Showing 9001 words to 12000 words out of 30354 words

Chapter 4 - MASARAUTAR GOBIR Book Complete Writing by Mrs Sadauki .txt

14 Dec 2024

1372

ke a gashe bisa garwashi.
Ganin yadda Fatimah ta shiga nishaɗi yasa Amadi mayar da abun wasa sai kifin ya gasu sai kuma ya mayar da shi ɗanye ita kuwa wawiya sai dariya ta ke saboda ita ba ta ganin dogon hannun da ke yin masanyar kifin balle ta farga da rufa ido ake yi mata.






★★★ MARADI




"Ta ya aka yi kika shigo rayuwata ba tare da na shirya ba?"Yarima ya tambaya bayan ya hau kan gadon da Saffa take zaune a tsakiya.
"Ta yadda ka yaudare ni kace za ka sa Prince Khalid ya so ni bayan na ci amanar ƴar uwata"Saffa ta basa amsa
"Ban yaudare ki ba,akasi aka samu ko da na farka ban ga Marwa ba sannan sai naji wai an shirya hidimar auren mu"Yarima ya faɗa,Saffa ta taɓe baki tace "dama ranar da Amma ta zo sashen mu na yi mafarkin haka,ƙaddara za ta raba mu kuma za mu sake kasancewa a tare sai dai ban san tsawon wane lokaci hakan za ta faru ba"
"Ko da ta dawo nan to za ta zo ne a ƙuraren lokaci,saboda sai bayan Yarima ya hau karagar mulkin da ta ke tamaƙa za ta ɗora wanin Yarima"murya Amma ta daki kunnuwansu duk sai suka waigowa su na kallonta cike da mamaki saboda sun kulle ƙofa ta yaya ta shigo kenan?




Amma ta saki murmushi tace "da zarar kun raya daren farkon ku to wannan tsohon banzar zai sabka daga karagar mulki kai kuma Yarima ka hau"a zafafe Yarima ya yo kan Amma ya ɗaga hannu zai sharara mata mari ta riƙe hannunsa ta na "kul!kul!Kar ka soma taɓa fuskar nan yin haka zai sa ka samu tsinuwar Mala'iku saboda wannan fuskar ta mahaifiyar ka ce"
"Mahaifiya?"Yarima ya maimaita kalmar ,Amma ta juya baya tace "tabbas Yarima kai Ɗana ne,na jima ina jiran wannan ranar wacce za ta zo na fasa ƙwan" sam Yarima bai samu bakin magana ba sai Saffa ce ta tambayi Amma "ta yaya kika zamo mahaifiyarsa?sannan shi kuma Prince Khalid fah?"
Amma tace "labari ne mai tsayi,yanzu dai zan barku domin raya wannan daren zan koma sashena jiran har izuwa lokacin da zan ji an buga tamburan juyin mulki"ta na gama faɗa ta fice ba tare da ta jira cewar su ba.




Saffa ta dafa Yarima tace "tabbas biri yayi kama da mutum,sai yanzu na ida fahimtar mi yasa Amma ba ta son Prince Khalid ya auri Marwa" Yarima ya dubeta yace "mi kika gane?"ba ta basa amsa ba ta fara tura masa saƙon da ya zautar shi izuwa raya daren farkon su.








Washegari
Masarauta ta tashi da wani firgici sakamakon wani mummunan ciwo da ya kama mai martaba,wanda aka kasa gane taƙamaimai na miye.
A rikice Yarima ya nufi palais bai ma tsaya bin ta Saffa ba wacce ke cikin mugun hali.
Sarki ya kalli Yarima sai dai babu bakin magana sakamakon wasu gunduma-gunduman ƙuraje da suka fito masa a dukan jikinsa har ma da cikin bakinsa.
Idon Yarima taf hawaye yace "Baba..."daga can bayansa Amma ta katse sa wajen cewa "kul kar ka kuskura ka sake kiransa da Baba,domin shi ɗin ba mahaifin ka ba ne.Wannan azzalumin da kake gani shi ya kashe mahaifin ka domin ya hau sarauta sai dai ka sani daga yau shikenan taka ta ƙare,kai da ganin kujerar mulki sai kuma a lahira dan yau ba sai gobe ba zan sa a mayar da can ɓangaren bayan masarauta shegen yaron ka yayi jinyar ka"Amma na faɗar haka ta zo ta janye Yarima daga gare sa ta na mai kuma cewa "taso yarona yau zan guntsura maka labarin masarautar nan mai cike da abun al'ajabi"




"Ba na so ki bari zuwa wani lokaci yanzu zan kai Sarki a duba sa,ko da ace zancen ki gaskiya ne to doli na yi biyayya ga Sarki dan ko ba komi shi ya raine ni tun ina ɗan yaro"Yarima ke faɗa kafin ya fita waje dan zaɓar masu maganin da aka kirawo dan duba Sarki.






