Showing 30001 words to 33000 words out of 42899 words

Chapter 11 - A'isha-Saddika Book 1 Complete Document by Sumyya Takori .txt

sharo ba shanu), but today he looks pale har fiyeda Taiwo uwar kankanba idan ta raunana.
A ganinsa tunda har uwar data haifeshi ma ta fara yarda da zargin da duniya ke masa na cewa wai (he is gay), don kawai yana rayuwa a cikin turawan yamma, kuma yana practicing wasansu na tseren Doki a matsayin sha’awar ransa kuma sana’a mai girma, hujjar kowa ta makala masa wannan zargin shine kawai don ya ki yarda yayi aure ko kawo mace gidansa da sunan matarsa?
Zargi wani abu ne mai girma da muni a musulunci balle zargi irin wanda duniya ke masa. Auren ai Sunnah ne ba farillah ba tunda Alhamdulillah yana iya rike kansa ta hanyoyin da addini ya koyar.
Kusan kullum baka Abdulrasheed da azumin litinin da alhamis a bakinsa, baya kallon haramun, balle kai kansa inda ake aikatata, he is always busy planning and scheduling his Polo time-tables across the globe da tsara ayyukansa na Consultation a matatar man fetur a (Qatar refinery). Zina ai sai mutum ya bata kafa take shigowa rayuwarsa.
Ga kuma addu’ar tsayayyyar Uwa irin Nenne Sappa a kansa kullum wadda zamu iya cewa itace babban makamin dake katange Abdulrasheed ga ayyukan sabo in akayi la’akari da yanayin rayuwar ‘yan Polo.
Duk da cewa Nenne ta yi dana sanin furta masa damuwarta, amma kuma hakan ya taimakawa zuciyarta, yanayin da ya shiga kadai yasa ta rage tasirin zargin na mutane daga ranta akan dan nata, ko daga irin halin rudu da damuwar da ya shiga akan maganar kadai ta gane ba haka bane, zargi ne mai muni ake masa da shaci-fadin mutane da basu da gadon ka sai gadon magana akan ka.
Ita kawai tayi la’akari ne da fadar nan ta hausawa dake cewa “ka haifi Da, amma baka haifi halinshi ba” kuma akace wai “ba’a shaidar ‘ya’yan yau”, da kuma yadda kana tufka a matsayinka na uwa; modern society da influence na ilmin zamani na warware maka tufkar ta baya, musamman shi AbdulRasheed da in akayi la’akari da irin ‘life-style’ dinsa, wato yanayin rayuwarsa da yadda yake gudanar da ita gabadaya kome aka ce akansa al’umma bazata musa ba.
“To me ya hanaka aure har yau Kehinde? Na roke ka da girman Allah yau ka gayamin. Ni mahaifiyarka ce da baka da wanda ya fini ba kuma wadda zata rufa asirinka a duniya irina.
Shin idan baka sanar dani hakikanin matsalarka ba, wa zaka sanarwa a duniyarnan?”
Zuwa lokacin ya soma dawowa cikin hayyacinsa, amma maimakon ya baiwa Nenne amsar data dace da tambayar data yi masa, wato menene hakikanin abinda yasa ko zancen aure baya kaunar a yi masa? Sai ya bige da maida zancen wani kala daban, don Nenne ta bar zancen, don har gobe babu wanda ya san abinda Adetokumbo yayi masa kaf cikin zuri’ar su, daga shi sai shi Tokumbon, sai kuma Taiwo, sai ita shaidaniyar HASINAH! Da bai san a wace duniyar take yanzu ba. Sai kuma Allah da ya haliccesu.
Zai kuma cigaba da barin wannan zancen a ransa yana haunting dinsa shikadai ba tareda ya gayawa wani a danginsu ko iyayensu ba bayan Taiwo, albarkacin zumuncin Akanni’s da hadin kan gidansu.
