Showing 6001 words to 9000 words out of 30354 words
Chapter 3 - MASARAUTAR GOBIR Book Complete Writing by Mrs Sadauki .txt
ta shanye ruwan tas sannan ta janye bakinta.
Murmushi kan fuskar Saffa ta kama hannun ƴar uwarta tace "zo mu je na gwada maki wani abu "babu muso ta bi bayanta kamar raƙumi da akala.
Har suka fito farfajiyar gidan babu motsin kowa,Marwa ta fara jin jiri kafin daga bisani idonta su juye ta dubi Saffa tace "kin ci amanar zumunci tunda har za ki iya cutar da ƴar uwar tawaicin ki" ita ma Saffa kamar almara haka idonta suka koma kore sannan tace "akan Prince Khalid babu abin da ba zan iya yi ba"ba su sake yin magana ba Yarima ya fito daga cikin wani lambu ,hannun Marwa ya kama tare da janta zuwa sashen shi yayin da ita kuma ta waigo ta na kallon Saffa idonta taf hawaye ita kuwa Saffa cike da murna ta koma ɓangaren Amma ta shige ɗakin da aka saukar da Marwa tare da haye gadon.
Tamkar wani gumki haka Marwa ta tsaya Yarima na cire duk wani abu da ya shafi tufafi a jikinta.
Gefe ya koma ya na ƙare ma surar jikinta kallo wacce zai iya cewa duk neman matan da yake bai taɓa cin karo da wacce ta kai kwatankwacin Marwa ba.
Yarima ya hura mata iska a idonta,luf ta lumshe ido ya ɗauke ta cak ya ɗora kan bed tare da yi mata rumfa,hasken ɗakin ya kashe can tsawon lokaci Marwa ta yi ƙara guda tal daga ita ba ta sake ko da motsi ba.
A ɓangaren Amma kuwa,ta na can ɗakin sirrinta.Ido rufe ta ke gudanar da aikin kafin daga bisani ta ji saukar wata tukunyar laka cikin tafin hannuwanta,ta miƙe tsaye ta nufi ƙofa wacce ta buɗe da kanta duk da idonta a rufe suke bai hanata nufar sashen da ta ajiye Marwa ba.
Ta na shiga ta fara kwarara ma Saffa wannan ruwan,da sauri Saffa ta buɗe idonta ta na jin yadda ruwan ke shiga cikin ɓargonta haɗe da jinin jikinta.
Wata guguwa ce ta taso,duk window sashen Amma da na Yarima suka shiga buɗe kansu,wani numfashi Marwa ta ja ta dawo daga doguwar sumen da ta yi.A hankali ta buɗe idonta ta sauke su kan fuskar Yarima,ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta yunƙura ta tashi babu alwala balle wanka ta saka kayan jikinta.
Farfajiyar masarauta ta fito ta nufi ƙofar fita,ta na zuwa kusa da ƙofa sakatar ta fita daga gidanta yayin da ƙofar ta buɗe ita ma da kanta Marwa na saka ƙafarta a waje taguwar masarauta ta yi wani irin kuka.....
[06/09 à 08:38] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR*
LoVe and HoRoR StOrY
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya.
_____________________
5-6
Guguwar da ta taso haɗi da iska mai ƙura yasa Marwa rufe ido kan ta farga numfashinta ya rabu da gangar jikinta.Cikin iska aka dinga hura gangar jikinta da ruhinta izuwa wata duniyar.
Kwance take bisa wani aga-lemu gefenta wata tsohuwa ce ta na jujuya wasu ganyayyaki a ƙwaryar ruwa.Kamar mai wankan biƙi haka ta rinƙa yi ma Marwa har sai da ta dawo hayyacinta,idonta ta buɗe ta na jin sun yi mata nauyi.Bisa fuskar dattijuwar ta sauke idonta,hasken da ke tsakiyar goshinta ya sauka cikin idon Marwa tamkar yadda ruwa ke shiga ƙarƙashin ƙasa.