Amma ta ƙyalƙyace da wata dariya tace "kai da tashi har abada a haka za ka ƙarasa rayuwar ka cikin datti ka na ɗoyi ka na wari,yadda ruwan ƙoramar kuffa suka ratsa gangar jikin Saffa haka ciwo zai rinƙa nuƙurƙusar ka ta ciki hhhh"Amma ta fara dariya sai kuma ta gumtse sakamakon ganin Sarki na murmushi cikin ƙarfin hali ya buɗa baki duk da ya san in yace yayi magana zai ji zafi kamar ransa zai fita amman ya gwammaci ya mayar mata da martani.






"Ba'a yabon ɗan kuturu sai ya girma da yatsun sa goma,tun kafin ki shigo wannan masarautar na san da zuwan ki da kuma ƙudirin ki.In ba ki manta ba kece mace ta wajen goma da Sarki Salis ya auro amman duk sun mutu sai ke ce kawai kika rayu,kin san dalili?"Sarki na kawowa nan yayi wata dariya wacce da ace akwai ƙaramin yaro kusa da sai ya ruga tsabar tsoro.
Shiru Amma ta yi ta na nazarin lafuzansa,tabbas ita ce ta goma cif kuma ita ɗaya ta yi rai sannan ta rayu.Jikinta ne yayi sanyi amman ta dake tace "ina jin ka miye dalilin?" Sarki ya girgiza kai maƙoshin sa na ciwo kamar ana zuba masa ruwan dalma ya daure yace "ki jira lokacin zai zo"daga nan Yarima ya shigo da wani mai bayar da magani,kallo guda malamin yayi masa yace "mugun sihiri ne aka yi masa,ba zai taɓa warwarewa ba har sai wanda ya yi sa ya bada makarin"
Prince Khalid wanda ke shigowa yace "gyara maganar kai mai bada magani,babu cutar da Allah ya sauko face sai yayi maganin ta .Kuma Allah SW ya ```«Wanunazulu minal ƙur'ani mahuwa shifaa, mun saukar da alƙur'ani ne domin ya zamo waraka a gare ku»```
In ba za ka iya ba ni ka bar ni zan yi jinyar mahaifina"
Amma wacce ita ce Ummul aba'isin cutar ta dubi Prince Khalid,wani banzar kallo ya watsa mata wanda mamaki da firgici suka bayyana ƙarara kan fuskar ta.
Mai magani ya ji haushi yayi tafiyar sa,Yarima ya kalli Prince Khalid cike da haushi yace "mi ka yi kenan?"
"Miye ruwan ka? Ina ce dai mahaifina ne ba na ka ba ko?ko kuwa ba ka ji abinda uwarka ma ciyar amana ta faɗa ma ba?"Yarima ya cakumi wuyan Prince Khalid sai kuma kogo ya juye da mujiya sakamakon bugasa da ƙasa da Prince Khalid yayi tare da hayewa bisa kan ruwan cikinsa ya na ta bugu.
Wani kullu mai ɗauke da furanni Amma ta ɗauka ta bugawa Prince Khalid a kai ya saki wata irin ƙara kafin ya faɗi a sume cikin jini .






Cikin ƙanƙanan lokaci aka kwashi tsohon sarki izuwa ɓangaren baya kamar yadda Amma ta zarta kafin a wuce da Prince Khalid asibitin masarauta.
Ɓangaren guda kuma tuni an fara bushe-bushen algaita da kiɗa ganguna,ba'a wani ɓata lokaci ba aka naɗa Yarima sarkin MASARAUTAR GOBIR.






Amma ta tura Jakadiya gun Saffa ta kimtsata da taimakon wasu kuyangi,sosai ta jigata shiyasa ma ba ta samu halartar taron naɗin sarautar ba.
Cike da ƙasaita irin ta sarakai ya shigo ɓangaren da Saffa take "Queen fito ki ga mijin ki cikin kayan sarauta,daga yau za mu koma sashen tsohon Sarki dan tuni an fara gyara shi"Sarki Bilal ke faɗa yayinda ya buɗe hannuwansa ya na yiwa gimbiyar tasa jawabi,cike da murna Saffa ta shiga jikinsa.A ƙasan ranta ba ta son shi amman ganin ta shiga daula yasa hankalinta ɗan kwanciya kuma ko ba komi za'a kirata da matar sarki,uwa uba za ta iya taka duk wanda ta so ciki kuwa har da Prince Khalid dan ta sha alwashi ko sau ɗaya ne sai sun haɗa shimfiɗa.