Yau ace wani cikin zuri’ar Emir Abdulrasheed Akanni yana zina da macen da ba tasa bama abu ne da zai taba mutuncin su bakidaya, abun kunya ne ba karami ba, ga zuri’ar sarki Abdulrasheed Abdullateef Akanni a idon talakawansu dake ganin martabarsu da girman nasabarsu, wanda zai iya lalata hadin kan gidansu gabadaya wanda gida ne ko kuwa zuri’a ce data zamo abun buga misali a ciki da wajen jihar Ilorin.
Sai ya maida abun zolaya ga Nenne, bayan ya maida murmushi mai sanyi akan fuskarsa, Prince ya soma magana cikin lallashin mahaifiyarsa.
“To yanzu Nenne, ki gayamin saboda Allah, duk fadin Najeriya wacece kike ganin zata aureni da tsillin furfura kamar yadda Fatima tace, umh?
Ta kuma kaunace ni da furfurar nikadai ba tare data hada soyayyata data wani na ba? Ba kuma don abin duniya da reputation dina (shaharata) a kan wasan Polo ba, soyayya pure nake nufi tsarkakakkiya ta saboda Allah! A dai yawan shekaru irin nawa, wadanda babu sauran kuruciya a cikinsu yanzu?
Believe me Nenne, duk matan zamanin nan, ina fade ina karawa kullum (are nothing but gold-diggers) sannan karnukane babu daraja a tare dasu.
Daga kan HASINAH AMBURSA… na gama rufe babin mata Nenne, (they just want money over pure LOVE), don haka basa gabana gabadayansu Nenne, har abada babu ni babu ‘ya’ya mata”.
Nenne sai ta bishi da ido zuruuu! Ta kasa gane inda zantukansa suka dosa. Me Hasinan da ta san yanaso kamar ya cire ransa ya bata tayi masa da ya karya zuciyarsa haka?
Ashe a kanta ne yake gudun mata tun zamanin samartakarsa?
Ta dade bata kara jin komai game da Hasinah din ba. Ko daga bakin aminiyarta uwar dakinta (Taiwo) bata kara jin zancenta ba. Wacce a baya kullum suka hadu bata da aiki sai lallashin Nenne ta barshi ya auri Haseenah.
A lokacin AbdulRasheed ya koma ya jingina da filo a jikin gadon jinyarsa, ya runtse idonsa a hankali yana motsa hannunsa na dama kadan da aka kwance daga daurin karaya. A can kasan zuciyarsa magana yake shikadai wadda baisan tana fita a fatar bakinsa ba, tana shiga kunnen mahaifiyarsa.
“I am now a hopeless romantic. I want an idealist (true love)”.
Wanda ya riga yayi amanna da cewa babu shi sam-sam a zamanin yanzu. Babu irin soyayyar da yake burin samu!
Domin y agama yardarwa kansa a wannan qarnin da muke ciki, wani qarni ne da mafi yawan mata suka daina soyayya irin wadda yake buri ta domin Allah, ba don komai ba sai don zukatansu sun zarme da kwadayi da son rayuwar duniya da ta wuce kima, hakan yasa suka zama insatiable ga mazan da Allah ya basu masu yi musu kauna ta gaskiya, suka maida kawunansu sex slaves to rich men (sun zamar da kansu bayin biyan bukatar gangar jikin maza masu kudi ko mulki, soyayya ta hakika ta gushe a zukatan mata.
Engnr. Abdurasheed ya kara kishingida sosai yana cigaba da cewa da kansa da kansa.
“I am a hopeless romantic. I want true love!”.
(Karin haske). “Prince AbdulRasheed (Kehinde) Idrees Akanni, yana nufin ya riga ya yardarwa kansa cewa babu soyayya ta gaskiya, true love is hard to find, or does not exist at all, matan yanzu duka are incapable of that...!”.
**** **** ****
Ba jimawa saboda irin kulawar da yake samu ya karasa warwarewa, aka sallamesu. Suka koma gidansa.
