagos ta jirgin sama, domin daga Gombe kai tsaye suka tashi a jirgin Azman mai zuwa Ikko.
**** ***** ****
MURFIN LITTAFI NA DAYA
Ga dai Aisha-Siddiqah a hanyar zuwa Lagos gidansu Prince ABDULRASHEED IDRIS (KEHINDE) AKANNI, gidan da ga dukkan alamu zai zame mata fadar rayuwar aure da surukuntaka, ga dai Aisha da Prince (Fullatana da Bayarabe) na shirin zama mata da miji kamar yadda manyan alamu suka nuna, alhalin Aisha ga hasashenta da alkiblarta da take-takenta akan kabilar Yarbawa.
Mu biyo Siddiqah Petel ‘yar Ummanta, don jin cikakken labarinta, yadda zata kaya tsakanin ta da Polo Legend na Africa da turai, wato Yariman Ilorin PRINCE ABDULRASHEED (KEHINDE) IDREES AKANNI, mijin da kaddara ta zabar mata su fafata har su baiwa hammata iska a fagen soyayya, wanda ya kasance dan asalin kabilar Yarbawa.
Yanzu ne zamu shiga cikin gundarin labarin Aisha da Prince. Har yanzu a himfidar labarin muke.
Abinda zamu so sani a gaba shine; Shin ko Aisha-Siddiqah zata barranta kanta daga matan da Prince Abdulrasheed ya riga yayiwa kudin goron maha’inta, mayaudara, masu saka khairan da sharran, sannan (gold-diggers&insatiable)?
A cewarsa dai “duk mata marassa godiya ne, da yawansu mazinata ne, marassa tsoron Allah ne, sannan basa yin soyayya ta fisabilillah!
Ta yaya Aisha zata goge wannan perception din daya ya riga ya ginu tun kuruciya daga kwanya da zuciyar Prince Abdulrasheed Kehinde?
Shin ko Prince zai samu irin soyayyar da yake fata, yake kwadayi, yake mafarki, yake kuma burin samu shekara da shekaru daga Aisha? Mun ji dai sanda yace “He’s a hopeless romantic, in search of true LOVE! Wanda ya riga ya amince babu shi a duniya”.
Shin ko Aisha-Siddiqah zata so kabilar Yarbawa tunda ga dukkan alamu kaddarar rayuwarta na cikinsu?
Mu karasa a littafi na biyu wanda tare suke da dan uwansa.
Taku har abada
SUMAYYAH ABDULKADIR
(TAKORIN TAKORITES)
07030137870
WHATSAPP ONLY.
10/4/2024
(PAID BOOK)
(INA TALLATA MUKU AISHA LAME ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa fata hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari.
-Takorinku