Showing 33001 words to 36000 words out of 42941 words
Chapter 12 - BABBAN KUSKURE COMPLETE BOOK BY RASHEEDAH A KARDAM.txt
na zama Hasna ta nufi k'ofar d'akin Haiydar ta kwan-kwasa kamar a kunne Falmi sai gata ta fito tana karairaya ganin Hasna ta ja tsaki ta ce"ke lafiya zaki zo kina tashin mutane da safen nan?". Hasna ta kalleta a wulakance ta ce" gun d'an uwana nazo ni da Mahaifinsa ke son ganinsa". Falmi tayi dariya kice min ke da tsoho kuka zo". Ran Hasna ya baci ta juya ta koma falo Falmi ta biyo bayanta ta ce"aa Tsoho ne haka a gidan mu". Abba yana jin ana bada labarin rashin kunyan Falmi bai tab'a gani ba sai yau ransa ya b'aci sai karairaya take tana fad'an banzan magana Haana cikin fushi ta kaiwa bakin duka wanda saida jini ya zuba, Abba kasa cewa komai yayi ila fitowa daga gidan Hasna ta kalleta ta ce" ki iya da bakin ki don bazaki tab'amin iyaye na kyaleki ba banza shasha". Fuuuu Hasna ta bi bayan Abba sai a lokacin suka ga motan Haiydar kenan yana gida. Ran Abba ya gama b'aci amma ya daure ya boye ya ce"Hasna muje gida ki d'auko ma Aishat wasu kaya acikin kayanki". Haka ko akayi suka dawo Asibiti da kayan Hasnat. Satin Aishat d'aya a Asibiti aka sallameta jiki yayi sauki, wanda duk kwanakin nan Haiydar bai tab'a tako k'afarsa ba abun yayi ma umma ciwo amma taki nunawa a b'an garen Aishat ma haka.
Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b'an gare na zuciyarsa baya kin dad'in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya.
*®NWA*.
*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDIL SHAKUR)*
*RASH KARDAM💕*
[7/17/2016]Rash Kardam 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🙆🏻BABBAN KUSKEREN🙆🏻
🙆🏻DANA TAFKA 🙆🏻
🌻🌻🌻
🙆🏻🙆🏻
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-219~220.*
Hajiya tasa ka Hasna taje ta d'iba ma Aishat duk wasu abunda zata buk'ata ta koma gidan su da zama kulum tana cikin sanyaya mata zuciya akan halin Haiydar.
Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b'an gare na zuciyarsa baya jin dad'in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya sai dai abun na damunsa a cikin zuciyarsa kulum yana cikin tagumi da damuwa.********************
8months latter.
Cikin wa'yan nan watannin abubuwa da dama sun faru harda fara jaraban Aishat sunyi WAEC yanzu suna NECO har sun kusa gamawa, yanzu driver Hajiya ta samar mata shi ya ke kai ta ko ina, Hajiya kuma ta dage da addu'a akan halin da Haiydar ke ciki tanayi kullum bata daina ba.
Rayuwan Falmi da Haiydar ko abin tausayi don tana gasa masa aya a hannu bana wasa ba duk ya rame yayi baki kamar ba ASP A.K BABA ba. Kuma duk da tsareshi da Falmi keyi bata bashi hakkinsa wataran sai ya mata kuka kafin tasa ya ajiye mata kud'i tukun ta kulashi, a hakama sai ya sha masifa kafin ya samu.
