Showing 15001 words to 18000 words out of 30354 words

Chapter 6 - MASARAUTAR GOBIR Book Complete Writing by Mrs Sadauki .txt

14 Dec 2024

1381

ƙarfe da Kaka ke ajiyar shi shekara da shekaru don ko da na buɗe ido na ganta da abin ta sannan in ciwon mutum yayi ƙamari wasu na zuwa ta basu magani.


Sosai na yi mamaki ganin tsofin hotuna waɗanda za su kai ɗaruruwan shekaru a cikin akwatin.A hankali nake dubawa har na zo kan wata sarauniyar kifaye,yanayin fuskarta kawai zai tabbatar ma ita ɗin muguwa ce.Abubuwan ban tsoro na ta ci karo da su waɗanda na cika kallo kuwa sai na ji idona sun yi wani zuuuuu! Kamar su na zuƙo wani abu.Jin kamar motsinta kawai sai na yi saurin na mayar da komai na tura akwatin.




“Ku shigo” cewar Kaka alamun baƙi ta yi ,don dama jefi-jefi ta kan same su.
“Sarah ki fita waje ina har mu gama” Kaka ta umarce ni.
Fitar na yi kamar sauran lokutan da in ta samu ziyara haka za ta ce na fita ni kuma sai na yi amfani da wannan na je wurin wasa sai dai yau wani abu ya shiga kwanyata na son sanin shin mine ne Kaka ke yi da kullum take fiddo ni waje?


Sai da na bari an ɗauki kamar minti biyar sannan na yi ƙoƙarin tashi daga inda nake saboda yadda zuciyata ke azalzala ta sai dai abun mamaki ji na yi ƙafafuna sun riƙe ba zan iya tashi ba kamar wacce ta samu shanyewar jiki.Ina nan cikin wannan hali har baƙin suka fito waɗanda suka kasance mata biyu ne uwa da kuma wata budurwa.Abun mamaki sai a lokacin ƙafafuwana suka saki,Kaka ta bini da wani kallo ta na mai jingina da lanlaga-langan ƙyauren ɗakinmu.






“Tun yaushe kika fara jin wannan canjin?” ta jefo mini tambaya.
Na miƙe tsaye ina cewa “wane irin canji?”
“Na son ganin abin da nake yi” ta bani amsa kai tsaye.Na turo baki gaba na ce “to mine ne kike yi?”
“Ki na son sani?” ta tambaye ni,na gyaɗa kai alamar eh tace “sai kin faɗa min mi ya faru da ke cikin ruwa” ban san ko mine ne dalili ba haka kawai na ji ina son ɓoye mata,na ce “babu komai ni da na faɗa ruwa ta ya za a yi na san abin da ya faru? Ki tambayi su Laila kawai”
“To shikenan” Kaka ta faɗa amma tabbas a cikin ƙwayar idonta ina ganin ƙin yarda da zancena wanda kuma ban san dalili ba.




Da dare bayan mun ci abincin Kaka ta soma yi mini gatana irin ta ababen tsoro,don ina son irin wannan labaran a haka na soma jin bacci kamar kullum sai dai na yau ya sha banban da sauran baccin da nake yi don kuwa idona a rufe suke amma ras nake ganin Kaka wacce take yi mini wasu abubuwa da na kasa gane su.
Gashin kaji ne na ga ta maƙala bayan kunnuwan ta,ban gama mamakin dalilin yin haka ba har sai da na ga ta rikiɗe ta zama kaza sannan ta tashi sama.Maimakon ni da ke kwance cikin ɗaki na zamana a nan a'a duk inda Kaka ta nufa ina kallo,gidajen mutane ta dinga bi ta kasaye rufin ɗakinsu ban san dalilinta na yin haka ba sai da ta gaji da yawo kafin ta dawo ta gida.Siffarta ta ɗauka ta mutum daidai nan kuma baccin gaske ya ɗauke ni ban farka ba sai washegari,babu sallah babu salati haka na fita na yi fitsari na wanke ido.Wata irin yunwa nake ji,sai yanzu na nufi Kaka wacce ke zaune kan tabarmar kaba ta na zuba taba cikin leda.Tsaye na yi cak ina kallon ƙafafunta da suke sak irin na kaza,da sauri na ɗauke idona da na ga za ta ɗago kai.