Zumbur Marwa ta tashi zaune ta na raba ido kafin ta maido dubanta ga dattijuwar cikin wani yare wanda ita kanta ba ta san na miye ba Marwa ta fara magana "Maa sun cutar da kansu da kansu,a duniyarmu kowanne ɗan Adam kansa kawai ya sani saboda biyan buƙatarka sai ka cutar da wanin ka..."Marwa ta ja numfashi yayin da Maa wacce ta kasance baƙar mace tace "kamar yadda kika faɗa ɗin dai tun farko kansu suka cuta ba ke ba,amman ki sani wannan al'amari ya na cikin kudin tsafi a rubuce.Ita kanta Amina da ta san wahalar banza take da ba ta raini ajalinta ba"
Marwa ta dubi Maa da alamun tambaya sai dai ba ta ga fuskar yin tambayar ba,hakan yasa ta miƙe kamar yadda ta ga Maa ta yi.
"Biyo ni"shine abin da ta faɗa tare da yin gaba,daji ne suka shiga ratsawa wanda sai an ɗauki tazara sosai sannan ka hangi gidajen mutane.
Marwa ba ta yi ƙasa da gwiwa ba wajen tambayar ma "ina ne nan?" Ba tare da Maa ta juyo ba ta bata amsa da " *Yanki Ifiritu* ne"Marwa ta kuma sake tambayarta da "amman ya aka yi na ga bil'adama ne ke rayuwa ba Jinnu ba kamar yadda na ji sunan?"
"Saboda ƙarni biyu ne,akwai gidajen Jinnu fiye da na bil'adama ke ba kya ganinsu ne saboda ƙarfin power ɗin ki bai da yawa,duk wani bil'adama da za ki gani a nan to ya na aiki da aljanu ne.In ma dai shi matsafi ne,ko ɗan siddabaru,ko kuwa Mayu"jikin Marwa ya soma rawa tace "amman ni mi ya kawo ni nan?"Maa ta ja ta tsaya ta dubeta da kyau tace "ƙaddarar ki,ko dama can nan ne asalin ki yanzu kuma kin dawo gida"
"Ban gane ba,dama can na taɓa rayuwa a nan?"
"A'a ba ki taɓa rayuwa ba amman ainahin tsatson ki a nan suka rayu,kuma cibiyar ki a nahiyar nan aka rufeta"Maa na gama bata amsa ta yi gaba sai kuma ta tsaya tare da waigowa tace "ya aka yi kuma kika tsaya?Tafo mana"jiki babu ƙwari Marwa ta bi bayanta suka ci gaba da tafiya har sai da suka zo daidai wata bishiya sannan suka zauna dan hutawa.
"Ya aka yi na tsinci kaina a nan Nahiyar?"Marwa ta tambaya,Maa ta murmusa tace "lokacin zuwan ki ne yayi shi yasa"
Marwa ta ɓata rai ta kuma tambaya "ina son sanin yadda aka yi na zo wannan duniyar alhalin ni a ƙofar Masarauta kawai na iya tunawa"
Maa tace "ɗaga kan ki sama"a hankali Marwa ta ɗaga kanta sama abun mamaki kanta ta gani lokacin da ta fito daga masarauta har sadda guguwa ta taso ta dabaibaye ta kafin ta wuwulniya da ita cikin iska,sai kuma ta faɗo cikin ciyayi ba'a ɗau lokaci ba sai ga dattijuwar nan mai suna Maa ta ɗauketa cak izuwa inda aga-lemunta yake shimfiɗe daidai nan girgijen da ke kamar magiji ya ɓace ɓat.
A maimakon Marwa ta ji tsoro sai kawai ta ji wani ƙarfi da kuzari sun zo mata,ido ta lumshe ta na sauraren bugun zuciyarta "tabbas wannan ya na ɗaya daga cikin jerin mafarkan da nake yi"tayi furucin idonta a rufe.