A wannan dan zaman jinyar da Nenne Sappa tayi na dan ta Prince AbdulRasheed Kehinde, a kasar Argentina, ya basu damar samun shakuwa da wani irin kusanci da juna na uwa da data wada y agama mallakar hnkalinsa amma still yana bukatar kulawar Nenne da zamanta a gefensa, shekaru da yawa basu samu damar zama tare na lokaci mai tsaho irin haka ba, saboda yawace-yawacensa na Polo a duniya.
Nenne ce ke dafa masa duk abinda zaya ci da kanta kullum, wanda shi da kansa yake zabar abinda zata dafa masa, haka take saka shi a gaba sai ya ci sosai, sannan ta tabbatar da ya sha magungunansa akan kari, wanda take barowa da hannunta akan farin tafin hannunta ta zuba ruwa a tambulan mai garai-garai ta bashi ya hadiya akan idonta don Abdurasheed baya son kwayar magani sai akan idon Nenne don baya son abinda zai bata mata rai tun yana yaro.
Saida AbulRashid ya warke ragas har ya fara shirin komawa wajen aikinsa a Qatar sannan sukayi sallama shi da Nenne da ‘yar uwarsa Fatima, Taiwo ta tabbatar masa zata sameshi a Qatar in ta samu leave ta ga jikin nasa. Sun kwana hira shi da Nenne yau, zancen da baya so ko kankani a yi masa wato zancen aure itama tana avoiding dinsa yanzu, don bata son ganin yanayin tashin hankalin da yake fadawa a duk lokacin da tayi subutar bakin yi masa zancen aure.
Su Nenne zasu koma Lagos a washegari, don lokacin tafiyar Nenne aikin Hajj na wannan shekarar ya kusa.
Sun tashi zuwa Lagos da kwanaki biyu, shikuma ya tashi zuwa Qatar inda ya koma bakin aikinsa cikin koshin lafiya.
**** **** ****
FGC BILLIRI, GOMBE

Yarbawa masu kwalo-kwalo, da Duwawu kuke tukin tuwo!!!”.
Bisola ta kauda kai bata kula ta ba, ta ci gaba da tukin Teba da take yi da ludayin karfe a cikin robar cin abincinta mai fadi. Wannan duk bai ishi siririyar yarinyar ba mai siririn hanci da manyan idanu masu walainiya, hakoranta yiri-yiri farare kal kamar kankara, ta sake leka fuskar Bisola cikin matukar tsokana da iblisanci irin na ‘yammata ‘yan makarantar kwana da aka fi sani da teenagers.
“Nace ko ba ku bane? Yarbawa masu kashi a kwano?!”
Jikake kyal-kyal-kyal. Yaran dakin da duka ‘yammata ne masu tashen balaga wadanda a shekaru basu fice shekaru 15 zuwa 16 ba, in sun yi da yawa 17, dukkansu sun kara kyalkyalewa da dariyar shakiyanci da shegantaka (mockery).
Karo na sau ba adadi da AISHATU-SIDDIQAH YUNUS tasa Bisola Akanbi kuka, sanadin wannan wakar da irin wannan cin zarafin da take mata a gaban sauran yara tsararrakinsu da suke kwana daki daya. Ko a aji ko a filin wasa ko a hostel kai har a masallaci in taga Bisola sai ta mata irin wannan tsokanar. Sauran daliban kuma, wadanda suke gang din Aisha duk sanda Aisha ta fara yima Bisola wannan wakar ta shakiyanci wadda take yi tana juya siririn kwankwasonta (irin dai na yadda yarbawa ke juya mazaunansu) wanda baya wani motsawa sabida sirantarta sai sun daddage sun barke da dariya.