“ lafiya kika yi tsaye nan?” ta tambaye ni.
“Yunwa nake ji,kuma kin san jiya ban je na taya Lantana sayar da abinci ba ballantana ta bani” na bata amsa,ko kafin ta ce wani abu Sailuba ta shigo gidanmu da sallama.
Da sauri na gaishe ta,ita kuma ta shiga gaida Kaka kafin ta maido dubanta gare ni ta ce “jiya ba ki gama mini aiki ba kika rufe shago ina makullin yake?”
Na waro ido kafin na fara lalubar riga ta ai kuwa na ci sa'a ya na ciki,na fiddo na bata ta karɓa kafin ta ce “mu je to ki ƙarasa” haka na bi bayanta muka tafi salon ɗin inda take yi wa mutane gyaran gashi da farce ,ta na yin kitso kuma da lalle.


Tun da na ga mota a parker na san hajiyar birni ce ta zo,don haka duk muke kiranta.Duk bayan watan-wata take zuwa ta na sayen gashin mutane da ya zubo wurin gyara,ban san iya lokacin da suke tare da Sailuba ba amma dai na san wannan shine business ɗin su.
Bayan Sailuba ta buɗe ɗan madaidaicin shagon ta ɗauko wata ƙatuwar leda ta zazzage duk gashin mutanen da aka tara, sai a lokacin Hajiya ta shigo ta karɓa ita kuma ta bata maƙudan kuɗi ta karɓe ta na godiya tare da cewa “hajiya sai kuma in kin sake dawowa”har mota ta yi mata rakiya kafin ta dawo sai fara'a take ta na ƙirga kuɗin.Karon farko da na ji ina son sanin dalilin business ɗin sayar da gashin mutane,na ce “anty wai don Allah mi hajiyar birni ke yi da gashi nan”
“Ina na sani Sarah ? Ni dai ba ta bani kuɗina ba? Can ita ta sani in ma dai dafa shi za ta yi ta ci.Ɗauki tsintsiya ki share wurin kafin mutane su fara zuwa sannan ki ɗauki allon sanarwa ki fidda shi waje” ta na gama faɗa ta fice ta bar ni da tambayoyin da bani da amsar su sai dai na sha alwashin sai na binciko su.....








*Gajeren labari ne*🌚
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*👁️
👁️👁️👁️👁️👁️
HoRrOR story☠️


Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️


*FCWA ☀️*




3-4


Cikin sauri na share shagon na goge tile da kuma ƙaton bancin da aka jera mayuyuka na wanke gashi da kuma wanda ake shafa wa bayan an fiddo mutum daga tukunya.
Zaune na yi na ɗauki hullar jiya da ban ida saƙawa ba,ina tsaka da yi sai ga anty Sailuba.Leda ta miƙo min ta dambu na karɓe na huda bakin ledar na soma ci ina shan ruwa har na gama.
Ɗan ƙaramin rediyo anty Sailuba ta kunna muka fara shan kiɗa,wasu ƴan mata uku ne suka shigo ɗaya na santa ta na zuwa gyaran gashi, biyun kuma baƙin fuska ne.


“Sannun ku da zuwa ku zauna,Sarah kawo musu ruwan sanyi Watsima sai yau aka dawo ina ta zuba ido shiru” anty Sailuba ta faɗa fuskar nan tata cike da fara'a don a haka take saye customer ɗinta.


Kan kujera duk suka zauna yayin da Watsima ta biɗe kai ta na cewa “wallahi anty Sailuba gashina duk ya lalace dubi yadda ya koma,shi yasa na zo ki gyara min shi da kyau biki ake na ƙawarmu”
Ruwan sanyin na miƙa wa kowacce leda ɗaya,kafin na zuba idona kan gashin Watsima da ya cicire a gaba sannan tsayinsa ya rage ba kamar wancan zuwan da ta yi ba.




