Showing 30001 words to 33000 words out of 42941 words

Chapter 11 - BABBAN KUSKURE COMPLETE BOOK BY RASHEEDAH A KARDAM.txt

14 Jan 2025

1597

koma gun Malamin nan inaga asirin nan ya karye ne". Gwantsi ta ce"ni ko in da ni ne ke Falmi bazan tayar da hankalina ba tunda gaki kintara kud'i kin dawo babbar mace, gaki da naira kuma ai Haiydar yana sonki da yawa tunda ke kikace da hannusa ke baki kud'in nan". Falmi ta ce"ke fa zabaki gane bane Haiydar nawa ne ni kadai da kinga abunda Indo ta min jiya sai kin bani goyan baya dari-bisa-dari". Wata Mama Zeey da ta ke gefe ta ce" ina bayanki karki ragar musu ko d'aya ai kishiya ba abin so bace kishiya! Kishiya!! Kishiya!!! ina bayanki a gama da ita kawai ki huta". Haka suka ci gaba da hiransu kowace da gur-guwan shawaran da take bata a gun.
Haiydar yana office duk ya ji hankalinsa ya tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye zuciyarshi ba abunda take tunaso masa sai Aishat, haka kurun ya tsinci kansa da son ganin Aishat a wannan lokacin cikin hanzari ya tattara komai daman time d'in tashi ya kusa. Da sauri ya fito ya nufi motarsa ya shiga cikin sauri ya ke tuk'in sai da ya kusa shiga unguwamsu gabansa ya soma fad'uwa sai gumi ke ketomasa, k'ara gudun motarsa yayi ga gumi sai k'ara keto masa yakeyi duk da sanyin A.C da ke motar amma bai hana sa yin gumi ba. Tun daga nesa ya ke hango wani mota sak irin na Aishat amma sai wata zuciya ta ce masa" mai zai kawo Aishat nan kawai dai kalar motar ce d'aya, ko da ya iso gun k'ofofin motar a bud'e ya ke, ganin school bag d'in Aishat bai san lokacin da yatak wawan burki ba ya fito daga motarsa. Da gudu yayi gum motar baiga kowa ba sai ya lek'a ciki ba ta nan ga hijab d'in mak'arabtarta a gun da hularta, sai takalminta kafa d'aya ko da ya kali kasa nan yaga jinin da ya d'id'iga a hankali ya soma bin jinin har ya kaisa gun da 'Yan iskannan suka aje motarsu, nan ma yaga alamar kafa inda kayi kokawa da kuma alamar ta k'arfi aka d'auketa, ga tayar motarsu da yayi ribas da kuma yanda ya tashi. Haiydar baisan lokacin da yasaki k'ara ba ya na kiran"Aishat! Aishat!! Aishat! Kina inane? Mai ya same ki? Wa ya tab'a min ke?". Fad'uwa yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k'araji yana ihu ga hijab d'in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare.


Masu karatu sai kun gansa abun gwanin ban tausayi ni kaina Rash bansan lokacin da hawaye yasoma gan-garo min ba.



*ยฎNWA*




*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*




*RASH KARDAM๐Ÿ’•*
[9/12, 8:26 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: ๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป
๐Ÿ™†๐ŸปBABBAN KUSKEREN๐Ÿ™†๐Ÿป
๐Ÿ™†๐ŸปDANA TAFKA ๐Ÿ™†๐Ÿป
๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป
๐Ÿ™†๐Ÿป๐Ÿ™†๐Ÿป

NA


ยฉRASHEEDAH .A. KARDAM.


