Showing 21001 words to 24000 words out of 30354 words

Chapter 8 - MASARAUTAR GOBIR Book Complete Writing by Mrs Sadauki .txt

14 Dec 2024

1373

nesa da na fara hango ruwan sai nake jin kunnuwana na amsa kira, ina isa daidai gaɓarsu na yi tsaye ina kallon yadda suka soma yin zillo tuni munduwar wuyana ta fara motsi ta na ɗaukar wani haske.Ido biyu ba cikin bacci ba na soma jin tafin ƙafata na yi mini ƙaiƙayi,ko kafin ƙyaftawar ido na rikiɗe na zama Siren (sirène ) ina daga kwance gaɓar ruwa nake ƙarewa bindin nawa na kifi kallo sai motsi yake ya na fitar da haske.Kamar wata kifanya na yi tsalle na faɗa ruwan,ƙasa sosai nake nitsawa ina jin wani sanyi da daɗi na ratsa ni.


Idona buɗe suke taram haka kuma sheɗa ta daidai take babu alamun gargada irin in mutum ya shiga ruwa.Ina tsaka da yawo cikin ruwan na soma jin dariya,na juya na soma bin inda sautin ke fitowa har na iso kusan wani dutse.Wata budurwa da saurayi na gani su na wasa haɗi da hirar masoya,su ma iri na ne rabi mutum rabi kifi.Budurwar na gani na ta nufo ni ta na cewa “ waooo! Princess” ƙyafƙyaf kawai na yi da ido ina kallonta har ta iso gare ni ta na shafa goshina wanda sai a yanzu na farga akwai wani tambari a jikinsa na haske.


“ Ya aka yi kika zo wannan ƙasar? Ko wani aiki kika zo yi?” abun mamaki kasa magana na yi duk da kuwa na so buɗe baki,saurayin ne ya zo da sauri ya ja ta gefe ya na cewa “ Sarlah ya kike tsayuwa kusa da ita ko ba ki tambarin Masarautar Goma ne da ita ba?” haka suka tafi suka bar ni cike da mamaki.




Sama-sama na soma yi har na fito gaɓar ruwan ,so nake na koma gida.Sai bayan na fito ne bindin ya ɓace na dawo da ƙafafun mutane,na saki murmushi ina jin wani daɗi yayin da kuma zuciyata ta yarda ta lamunce mini tabbas ina da wata baiwa ba daidai nake da sauran mutane ba. Ina zuwa gida na ga takalmin mutane a ƙofar ɗakinmu,ban nemi izini ba na shiga.




Sai na tarar da wata mata a zaune yayin da Kaka kuma ke ta wasa da ɗiyan wuri ta na zayyano mata abubuwan da za su faru gobenta.Wato dibo Kaka take,macen ta yi godiya ta biya kuɗi irin sosai ɗin nan kafin ta fice.Na dubi Kaka wacce ke ta faman ƙirga kuɗi kamar ba ta gan ni ba,na yi gyaran murya na ce “Kaka...” ta yi saurin katse ni da “kin ga Sarah wuce ki bani wuri ban ƙaunar ganin ki,rainon ki bai yi mini rana ba sam.Ban ga amfanin zama da ke ba don haka ki kwashi inaki-inaki ki bar min gidana”




Wata irin dariya na soma wacce sama ban lura da ruwan da suka fara ɓulɓulowa daga ƙasa ba har sai da suka kawo daidai wuyana.Tsit na yi ina kallon Kaka wacce ke ta ƙoƙarin fita daga ɗakin amma ta kasa,“za ki mayar da ruwan nan ƙarƙashin ƙasa ko sai sun kashe ni ” ta faɗa a tsorace ta na riƙe bango hakan kuma sai ya ƙara bani wata dariyar amma na gimtse munduwar wuyana na lalubo na riƙe ina yi wa ruwa magana da idona,a sannu a hankali suka yi ƙasa har suka ƙwafe.
Da wani irin saurin Kaka ta cillo ni waje ta na mai cewa “ashe duk yadda nake tunani kin wuce nan,ke annoba ce ba zan iya zama da ke ba”


