Showing 15001 words to 18000 words out of 42941 words
Chapter 6 - BABBAN KUSKURE COMPLETE BOOK BY RASHEEDAH A KARDAM.txt
π»π»π»
ππ»ππ»
NA
Β©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-141~145.
Suka d'au hanyan gidan sa, Indo ko in banda hawayen takaici babu abunda takeyi, tana rokon Allah ya kawo mata d'auki a rayuwanta.
Haiydar ko bai kyale Falmi sai da ya tabbatar ya gamsu sosai, ya mike ya shiga wanka. Bayan ya fito yayi Sallah isha'i kenan ya d'auko wayarsa, mai zai gani 60miss call na Hajiya 20 na Sadiq 46, sai na Ghali da wasu abokansa, sam ya manta da zasuje dinner sai a lokacin ya tuna, cikin hanzari yasa d'anyar boyal d'insa mai ji da shek'i, ya kawo agogon hannu ya d'aura ya sanya takalminsa, ya d'auko hularsa itama fara yazo gaban miro ya na d'aurawa, Falmi dake kwace jiki ba k'arfi ta mike cikin zuciyarta ko cewa take"nayi ma kaina gashi ban hanasa zuwa dinner ba, gashi ya gurjeni son ransa amma dole na b'ata kwaliyan nan kuma bazaije ba.
Tana d'ingisawa tazo ta tare qofan fita Haiydar ya gama shiryawa yazo zai wuce tace"baka isa ba yau kaje dinner auren wata marar asali.
"Yar titi kuma tsintaciyar mage bazai yuwu ba.
Haiydar yace"kiyi hak'uri ana jira na kuma kinga mutane sunzo doni ne.
"Ni badan Yar aiki zanije ba.
"Sabida mutanen da suka taru domin ni zanje in fita kunya.
"Falmi kinsan ina matuk'ar qaunanki.
Falmi tace"k'arya ne *MAYAUDARI* maha inci kawai.
"Da kana sona bazaka yarda ka auri Indo Yar aiki na ba.
"Haydar yau ko ni ko kai don ba inda zakaje maci *AMANA* kawai.
"Ka kasa rike *AMANA TA* da iyayena suka baka.
Ganin zata b'ata mishi lokakaci ya d'auko key zai bud'e qofa tazo ta rike hannu qofar. Ganin bata da nutsuwa a tare da ita, kuma ya mata magana duk taki fahimta. Wata zuciya tace"bata k'yak'yawan mari zata fi fahimtan wannan yaren.
Sai da ya gyara hannusa ya bata lafiyayen mari, take Falmi takoma gefe don sai dataga wasu Stars suna mata shining. Haiydar ya bud'e qofa har yafito harabar gidan yana shirin sanya k'afarsa waje kenan, Sai ga su Sadiq nan suka fara tambayamsa lafiya?.
Sadiq ya fara masa surutu Haiydar yace"mutafi lokaci ya kure.
Yazo sai shiga mota kenan, Falmi ta fito da gudu ta rik'e murfin motan tana cewa"yau ba inda zakuje indai inanan.
"Alo tsiya alo danja ba mai fita da kai.
Cikin takaici ya tureta ya rufe motar.
Falmi batayi k'asa a gwiwa ba ta je ta tatare gaban motar tabaje tana cewa"yau sai dai in ta kaina zakubi ku fita ehe.
"Sai ku kasheni in huta.
Haiydar bai ma lura da Indo da take gefe tana hawaye ba. Takaici duk ya ishesa da kunya, gashi a gaban abokansa.
Sadiq ya mata Horn amma taki matsawa sai ihun da take kurma musu kamar masu satan mutane. Cikin zafin rai Haiydar ya bud'e qofar mota.
Ga d'an wannan ina samu lokaci zakujini da daddare in nasamu lokaci, in bansamu ba kuwa sai bayan *SALLAH* In Allah ya kaimu da rai da lafiya.
DEDICATED TO
AISHA MUHAMMAD
(MAMAN ABDUL SHAKUR).
RASH KARDAMπ
[9/12, 8:17 PM] π¬ππSalmaπππ¬: π»π»π»π»π»π»π»π»
ππ»BABBAN KUSKERENππ»
ππ»DANA TAFKA ππ»
π»π»π»
ππ»ππ»
NA
Β©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-146~150.
