Showing 21001 words to 24000 words out of 42941 words
Chapter 8 - BABBAN KUSKURE COMPLETE BOOK BY RASHEEDAH A KARDAM.txt
gyaran jiki, hatta yanda Indo zatayi tafiya saida suka koya mata.
Bayan kwana biyu suka zo mata da form d'in makarantar kwaliya ta cika, da kanta ta biya kud'in kasancewar tana samu 'yan kud'i, a haka ta fara zuwa.
Hajiya ganin jarabawan Indo yayi kyau hakan yasaka ta bata motarta, ranar da Falmi tasamu labari kamar zatayi hauka a gidan, don saida Hajiya ta tsayar mata ita da Aliyu, don motar Falmi bai kai na Indo ba.
Sanah suna hira da Sadeey da Indo, Sadeey tace"Indo gaskiya ni bana son ana kiranki, da Indo nan sai kace yar kauye.
Sanah tace"kamar kina raina.
"Shawara daga yau duk wanda yace miki Indo, in ba wanda kike jin kunyarsa bane karki amsa.
Tun daga ranar sunan Indo ya b'ata yakoma Aisha, nima Rash nace" daga yau na daina cewa Indo sai Aishat.*********
2yrs later
Wata k'yak'yawan budurwa na hango, tana fitowa da ga cikin gida ta na k'ok'arin bud'e motar ta, mai k'irar RANGE ROVER, sanye take cikin wani doguwar riga ya d'an kamata daga sama, sai d'an k'aramin cikinta dake a shafe ya fito. Hakan shi zai baka daman gane irin halittan da ubangiji ya mata, harta shiga mota ko mai ta tuna cikin damuwa tace"oh shirt! Da sauri ta fito ta nufi hanyan cikin gidan, gudu-gudu sauri sauri, sam bata ankara da wanda ke fitowa ba, sai jin garam sunyi karo da mutum. Ko ta nuna alamar damuw ta d'ago kai tare da d'an zaro gilashin dake idota, sai da ta d'an rausaya ido, ta wani kashe murya tace"oh i'm sorry! you guy.
Bata jira amsan shi ba ta sakai ta wuce abunta, Haiydar da tsananin mamaki kasa motsi yayi, shafa ida ta buge sa yayi, haryanzu dadda d'an k'amshin ta yana tashi. Wani yawu ya had'iye da ya tuna yanda take sarrafa mazaunanta, da k'irjinta.
Tabbas Allah yayi halita a gun, cikin zuciayrsa ko cewa yake"wannan taci a kirata da zallaziya ko zank'aziya hmm wannan tamk'ar ita tayi kanta.
"Gaskiya ta had'u ba k'arya.
"Gashi ta had'a duk wani abunda nake so ajikin mace amma taya zan tink'areta?.
"Hmm ni shakkanta na ke ji ma yanzu.
Wata zuciya tace"to ko kana jin shakkanta sai ka tin k'areta, ai girmanka zai zube.
Yana tsaye tazo ta wuce sa, motarta tashiga sai da ta yi ribas, kafinta ta da kura ta bule Haiydar ta wuce da gudu.
Haiydar ko gizau baiyi ba ila bin motarta da kallo.
Zuciayrsa tana masa wani irin abubuwa nai wuyan fasaruwa, kasa motsi yayi don duk jikinsa ba k'wari.
Masu karatu wai shin wata yarinyace wanna, da har zata iya taka Haiydar, ta masa wannan wargin batare da ya d'au mataki ba?.
Don son jin wannan amsar ku biyo ni.
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH LUV๐*
[9/12, 8:17 PM] ๐ฌ๐๐Salma๐๐๐ฌ: [7/6/2016 Rash Kardam] ๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป
๐๐ปBABBAN KUSKEREN๐๐ป
๐๐ปDANA TAFKA ๐๐ป
๐ป๐ป๐ป
๐๐ป๐๐ป
NA
ยฉRASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-170~173.
Ko da suka dawo gida, Hajiya ta zaunar da Indo tayi mata nasiha, game da aurenta, sanan ta k'ara da cewa"Aisha kiyi hak'uri ina sane, da duk irin abunda Aliyu yake miki.