Zuwa wannan lokacin na fahimci Kaka ba da wasa take ba,hakan yasa hankalina ya tashi na soma roƙonta “Kaka in kin kore ni ina zan je? Ke ce komai nawa ke kika raine ni ban san kowa ba sai ke”
“Ban haɗa komai ba da ke wallahi tsintar ki na yi da tunanin za ki yi mini amfani a gaba ki gaje ni ashe musamman da na ga ki na ɗauke da *MAITAR IDO* ashe ban san bala'in naki ya wuce nan ba sai yau na ida ganewa Mamy Water ce ke ”
Idona na zubar da ƙwalla nake kallon Kaka,tuni kuma ƙwaƙwalwata ta soma hargitse wa.Ana kiran sallar magrib haka Kaka ta jefo ni waje ni da jakar kayana ta kama gidanta ta rufe,kan dakali na zauna ina ta wasiƙar jaki har aka yi sallar isha'i.Ganin dare na ta ƙara yi na miƙe tsaye na soma tafiya,direct gidan anty Sailuba na nufa don ita ɗaya ce yanzu ta rage min wacce nake tunanin za ta zame mini bango.Da sallama na shiga gidan,tun kafin na ƙarasa nake jiyo sautin muryar mijinta Bilal ya na cewa “wallahi Sailuba ko mi za ki yi sai na ƙara aure,kuma goben nan zan je na yi wa Hajiya bayani ta samo min mata cikin danginta tun da ni ko na nema ba za ki bari ba” kai na kutsa na shiga ɗakin,anty Sailuba ta juyo ta na kallona a zuciye “uban mi kika zo yi kuma yanzu cikin dare?” ban bata amsa ba sai mijinta da na ƙure cikin ido ina mai taɓa munduwa ta ni kaina ban san dalilin yin haka ba.
“My Lub Baby wane ni na yi miki kishiya don Allah ki kwantar da hankalin ki ina mugun son ki” Bilal ya faɗa ,ni kuma na saki murmushi ashe duk anty Sailuba ta ga komai.Hannuna ta ja muka fito waje kafin ta ce “ke mine ne kika yi wa mijina? Ko ke ma bokancin kike yi kamar Kaka” na girgiza kai na ce mata “a'a ina da MAITAR IDO ne mai sarrafa abin da duk nake so,kin ga gashin Leemat ma ni ce nan na mayar da shi yanzu kuma na juye tunanin mijin ki babu ke babu kishiya” anty Sailuba ta rungume ni ba tare da tunanin wannan ɗin fa abun gudu ne,ta ce “ina na za ki je?” bayani na yi mata kan cewa Kaka ta kore ni daga gidanta sai a lokacin kuma na ji hawaye ,ta goge mini su ta na cewa “sai ki zauna gidana” sai ta ja hannuna muka koma ciki.....








Ga waɗanda suke son fara payment ƙofa a buɗe take 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*


HoRrOR story☠️


Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️


*FCWA ☀️*




9-10




Ko da muka koma ciki mijinta bai falo alamun ya na can ƙurya ,anty Sailuba ta kai ni wani ɗaki ɗan madaidaici babu komai cikinsa sai dangin abinci.Ta je ta ɗauko tabarma da kuma wani ƙaton bargo ta shimfiɗa min,“ ki kwanta a nan zuwa gobe da safe in Allah ya kai mu za mu sake yin magana” kai na jinjina mata ta fice ta bar ni nan.