Tabbas Allah baya bacci kuma shine maji rokon bawansa don shi ya ce mu rokesa zai amsa mana sai dai ya jinkirta don ya ga imanin bawansa. Haka abun ya faru a gun Hajiya don yau Haiydar yana office yaji kaman an tsikaresa take ya tuna abunda ya faru da irin rashin zuwa gun iyayensa har kuka sai da yayi, cikin hanzari ya mik'e ya nufi gida wanka yayi yasaka kaya mai kyau ya fesa turare yayi kyau amma ya rame yayi duhu amma kyansa nanan hancinsa ne yakara fitowa. Ya fito falo sai zuba k'amshi yakeyi dai-dai lokacin Falmi ta fito ganin wanka da yayi ranta ya b'aci da sauri ta nufosa sam yau ta manta bata shafa turare bare ta kuskure bakinta da magani ta ce"kai Haiydar ina zakaje harda yin wanka haka? Ko kamanta kana k'ark'ashin izini nane?". Bai tanka mata ba don zuciyarshi na azal-zala ganin zai fita tazo tasha gaban sa daman yana cike da ita yanda da safe tayi ta masa tsawa kamar shi d'anta ne, kwalan rigan sa ta sha cikin hanzari ya bata kyawawan mari ya fara ball(kwallo) da ita saida ya jibgeta son ransa ya fita, motarsa ya shiga sai gidan Hajiya masu gadi na ganinsa sai da sukayi mamaki da sauri ya ajiye motarsa ya nufi cikin gidan da sallamansa ya shiga, Aishat ya fara hangota tana jikin Hajiya Hasnat ma ta hango shi kasa d'auke idonsa yayi akan Aishat Hajiya na ganin sa tayi hamdalah amma ta d'aure fuska dole ta gwada masa kurensa duk da ba da sonsa bane. Hajita ta ce"Hasna Aisha maza tashi ku shiga d'aki da sauri suka mik'e Aishat duk da taji dad'in ganinsa amma zuciyarta na suya da abunda ya mata da sauri tayi d'akinsu da gudu ta fad'a kan gado ta fara kuka mik'ewa tayi ta d'au hoton Abban ta da Ummanta da na iyayen Abban ta tare da awarwaron zinari mai tsada da kyalli nan tasa a gaba tana kalon su tana kuka. Hajiya ta ce"lafiya dai ko? Amma b'atan kai kayi yau ko?" Ya russuna ya gaida ta ta amsa cikin sakin fuska san nan ta ce"yauwa da man kai nake jira tunda yau Allah ya kawo ka inaso ka ba ma 'Yata takardan sakinta don bazata koma gidan ka ba wannan shine hukunci dana yanke kuma umurni nake baka ba wai shawara ba". Haiydar ya durk'usa akan k'afarsa ya soma kuka yana bata hakuri. Hajiya ganin ita tsaya kallonsa zai sa ta kayara ta mik'e ta bashi guri d'akinta tashiga taga Hasna ita kad'ai ta ce" Hasna ina Aishat d'in?" Hasna ta ce" tana d'akin mu ina ga". Hajiya ta mik'e ta nufi d'akin su sam Aishat tayi nisa cikin tunanin iyayenta bata san da shigowar Hajiya ba. Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k'arso da sauri don ganin hoto hannuta wannan Awarwaron gwal d'in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k'irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d'aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad'in La....mi.....d bata k'arasa ba ta yanki jiki ta fad'i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d'akin ta saki razananne k'ara tayi kanta.
Ni Rash danake gefe na ce" to mai ke shirin faruwa kar dai ace......... Bari dai zamuji koma miye.
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM💕*
[9/12, 10:05 PM] 🍬🛍💍Salma💍🛍🍬: [6:58PM, 7/18/2016] Kardawiya😎: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🙆🏻BABBAN KUSKEREN🙆🏻
🙆🏻DANA TAFKA 🙆🏻
🌻🌻🌻
🙆🏻🙆🏻
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-221~222.*
Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k'arso da sauri don ganin hoto hannuta wannan Awarwaron gwal d'in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k'irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d'aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad'in La....mi.....d bata k'arasa ba ta yanki jiki ta fad'i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d'akin ta saki razananne k'ara tayi kanta. Hasna ta fara jijiga Hajiya amma ina ta sume Aishat ma da sauri ta sauko tazo ta k'ank'ame Hajiya tana kuka, Haiydar da ke falo jin k'aran Hasnat yasa