Showing 18001 words to 21000 words out of 30354 words
Chapter 7 - MASARAUTAR GOBIR Book Complete Writing by Mrs Sadauki .txt
kuma abun mamaki sai na irina ta miƙe tsaye ta na tambayar Kaka “har lokacin tafiyar tamu yayi?”
“Eh fito mu tafi jirgi na jiranmu” sai ta ja hannuna muka fito,ni kuwa sai ware ido nake na ga inda zan ga jirgi sai dai ina abin ya wuce tunanina.Turmi Kaka ta kada kwance hannuna na cikin nata muka shiga turmin nan kawai sai gani na yi ya tashi da mu sama.Da mamaki na tambaye ta “amma Kaka dama turmi ya na iya tashi sama?”
Ba ta bani amsar tambayar da na yi mata sai bayani ta soma yi mini,“leƙa ƙasa ki ga yadda duniyar da muka baro take” na je na kama bakin turmin na leƙa sai na duk ga gidajen mutane nan da kuma ababen hawa,na waro ido ina mamaki na ce “ya na ga garin duk yayi duhu alhalin nan sama kuma hasken rana?”
“Duniya biyu ce mabanbanta,daren can shine safiyar wannan duniyar.A sannu za ki saba za ki ji wannan ɓoyayyar duniyar ta fi waccan daɗi,tun tuni nake son kawo ki amma kika ƙi bani haɗin kai sai yau da zafin ɗaukar fansa ya ci galaba a kan ki” ina shirin yi mata wata tambayar ta ce “shuuut! Mun kawo Dutsen Muradi ki nutsu ki aiwatar da komai yadda ya kamata”
Kan wani ƙaton dutse jirginmu na turmi ya sauka,yanzu ma Kaka ce ta kama hannuna muka fito “ ki faɗi abin da ya kawo ki mana kin yi wani tsaye” Kaka ta faɗa ta na kallona,“ to ai ni ban san ya zan yi ba” na faɗa ina ƙyafƙyaf da ido.
“Sunan ta za ki kira ”
“Leemat!” na faɗa cikin rawar murya,wani haske ne ya soma sauko wa daga sama mai gamar gajimare kafin ya tsaya a gabanmu,ta cikinsa nake hango Leemat a kwance jikin wani matashin saurayi sai shafar mata gashin da aka kitse yake.
Maimakon muradin gashin ya zube kamar yadda na zo da niyyar,a'a sai na canza ƙudiri na kafe tsorayen da ido ina mai cewa “ ku zama macizai ta yadda saurayin kawai zai iya ganinsu” ko baki ban rufe ba kuwa tsorayen suka fara motsi kafin su zama macizai su na fiddo halshe.Saurayin ya fasa ihu tare da koma gefe ya na rawar sanyi tuni fitsari ya soma yi masa zuba,sai haƙuri yake bai wa Leemat kar ta cutar da shi ita kuma ta na tambayar mine ne gashin kanta yake yi mata nuni wanda yasa ta nufi madubi don dubawa sai dai kafin ta isa ne Kaka ke ce min “ da zarar ta isa ga madubin mutuwa za ta yi don shi mirror bai ƙarya ki yi saurin dakatar da ita”
Take na ruɗe jin zan yi kashin kai na ce “ ta yaya Kaka? Ya zan tsayar da ita ?” kafin kuma ta bani amsa na ƙure ƙafar Leemat da ido nan take ta ɓangwale ta faɗi ƙasa timmm daidai nan kuma Kaka ta yi wani furuci komai ya tsaya cak ciki kuwa har da tsintar kaina kan katifa kuma numfashina ya dawo gangar jikina.
A firgice na tashi ina dafe zuciya,sai kuma na yi saurin sauka na ɗauko ruwa na sha ina mai cewa “ na yi mummunan mafarki ” don ni duk a tunani mafarkin ne na yi ba gaske ba.Kan shimfiɗa na je kwanta,sai kuma na shiga tambayar to ina Kaka ta tafi cikin daren nan ƙila ko banɗaki.Ban kai ga samo amsa ba na ji wata uwar ƙara rudududuuu kamar ta sama za ta faɗo,tsoro ya kama ni na ƙanƙame jikina.Ina cikin wannan yanayi Kaka ta buɗo ɗaki ta shigo cakwal-cakwal da ƙafafunta na kaza,ido na murza na dai ga har yanzu ba su canza izuwa na mutane ba sai kuma na tuna tun jiya fa haka suke har lokacin da anty Sailuba ta zo ta ja ni muka tafi saloon.