Anty Sailuba ta shiga tatataɓa gashin ta na cewa “ doli gashin ki ya lalace mana Watsima,ba ki zuwa saloon sai fa in za ku yi sabga da ace ki na zuwa akai-akai wallahi tsaf za ki ga ya miƙe yayi tsayi.Bari na nuna miki wani sabon man tado gashi,zan saka miki shi yanzu in na wanke miki kai in ki yayi miki kuma sai ki saya” ta faɗa tare da zuwa gaban table ɗin ta ɗauko wata ƴar kwalba ta miƙa wa Watsima kafin ta ce “ wannan ƙawayen ki ne?”
“Eh su ne nake baki labari waɗanda na ce miki ƴan uku ake kiranmu ” ta bata amsa.


Anty Sailuba ta ce “ Allah sarki ga shi kuwa har kun so ku yi kama da juna,su ba za a yi musu gyaran gashin ba?”


Watsima ta kalle su kafin ta ce “ kun yi shiru sai kace wasu kurame ita wannan kitso za a yi mata ita kuma wai a ɗinka mata gashin doki ya haɗe da na ta”


Anty Sailuba ta yi dariya kafin ta ce “ Sarah zo ki yi mata kitso ki aje hankali sosai kin ga yau ta fara zuwa ina son ayi mata wanda za ta jawo mana customers” ta ida zancen cikin raha.


Wacce aka ce zan yi wa kitson ta ce “ wannan ƴar yarinya ? Na zata ke za ki yi min” sai ta ɓata rai.
Anty Sailuba ta ce “ wai don a yi sauri ne na ce haka,amma in ni kike son duk ɗaya ne .Watsima ke zauna ta wanke miki gashin in ta gama miki sai ta ɗinka wa wannan gashin dokin”




Ita Watsima ta san ni sarai,shi yasa ba ta yi gardama ba ta zauna na shiga wanke mata gashin nata.Bayan na tsane shi da towel sai na soma saka mata kwarkwaro daga nan ta shiga tukunyar busar da gashi.
Na maido dubana ga wacce zan saka wa gashin dokin na ce “ kin zo da mèche ɗinki ko saya za ki yi?”
“A'a saya zan yi ai ku na sayar wa ko?” ta tambaye ni,na bata amsa da “ eh bari na ɗauko ki zaɓa” kalolin na kawo mata bayan ta zaɓa ta koma ƙasa ni kuma na hau kujera na soma saƙa mata ita tsawon lokaci muna abu ɗaya don akwai wuya kafin na je na duba gashin Watsima tuni ya bushe kuwa.Na kashe casque ɗin ita kuma ta fito ta zauna kan kujera,mai na ɗauko da niyyar shafa mata sai kuma na ƙure gashin da ido.


Wani haske na ga ya dalle gashin wanda kuma ina da tabbacin daga cikin idona yake,haka kawai na ji ina son gwada wani abu da ban san taƙamaimai mine ne ba.Can ƙasan zuciyata na raya ‘ gashi tsiro ka yi tsayi’ ai kuwa haka na ga ya ƙara tsayin na saki murmushi ni ɗaya zan sake ƙara gwadawa Watsima ta ce “ wai ba za ki gyara mini gashin ba ne na tashi?” da sauri na shiga shafa mata mai sannan na shace.


Daga can anty Sailuba ta ce “ kin ga kuwa wallahi gashin ki har ya ƙara tsayi yanzu da kika shiga tukunya,mutane sun kasa ganewa ka wanke gashi gida ba ɗaya yake da ka zo saloon ba”
Cike da murna ita ma Watsimar ke duba ƴar jelar gashinta da na ɗaure,ta ƙara tsayin ba ƙarya wanda kuma ni kaɗai na san wannan sirrin.