Ba Bisola ce take basu dariya ba, karewa ma tausayi take basu, sabida yadda Aisha ta matsa mata, ita Aishar ce take basu dariya yadda take daddagewa tana juya kwankwaso da ‘yan mazaunanta da sunan kwaikwayon tukin tuwo ko Tebar Yarbawa, alhalin kwankwason nata duka bai fi girman a hada tafin hannu biyu ba. Farin jininta a wurin tsararrakinta kuwa sabida kiriniyarta da kyawunta da kaifin bakinta, ga wauta da gwalangwaso abin ba’a magana.
Bisola Akanbi kullum Aisha ta fara mata waka saita koma gefe cikin muzanta kamar mujiya a cikinsu, don yadda Aisha tasa ‘yan dakinsu suke nuna mata wariya da kyama wai don kasancewarta bayarabiya daya tal a hostel dinsu, cikin dalibai masu yawa hausawa da fulanin Gombe da suka fi yawa a FGC Billiri, wadda aka kawo daga jihar Ibadan, aikin asibitin federal government ne ya kawo iyayenta garin Gombe, har yayi sanadin da aka yi mata transfer zuwa FGC Billiri.
Bisola Akanbi musulma ce gaba da baya. Yarinya mai hakuri da rashin sakewa da hausawa. Har ya zamnto daga zuwanta Billiri zuwa yanzu su Aisha da gang dinta su Amintako, Ramatu da Zannura suna neman jaza mata ciwon damuwa, sabida yadda Aisha ke nuna kamar itaba cikakkar mutum bace, ko kuma ba daya take da sauran dalibai ba, wai tunda ita bayarabiya ce. Kabilanci muraran a wurin Aisha abin ba’a cewa komai.
Yau dai abinna Aishatu-Siddiqah Yunus, ya kai Bisola Akanbi bango, duk hakurinta Aisha ta kaita karshe, don ta sa an wareta daga cin abinci tare dasu a dakin, sabida itace gang leader ta dakin gabadaya, ‘yan dakin tun kan a kawo Bisola suna yin ciyayyar abinci a dakinsu. Da aka kawo Bisola daga baya suna ci har ita, yau Aisha tace idan har basu cire Bisola daga ciyayya ba ita zata daina ci tareda su, don ita bata son cin abincin yarbawa ko ci tare dasu, alhalin taji ana fadin suna kashi a kwano, don haka Bisola ita kadai aka zuba mata nata a plate, aka tura mata gefe wai don ita bayerabiya ce. A cewar Aisha Yunus, gang leader ta ‘yan aji hudu (SS 1) bazata ci abinci da Yarbawa masu cin dodon kodi da hannunsu ba.
Wannan abu yaima Bisola ciwo. Kasancewar ta dade tana shaqa daga Aisha, ta yi hakuri mai yawa da Aisha, hakurin da ya hada da dan tsoro-tsoro, kasancewar Aisha nada wasu ilhamomi, watau kwarjininta da kyawunta da kaifin harshenta dake sawa aji ana shakkarta, sannan duk ‘yan gang dinta su Amintako halinsu daya da ita na tsokana da fin karfin wanda bashi da baki kamar Bisola. Amma yau? Dama aka ce mai hakuri bai iya fushi ba.
Da kuka Bisola taje (staff room) ta gayawa Discipline Master duk abinda Aisha ke yi mata a hostel, a aji, a library, a wajen wasa ne dama duk inda ta ganta tun zuwanta FGC Billiri.
“This is Mockery! Derision!”
Inji Malamin cikin bacin rai.
Discipline Master Uncle Sayyadi ya cika da mamaki, ransa kuma dana sauran malamai ya baci sosai, ace a makaranta ta gwamnatin tarayya (unity school) ta Najeriya ake irin wannan abin Allah wadai su malaman basu sani ba? Nan ya aika Head Girl Hasiya Mato, yace maza-maza ta kawo masa Aisha-Siddiqah Yunus ofishin malamai (dead or alive), sannan yace Bisola ta zauna a gefe, yau sai ya ga uban Aisha. Bisola ta koma gefen Teacher din tana sharar hawaye domin hakika Aisha Yunus, ta zame mata matsala cikin makarantar, ta dade tana cutar da feeling dinta.