Masarauta
Wani sanyi laƙas ne ya shiga ɓargon Saffa yayin da zuciyarta ke tuƙiƙin baƙin ciki,wanda ba komi ya haifar mata da haka ba sai jin furucin Amma "da taimakon wannan sihiri kin zamanto matar Yarima Bilal,babu ɗaurin aure ko siga balle wani rabon goro kawai zuwa gobe za'a kai ki sashensa,a yadda nake faɗa maki wannan lafazin to haka duk sauran al'ummar da ke cikin masarauta za su ji tamkar an ɗaura auren ku ne shagalin biki kawai za'a yi.Kar kiyi baƙin ciki ƙaddarar magajin masarautar nan ta zo da wannan"Amma ke magana idonta a rufe kafin ta ci gaba da yin tsafe-tsafenta ita kuwa Saffa ƙuri ta yi mata ta na auna ko wace kalma bisa sikelin hankali,abin da ta fahimta zaman dadiro za su yi ita da Yarima Bilal.
Saffa ba ta tsinke da lamarin ba sai da ta ji busar algaita yayin da gefe ɗaya kuma dogari ke shelar shagalin bikinsu,abin da ya fi ɗaure mata kai shine ambaton sunanta da ya ke a maimakon na Marwa.
Da sauri Amma ta buɗe ido ta zuba su cikin na Saffa wacce ke kwance wiƙi-wiƙi da ido,Amma ba tace komi ba ta fito.
Ɗakin sirri ta shiga sai dai allon tsafinta ya ƙi bata amsar komi dangane da canji da aka samu maimakon Marwa ta ga Saffa ce .Ta sauke ajiyar zuci a fili ta furta "ƙila ita mai ƙohin ni ce ban gama tantancewa ba,amman alƙalamin ƙaddara ba zai taɓa canza abin da ba haka yake ba"da wannan ta yi murmushi ta shige toilet saboda sallar asubah tuni ta wuce.
A nutse Prince Khalid ke shirya Yarima fuskarsa fal annuri yayin da ta Yarima take a turɓune baƙi ƙirin duk da kuwa yau ta kasance ranar walimar bikinsa wacce shi ma tashi kawai yayi ya ji hakan a ran
sa kamar sauran al'umma.
"Ina ta ya ka murna, yau za ka yi daren farkon ka da zarar an gama shagali"Prince Khalid ke magana lokacin da ya gama kimtsa Yarima.
Bai amsa ba sai tunanin Marwa da ya adabi rayuwarsa,ya rasa sam nutsuwarsa idonsa ita kawai suke son gani ga wani irin ciwon sonta da ya shige shi daga jiya zuwa yau.
Wasu kuyangi suka shirya Saffa tsaf cikin kayan amare irin na sarakai,sosai ta yi kyau.
Kujerar kusa da Yarima waɗanda suka yi mata rakiya suka yi mata masauki,nan hall ɗin ya hau taɓi ana ihu haɗi da shewa.
Amma na can gefe ta hakimce fuskar nan kicin-kicin babu annuri yayin da Sarki Garba bakinsa ya zama kamar gonar auduga.
Kiɗa aka sa,Yarima ya dubi gefenta ya na mai miƙa mata hannu.Jiki a saɓule Saffa ta ɗora nata a kai shi kuma ya ja su izuwa cikin filin suka taka rawa,nan Mai martaba ya shiga ɓarin kuɗi Amma ta yi wani ƙyaci.
Prince Khalid kuwa ya na lura da ita kasancewar kusa da ita yake,amman ya kasa cewa komi saboda wani dutse da ya zo ya tsaya masa a zuciya wanda ya kasa gane na mine ne?abu guda yake ji shine kamar ya na son wani abu amman wani mai ƙarfi ya dishashe abun ta yadda ya kasa tunawa da muradin zuciyar.
★★★ MADARUMFA
Wani irin zazzaɓi ne ya rufe Fatimah,magani kullum cikin bata kaloli ake amman kamar ana ƙara ma abun ƙarfi.
Cikin ƴan kwanaki ƙalilan duk idonta sun rumza,yayin da suka yi wani ja saboda rashin gamsashen sauƙi.