Na buɗe baki da niyyar tambayar ta “ Kaka wai...” amma sai ta katse ni ta hanyar cewa “ rufe mini baki tun da ke ba ƴar goyo ba ce,na taimaka miki don ɗaukar fansa shi ne kika baro ni can don ki nuna mini wuyan ki ya isa yanka ƙarfin ikonki(ƙarfin tsafi shine sai miyagu ke ɓoye shi su ce ƙarfin iko) ya ma fi nawa.Ina ce dai ni ce nan na raine ki tun ki na tsuman goyo,kuma ki sani daga yau na raba hanya da ke sai ki yi abin da kika ga dama tun da kin ishi kan ki.Sai dai ki sani tsohon kai ya fi sabon kai dafi ” ta na gama faɗa ta yi gaba ta nufi wani ɗan lungu da muke aje kaya.Wani ƙaton bindi na ga ya na yi mata reto kamar jela,duk ɓaɓatun da gama yi sam ban fahimci abin da take nufi ba don har zuwa yanzu duk na ɗauka mafarki ne na yi.
Kayan jikinta ta canza sannan ta raɓa gefe na ta kwanta,hakan ya bani damar ganin salewar da gefen fuskarta yayi kamar wacce aka ƙona ga wuta.
“Mi ya same ki kuma haka?” na yi tambayar ina shirin ɗora hannuna kan ciwon amma sai ta yi amfani da nata wurin buge ni tare da ɗora min yatsunta sak irin na mage don firgici har sai da na yi baya “ in kika kuskura kika taɓa ni zan yayage miki fuska” a tsorace na kai kaina na jingine ga bango.
Ƙiri-ƙiri yau Kaka ta fito mini da ɓoyayyar siffarta,“ don Allah ki yi haƙuri ni ban mi na yi miki ba” na faɗa a tsorace ,“hum” ta yi wani ƙyaci kafin ta juya min baya ƙaton bindinta kuwa sai wani motsi yake kamar yadda mage ke yi.
Muƙut! Na haɗiye wasu yawu kafin na ce “ wai Kaka wannan duk mine ne? Ƙafafuwan kaza ga kuma bindin mage a bayan ki?”
Ba ta juyo ba ,amsa ta bani kai tsaye “ iya nawa kawai kika gani? Ke naki fa?”
“Ni ai banda ƙafar kaza”
“To ki duba wane kala gare ki” ta bani amsa .
Furucinta yasa na tashi zaune don duba ƙafafuna sai dai mi zan gani? A madadin ƙafafu wani shabcecen bindi kifi ne tun daga wajen ƙuguna zuwa ƙasa na kifi ne.Ban san lokacin da na fasa wani uban ihu ba ina motsa bindin mai ɗauke da wasu ababe kamar mafarfeci.
Ihun da na yi yayi daidai soma zubar ruwan sama masu mugun ƙarfi kafin ƙyaftawar ido ɗakinmu ya cika da ruwa.Hankalin Kaka a tashe ta soma tsalle-tsalle don kamar yadda mage ba ta son ruwa to ita ma haka take,ni kuwa maimakon ace na ji tsoron ruwan a'a sai na ji kamar ma na zo gidana ne .Ko kaɗan ban ji irin wannan yanayin ba na son fiddo kai waje,hasali ma wutsilniya na soma yi cikin ruwan ina yawo kamar wata ƴar ruwa.Munduwar wuyana ce ta soma fitar da wani haske mai ƙuna ,tsabar yadda hasken ke da ƙarfi har sai yasa na wani abu ya caki kwanyata da kuma daidai saitin zuciya ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai a washegari na tashi tuni kuma rana ta fito wantsar.Na yi miƙa na tashi zaune ina hamma,Kaka ta shigo ɗakin ta na mai cewa “sai yanzu kika ga damar dawowa?”