ya hauro sama da gudu ya nazuwa yaga Hajiya a k'asa duk ya rud'e sai da ya jijigata da sauri ya mik'e yayi cikin bayin d'akin ya d'ibo ruwa yana zuwa ya watsa mata, ya k'ara watsa mata take ta saki sassanyan ajiyar zuciya gefen idonta hawaye ne ke zuba. Ta ja jikinta ta jin gina da jikin gado Haiydar da su Aishat sai sannu suke mata Haiydar ne ya bata ruwa mai sanyi tasha ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce"Aishat ina son ki fad'amin gaskiya dan Allah ina kika samu wannan awarwaron da hoton d'an uwana k'anina Lamid'o wanda shekara da shekaru ya rasu?". Haiydar da Hasna sun zuba ma Hajiya da Aishat ido suna masu mamaki da rud'u a cikin al'amarin Aishat jiki a sanyaye ta ce"Hajiya wannan hoton Mama na ne da Baba na sai d'ayan kuma Mama na ta ce Baba na ya ce mata Kakan ni na ne suke d'ayan". Cikin hanzari Hajiya ta mik'a hannu zuwa inda hoton ya ke ta d'auko tabbas ko makawa babu Lamid'o ne d'aya hoton kuma ita ce a ciki tana budurwa sai Lamid'o yana k'arami ya dai girma ba sosai ba sai Iyayensu dukkansu sanye suke da alkyabba wanda taji ado da k'ayatarwa cikin rashin fahimta ta ce"Aishat ban fahimce ki ba kina so ki ce min Lamid'o shine Mahaifin kuma kenan bai mutuba?". A fili ta ce"Aliyu to kodai in mutum ya mutu yana dawowa ne?". Aliyu ya kalli Hajiya tabbas bata hankalinta don a rud'e take. Aliyu cikin sassanyar murya ya ce"ai duk wanda ya mutu baya dawowa sai dai in daman bai mutum ba". A hankali ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce"Aishat ina so ki bani labarin ki iya yanda Mahaifiyarki ta sanar dake". Ba tare da b'ata lokaci ba Aishat ta basu labari ta harzuwan Mamanta garin Bauchi, idon Hajiya cike da kwalla ta ce"tabbas ke 'Yar Lamid'o ne ga saida nan wannan awarwaron da kuma cewa Mahaifiyarki ta je Gombe ta nimi 'Yan uwansa da hoton nan ya isa sai da bare wasu sassan jikinki duk irin na Mahaifinki ne shiyasa ko da yaushe nake jinki a jikina tamkar 'Yar dana Haifa, a sai da 'Yata nake tare nan Hajiya ta fashe da kuka wanda itama Aishat kukan farin ciki takeyi Hajiya ce ta mata alamar tazo kusa da ita tana zuwa suka rungumi juna suna kuka zuwa wani lokaci suka tsagaita Hajiya ta kali Aishat ta ce"ke ba 'Yar shege bane da ake fad'a miki haka ke 'Yar gatace kuma 'Yar dangi kafin muje gimbe ya kamata ki san ko ke wacece kuma waye shi Muhammad Lamid'o". Haiydar ko yafi kowa farin ciki da bayyanan iyayen Aishat asai 'Yar uwansa ce kanwan sa tabbas sai yanzu yake jin kunyan zagin shegen da yamata tabbas yasan dole yanzu Hajiya ta k'ara hura masa wuta a kan Aishat don yasan yanda Hajiya take tsananin son d'an uwata Lamid'o bare ace yarsa dole ya k'ara kwantar da kai. Hajiya ta ce"Kamar yanda ki ka gani a hoton nan Mahaifin mu Sarkin Fulani ya kasance shahararen mai kud'i a cikin garin Gombe tun asalin Kakan mu shine sarkin Gombe kinga kenan wannan Sarautan tana k'ofar gidan mu ne lokacin da Kakan mu ya rasu sai ya zamana Mahaifin mu Sarkin Fulani bazaiyu a bashi Sarauta ba, sai aka d'auka aka bama Wazirinsa kinga daganan Sarauta ta bar gidan mu kenan ko da Mahaifin mu ya girma ba halin k'arban Sarauta sai aka bashi Sarkin Fulanin Gombe wanda alokacin matan sa biyu ne sai nice 'Yarsa ta farko kuma bai kara haihuwa daga kaina ba sai bayan shekara biyar aka Haifi Muhammad wanda ake kira da Lamid'o kasancewan shine d'a namiji d'aya ma Sarkin Fulani ya d'auki son duniya ya d'aura masa wanda hakan ya ke kona ran Kishiyar Hajiyan mu tun yana k'arami take kai masa hari da niyar kasheshi Allah bai bata sa'a ba har yasoma tashi, ana haka akayi aurena da Baban su Aliyu muna zama a cikin garin Gombe lokacin a gun yake aiki kafin mu dawo Bauchi da zama kasancewar shi d'an k'aramar hukuman Katagun ne da ke Bauchi, bazan manta da ranar da Abban mu ya dawo daga saudi ba rannan nazo gida masa murna da dangi duk mun had'u a gida".