Ta na kwance sai ta ji kamar an dadaɓata,buɗe ido ta yi a hankali sai ta ga wulgin wani baƙin abu ya wuce da sauri ta tashi haɗi da ƙwala ƙara.Innaro ta haska fitila ko kafin ta tambaye ta lafiya ta faɗa jikinta ta na kuka, addu'a ta fara tofa mata sai tayi luf sai barci.
Washegari
Innaro da kanta ta je gidan su Amadi wajen Malam ita da Fatimah,su na shiga gidan Fatimah ta arta a guje cikin rashin sa'a ta ci karo da Amadi.
"Ƴar fullo har kin zo?dama na san sai kin zo nan saboda ke ma ki na sona"maimakon Fatimah ta ƙwace daga riƙon da yayi mata sai ta sakar masa murmushi tace "Ahamadina dama nan ne gidan ku?"murmushin nasara yayi ya jawota zuwa ciki.
Inna ta dube sa da kyau tace "dama ka san ta ne?"Amadi ya washe baki yace "matata ce wacce nake gani a mafarki,ƴar fullo ta"cike da mamaki Innaro ke kallonsa,malam yace "ka ga Amadi wannan marar lafiya ce da aka kawo min yanzu fah"
Yace "na sani malam ,in shaa Allah ni zan warkar da ita ku bar komi cikin hannuna"
Innaro ta shiga yi masa godiya tunda dama tun kafin ta zo an shaida mata Ɗan har ya fi uban iya aiki.
Tun daga wannan rana Amadi ke baiwa Fatimah magani wanda ba komi ba ne sai sihirin son shi da yake ɗura mata,a sannu jikinta ke yin sauƙi ta na samu barci babu wata matsala sai dai soyayyar Amadi ta cika zuciyarta da ɓargon jikinta.
A kwana a tashi soyayyar Amadi da Fatima ta girma har ta fara hayayyafa,Amadi bai ƙasa da gwiwa ba wajen neman aurenta amman Innaro mahaifiyar Fatimah ta yi tsalle ta dire tace ba ta san wannan ba sam ba za ta aura masa ƴar ta ba.
Tashin hankali maras misaltuwa ya shigi Amadi, Fatimah ma haka dan kusan ma ta fi shi damuwa.
Amadi ne zaune gaban gaɓar ruwa jikinsa babu kaya tumɓur yake haihuwar uwarsa,idonsa a lumshe ya na motsa bakinsa.A sannu a hankali ruwan suka fara tunkuɗowa suna zuwa gunsa har ya zama sun kai shi can tsakiyar gulbin,wani haske ya gewaye shi mai kama da garwashin wuta kafin wata murya ta fara yi masa magana kamar haka ```baƙar akuya mai gemu,jajayen bunsuru biyu sai budurwa kaza wacce ba ta taɓa yin ƙwai ba.Ka yanka su ka zubar da jinin cikin gulbin mawaliya```
Kamar walƙiya sai kuma ruwan suka janye suka koma inda suke,Amadi ya tashi ya ɗauki kayansa da ya maida sannan ya wuce gida.
Washegari gari kuwa Amadi ya bazama cikin kasuwa ya sawo abubuwan da aljan
nunsa suka buƙata,zuwansa gida ke da wuya ya yanke su kaf bayan ya tara ƙwarya jinin ya zuba a ciki.
Duk abin da yake Inna na kallonsa sai dai ita zuwa yanzu al'amarin Amadi tsoro yake bata,Amadi bai taushe hannu ba ya isa gulbin mawaliya ya zuba jinin.Da farko jinin sama ya yi ya takure gu ɗaya kafin daga bisani a fara jansa zuwa ƙasa kamar yadda yaro ke shan daddaɗar madara.
Wani gurnani haɗi da nishi ya taso daga ƙasan ruwan can kuma ya ɗauke,ganin haka Amadi ya nufi gida.
Mutane ya tarar ƙofar gida sun yi cirko-cirko ana leƙen gidansu kafin a juyo duk ana kallon sa.......
[07/09 à 07:40] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR*
LoVe and HoRoR StOrY
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya.