Sam Haiydar bai ma lura da Indo, da take gefe tana sharan k'wala ba. Sadiq ya mata horn amma Falmi taki matsawa, sai ihu take musu kamar wacce tayi hauka. Cikin zafin rai da qunar zuciya Haiydar ya bud'e murfin motan ya nufota, kasancewan gidan da hasken k'oyayen wuta, yasa ta ga Haiydar ya nufota. Sai data ga ya kusa da ita da sauri ta mik'e taje jikin motar ta bud'e side din da Indo take, ta soma shiga duk ta buge indo ta ture ta, tana shirin haye kanta ta zauna ne Haiydar ya finciko ta, cak ya d'agata tana turjewa sai da ya kaita dakinta, yasaka key ya fito. Duk ta ya mutsa masa kayan jikinsa. Takaici goma da ishirin ya had'u masa, zuciyar sa sai rad'ad'i take masa tamkar zata fito waje. Ji yake ina ma da zai iya kuka, tabbas da yaji sassaucin zafin da zuciyar sa ke masa.
Da k'yar ya janyo k'afarsa ya shiga mota, sai a lokacin ya lura da Indo da ta had'a kai da gwiwa tana rusan kuka. Nan yaji wani sabon bak'in ciki ya tur nukesa. Shi kenan shikan yazu ya rasa farin cikinsa, ga auren yar aiki, ga Falmi ta rikice masa. Bai san lokacin da yasaki wani tsaki mai k'arfi ba.
Haka aka ja motar duk da sun makara, suka nufi gun dinner, mutane har sun soma tafiya, MC ya fara magana da ayi a hakuri, a zauna ga ango sun iso. Sai da abokai suka shiga, ya rage daga Ghali sai Jiddah da Sadiq da Hasna, Su zasu shigo da Amarya da Ango.
Amarya da Ango a gaba, sai abokai a bayansu, bayanda Ghali baiyi ba akan Haiydar ya rike hannuta fir yaki. Harda d'an matsawa gefe, ya bar tazara a tsakaninsu. Jidda ta jawo Ghali tace maasa" kasan me kai ka dawo gefen Ango, ni zan dawo gefen Amarya, in munzo dai-dai qofar shiga ka d'an ta kurasa. In hanyar yaji ya takura, dole zai matsa ya mannu da Amaryan. Hasna kuma saita san yanda zatayi, ta manna hannusu guri guda, nasan ba haufi zai rike hannuta. Aiko haka akayi Jiddah ta cike gu, wanda yasaka Indo matsawa kusa da Ango, shi ma haka Ghali ya masa, dai-dai lokacin DJ ya sake musu kidan Loakcin kine yayi Amarya yar *AMANA*. Kasancewar Haiydar na son wak'ar, bai san lokacin da ya saki lallausar murmushi, wani farin ciki ya ratsa zuciyarsa, yasoma bin wak'ar a hankali. Hasna ko hannu Indo ta kama ta d'aura kanna Haiydar. Take yaji wani sanyin dadi ya ratsa zuciyarsa, sai ya samu kansa da k'ara rik'e hannun. Ya d'an janyota jikinsa, sabida laushin fatarta da kanshim da ke tashi a jikinta, ya mantar da shi da wa ma yake tare.
Indo ko sai niman zillewa take, don tun da take in banda ranar da suka dawo daga gidansu Haiydar yayi hug d'inta sai ranar walima, namiji bai taba mata irin wanann rikon ba, sai yau. Shiko sai janyota yakeyi cikin jikinsa. Masu k'aratu karkuga yanda suka burge, suna sanya k'a farsu cikin Hall d'in, masu d'aukar photo suka fara, Jiddah tace"ma Hasna bari kuga next target d'in mu. Hasna yi sauri ki d'an zo kusa da Aisha, kin ga ta kalminta na da tsayi, ki d'an samata k'afa kamar zata fad'in, zai taro ta tunda kinga rabin jikinta ansa yake, ba zai bari ta fad'i ba. Ina son ayi shooting d'insu a haka don ya isa gun Falmi, ni kuma zan d'aukesu da IPhone d'ina. Sai ki tutura masa a wayansa. Hasna ta d'aga ma Jiddah hannu, ta sara mata alamar target d'in yayi. Hasna ta yi saurin sanya ma Aisha Indo k'afa sai gata zata fad'i, da sauri Haiydar ya tarota, ya rik'ota duk gaba d'aya ajikinsa take, ita kuma ta rufe ido ta sadak'ar fad'uwa zatayi, shiko kallonta yakeyi, da d'an k'aramin bakinta nan, mai d'aukar hankali. Sam ya manta ida suke, sai ji yayi ya samu kansa da yi mata kiss a lab'en bakinta. Haiydar sai da ya wani lumshe ido, azuciyar shi ko cewa yake"tabbas mata suna suka tara. Don kiss d'in da yayi ma Indo, wani laushi yaji a leb'en bakinta, ga k'amshi gamida zaki. Jama'an da suke hall d'in, abun ba k'aramin burgesu yayi ba, take suka saka sowa da ihu. Masu camera kuwa suna kan aikinsu, haka Jiddah ma ta d'aukomai harda yin editing. Abun sai wanda ya gani, Don ko ni Rash sun burgeni, amma ina tunani photo nan in ya isa gun Falmi da k'aramar yaki.