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM💕*
[9/12, 10:05 PM] 🍬🛍💍Salma💍🛍🍬: [10:16PM, 7/18/2016] Kardawiya😎: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🙆🏻BABBAN KUSKEREN🙆🏻
🙆🏻DANA TAFKA 🙆🏻
🌻🌻🌻
🙆🏻🙆🏻
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-223~224.*
Abban mu ya dawo daga Saudi na zo gida masa sannu da dawowa da wasu dangi bayan ya huta ya ciro tsara ba ya bai ma 'Yan uwa da abokan arziki ya raba musu su Hajiyar mu ko wanna awarwaron ya sayo musu wanda kud'insa bana wasa bane anan yaraba musu ana bama Hajiyar mu nata Lamid'o yasa kuka shidai sai dai abasa wannan awarwaron ne na zinari ya masa kyau ba irin rarrashin da ba'a masa ba yaki nan Hajiya ta d'auka ta bashi kyauta. Haka rayuwa yaci gaba da tafiya Sarkin Fulani na gwada mana gata kasancewar mukad'ai ya haifa 'Ya'ya biyu bayan wasu shekaru Lamid'o ya girma a kwai ranar da bazan manta ba ranar da muka masa ganin k'arshe ranarda kishiyar Hajiyar mu ta aiki driver (mai tuk'a mota) garinsu Lamid'o naji zasu tafi ya ce shi sai ya je Alkaleri kasancewar ita 'Yar garin ne nan Lamid'o ya d'au yar jakarsa yasa kaya kala 2 kasancewarsa mai tsafta ne kuma sai washe gari zasu dawo, kuma duk inda ya ke baya rabuwa da hoton iyayen mu wanda mukayi tare don shima ya shaku da baban mu sosai, suka tafi da driver(mai tuk'a mota) can kusan yamma sai ga wasu mutane da kukan su wai Lamid'o sunyi hatsari harshi kamma ya kone k'urmus sai tokan sa akà gani to kinji labarin rabuwan mu da Lamid'o wanda sanadin rasuwarsa yasa hawan jini ya kama Hajiyar mu itama bata dad'e ba Allah ya mata rasuwa. Aishat wacce take hawaye ta sauke ajiyar zuciya Hajiya ko ta ce"Hasnat je d'aki ki d'auko waya na kira Abba na in sanar masa don na san zaifi kowa farin cikin ganin 'Yar Lamid'on sa" Hasna ta d'auko waya Hajiya ta kira Sarkin Fulani ta koro masa bayani cike da murna wanda sai da yayi kwalla harda sujudu shukur yayi nan take yasa aka bama Aishat suka gai sa. Hajiya ta karb'i wayar Sarkin Fulani ya ce" Gobe ku biyo jirgi da wuri kuzo naga jikata don bana jin dad'i ne ni da yau nazo". Hajiya ta saida masa suna zuwa, take Hajiya ta sanar ma Babansu Haiydar shima yayi murna ya ce"in Allah ya yarda cikin satin nan shima zai dawo". Haiydar shi ya je ya musu komai harda shi a tafiyan, ranan Aishat kasa bacci tayi dan farin ciki da murna harda yi nafiloli ta gode ma Allah tare da addu'a Allah ya jikan mamanta.
Washe gari da safe suka shirya sai gombe, tun daga Airport suka ga jerin dogaraye suna jiransu ga wata rantsaysiyar lemozine k'atuwa da akaje d'aukarsu a cikin ta. Aishat kam in banda kalo ta dawo kamar 'Yar k'auye sai kale-kale takeyi har suka zo wani k'aton katafaren gida wanda in aka bar Aishat sai ta ce wannan shine white house da ake fad'a na Abuja. Suna sauka nan dogaraye suka fara gaishesu har suka shiga falo, Sarkin Fulani dake Falon idonsa nakan Aishat tabbas wanan jinin sa ne take idonsa ya kawo kwalla duk da yana daurewa hannu yamata alamar tazo ya rike hannuta tare da dafa kanta yana hawaye ji yake kamar Lamid'o ya rike sai da suka zauna kowa ka gani fuskan sa d'auke da fara'a da farin ciki in ka d'auke Hajiya k'arama da ko dariya batayi nan Sarkin Fulani ya sake niman jin k'arin bayani Hajiya ta basa labari Aishat ma ta d'aura da iya sanin ta nan ya rungumi jikarsa yana kuka itama tanayi. Ana haka sukaji an turo k'ofa tare da sallama dukkansu suka d'ago kai tare da kallon k'ofar ko ni ma Rash dana kalli k'ofar wani farin bafulatani dogo mai karan hacci kyakyawane wanda za'a kwatanta a gurin