Ban fahimci tambayarta ba hakan yasa na ce “Kaka ni da ke bacci ina kuma na je? Bari na yo fitsari na baki labarin mafarkin da na yi cabbb wai Allah na gode ma da mafarki ne” sai na sauka daga katifar na fita waje abun mamaki duk ruwa ne a kwance.Buta na ɗauka na raɓa ta inda babu ruwan na je na shiga banɗaki,ina fitowa na wanke fuska da ƙafafuwana sannan na koma ɗaki ina tambayar Kaka “wai ruwa aka yi jiya? Kuma ba lokacin damina ne ba”
“Sarah kar ki raina mini hankali ki dinga yin abu kamar ba ki san mi kike yi ba,wuce dai ki tafi tun ɗazu Sailuba ke ta aikowa kiran ki” ficewa na yi na nufi saloon.Ina shiga na tarar da Leemat zaune a ƙasa yayin da kuma ƙawarta Watsima ke kwance kitson da aka yi mata jiya sai faman faɗin “washhh! Washhh” take yi yayin da ita kuma anty Sailuba ke ta masifa ta na cewa “ in ba abun ki ba Leemat daga saurayi ya ce kitson bai yi ba shikenan sai ki kwance?Allah duk da kin biya ni na ji zafi fa”
“Anty Sailuba wallahi a rayuwata dama ban son kitso ,saboda na ci kuɗinsa ne na zo kika yi mini amma don wulaƙanci ba ki yadda ya fita daga ɗakin a guje ba kamar ya ga wata aljana”
Watsima ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “In dai ya baki kuɗin iPhone ɗin ai shikenan ”
“Ai ban yarda ma na raɓe shi ba sai da ya damƙa mini ita ga hannu,ta na can na baro ta a caji yanzu in gama wanke mini zan je na kunna ta na yi ta selfie ”
Daga wannan ban sake sanin abin da suke tattauna wa ba sakamakon duniyar tunani da na lula ‘ kenan dama ba mafarki ne na yi ba a daren jiya?’ na tambayi kaina kafin kuma na yi wani makirin murmushi na ƙara cewa a zuci ‘ in dai haka ne kuwa Leemat ba zan bari ki yi selfie ɗin nan ba,wato za a yi mana burga da dogon gashi ’
Ina nan zaune ina ɗinka hulla aka gama kwance mata gashin,anty Sailuba ta wanke mata shi ta saka mata kwarkwaro sannan ta je ta zauna kan kujera aka ɗora mata tukunyar busar da gashi.
Sai da na kwatanci gashin ya kusa bushewa kafin na ƙurawa tukunyar ido ina bata umarnin ta ja gashin Leemat ya shige can ciki ko minti biyu ba a yi ba kuwa tukunyar ta soma yin wata irin ƙara ta na fitar da haƙi haɗi da ƙauri.
Hankali tashe anty Sailuba ta je za ta cire wayar lantarkin da ganga na kalli ƙawarta na ce ‘ɓangwale ki faɗi’ ji kake timmmm anty Sailuba ta faɗi tuni Leemat ta soma kuka haɗi da ƙoƙarin tashi amma ta kasa saboda yadda tukunyar ta riƙe gashin gam.Hayaƙin da ya soma fita na baiwa umarnin ya ƙara farashi ai kuwa shagon ya turniƙe da hayaƙi,Watsima sai tari take ta na cewa ta shiga uku ba ta ganin komai yayin da kuma anty Sailuba ke kukan ƙafarta.Sai a lokacin na miƙe na nufi Leemat,daidai gabanta na tsaya kafin na ƙuwara casque ido sai komai ya tsaya cak na jawo ta ina cewa “yi sauri ki tashi tun da an samu kin fito”
Anty Sailuba da Watsima sai salati suke yi su na taɓa hannu ganin yadda gashin Leemat duk yayi wani iri kamar an kaɗa taliya ƴar murje.Kan kujera anty Sailuba ta zauna da Leemat wacce ke ta matsar ƙwallla,ɓarin mai aka yi mata iri-iri kafin a soma shatar gashin nan take ya soma zubewa ya na faɗuwa ƙasa sai ga Leemat da ƙwaiƙwayayen gashi....