“ A gaishe ki ƴar yarinyata aikin ki na kyau” anty Sailuba ta faɗa bayan na kammalawa ɗayar ita ma.
Wacce ta ke yi wa kitson ta yamutsa fuska ta na kallona kafin ta ce “ ɗiyar taki dai ƙazama ce dubi jikinta kamar almajira da wani baƙi nata kamar zunubi”
Anty Sailuba ce ta shigar min “ a'a yau dai ne ta tsaya da dauɗa shi ma don ba ta shirya ba na je na kirawo ta amma ta na da tsabta”


Ta tuntsire da dariya ta na kallon kaina wanda yake ɗauke da kitso ƙire-ƙire saboda yadda banda gashi kafin ta ce “ da wani gashi nata kamar gammo! Ko da yake yawancin ƴaƴan masu salon suke babu gashi duk aci gwaigwai ne”


Zuwa wannan matakin tuni raina ya ɓace amma ban ce komai ba sai gashinta da na ƙurawa ido, dogo ne mai santsi duk yadda aka yi ta gama iri da Fulani .A take kuma baƙin ciki ya kama ni ‘ Allah sa gashin naki duk ya zube’ na faɗa a zuci ina mai ci gaba da kallon gashin yayin da idona kuma sai vibration suke suna min wani zuuuu!


“ Je ki yi wanka ki dawo kar ki biye mata,ni kam mine sunan ki?” anty Sailuba ta buge da tambayarta bayan ta umarce ni na je na yi wanka.
“ Leemat” ta bata amsa nan ne na san sunan nata da haushinta kuma na fita na wuce gida.


Ina shiga na tarar Kaka ba ta nan sai ɗaki da ta rufe shi ma ba kwaɗo,na buɗe na shiga.Jakar kayana na jawo don fiddo kayan da zan saka abun mamaki kuma sai na tarar da munduwa ɗina a sama .Cike da murna na ɗauke ta na mayar a wuyana,tsakar gida na fito na cika buta da ruwa na je na yi wanka da wani guntun sabulu .Ina fitowa na saka kayan da na fitar kafin na nufi gidan anty Hinda mai sayar da abinci.Ta na gani na ta haɗe rai na san fushi take da ni saboda jiya ban zo ba,na sosa ƙeya na ce “ ina kwana anty?”
“Lafiya!” ta amsa mini da shi kafin ta ɗauko wani bokiti mai ɗauke da wasu ruwa kamar sauran wanka don har da sabulu-sabulu amma haka ta buɗe tukunyar mita ta juye su.
Sai kuma na ga ta kalle ni a ɗan daburce kafin ta ce“am...yau ba ki je wurin Sailuba ba ne?” ni kuwa ganin ta saki ranta yasa na watsar da zancen ruwan dauɗar ta zuba a miya na ce “na je yanzu ma can zan koma,dama biyo wa na yi na baki haƙuri abin da yasa jiya ban zo ba ruwan Gulbi na faɗa sai bayan magarib na farfaɗo ” ta shiga tashin hankali sosai kafin ta ce “Allah tsare gaba,to in kin tafi don Allah ƙarfe biyu na ɗaya na buga wa ki wuce can inda muke sayar da abinci kin ga dai yau mai yawa na yi fiye da na kullum” da to na amsa mata kafin na koma saloon har an kusa ida mata kitson ,yanzu ma da na dawo sai da ta tsokane ni “aci gwaigwai an jiƙa dauɗa da sunan wanka”
Anty Sailuba ta ce “Leemat ban son haka fa” dariya ta yi tare da ci gaba da yi min sharri,tsabar iskanci ma da za su tafi haka ta sa yatsa a fuskata ta na dirzawa ta na cewa “wallahi duk baƙin ta ne na zata ko dauɗa ce” na ture hannunta ina hararenta ta dungure min kai ta na sa tissu ta goge yatsanta ta ce “na shafo dauɗa” sai ta kai yatsan ga hanci ta na sunsuna wai wari nan fa suka shiga yi mini dariya,ni kuma kawai sai na fashe da kuka bayan tafiyar su ne anty Sailuba ke ce mini “ke wasa fa take yi miki kawai don a yi dariya” sai dai duk yadda ta so shawo kaina ƙin yarda na yi kawai dai na haɗe abin a zuci na kammala mata aikin da zan yi kafin na wuce wurin sayar da abincin.