★★★DUNIYAR IFIRITU




Tuni Marwa ta saba da Maa,abu guda ke damun ta soyayyar Prince Khalid.Duk yadda ta so hakice sa daga ranta amman abu ya gagara,yanzu haka ma zaune ta ke ta na tunanin sa.
Ba ta san da zuwanta ba sai ji ta yi ta dafa kafaɗarta,ta ɗago ta kalleta gami da yin murmushin ƙarfin hali.Maa ta girgiza kai tace "ba zan hana ki tunanin Muradin Ruhin ki ba,sai dai ina son ki ɗaura ɗamara yaƙar maƙiyan ki tun kafin yaron cikin ki ya zo duniya"Marwa tace "yaron cikina?"Maa ta bata amsa da "ƙwarai kuwa,ki na da juna biyu kuma a yadda ya zo a littafin taswira namiji ne za ki haifa,wanda shine kuma zai zamanto ƙaddarar komawar ki masarautar"
Tashin hankali ya bayyana ƙarara kan fuskar Marwa ,murya a ɗan harɗe tace "Maa ta ya aka yi kika san ina da ciki kuma har da abinda zan haifa?sannan duk ba wannan ba ni gaskiya ba zan koma masarauta ba"
Murmushi kawai Maa tayi haɗi da tona ƙasa ta fiddo wani littafi wanda duk ya tsufa sosai,Marwa ta miƙa masa shi tace "ki ajiye sa gun ki,duk dare na Allah zan karanta maki page guda sannan nayi maki bayani ta yadda za ki gane"
Marwa ta karɓi littafin abun mamaki sai da zuciyarta ta motsa ga wani irin gumi da ya keto mata,Maa tace "iya wannan kawai ya isa ya tabbatar min da komawar ki masarauta domin ke ce fitilar da za ta haska ta"
Kan Marwa ya ƙulle ta tambayi Maa "fitilar masarauta kuma?"
"Ƙwaran gaske domin ke ce ke ɗauke da kabewar kan kabari ba Saffa ba"
Marwa dai sam ta kasa gane inda zancen Maa ya dosa wannan dalilin yasa ta shiga ƴar bukar su ta ajiye littafin kafin ta fito ta nufi inda ƙorama take.
Sawun tafiya ta fara ji a bayanta,da zarar ta waiga kuma sai ta ga babu kowa.Wannan ya sa tsoro wanzuwa a ranta,innuwar mutum ta gani ta na biye da ita kawai sai tayi tsaye cak ita ma innuwar ta tsaya.
"Amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar haƙuri"ta ji muryarsa daga bayanta,da sauri ta juyo saboda zaƙin muryar sa ya wuce misali sai dai tozali da kyakkyawar fuskarsa ya haifar mata da tsoro.
"Mutum ko aljan?"ta samu bakinta da furtawa,shi kuwa ya bata amsa da "aljan" Maa da ke bayan sa tace "Maheer kar ka firgita ta mana"yayi dariya yace "Maa tambayata ta yi ni kuma na bata amsa"
Maa tace "amsar ce ba ta dace ba dan kwanyarta ba za ta ɗauka ba"ya kuma yin murmushi yace "daga faɗin gaskiya?"
Maa ta murɗe kunnensa tace "kai dai ba ka jin magana"ya kama gun ya na mai fidda sautin "Washhh!" Marwa kuwa sai kallon sa take sosai ta shagala sai da muryar Maa ta maidota hayyacinta inda ta ke cewa "Ɗan Sarkin Aljanu ne amman shi ɗin ya kasance Musulmi ,shine malamin da zai koyar da yaron ki karatu daga zarar kin haihu"
Marwa ta murmusa ta na mai kallon Maheer,so take ta tantance shin da gaske aljanin ne ko kuwa?
Maa tace "ki gaishe sa"
"Assalamu alaikum"ta faɗa kamar wacce aka yi ma doli,Maheer ya amsa mata sallamar sannan ya ƙara da "da ace addinin Musulunci bai soke auren jinsi biyu ba da tabbas Yarima ya samu matar aure"ambatar sunan Yarima ya saka zuciyar Marwa motsawa daga tabon da ke cin ruhinta,Maa ce ta basa amsa da "da kam na tsaya maka har inda ƙarfina ya ƙare duk da dai littafin taswira ya gama tsara mata kudin ƙaddararta"
Maheer ya ɓata fuska yace "littafin tsafi har wani littafin ƙwarai ne da mutum zai yarda da shirmen sa?mu Addinin Musulunci ce mana yayi komi na Allah ne,daga gare shi mu ke kuma gare shi zamu koma sannan shi ya tsarawa kowa rayuwar da zai yi.Misali kamar gimbiya Marwa daman Allah ya ƙaddara za ta zo nan sai dai kawai ace sharrin tsafin ku ne sila"
Fuskar Maa ce ta yi baƙi ƙirin jin Maheer na sukar su amman babu yadda ta iya saboda sanin kanta ne Maheer bai taɓuwa gare su saboda ƙarfin imaninsa.