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*👁️
👁️👁️👁️👁️👁️
HoRrOR story☠️
Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️
*FCWA ☀️*
7-8
Wani irin daɗi yake ratsa ni ganin Leemat na kuka ta dalilina, wannan kuma bai rasa nasaba da MAITAR IDOna don duk wani mugu ya na jin daɗin mugunta musamman ga waɗanda suka taƙile shi.
Leemat za ta kwashe gashinta don tafiya da shi amma anty Sailuba ta yi saurin hanata “ haba ke kuwa in kika tafi da shi a zai dinga tuna miki baƙin ciki,bari na baki mai ki dinga shafa wa gashin in sha Allah zai dawo normal” cike da siyasa anty Sailuba ta yi mata wayo ta karɓe gashin ta haɗa ta da mai ita kuma doluwar ta karɓa ba tare da ta san sayar da shi za a yi ba.
Ko kuɗin gyaran gashin ba ta karɓa ba suka yi tafiyar su,ita kuwa anty Sailuba tamkar ma ta yi murna da hakan .Ƙaton gwangwanin da take ajiyar gashi ta buɗe ta zuba kafin ta juyo ta kalle ni ta tuntsire da dariya ta ce “ ikon Allah! Ki na ga fa jiya Leemat ta yi ta miki sharri yau ita ma gashinta ya koma irin naki ”
Na saki murmushin ni ma kafin na ce “anty yunwa nake ji”
“To acici ga abincin ki can tun ɗazu na ajiye miki shi” ta nuna mini da yatsanta na je na ɗauko.
Zazafen tuwon shinkafa ne da miyar kuɓewa sai ƙamshi yake da alamu kuma girkin gida ne,ido kawai na ƙura ina kallon abincin wanda zuciyata ta shaida mini ‘an saka maganin mallaka’ da mamaki na ɗago na dubi anty Sailuba na ce “wai anty tuwon nan tun na yaushe ne?”
Cike da masifa ta ce “babu ruwana da iskanci kamar ya na yaushe ne? Na sunan haihuwata.”
“Daga tambaya?”
“Ni na girka shi da kaina,kin samu ma na zuba miki sauran abincin mijina duk da uban kishin da nake da ”
Anty Sailuba ta na da aure sai dai kusan shekara biyar ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba,ta na da mugun kishi sannan ta na son mijinta sosai kamar ta mutu.Duk in ta ji labarin yayi sabuwar budurwa haka za ta samo lambarta ko kuma ta je har gidansu yarinyar ta ci mata mutumci.
A zuci na ce ‘shikenan Bilal ka shiga uku , Allah kaɗai ya san bayan maganin mallaka wane iri ake baka kuma’ a zahiri kuma cewa na yi “a'a gaskiya ba zan ci tuwon nan ba,yo ai in na yi hakan kamar na nuna raini ne a gare shi ” na kuwa rufe abincin.
Anty Sailuba ta ƙure ni da ido kafin ta ce “ki ɗauka ki ci babu ruwana da shashanci”
“Allah anty na ƙoshi ba zan ci wannan ba” na bata amsa don kuwa na san abu da magani ba zan cuci kaina ba.
“Ke kika sani yi ta zama da yunwar don kan ki” ta faɗa tare da ficewa.Ina zaune ina tunanin ina zan samu abinci sai ga ƙawayena,da murna muka rungume juna kafin na ce “ ku shikenan tun ranar nan ba ku neme ni ba”
Laila ta ce “ ke ɗin ce kin bamu tsoro sosai nitsewa kika yi cikin ruwa fa,hankali tashe muka je nemo masu ceto har sarkin ruwa fa sai da ya shiga neman wai a bai gan ki ba ” sai ta yi shiru hakan yasa Farida ci gaba da cewa “ amma Kaka na zuwa ta yi wasu bubuwa sai ganin ki muka yi gaɓar ruwa kamar wacce aka jefo,to shine fa duk muka ji tsoro saboda mutane na ta cece-kuce akan lamarin”
“Don mi?” na yi tambayar,sai da suka kalli juna sannan Laila ta ce “ wai Kaka bokanya ce” na waro ido Farisa ta harare ni ta ce “ kamar ki ce ba ki yarda ba don dama tun tuni ana zarginta da hakan”
Na haɗe rai na ce “ kun ga ban son wannan...” Laila ta katse ni “ to in ba boka ba wake bada magani? Kar ki manta in ciwo ya ta'azzara har gidanku ake zuwa karɓar magani”
“Ni dai duk a bar wannan zancen yunwa nake ji” na faɗa don haka kawai na ji ban so a ci gaba.