*ยฎNWA.*


*Pg-210~213.*


Fad'uwa Haiydar yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k'araji yana ihu ga hijab d'in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare. Ya dad'e a haka ya kasa tab'uka komai sai kuka tamkar mace kamar ba jarumin d'an sanda ba mai hazak'a da kwazo wayarsa ne tayi k'ara yana kuka ya ciro daga aljihunsa ya ga sunan Hajiya kafin ya d'auka harta tsinke.
B'an garen Hajiya ko ta ce"yau lafiya banga Aliyu ya d'au wayata ba?". Kamar ta ajiye wayan sai wani zuciya ya ce"kawai ki sake kira kiji lafiyarsa dana d'iyarki". Cikin hanzari ta danna kira. Haiydar jin waya na ringing ga jikinsa sai b'ari yakeyi (daman wannan yanayinsa ne in ransa ya b'aci jikinsa b'ari zainayi). Da kyar ya iya danna gun amsa kira yasa a kunnensa kuka yakeyi yana kiran Aishat! Ciki razana Hajiya ta ce"Aliyu lafiya mai yasamu Aishat?". Bai iya amsa mata tambaya ba sai ce mata" Hanyan gida b'ata Aishat". Sam kwakwalwarsa ta kasa tuno masa ma ya zai had'a kalman a dai-dai ya fad'a Hajiya cikin kid'ima tun da taji yananyi Haiydar tasan abun ba k'arami bane, ta d'auko hijab d'inta ko Abban su Haiydar dake hanyan dawowa yau bata sanar masa ba ta fito a gi-gice, bata tsaya kiran driver ba(mai tuk'a mota) kasancewar daman ta iya mota da sauri ta figi mota tun daga nesa take horn ma mai gadi, shi kansa mai gadi sai da ya rud'e da horn d'in da takeyi ai ya na wangale gate(gareji) da mugun gudu ta fita. Gudu take shararawa cikin min tunan da baifi hud'u ba ta soma hango Haiydar ga kuma motar Aishat! Gudu ta k'ara tana isowa ta gansa a durk'ushe a kan gwiwansa zuwa tayi da sauri ta rugumesa tana jijiga sa ta ce"Aliyu lafiya? Ina Aishat d'in?". Jinsa a jikin Hajiya ya saki sassayan ajiyar zuciya sai a lokacin nutsuwa ta zomasa, cikin kuka ya sanar da Hajiya abinda ya tarar Hajiya ta ce"innalilahi wa inna ilaihi raji'u ai ba zama zakayi kana kuka ba, kaman ba jarumin police ba?" Abunda ya da ce zamuyi yanzu tashi kabi sawun motar sannan ka kira duk wata ma'aikatar police da ke kusa a sane dasu don a baza matakan tsaro. Haiydar ya shiga motarsa zuciyansa na suya gun aikinsu ya kira yasanar musu ya ce"susanar da sauran ma'aikatar hukumar 'Yan Sanda a bazama wasu su biyo sa, hayar da mota tayi yafara bi har ya fitar dashi bakim ti-ti, daga nan kuma hanya ta kasu kashi uku ya tsaya yana tunani sai ga wasu motocin police('Yan sanda) sun iso mota uku nan suka kasu kashi uku d'aya yabi Haiydar biyu suka bi sauran hanyoyin. Abu wasa-wasa suna neman Aishat ba labarinta gashi har anyi sallah isha'i.
Aishat tare da 'Yan iska tafiya sukeyi sai shiga cikin daji sukeyi yayinda jinin jikinta sai zuba yakeyi kasancewar ta mai yawan cin abinci mai kyau tanada wadattace jini amma sanadin zuban da yayi da yawa ya haddasa mata jin jiri, idanunta suna wani iri, hakan baisa Ogan 'Yan iskan nan yayi niyan saurara mata ba sai aika mata da mayen kalo yakeyi.
Su Haiydar ko sunyi nima harsun gaji amma shi baijin gajiya a tare da shi zuciyarsa suya yake masa yama rasa wani irin kalan hukunci zai yanke ma wanda ya d'au Aishat d'insa tabbas ba zai iya saurara masa ba baran yanda yanzu yake jin tsananin k'aunar Aishat na yawo a jinin jikinsa da jijiyoyinsa tafiya suke ga dare yayi ko da ya kali agogon da ke hannusa 11:49 wani kwana ya gani wanda ya lula cikin deji kuma hanyar k'aramace mota bazata sake acikin hanyan ba wasu suna cewa kar abi hanyan halane ko sunbi ta gun gashi yayi daji ko da Haiydar batunsu ransa da ya b'aci ya finciki motar ya shiga cikin dajin, sauran suna ganin ya shiga suka bisa a baya sai yayi tafiya sosai sai yaga wani abu a gefe kamar mutum ne ko tudu, da sauri ya tsaya ya fito da wani touch light d'insu mai haske yana haskawa ya hango Aishat kwance bata motsi da gudu yayi gunta yana haskawa yaga jini na fitowa daga k'asan skirt d'in makarantarta wani razazane k'ara ya saki ya soma jijigata ganin bata motsaba, dai-dai lokacin sauran police d'in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce"ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku". Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari.