Yadda na ga dandazon mutane duk sun yaɓe anty Hinda sai abin ya bani mamaki don mun sha yin kwantai sai mun dawo da abinci gida yau kuma abun mamaki tururuwa saya ake.Ashe farkon mamakina ne ban ma ga komai ba,sai da na ƙarasa na soma taya ta sayarwa hatta yadda ake zuba abincin an rage awo amma haka muka sayar da shi tasss sai wanda ta zuba mini .Sai da na wanke robobin da aka ci abinci sannan na zauna na soma cin abincin hannu baka hannu akushi,daga nan gida na wuce amma har yanzu Kaka ba ta nan ganin haka na koma saloon ba ni na koma gida ba sai wajen taran dare.
A zaune na tarar da Kaka ta na sauraren rediyo ,bayan na gaishe ta tare da tambayar inda ta je na samu wuri na zauna.Amma sai na ga Kaka ta ƙure cikina da ido,ban kai ga tambayar ta lafiya ba kuma na ji ya fara mirɗa mini.Maimakon in yi zawo a'a kumfa ne ya soma fito mini ta baki kamar akuyar da ta haɗi leda.Kaka ta yi ƙyaci kafin ta bani magani na sha nan na soma amai kamar zan amayar da hanjin cikina,“haba Hinda da ni kike zancen!” ta sake yin wani ƙyacin.....








*Gajeren labari ne*🌚
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*👁️
👁️👁️👁️👁️👁️
HoRrOR story☠️


Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️


*FCWA ☀️*




*NB:* Maitar ido iri-iri ce akwai ta tsafi,akwai kuma wacce ake haifar mutum da ita irin tace wacce in mai ita ya kalli abu da ya burge shi ko akasin haka sai kuka abin ya lalace.Itaciyar bedi ta sha mutuwa silar Maitar ido,wasu sun san su na da ita wasu kuma ba su sani ba.In sha Allah a sannu zan faɗi alamominta da kuma yadda mutum zai yi rabu da ita.




5-6




Na sha baƙar azaba sosai kafin na samu aman ya tsaya,Kaka ta ce “je ki kwanta ” ban musa ba na haye katifa a gajiye,sai dai tuna abin da Leemat ta yi mini yasa na ji baƙin ciki ya rufe ni.Na yi ƙwafa kafin na ce “wai Kaka don Allah baƙin nan na wane ne na kwaso? Tsakanin Inna da Abba waye baƙi?”


Abun mamaki tambayar tawa ce na ga ta razana Kaka,sai ta kasa bani amsa sai motsi take da baki ni kuma na ƙara jin haushi na ce “a gaskiya ko ma dai wane ne na biyo ya cuce ni,yau an wulaƙanta Ni an tozarta ni saboda kawai ni BAƘA CE(Sajida Nijar)”


Kaka ta ce “mi ta yi miki? Sannan wane mataki kike son a ɗauka kanta?”
Jin abin nema ya samu har da tashi na yi zaune ba tare da na san wannan ne farkon jefa rayuwata a cakwalkwalin ruɗani,na ce “so nake ta zama baƙa kamar dai ni,sannan gashin kanta wanda ta yi mini gori a ɓata shi ya zamana nawa ma ya fi nata kyau da tsayi”


Kaka ta saki murmushi wanda a cikinsa na hango tsantsar farin ciki kafin tace “Sarah kin tabbata ki na son haka?”
Ba tare da wani tunani ba na ce “eh sosai ma Kaka”
Ta ce “kin shirya?”
“A shirye nake ai” na faɗa ba tare da na san shirin mi Kaka ke nufi ba,ta ce “to babu damuwa yau za mu je ki ɓata rayuwarta da kan ki,don haka kwanta ki yi bacci tun kafin dare ya tsala ”


Cike da murna na kwanta ina tunani ƙila acid za mu je mu watsa mata sannan mu datse gashinta,da haka bacci ya ɗauke ni.Na ɗauki lokaci mai tsayi a cikinsa kafin na ga Kaka na yi min irin wannan abun na jiya,wasu ruwa ne take yayafa min ta na yin wasu surkullen da ita kaɗai ta san ma'anar su.Abu guda na sani shine bacci nake,amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login