“ Ina da kuɗi mu je tashar kwaɗayi ” Farida ta faɗa ta na buɗe tafin hannunta kuɗi ne kuwa masu ɗan yawa,na ce “ ku je ku biyu ku sayo ni zan zauna nan kar anty Sailuba ta yi faɗa ” ba su musa ba suka fita ai kuwa ina nan zaune sai ga wata mata ta kawo ƴarta ƴar shekara goma a wanke mata gashi.
Zaunar da ita na yi na soma wanke mata da sauri don haka kawai ban so ace ita ma ƴar mitsitsiyar nan an sayar da gashinta ga hajiyar birni.Sai dai duk saurin da nake a banza,ina daf da idawa anty Sailuba ta dawo idonta duk sun yi ja sosai.Sama-sama suka gaisa da Uwar yarinyar kafin ta samu wuri ta zauna ta na kallon yadda nake yin komai.Bayan na gama mata ta biya kuɗi suka tafi,gashin yarinyar nake son ceta sai dai na rasa ta ya zan yi haka.
Anty Sailuba ta ɗauki masharcin da na shace mata kai ta shiga cire gashin da ya laƙe,ina ji ina gani ta jefa shi cikin gwangwani.
Su Farida suka dawo,taliya ce suka sayo mini sai hanjin ligidi na karɓe na shiga ci yayin da anty kuma ta aike su .
Haka muka yi ta samun customer har lokacin tafiya ta yayi gidan anty Hinda,ina zuwa sai na ga ta haɗe rai amma ban damu ba na shiga taya ta sayar da abincin yau ma dandanan muka sayar sai dai ko loma ɗaya ba ta bani ba.
Na yi rau-rau da ido na ce “ anty ina nawa”
“ Ni ai ba zan sake baki abinci ba,yau tun safe Kakar ki ita ta tashe ni daga bacci ta yi ta min masifa ta na zagina wai kar na sake baki abinci to wannan ma yasa na yanke shawarar sallamar ki” ta faɗa tare da ɗauko kuɗi ta miƙa mini.
Na ƙi karɓa ina bata haƙuri amma ta ƙi haƙura har gidanta na bita,muna shiga ƴarta budurwa mai sunan Sharifa ta taso cike da wulaƙanci ta na cewa “ uwar mi kika zo yi gidanmu? Dama shi talaka bai iya samun wuri ba,ɗazu don rashin mutumci kika turo mana wannan tsohuwar Kakar taki ta zo ta yi wa mutane hauka.Duk alherin da muke yi muku ba ku gani ba har da wani cewa an zuba miki guba a abinci”
Anty Hinda ta ce “ kin ga Sharifa zo ki ƙirga kuɗin nan mu ga ribar da muka samu” ta na hararena ta karɓi kuɗin da ke cikin wata roba ta koma gefe ta na ƙirgawa ta na masifa “ daga yau ni zan dinga taya uwata sayar da abinci sai ki tafi ba mu buƙata” da ta ga na ƙi gusawa ta juye kuɗin ƙasa tare da cika robar da ƙasari ta watsa min a fuska har sai na ji tsoro.Duk wannan bai ishe ta ba sai da ta wani ja ni ƙiiii ta cillo ni waje ,zuciyata ce ta soma tafasa yayin da duk illahin jikina nake jin ya ɗau zafi kamar garwashin wuta.Ni kaina ban san lokacin da na ɗauki hanyar Gulbi ba,kawai haka na ji a can ne kawai zan samu salama.Tun daga