"Ya kamata ka koma kar Sarki yayi neman ka"Maa ta faɗa ta na mai kawar da kai,Maheer yace "kin matsu na tafi ne dan kar na rinjaye ta ko kuwa?"
Maa tace "ai ko yanzu ta na yin sallah da sauran ibadun ta, wannan dalili ya sa mu ka tsaya bakin gari saboda isar ta can da matsala ka san tsakanin sihiri da Alkur'ani kamar wuta ce da karmami"
Maheer ya ƙanƙance ido yace "Maa kenan kin san alƙur'ani jagaba ne akan komi na duniya?amman miyasa ba za ki aje bokanci ki tuba ga Allah ba?"
Maa ta dube sa tace "a'a kudin ƙaddara ya tsara min haka"ganin dai Maa ba za ta fahimta ba yasa Maheer yi masu sallama ya fara tafiya bai yi nisa ba ya ɓace a idon Marwa.
Ta sauke ajiyar zuciya "Maa miyasa ya ke zuwa nan alhalin shi ya kasance Musulmi kuma kin ce sai Ifiritu da masu aiki da su kawai ke wannan Nahiyar?"Marwa ta yi wannan tambayar ta na mai maida dukan hankalinta ga Maa.
"Shi ɗin zuciyarsa tsarkaka ce,a kullum burinsa bai wuce ya mayar da wannan Nahiyar ba yankin Musulmi.A lokacin baya duk ranar juma'a ya ke ziyartar mu,zai zo yayi wa'azi wani sa'in kafin ya gusa sai ya rinjayi wasu sun shiriya kama daga bil'adama zuwa Jinnu " Maa ta bata amsa ta na mai sunkuyawa ta ɗauki wata sarƙa.










★★★ MADARUMFA




Yamma lis su Amadi suka dawo gida ,a bakin ƙofar gidan su Fatimah suka tsaya su na hira.
Abdu ya zo suka gaisa da Amadi sannan ya shaida masa saƙon Innaro,kamar wani mutumen kirki haka Amadi ya shiga godiya.
"Ki shiga ciki amaryar Amadi magrib ta gabato zan je na yi sallah na je bakin gulbi yau aikin dare zan yi"
Fatimah ta ɓata fuska tace "Ni dai gaskiya ka canza sana'a dan ba zan lamunci wannan ba"
Amadi yace "mi kenan?"ta bashi amsa da "fitar dare mana"
"Kar ki damu in dai wannan ne,ina ce ma dai gulbin ya kusa tafiya sai kuma wata shekara.Am...ki shiga gida sai gobe da safe zan zo nan kafin na wuce aiki"
"To ya maganar turo da magabatan naka ko har ka manta?"Fatimah ta tambaya
"Ta ya zan manta ke ma,ai sai in babu rai a gangar jikina dan na tabbata ko haukacewa na yi ba zan manta wannan babban abun farin cikin ba.In shaa Allah gobe zan turo da komi kin ji amarya ta?"da sauri Fatimah ta rufe ido dan kunya gami da rugawa cikin gida shi kuwa Amadi ya na dariya ya nufi na su gidan.






Washegari
Sai da amadi ya cika alƙawarin sa na zuwa ya ga Fatimah kafin ya wuce bakin rafi.
Duk wunin ranar Fatimah cikin murna ta yi sa ganin dangin mahaifanta tuni sun hallara domin tarbar bakinta.
Lauriya da sauran ƙawaye sai murna suke taya Fatimah yayinda tuni dangi Amadi sun hallara sai buɗa ke tashi,bayan an karɓi sadaki aka ɗaura aure kamar yadda al'adar garin ta ke.An tsayar da sati biyu ranar da za'a yi walima kafin amarya ta tare gidan mijinta.