Haiydar cak ya d'aga Indo, bai ajiyeta ko ina ba, sai kan kujeran da aka musu mazauni, ya sak'aka hannusa cikin nata. Hasna da Jiddah ko sai murna suke, don ba wanda zai gane cewa Haiydar ba son Indo yake ba, niko Rash na tab'a k'awata Lovely Aisha Mazoji nace"Lovely kin ga kirsan mata ko, da kirsa da dabara Jiddah tasa Haiydar ya manta k'iyaya, ya shagala da soyayya. Aisha Mazoji tace"taya ni gani kam, kuma in an tab'ashi, ya iya kurin baya son bak'ar mace, sai gulmar tsiya.
"Kiga yanzu a gaban mu harda mata kiss fa.
Nace"hmm kedai bari kawai zamuga yanda wannan drama zai k'are.
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAMπ*
[7/4/2016] Rash Kardam π»π»π»π»π»π»π»π»
ππ»BABBAN KUSKERENππ»
ππ»DANA TAFKA ππ»
π»π»π»
ππ»ππ»
NA
Β©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-151~155.
Haka aka gudanar da dinner kowa cike da farin ciki, Haiydar kam tun da ya rike hannu Indo ya kasa saki. Sai da aka gama taro suna sauk'owa Sadiq ya kasa hakuri yazo kusa dashi, yace"ASP Aliyu Khaleed Baba. Sai da Haiydar yayi murmushi yace"Haka sunan yake A.K Baba. Sadiq ya cigaba da cewa "gaskiya yau naga lurv, wato wannan kiss d'in ma duk acikin kiyayyar ne ko?.
"Da tsanar bak'ar mace. Sadiq yana wani shu'umin dariya Hasna da ke gefe itama dariyan tafara, sai alokacin Haiydar ya dawo hayyacinsa, ko kalon gunda Indo take baiyiba, ya tureta wanda k'ad'an ya rage ta fad'i, Hasna ta taro ta. Ghali yace"kaga Man d'in nan kora kunya da hauka zaka mana. Ko sauraronsu baiyi ba ya nufi mota. Indo ko daman atakure take don tayi hawayen har ta gaji, ba wanda ta bari ya gane kuka take, ta b'oye har aka gama taro. Hasna ta rikota, tazo zata sata motar da suka zo, Haiydar ya daka mata tsawa"kee ina wasa dake ne?.
"Ni sa'anki ne?. Sadiq ya iso gunsu yace"mai kake nufi ne?.
"Da wani mota kakeso tashiga?.
Cikin harzuk'a Haiydar yace"in dai zata shiga motar nan sai dai in koma a qafa. Gannin yanda ya yake masifa, yasa Sadiq ko magana bai k'aramasa ba, Yace"Hasna kushiga mota in mai daku gida.
Hasna ta rik'o hannu Indo suka shiga mota sai gida.
Haiydar ko kansa ya jawo ya dawo gida. Ransu Ghali ya baci sun bar masa motan suka tafi.
Ko da ya dawo gida dakinsa ya nufa ya kwanta, baibi ta kan Falmi ba, bare yaja ma kansa magana.
Washe gari a harabar gidansu aka shirya crossing sword, police ne suka sha kakinsu da mopol, sai wasu friends d'insa yan *WAI BURGET* su kuma sun sanya kaya Green white green. Abun dai sai wanda ya gani. Police sun cire yan Colour paty da yan Sub gard n gard Commander. Haka yan WAI ma.
Ba abunda ke tashi a filim sai kid'an Band, har wata yar waka suke musu, da busa mai dad'in sauraro.
Amarya na hango cikin shigar cut less mai kalar blue da baki, sai handbag da takalmi blue da baki. Ta sha gwagwaro tayi kyau sosai da sosai. B'ab garen Falmi ko dak'yar su Meesha lurv da Xhara BB, su tursasata tasaka less light pink, gata fara bai mata wani kyauba. Fir taki tsayawa tayi make-up, duk kishi ya dameta. Ta dauro d'an kwali suka fito, gun Haiydar suka nufa, sai wani harara take aika masa, in ta ga Hasna ko ji take kamar ta shak'eta. Ana ahaka akace Amarya da Ango da Uwargida su fito za'ayi Inspection kafin a fara gabatarda bikin. Haiydar ne yazo dai-dai inda Falmi take yariko hannuta. Sai k'ok'arin fisgewa take, yace"kinga mutane a nan gwamma ki tsaya. Tsaki tayi masa ta kauda kanta gefe. Ana haka sai ga Jiddah da Hasna sun riko hannu Indo, ae take kalo ya koma kanta, don hatta mazan da ke gun sun yaba da tsarin kwaliyarta. Cikin nutsuwa take takawa, Haiydar tun da ya d'aga ido ya kalleta, ya kasa d'auke kai yarasa mai yasa duk lokacin da ya kalleta, sai yaji wani abu gameda ita. Sam ya shagala da kallonta, sai da Falmi ta mutsunesa ya dawo hayyacinsa. Hasna ta saka Indo a gefen damansa, yayin da Falmi ke hagunsa. Wasu police ne biyu da wuk'a a hannusu sai shek'i take suka mik'e, tare da sarawa da buga k'afarsu a k'asa. Ba tare da b'ata lokaciba masu band suka saki kid'an taken k'asarmu *NIGERIA*.