*ยฎNWA*




*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMA ABDUL SHAKUR)*


*RASH KARDAM๐Ÿ’•*
[9/12, 8:50 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: [8:05PM, 7/16/2016 ๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป
๐Ÿ™†๐ŸปBABBAN KUSKEREN๐Ÿ™†๐Ÿป
๐Ÿ™†๐ŸปDANA TAFKA ๐Ÿ™†๐Ÿป
๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป
๐Ÿ™†๐Ÿป๐Ÿ™†๐Ÿป

NA


ยฉRASHEEDAH .A. KARDAM.


*ยฎNWA.*


*Pg-214~216.*


Dai-dai lokacin sauran police d'in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce"ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku". Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari. Gudu yakeyi sam ba nutsuwa a jikinsa wani wawan duka ya kaima sitiyari motar tare da furzar da wani isaka mai zafi zuciyarsa na masa rad'ad'i wai ace abunda yagama tanadi wani ya rigasa wasu zafafan hawayene suka zubo masa wata b'an gare na zuciyarsa ya ce"haba Haiydar duk da abin da ciwo kardai kace zaka guje ma Aishat don son da ka ke mata na gaskiya ne bawai jikinta kake so ba. A fili ya furta" Aishat a kowani hali ki ke ina k'aunarki ke ce SIRRI NA bazan gujeki ba". Wasu hawaye ne suka sake zubo masa, wayarsa ce tayi k'ara sunan Hajiya ya gano ya d'aga cikin muryan kuka ya ce"Hajiya an sameta amma sun mata fyad'e gata ko motsi batayi". Hannu a ka Hajiya ta d'aura ta saki salati ta ce"yanzu kuna ina ne Aliyu?". Ya ce"gani a hanya da ita zan wuce T.H". Hajiya ta ce"okay gamu zuwa da Abban ka yanzu shima ya dawo". Kashe wayar yayi ya k'ara gudu wanda kiris ya rage motar ta kwace a hannusa Allah ne ya kare. Bai dad'e ba ya isa Asibiti take a ka shiga da ita Emergency Haiydar ya gagara tsaye ya gagara zaune sai safa-da-marwa ya keyi a k'ofar idonsa na zubar da hawaye, Hajiya ne da Abba suka iso kalonsu kawai yayi ya fashe da kuka mai cin rai, Hajiya ma hawaye tafara don abun ya mata ciwo bana wasa ba.
Falmi ko gidansu ta nufa ita da Mum d'inta suka tafi gun boka ita duk a zatonta an gama da Indo dan haka ta ce"boka kaban maginda sai abunda na fad'a ma Haiydar zai yi ba kuma zai ki bin umarni na ba". Bokan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ya ce"anyi angama yarinya kinzo inda za'a share miki kukan ki hahahah". Kwarya ya d'aga sama saiga wasu magun-guna sun zuba a ciki nan ya mik'a mata ya ce"ga wannan turaren ki tabbatar kulum kinshafa a jikinki, sannan wannan maganin ki kuskure bakinki da shi kulum". Falmi cikin zud'i ta ce"anyi an gama boka". Bokan ya kara wata dariya kafin ya ce"maganin mu da doka kisani duk randa kika tsallake d'aya aciki asiri zai karye kuma zai miki wulakanci mummuna". Ta ce"zan kiyaye boka". Kud'i ta zuba masa suka tafi.
A can asibiti kuwa Dr ya bata taimakon gaggawa saida numfashinta ya dai-daita kafin suka duba kasanta asai ba fyad'e a ka mata ba kukkurjewa tayi acinya wanda ya janyo mata zuban jini. To ni Rash abun ya d'auremin kai bare masu karatu, amma bari mu wai-wayi baya, in baku manta ba na ce muku"ciwon da Aishat taji ya haddasa mata zuban jini sosai wanda haryasa idonta yin wani iri". Bayan da 'Yan iskan nan suka cigaba da tafiya da ita jininta ya zuba ga razana da tayi hakan ya sanya ta yanki jiki ta fad'i tayi dogon suma idanunta sun kafe, 'Yan iskan nan da suka ga haka sun d'auka mutuwa tayi, shiyasa Ogansu ya ce"kawai su yarda ita anan tunda ta mutu ba amfanin su fita da gawa karma a kamasu". Tundaga bakin hanyar da zai shigarda mutum dajin da aka sameta suke janta a kasa wanda yasa skirt d'inta kwayewa jikinta ya jijiciwo kunji dalilin zuban jinin bari mu koma labari. Ko da Dr ya gama dubata ya gito cikin hanzari Haiydar da Hajiya sukayi gunya a tare suka jefo masa tambaya "Dr ya jikinta?" Dr ya ce"da sauki Alhamdulilah kuma ba fyad'e aka mata ba kurjewa tayi, ga jini ya zuba da yawa don haka muna buk'atar jini cikin sauri Haiydar ya ce" Dr muje a d'ibi nawa a samata". Cikin ikon Allah jininsu yayi dai-dai aka samata Dr ya ce"ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b'aci". Haiydar ya amsa da "to". Ya kalisu Hajiya ya ce"barinje gida na d'auko mata wasu kayan". Hajiya ta kalli agogo wayanta karfe biyu da rabi ta ce"to kaje Allah ya kareka". Ya amsa da "Ameen". Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d'in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k'ofar falo.