"Abunda yasa ba zan takurasa ba a kwai lokacin dana ke jira, zan ramamiki duk abunda ya ke miki, inaso ki nutsu kiyi karatu nan gaba sai Haiydar yazo da kansa yana baki hakuri.
"Alokacin ne zamu rama duk abunda ke mana, Hajiya wani murmushin mugunta tayi, kafin taci gaba da cewa"zan saki a makaranta islamiya, don ki rage yawan zaman gida.
"Sannan ki k'ara hak'uri da duk abunda zasu miki, wataran zakici riban hak'urin ki, har sai ni da kaina nazo, ina cewa Aisha ki d'an ji tausayin Yayanki, ki sassauta ma Haiydar. Hasna ne tayi murmushi don itama tanason ta ga wannan ranan.
Hajiya tace" a kwai motar da Abban na, Sarkin Fulani(Gakansu Haiydar ) ya ban range rover zan baki ita, tadawo naki halal malak.
"Zansa Hasna ta koya miki mota amma sai naga kunyi jarabawa, da irin sakamakon da kika fito da shi kafin na damk'a miki motarki a hannuki.
"Sai gobe zaki fara zuwa school, in kin dawo da kaina zan maidaki gida, kuma zansa driver yana kaiki makaranta.
"Ku tashi kuje ku huta Allah ya muku Albarka.
Suka amsa da"ameen.
Gidan Haiydar ko yau ya dawo da niyar ko ta kwana, don yau yayi niyar karb'a hakkinsa a gun Falmi.
Don yayi hak'uri har ya gaji, rabonsa da ya kusanceta har ya manta.
Wanka yayi ya nufi d'akinta, yana zuwa ya tarar ta baje a gado, tana sharan baccin ta.
Hawa gadon yayi, yazo kusa da ita ya kwanta.
Salon sa da yake rikitar da mace, ya fara aika mata sak'onsa.
Cikin bacci Falmi taji ana shafata, farat ta farka ganin Haiydar yasa ta rik'e hannusa, tace"mai kake shirin yine?.
"Ko ka manta dokata ne?.
"Matsawan kana son biyan buk'atarka sai ka ajiye min kud'i.
Cikin da shashiyar murya Haiydar yace"haba Falmi anya kina tsoron Allah kuwa?.
"Matar aure na na sunnah, don zan kusanceki sai na biya kud'i.
"Kisani fa hakan haramun ne.
"Kisani mala'iku su tsine miki fa?.
Falmi tace"ai yau in har kaga ka samu abunda kakeso to kasaka min kud'i har 200k.
Haiydar yace"Falmi bayan kud'in sadakin dana biya?.
"Ki sani bana son miki ta k'arfi.
"Ina rok'onki da kiji tausayina, ba wai don bana da kud'in da zan baki ba, a'a saidan hakan baida kyau.
"Kuma duk irin k'yautata miki danakeyi ba k'ya gani?.
"Yaushe na baki 300k fa falmi?.
Tsaki ta ja ta mik'e, za ta sauk'a daga kan gadon, ya fincikota, sak'onni yasoma aika mata dashi.
Duk iya k'arfinta ta kasa kwacewa sai tasoma masa ihu.
( kira gareku mata masu irin wannan halin, kusani baida kyau, Allah da mala'ikunsa, suna tsine wa duk matar da mijinta ya nimeta, ta juya masa baya. Ko kuma ta nimi sai ya bata kud'i kafin ya kusance, ta kamar yanda Falmi takeyi. Dan Allah ku kiyaye inda maiyin haka ku daina. Kisani duk randa kika faranta wa mijinki rai shi da kanshi zakiga canji a gunsa kuma komai kika roka matsawan na dashi zai baki, amma ba kice sai ya baki kafin ki basa hakkinsa ba, hakan haramu ne. Allah ya tsaremu da aikata hakan ameen).
Bai k'yaleta ba sai kusan asuba, wanka yaje yayi ya kwanta, yana tunani irin halin Falmi sam baida k'yau.