Duk wanda suke gurin saida suka mik'e tsaye, tare da kame domin girmama qasarmu. Cikin busa mai dadi, akayi kidan National anthem, yayi da mutane ke bin sautin kidan har aka gama. Mutanen dake gun suka saka tafi raf-raf.
Aka zauna nan masu band suka cigabada bugawa, ni da lovely na munsaki baki sai kalo muke, nan wayan nan police biyun nan suka soma paret, suka iso har gabansu Haiydar suka sara masa, tukunan su juya tare da buga kafa, sukayi masauni a gabansu. Anan masu kaya kalan green white green suma suka fito, bayansu Haiydar suka tsaya . Karan kidan ya fara tashi da k'arfi. Take suka soma zaga filin da paret, in gun manyan Haiydar suka je, sai ya sara musu in k'ananan sane, su sara masa. Masu camera sai d'aukarsu sukeyi. Sai da suka zaga ko ina, kafin suka zo suka zaun. Gard d'in police suka fara wucewa, suna parret suna zuwa gun Haiydar da iyalansa, sai su sara masa. Sai da police suka gama nasu kafin yan *WAI BURGET* suka faso karkuso kuga ihu da sowa, don yanda suke gudanar da parret d'indu, da tsarin komai abun burgewa ne. Fatyma S.Y itace parret commoder, yayi da Farida Jigides take yan colour patty. Gaskiya abun ya k'awatu sai wanda suka gani. Sai da aka gama parret tukun masu mik'a musu gifts suka taso.
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH LUVπ*
[9/12, 8:17 PM] π¬ππSalmaπππ¬: π»π»π»π»π»π»π»π»
ππ»BABBAN KUSKERENππ»
ππ»DANA TAFKA ππ»
π»π»π»
ππ»ππ»
NA
Β©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-156~160.
Ba yan gama wanan shagalin, Falmi ita da tawaganta suka koma gidanta. Yayin da Hajiyansu Haiydar ta kira Amarya d'akinta, ta bata wani abu a cofi tasha. Hajiya tace"ki k'wanta ki huta sosai. Sai da a kayi sallan magriba Hajiya tasa ta gaba taci abinci mai yawa. Hajiya ta saka ruwa a murhu, tare da lalle da magarya ya dahu sosai, sanna tasaka ruwa daban wanda ba komai aciki, ta juye farin ruwan a bokiti ta surka ta kai bayi. Kafin ta d'au wani bokitin ta tace ruwan lallen nan, da rariyan ta, sannan ta d'auko madaran turaruka kala-kala tasaka mata madaran turaren wanka acikin ruwan lallen. (Shi ruwan lallen ba'a cika ruwa da yawa sosai, d'an dai-dai za'a saka). Ta kai bayi tace"Aisha tashi kiyi wanka zaki ga ruwan biyu ne, kiyi wankan sabulu da farin, ki tabbatar ki dirje ko ina. Bayan kingama wankan sabulu, sai ki d'auki ruwan lallen nan zakiga ba yawa, ki tabbatar kin game jikinki dashi ta ko'ian.
Aisha Indo ta amsa da"to Hajiya nagode. Saukowa tayi tashiga bayi, wanka sosai tayi kafin ta yiwankan lallennan. Tun daga bayi k'amshi ke tashi har falo.
Hajiya ta taho da kasko k'arami, Indo na fitowa tace"zo nan.
Fallen zani ta bata, ta lulub'u dashi kafin ta samata kasko tare da zuba turarukan wuta aciki masu kamshi.(masu k'aratu amfanin wannan wankan lallen, da turare yana saka jikin mutun yayi k'amshi, sannan k'amshin yana kama jiki, yana sa mutum kara haske da kyau. Sannan a zuba turare aciki zaki ringa kamshi ne sosai. Idan mutum ya fito daga wanka, bazai bari jikinsa ya tsan-tsame ba. Da ruwan zaki saka turaren wuta a kasko ki luluba jikinki, sannan ki tabbatar kamshin turaren na bin jikinki, in turaren ya k'are ki k'ara sakawa har sai kin tsan-tsame.zakiji k'amshin ya kama jikinki).
Hajiya ta d'auko atamfa riga da zani, acikin a kayan Indo ta d'auko kwalban turare yar mai duguri,