Na haye shimfiɗar na kwanta ina tunanin furicin Kaka wai ba ta haɗa komai da ni ba tsintata ta yi.Na juya kwanci wani sashen zuciyata kuma na hasko min wulaƙanci da Sharifa ta yi min ƴar anty Hinda.Na lumshe ido ina mai kai hannu na riƙe munduwar wuyana,‘ ko ya ake yi mutum ya je wannan duniyar da Kaka ta kai ni ? ’ na tambayi kaina a zuci abun mamaki kuwa zuciyata ce ta soma yin nauyi kamar an ɗora dutse kafin in samo amsar tambayata .Cike da jin daɗi na yi bacci wannan daren,tun da asubah anty Sailuba ta shigo ɗakina “ tashi ki yi sallah” shine abin da ta faɗa ,duk da ban taɓa yin ta ba hakan bai hana ni miƙewa ba na fito.Ƙofar falo na ga a buɗe hakan yasa na fita,banɗaki na shiga har zan hau masai sai na tuna mafarkin da na yi a jiya an nuna mini yadda zan ɗauki fansa ta wajen su anty Hinda .Na fita na samo baƙar leda sannan na koma banɗaki,a cikinta na kasaye duk abin da ke cikina sannan na miƙe ina dariya ni ɗaya.Da ido na yi wa ledar umarni ta ƙulle kanta kafin kuma na aikata can gidan anty Hinda.


Na fito na wanke jikina na koma ɗakina,gari na wayewa anty Sailuba ta sake shigowa tare da samun wuri ta zauna.
Ta ɗan ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ da farko dai ina yi miki godiya game da abin da kika yi min jiya,na biyu kuma abin da zan ce miki babu kyau cutar da mutane ki bari”


“ Shikenan ya bar zancen auren?” ita ce tambayar da na yi mata.
Ta ce “ eh ya bari sai kuma ya ɓullo da wata matsalar wai za mu tashi daga nan mu koma can gidan da ɗan uwansa ya gina kin san nan haya muke”
Na ce “ to ai hakan ba matsala ba ce kin ga kuɗin da yake biya na haya sai ku yi wani abu da su”
Ta girgiza kai ta ce “ uwar mijina ƴar masifa ce ta bugawa a jarida,kuma kin ga ita ma a can take.Yanzu dai mu bar maganar nan zo ki yi mini wanki ki share gida da kuma wanke-wanke kin san halin Bilal shi ma wani sa'in bai da mutumci shi yasa kawai na ce masa ƴar aiki na ɗauke ki”
Tashi na yi tsaye na ce “ babu matsala anty in dai zan zauna a nan ko ƴar aikin sai na zama” tulin kayanta da na mijinta na wanke ,na yi shara na yi wanke-wanke a ƙarshe na je na yi wanka sannan ta zuba mini waina da miya sosai na ci na ƙoshi.“ Ki shirya za mu je kasuwa abokan Bilal yau a nan za su ci abincin dare”
Na ce “ kenan yau ba za mu buɗe shago ba?”
“ Eh gaskiya tun da kaji za mu sayo sai kuma mun yi gyaran su”


Da muka fito za mu tafiya kasuwa ta ƙofar gidan anty Hinda muka wuce,tun daga nesa na hango ledar kashin da na yi tanadi ta na nan tsaye kamar haure jira kawai take lokacin da na ƙa'ide ta faɗi ƙasa.Na yi murmushin mugunta har na matsu ƙarfe sha biyu ta yi,da muka shiga kasuwa kuwa na yi ta gamuwa da abubuwan mamaki waɗanda normal mutane ba su iya gani.Yawancin ƴan kasuwa duk su na da layar da za ta jawo musu customer su sayi kayansu ba tare da sanin ita fa wannan layar ta na ɗauke ne da aljanu su ne kesa mutane sayen kaya ko ba su shirya ba,wani abun ma bai da amfani sai ka je gida ka yi ta tunanin mi yasa ma ka saye shi da ka bar kuɗin ka.