Head girl Hasiya din taje har dakinsu ta sako Aisha a gaba har ofishin malamai, duka malaman sun hada kai a ofishin suna tattauanawa akan al’amarin da Bisola ta kawo kara tana neman ayi mata iyaka da Siddiqah Yunus. Discipline Master yafi Bisola jin bacin rai, koda yace a kawo masa ita, kafin sui so ya shirbinawa dorinarsa man shanu sau uku kuma dama gashi lokacin san yi ne, yace a ransa yau zai ga karshen kabilancinta, zai gani idan ubanta ne ya wanzar da hausa bakwai da banza bakwai.
Malaman kowa na tofa albarkacin bakinsa akan kabilancin ‘yan arewa ga ‘yan kabilar Yoruba, da yawa ana samun hakan, wanda ko kadan bashi da amfani musamman ga yara masu tasowa ana saka musu wani nagetive tunani daban a ransu akan kabilar Yarbawa. Kamar su din wata halitta ne daban da hausawa da Fulani. Ko Hausa/Fulani din sun fisu wata martaba ne. Aisha ta iso sumui-sumui da ita don tasan kiran Malam Sayyadi ba alheri bane, ganin Bisola a gefensa tana kuka yasa ta gane kwabarta tayi ruwa yau, wato yau Bisola ta kai kararta, ai kuwa nan da nan cikinta ya duri ruwa.
Aisha da Bisola suka gurfana gaban Discipline Master, kan Aisha a sadde da ganinta kaga maras gaskiya. Discipline Master ya daka mata tsawa yace “maimaita tsokanar da kike mata kullum a kunnen mu muji, isashshiya diyar barbushe da tsimbirbira”.
Aisha tayi narai-narai da sexy eyes dinta akan malamin bafillacen, wadannan idanun na Aisha masu kama da hawaye ne fal ya taru a cikinsu, shi kansa Discipline Master din sai da ya kauda kai sabida kwarjinin idanun Siddiqah, ya taba cewa wani Teacher dan uwansa mai suna Malam Tafida ya daina kallonta, Malam Tafida yace shima bai san meyasa yake yawan kallonta ba, Uncle Sayyadi yace da Malam Tafida cikin takaici, “yarinyar nan in ka cika kallon ta musamman wadannan maganadisun idanun nata alwala bazata zauna a jikinka ba”. Bai manta dariyar da malam Tafida yayi ta yi ba a ranar, to yau ma hakan ce ta kasance. Discipline Master da Aisha tayi masa narai-narai da ido cikin rokon ta tuba bai san sanda ya zabura don kwato kansa daga tasirin idanun Aishah ba, ya buga dorinarsa a kasa cikin barazana.
“Zaki fada muji ko ba zaki fada kowa ya ji me kike yi mata ba?”
Maimakon Aisha ta bada amsa sai ta soma tumami a kasa tana kuka tana shura kafafu.
“Malam in ka dake ni Asma ta tashi zata yi, Malam ni asthmatic ce. Ummana kafin a kawo ni tace ayi mata alkawarin ko me zan yi za’a bani punishment, na aiki ko kneel down kowanne irine a bani, amma kar a taba mata lafiyar jiki na.
Wallahi Malam nima a bakin yaran unguwarmu naji”.
Discipline Master da sauran malamai duk suka saki baki da ido galala! Suna kallon Aisha-ikon Allah, irin kukan da take yi da tumami a kasa na shagwaba kamar karamar yarinya alhalin tayi 15, bayan ko dukan nata ma bai yi ba ya hanasu sake ce mata komai. Ta sake sakin kuka tana cewa Bisola ta mata sharri. Ai kuwa Disdipline Master ya fusata ya zuba mata dorinar a gadon bayanta guda daya, kafin ta farfado ya daddage ya sake zuba mata wata akan siraran kafafunta, yace “bari in saki kukan shagwaba da hujja, ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login