Gidan Hajiya kuwa, da safe Indo tayi wanka tasaka Uniform d'inta purple da light purple, riga da skirt sai barret. Hijab ta d'auko ta d'aura akan kayan, Indo tayi kyau sosai,
Hasna ne ta kaita school d'in.
Suna zuwa school d'in registration office suka nufa.
Bayan sun gaisa da uncle d'in jiya, Hasna tace"gata nan mun kawota.
Uncle d'in yace"ok wata yarinya ya kira, yace"ta je SSS1A ta kira masa Sadeey S Adam da Sanah S Matazu.
Ko da yarinyan ta tafi, bata dad'e ba saiga su sunzo.
Nan ya had'a su yace"su je su zauna tare.
Sanah da Sadeey suka kama hannu Indo suka nufi class. Hasna kuma ta wuce school d'inta itama.
*MASU NIMAN WANNA BOOK 'DIN DA WA'YAN DA SUKE MIN MAGANA TA PRVT, PLS KUYI HAK'URI SAK'ONNI YANA YAWA, BA WULA'KANCI BA. KUNA TAMBAYA A GROUP DAN ALLAH. KUMA 'YAN GROUP MAI SHI KUNA BAYARWA COS MUTANE SUNA YAWA, KUMA GA MESSAGES 'DIN MASU YIN COMMENTS, SUMA ZAN MUSU REPLY, INA HรU DA NIYAR INA GA SAK'O IN CIGABA DA TYPING, AMMA SAI NA TSAYA TURAWA MUNAE, WASU IN BAN TURA MUSU AKAN LOKACIBA SUNA FA'DAN BAK'AR MAGANA DUK IYA K'OKARIN DANAKE AMMA BASA GANI, DAN ALLAH FANZ A TAIMAKA ANA TURAWA A GROUPS IN AN TAMBAYA PLS N PLS*
GA WANNAN KUYI HAK'URI BAYAWA KAINA YA DAMEN DA CIWONE NASO NAYI YA FI HAKA๐๐ป.
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM๐*
[9/12, 8:17 PM] ๐ฌ๐๐Salma๐๐๐ฌ: [7/7/2016] Rash Kardam ๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป
๐๐ปBABBAN KUSKEREN๐๐ป
๐๐ปDANA TAFKA ๐๐ป
๐ป๐ป๐ป
๐๐ป๐๐ป
NA
ยฉRASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-174~176.
Sanah da Sadeey suka nufi class da Indo, ni ko Rash ina biye da su.
Tun shigarsu class, yan aji suka fara tambayan Sanah da Sadeey wacece?.
Sanah suka sharesu ganin sunyi hanyar sit d'in da ke k'usa dana su, wani yaro yace"kai new comer ce fa.
"Jiya ina gani aka kawo ta.
Wasu sukafara cewa ke kizo nan ki zauna, wani yaro yace"kai gaskiya tana da kyau.
"Zamu zama frds ko?.
Wani kalo Sanah ta musu, wanda yasaka shi yin shiru yana dariya.
Sit d'aya aka bata kasancewa kowa da sit d'insa, had'e da kuma lokansa na ajiye wasu littafa.
Sanah ce a farko sai sit d'in Indo a tsakiya sai Sadeey a baya. Ana haka Uncle d'in Biology yazo, darasin da yamusu shine. *CELL* sai da ya gama darasi yayi bayani sosai, ko da yazo yin Evaluation, ya tambayesu kamar haka, "class what is cell?.
Shiru ba wanda ya d'aga hannu, sai Indo ta d'aga hannu, ya nuna ta, Indo ta mik'e tafara cewa"Cell is the fundamental total unit of life. Cikin salon da take karatun, abun burgewa ne, bare muryanta tamkar mai yin busa. Tana gamawa tun kafin malamin ya bada umurni a tafa mata, 'yan class suka d'au sowa da tafi. Jikake raf raf raf, sannan malamin yace"well done good girl clapp for her once again.
A haka har aka tashi. School bus ne ya maidata gidan Hajiya.
Washe gari ta koma gidanta, Haka rayuwa taci gaba da tafiya, kulum school bus ke zuwa d'aukan Indo ya dawo da ita.