*ยฎNWA*




*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*



*RASH KARDAM๐Ÿ’•*
[9/12, 10:05 PM] ๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’Salma๐Ÿ’๐Ÿ›๐Ÿฌ: [7/17/2016]Rash Kardam ๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป
๐Ÿ™†๐ŸปBABBAN KUSKEREN๐Ÿ™†๐Ÿป
๐Ÿ™†๐ŸปDANA TAFKA ๐Ÿ™†๐Ÿป
๐ŸŒป๐ŸŒป๐ŸŒป
๐Ÿ™†๐Ÿป๐Ÿ™†๐Ÿป

NA


ยฉRASHEEDAH .A. KARDAM.


*ยฎNWA.*


*Pg-217~218.*


Dr ya ce"ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b'aci". Haiydar ya amsa da "to". Ya kalisu Hajiya ya ce"barinje gida na d'auko mata wasu kayan". Hajiya ta kalli agogo wayan ta karfe biyu da rabi ta ce"to kaje Allah ya kareka". Ya amsa da "Ameen". Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d'in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k'ofar falo. Cikin rashin sa'a kafin ta riskeshi har ya shiga d'akin Aishat ya d'ibi mata kaya kala biyu marasa nauyi ya fito kenan sukayi two eyes(ido biyu) da Falmi hannuta a kan k'ugunta cikin isa da gadara ta ce"kai daga ina kake a cikin wannan dare?". Haiydar duk sai ya ji komai ya kwance masa ya tsinci kansa da ba zai iya yi mata musu ko gardama bare yaki bin umurnin ta, sai da ya yayi jim kafin ya ce"daga Asibiti nake". Cikin hanzari ta ce"waye a Asibiti?" Haiydar ya kalleta ya ce"Aishat ce". Dammmm! k'irjin falmi ya bada sauti bata san lokacin da ta sanya hannu a k'irjinta ta dafe ba ta ce"mai ka ce?". Haiydar yasake mai-maita abunda ya fad'a nan take zuciyar Falmi yafara azal-zala ta ciji bakinta hannuta ta had'a ta buga tare da fara safa-da-marwa tana zagaya guri idonta ya kad'a yayi jajazur ta d'ago ta ce"yanzu a wani hali take?". Haiydar ya ce" jikin da sauki sosai". Ran Falmi in yayi dubu ya b'aci ta kalli Haiydar ta ce"maza kaje ka ajiye kayan nan ka wuce d'akinka". Da sauri ya amsa mata da "to". Amma wani bangare na zuciyarshi bataji dad'in haka ba yana so yaje amma ba halin yi mata musu. Haka Falmi ta tasashi gaba sai da yaje d'akinsa ya kwanta ta nufi d'akinta.
Acan Asibiti kuwa shiru-shiru hajiya suka ga bai dawo ba hankalinsu ya tashi sosai, da sassafe hasnat tazo musu da kayan tea da ruwan zafi har wajan bakwai Haiydar bai zoba, hakan yasa Abban da kansa ya ce"Hasna muje gidan Aliyu muga ko lafiya". Hasnat da sauri ta amsa suka nufi gidan a motan Abba suna zuwa mai gadi ya wan gale musu gate(gareji) suka shiga, Mai gadi yana ganin Abba ne ya gaidasu cikin mutunci da girmamawa, Hasnat ta bud'e falo taga bakowa ganin haka tayi magana ma Abba ya shigo kasancewar tsakanin Main falonsu da side d'in kowaccen su da taraza Abba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login