Ana shirin magrib Amadi ya shigo gida kamar kullum,bayan sun gaisa da Inna ne ta ke shaida masa an tsayar da bikin su sati biyu masu zuwa.Babu kunya Amadi ya fara taka rawa kafin ya wuce cikin ɗakinsa,ƙwarya da ke ƙarƙashin gadonsa ya ɗauko ya duba ya gani ruwan cikinta sun yi ƙasa hakan na nuni da gulbi ya kusa ƙwafewa.Ya mayar sannan ya fito yayi wanka ya tafi masallaci,ya na dawowa Inna tace "Amadi ga abincin ka nan rufe da faifai"ya girgiza kai yace "ai yau ba zan ci komi ba saboda murna,amman ina son na je wajen Ɗan Ladi mai balangu na saya mana mu ci ni da Fatimah kin ga sai mu taya junan mu farin ciki.Ke ma kin faɗan abinda kike so sai na biyo maki da shi"
Inna tace "a'a ni kam ba zan ci komi ba amman in ka fita ka biyo ma malam da fura sai na dama masa "da "toh"Amadi ya amsa kafin ya fice.






Direct wajen mai balangun ya nufa ,bayan ya saya sai ya wuce gidan su Fatimah.Har ciki ya shiga yayi sallama jin ta amsa masa yasa shi fitowa waje ya zauna kan dakali zaman jiranta,ba'a jima ba can sai gata ta fito cikin shigar atamfa da zane ta ɗaura kallabin wani yadi daban.
A kunyace ta zo ta zauna kafin ta gaishe sa,ya amsa ya na mai tambayarta mutan gida ta amsa masa da "alhamdullah,ya naku gidan fatan su Inna na lafiya?"
"Lafiyarta lau tace na gaishe ki sannan na kawo maki balangu"Amadi ya faɗa ya na mai buɗe ledar ya aje a tsakiyar su yace "Bismillah mu ci"a al'adar Fulani budurwa ba ta iya cin abinci a gaban namiji,amman kasancewar Amadi ya gama sihirce Fatimah haka ta saka hannunta suka cinye bulangun nan tas har da shiga gida ta ɗebo masu ruwa.
Hira suka yi sosai game da kawo lefen da aka yi da kuma yadda bikin su zai kasance,a ƙarshe suka yi ma juna sallama.










Bayan sati biyu aka yi walimar bikin su Amadi,dangi da ƙawaye suka rako amarya ɗakinta wanda ya kasance gidan iyayen Amadi a nan cikin ɗakinsa wanda ya sha gyara.
Bayan kowa ya watse Amadi ya shigo ɗakin amarya shi ɗaya, kasancewar duk garin Madarumfa ba za'a nuna wani ba a matsayin abokinsa.
Cike da bege da shauƙi irin na amare Amadi ya yaye maluluɓin da aka rufeta,a kunyace ta so ƙwace darar sai dai tuni Amadi yayi mata dirar mikiya.Duk yadda Fatimah ta so ƙwatar kanta abu ya cuttura saboda da dukan alamu shi Amadi so ya ke kawai ya cimma burinsa wanda kuma kusan agonye ne ne haka.
Ƙarar da Fatimah ta yi yayi daidai da faɗuwar Malam wanda shi kuma shigowar sa kenan,da sauri Inna tayi kansa ta na "Innalillahi wa'inna iley raji'un"ruwa ta yi ta zuba masa amman shiru.




Tsawon lokaci sosai Amadi ya fito daga ɗaki jin kukan mahaifiyarsa ya ƙi tsayawa,da sauri shi ma ya nufi malam ɗin kafin ya koma ɗaki ya ɗauko fitila ya haska malam.
Da sauri ya saki fitilar ya na mai furta" Innalillahi wa'inna iley raji'un" yayinda ita kuma Inna ta faɗi a sume.....
[08/09 à 08:24] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR*



LoVe and HoRoR StOrY


*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)


*Lambar waya:* +22795045822


*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.


*Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya.




_____________________






9-10








Jini ne ke fita a duk wasu ƙofofin fuskar malam,hanci,ido, kunnuwa da kuma baki.
Amadi ya saki fitilar zuciyarsa na bugun tara-tara,a doli ya fita ya nemo mai mota aka kai shi asibiti sai dai daga zuwansu aka tabbatar masu da rai ya riga da yayi halinsa.
Inna ta turje ta ƙi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login