Sannu a hankali sun shaku dasu Sanah da Sadeey, anan ne ma take sani asai Sanah yar gidan bababn Malaman nan ne mai wa'azin biki da gyaran Amare. Sai Sadeey kuma gurin gayu ba'a barta a baya ba. Niko Rash nace"lalle abun yayi wato kaya, ya tsinke a gaban mai kaba.
Aisha ta soma kilewa, duk da haka ita take aiki a gidan Falmi, ko kad'an bata nuna gajiyawarta, Haiydar ko ya saba da girkinta duk randa bata gida, ko ya je Hotel baya iya cin abincin su.
Indo ko mungun kama kanta take bata bari ma ya ganta bare ya nimi takura mata.
Falmi ko bala'in yau da ban nagobe da ban, Meesha lurv da Zarah BB sun bata shawaran ta kama kanta, ta fita hark'ar Indo tak'i, sabida duk randa Indo ta waye sai ta gane KUSKURENTA amma fir taki, tana bin shawaran mugayen k'awayenta, hakan yasaka suka zuba mata ido.
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM๐*
[9/12, 8:17 PM] ๐ฌ๐๐Salma๐๐๐ฌ: [7/8/2016] Rash Kardam ๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป
๐๐ปBABBAN KUSKEREN๐๐ป
๐๐ปDANA TAFKA ๐๐ป
๐ป๐ป๐ป
๐๐ป๐๐ป
NA
ยฉRASHEEDAH .A. KARDAM
ยฎNAGARTA WRITERS ASSOCIATION.
Pg-180~183.
Da k'yar Haiydar ya iya jan k'afarsa, zuwa gun motarsa ya shiga.
Yana shiga motar sai da ya d'an zauna, don gabad'aya ganin Aisha, ya haddasar masa da kasala a jikinsa.
Kansa ya d'an jingina a steering motar, ya lumshe idanunsa, ba abun da ke gani illa fuskan Aisha, da suran jikinta, suna masa gizo a idonsa.
Imagine ya farayi, wai ga Aisha tazo, cikin tafiyarta mai burgewa, kusa da shi tazo, tana masa k'wark'wasa, sai da ta matso kusa dashi, kiss ta manna masa a baki.
Shiko sai wani murmushi ya saki, tare da k'ara lumshe ido, wayarsa ce tayi k'ara, sai da yaja karamin tsaki, don bai so ya katse tunanin da yakeyi ba.
Ni ko Rash nace"da ka tafi sabgar gaban ka ne, da zaifi maka wanna kayan jaki da karan.
"Don yanzu Indo ta maka nisa, yanzu Indo matar manya ce.
Wayarsa ya zaro, sunan Falmi ya gani akan scream d'in wayan, tsaki yayi kafin ya d'aga wayar.
Cikin muryansa da ba yabo ba fallasa yace"hello ya akayine?.
Daga b'an garen Falmi tace"Haiydar pls ka turan kud'i a cikin account d'ina, ina..... Bai bari ta k'arasa ba ya katse kiran.
Ransa duk ya gama b'aci, sai huci yakeyi, cikin zuciyarsa ko cewa yake"wai ya rinyan nan tana da hankali kuwa?.
"Bata san hakki na da ke kanta, ta sauke ba amma ta iya tambayan kud'i?.
"Rabon da Falmi ta zo d'akina na manta, wai sai kasuwanci ta saka a gaba.
"Dole in d'au mataki akan ta.
Motarsa ya ja ya fice abunsa, zuciyarsa ko sai zafi take masa, don shi yanzu ya gaji da halin Falmi, ta soma hawan masa kai sosai.
Aisha ko tana fita daga gidan, gidan Hajiya ta wuce, tana shiga ta perker motar ta fito. Masu aikin gidan sai sannu suke mata, cikin girmamawa ta amsa musu.
Cikin falon ta nufa, da sallamarta ta shiga falon, Hasna da ke goge TV da gudu tazo ta rungumeta, tace"haba Aunty eeshat kinanan kwana biyu?.
Aisha tace"washhh nikam sakeni karki karyani, gwamma ke.