Kaji muka saye manya guda uku anty Sailuba ta miƙa min su na riƙe,daga nan muka wuce wurin ƴan yaji.Mun yi tsaye ta na cinikin nawa tiyar yaji,yayin da ni kuma idona ya sauka kan yaji wanda ake kira tsidagu irin ƴan mitsimitsi ɗin nan.
“ In ɗauki guda?” na tambayi mai sayar da yajin yayi murmushi ya ce “ ɗauka mana”
Cike da masifa anty Sailuba ta ce “ mi za ki yi da tsidagu kuma?” na ce “ kawai ya burge ni ne sai na ɗauki ƙwaya gudan.Haka dai muka yi ta zaga kasuwa har muka zo wajen ƴan sayar da nama,yadda na ga mata sun yi dandazo wajen wani alhalin duk ga ma su nama nan yasa na ji ina son ganin shi ɗin kuma wace irin laya yake amfani da ita.Kamar dole haka na duƙa ina kutsawa har na shigo gaba,sai dai kafin na miƙe tsaye sai idona ya sauka kan wasu ƙafafuwan jaki a tsaye daram,a hankali na miƙe sai na ga ashe mai sayar da naman ne .Ido huɗu muka haɗa da shi da farko ya ji tsoro kafin ya soma yi min magana da ido ba wai a bakinsa ba ballantana ace mutane za su ji.
“ Mi kuma ya kawo macen Siren cikin mutane? Ko da yake ba abun mamaki ba in ka shigo kasuwa babu kalar jinsin da babu”
Ni ma ta idon na mayar masa “ wane ne kai? Ya aka yi ƙafafunka suke na jaki?”
“ Ki tambayi Anaba ita ai ta san ni ”
Anaba sunan Kaka ne,jin furicinsa yasa na kai dubana ga naman da yake sayarwa duk babu ɗaya na ƙwarai mushe ne yake sayarwa in rago ya mutu ko saniya haka zai je ya ɗauko su inda aka jefar ya gyara shi ya zo ya na sayarwa ko da kuwa ya fara lalacewa shi zai san yadda yayi ya maida shi mai kyau a idon mutane irin shine kuma sai ka ga ka ci ka faɗi rashin lafiya.
Ban ankara ba ashe har mutanen da ke zagaye da shi duk ya sallame su sai da na ji muryar anty Sailuba na cewa “ Sarah ke? Tun ɗazu fa nake yawon neman ki” sai kuma ta harari mai sayar da naman kafin ta ja hannuna mu wuce.Sai da muka yi nisa na tambaye ta “ amma anty mi yasa ba ki sayi namansa ba ? Na ga ya fi kowa arha”
Ta ja baki ta ce “ arhar ce ke kai mutane ga hallaka,ni ma na taɓa saya lokacin da abokan Bilal za su zo amma abun mamaki suka ƙi ci wai naman nan da na saka ya lalace ko ban jin warinsa.A ƙarshe dai barina suka yi da shi sai ni da Bilal muka ci daren ranar kuwa muka dinga ƴar rige-rigen shiga banɗaki” na ƙyalƙyace da dariya kafin kuma na ce “ to anty mi yasa kuka ci alhalin an faɗa muku ya lalace?”
Shiru ta yi ba ta bani amsa ba, wannan kuma yasa na lalubo amsar da kaina ‘ saboda ita da mijinta normal mutum ne!’ sai kuma zuciyata ta bada darammm ‘ to in haka ne su abokan Bilal waye ya sanar da su? Sai in kuwa su ma matsafan ne!’ duk a zuci na yi maganar har muka kai gida babu wanda ya ce komai.


Mijin anty Sailuba ya karɓi kajin ya fita waje wani ya kama masa ya yanke,ni kuwa ƙatuwar tukunya na ɗora ta ruwan zafi .Sai da suka tafasa sannan na soma fige su yayin da anty Sailuba kuma ta ɗora girkin rana ,muna aiki muna hira har muka gama.
Sai bayan mun ci abinci ne na kama mata ta tsaga cikin ta fiddo hanji ,su ma duk muka gyara su sannan ta wanke ta ɗora kan tukunya.Tafarnuwa ta miƙo min ita ma na gyara ,aikin da nake ganin mai sauƙi ne sannu-sannu sai ga shi ya ɗauki lokaci don bayan ta dafa kajin sai da ta soya su sannan ta ɗora miya bayan ta gama kuma ta tsumbula su ciki.








#GIDAN ANTY HINDA




Cike da iya yi Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka,ragowar ruwan kuma waɗanda duk sun yi farin sabulu ta kawo wa anty Hinda su ta juye cikin miya sai murna suke.
Sharifa ta ce “Mama in muka ɗora da yin haka ai hajjin bana da mu za a yi”
Ita ma Hindar ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “ai kuwa dai musamman yanzu da na rabu da jikar bokanya ”
“Dama haushi take bani,yadda kullum cikin datti ko wanka ba ta yi”
Hinda ta ce “miƙo min ƙatuwar muciya na motso miyar nan ” muciyar ta miƙo bayan ta motsa miyar ta sa murfi ta rufe kenan ai kuwa sai ganin leda suka kuwa daga sama ta faɗo kan tukunyar miyar kwacaaaa.