Hasna ta saki dariya.
Aisha tace"Hasna ina Hajiyata ban ganta ba?.
Hasna tace"ta tafi dubiyar maralafiy.
Aishat tace"Allah ya dawo da ita lafiya.
Hasna ta kalli Aisha sama da k'asa tace"Baby Eeshat irin wannan wanka haka?.
"Gaskiya zaki rikita Yayana.
"Hmm Aishat duk gayuna yanzu kin d'aramin sosai, sai dai mu biyo bayanku.
Wani lalalusar mirmushi Aishat ta saki tace"ke ban son iskanci fa.
Hasna tace"gaskiya ne ae, ko da yake hausawa sunyi gaskiya da sukace, bakauye bai iya wayewa ba. Cikin zolaya tayi maganan, dariya suka saka dukkansu.
Aishat tace"barin je gidansu Sanah suna jirana zamuje saloon ne.
Hasna tace"okay! To sai kin dawo.
Har jikin motarta Hasna ta rakata, tashiga ta ja motar ta bar gidan.
Hmm masu karatu kenan Indo mu na da ne tawaye.
Gidansu Sanah ta shiga, tana ajiye motar tashiga gidan, Sadeey tace"ae na d'auka bazakizo ba.
Rausayar da kai Aishat tayi, tare da had'a hannu alamar ban hakuri, tace"tuba nake amin afuwa.
Sanah ne tafito da gyale suka wuce, sai yamma suka dawo, sai da ta ajiyesu a gida ta nufi gidanta.
Tun a harabar gidan, taga motar Haiydar yadawo, cikin zuciyarta ta fara tsara irin rikitasa da zatayi yau.
Tana shiga gidan bakowa a falo, side d'inta ta nufa, kaya ta cire tukun tayi wanka, saida ta tsane jikinta, tukun ta zauna a gaban madubi, ta kusa d'aukan awa d'aya tana k'waliya.
Three quarter ta d'auko tare da wani riga marar hannu, irin wanda ake d'auresa a wuya, rigan kalar ja, sai ta d'auko ribom ja ta d'aure kanta, bak'aramin k'yau tayi ba.
Main falo ta fito, sai da ta kunna CD, ta d'auko kaset d'in waka tasaka, don niman magana ta k'ure speaker, don ta san Haiydar baya son hayaniya sosai.
Kitchen ta shiga ta had'a zob'o, daman tayi girki kafin ta fita, a plate tasako a binci ta fito falo, ta zauna abinci taci ta k'oshi, ta tattara plate da cups d'in ta mayar kitchen.
Falo ta dawo sai da ta huta, ta je gun speaker ta k'ara volume a hankali tafara rawanta, cikin salon k'warewa take gir-giza jinkita.
Haiydar ko na bacci ya ji kid'a na tashi, har sai da ya toshe kunnesa, cikin masifa ya nufo falon, ko da ya iso falon kasa motsi yayi, don gani irin rawan da Aishat takeyi.
Aishat kuwa ganin Haiydar da gan-gan tasoma matsowa kusa da shi tana rawa.
ยฎNWA.
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM๐*
[9/12, 8:17 PM] ๐ฌ๐๐Salma๐๐๐ฌ: [7/8/2016] Rash Kardam๐: ๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป
๐๐ปBABBAN KUSKEREN๐๐ป
๐๐ปDANA TAFKA ๐๐ป
๐ป๐ป๐ป
๐๐ป๐๐ป
NA
ยฉRASHEEDAH .A. KARDAM.
ยฎNAGARTA WRITERS ASSOCIATION.
Pg-184~186.
A hankalin take rawa, mai d'aukan hankali, harta iso gun Haiydar, hannusa ta kamo tana rausayawa tamkar yanda turawa suke in suna rawa. Kwanto da fuskanta tayi akan k'irjinsa tare da lakace hancisa, ta d'ago da kanta tazo dai-dai kumatun Haiydar, ta sakar masa lafiyayan kiss, wanda sai da numfashin sa ya kusa d'aukewa. Salon rawan ta canza zuwa na India, da gudu tayi side d'inta, don tasan in ta k'ara minti biyar