Duk suka yi baya a tsorace su na zaro ido ganin kashi duk ya ɓata murfin tukunyar .
Cike da ƙyanƙyami Hinda ta ɗauke murfin ta je ta wanke shi,Sharifa kuwa cewa ta yi “Allah ma dai yayi sa'a ba a ciki ya faɗa ba”
“Ɗauko muzubi ku juye min miyata Allah kaɗai ya san abin da za a jefo min kuma nan gaba” cewar Hinda , Sharifa ta ɗauko ta dinga kwashe miyar dama ta dafu.


Ita ma Hinda wankan ta yi kafin su ɗora abincin kan baro,almajiri ya tura masu shi inda suke sayarwa .Sharifa an ci wuyar kwalliya,mutane ne suka fara zuwa su na saye kamar kullum sai da Hinda ta buɗe baki ta na zage-zage “ ƴan hassada ƴan baƙin ciki,to sai ku je ku sake biyan wasu kuɗin wannan aikin bai yi ba.Ni za a yi wa turen aljanu daga ganin kasuwata ta bunƙasa”
Customer ɗinta kuwa har da masu shigar mata,kafin kuma wurin yayi tsit babu wanda ya ƙara saya ga abinci jibge har bayan sallar Asar sai ƴar kallon-kallon suke ita da Sharifa.
“ Na fa ji tsoro kar aje dai ɗin sun ƙara tafiya sun kai wasu kuɗin wurin Malam,dubi shiru babu masu saya”
Sharifa ta turo baki ta ce “ ai ke ce da masifar tsiya tun da kin ga abun bai yi aiki ba ai sai ki yi shiru da bakin ki”
“ Ƙirga kuɗin mu ga nawa aka samu” cewar Hinda . Sharifa ta ɗauki robar kuɗi,yaji ta gani tsidagu babu wani tunani ta ɗauke shi ta jefar kuɗin ta ƙirga ta na turo baki gaba saboda ko icce ba za su saya ba.Ta miƙa wa Hinda “ tsidagun mine ne kuma za ki aje min cikin kuɗi?” Hinda ta tambaya ta na mai ɗauka ita ma ta jefar a ƙasa.
Sharifa ta ce “ na fa jefar da shi”
“Ƙafafuwa gare shi ballantana ya sake tsalle ya shiga?”
“Allah Mama na cire”
“Kin ga tashi mu je gida kin ga duk wasu masu sayar da abinci sun sayar sai mu”
“To wannan ɗin ya za mu yi da shi?”
“Ko almajirai sai na rabawa ”
Abincin suka mayar a baro suna gaba almajiri na bin su a baya har suka isa gida, Sharifa ta cika bokiti ta je ta yi wanka tun a cikin banɗaki ta ƙurma uban ihu ta na kiran Hinda .
“ Ke lafiyar ki? Ko ƙadangaren ne yau ma ya sake faɗo miki?” Hinda ta tambaya, Sharifa ba ta amsa ba sai fitowa ta yi da ɗaurin ƙirji ta na soshe-soshe.


“ Mama sosa mini ƙaiƙayi duk jikina ƙaiƙayi yake na shiga uku na lalace” haka take faman faɗa ,da farko Hinda ta ɗauka wasa ce sai da ta ga Sharifa na kuka har da majina sannan ta soma tayata, Sharifa ba ta samu sauƙin abun ba sai da jikinta ya bushe babu damshin ruwa.Tsabar wahala har sai ta rame,ta koma gefe ta na jan numfashi.


Hinda kuwa alwala ta yi don yin sallah nan ita ma ƙaiƙayi yayi mata wuf duk inda ke da damshin ruwa.Soshe-soshen ta yi ita ma har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login