_____________________
7-8
Ko kafin Amadi ya kai ga tambayar lafiya,Innaro wato mahaifiya ga Fatimah ta kuma sakin wani ihun ta na suratai maras kan gado yayin da kuma ta ke tiƙar rawa irin yadda ƴan bori su ke yi.
Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Amadi,da farko ya ji tsoro kar ace Malam ko Inna aka ɗauka matsayin sacrifice kasancewar lokacin da zai bayar da jinin da yayi alƙawari ya gabato.
Cikin gidan ya wuce tare da samun waje ya zauna ya na kallon yadda Innaro ta rasa hankalinta lokaci guda ba tare da ta shirya ba,a idon mutane aljanu ne suke ganin ta na da amman wurin Amadi shi ya san haukacewa ne ta yi.
"Innaro je ki zauna"Amadi ya faɗa cikin bayar da umarni,cak ta tsaya da rawar sai kuma dare-dare irin na sabon kamu.
Innuwa ta samu ta zauna,a zuci Amadi yace 'au !haukan bai gama rufe ki ba tunda har kin san banbancin innuwa da kuma rana'
Inna ta leƙo ta na mai ɓoyewa bayan ƙyauren ɗakinta,ta na tsinkayar Amadi ta ƙwala masa kira ya taso ya na ƙumshe dariya ganin Inna ta ɓoye a ɗaki har da saka sakata tsabar tsoro.
Ya na zuwa tace "dan Allah ka taimaka kace ta tafi gida, wannan masifa da mi ta yi kama mu na zaman zamanmu ka ɗebo mana fitina"
Amadi yace "Ni kuma?"Inna ta harare sa tace "eh kai ɗin ko ka zata ban san aikin ka ne ba?"Amadi ya sosa ƙeya kafin yaje gun inda Innaro ta ke.
Duƙawa yayi ya fara magana "Innaro kin yarda da auren mu ni da Fatimah ko kuwa?"da sauri ta gyaɗa kai shi kuma ya saki murmushi yace "to tashi ki tafi gida"kamar wata doluwa haka ta yunƙura ta tashi tare da fita waje ba ta zame ko ina ba sai gidanta nan ta tarar da Fatimah da Abdu.
Da sauri ya nufota ya na tambayar ta "Innaro lafiya?na zo na tarar Fatimah na kuka,ke kuma ba kya nan yanzu da kika dawo kayan ki duk sun yi dauɗa?"
Innaro ba tace komi ba ta wuce ɗaki,Abdu ya take mata baya.Ko kafin ya sake yin wata magana tace "maganar auren Fatimah a fara shiri,ban so ya haura sati biyu a kaita kowa ya huta"cike da mamaki Abdu ya kalleta yace "haba Innaro matsafin za mu bai wa aure?"Inna ta yi masa daƙuwa kafin tace "gidan uban wa ka ga yayi tsafin?kawai sharrin mahasada ne dan sun ga duk illahirin garin nan babu mai maganin aljanu kamar sa"
Abdu ya yi ajiyar zuciya kafin yace "to Allah kyauta"Innaro ta amsa masa da "amen" ta na mai bin bayansa da harare a zuci ta na cewa 'Ni ai nafi kowa sanin matsafi ne ,ni da ya turo ma ciwon hauka da rana tsaka duk da na ƴan mintina ne amman ai na wahala'
Fatimah wacce ke waje duk ta ji hirar da suka zanta,cike da murna ta cika bokiti da ruwa ta kai ma Innaro banɗaki kafin ta ɗaga labule tace "ki tasho kiyi wanka na kai maki ruwa"kai ta gyaɗa mata alamar toh kafin a zuci tace 'muguwa ai doli ki kai min ruwa tunda kin kwaso mana masifa mu na zaman-zamanmu'Innaro na shiga bayi Fatimah ta arce ba ta zame ko ina ba sai gidansu Amadi.
Da sallama a bakinta sai dai babu kowa sai kukan wani maras lafiya mai cutar Jinnu da aka kawo ma malam,har za ta fito sai ta tsinkayi riga da wando rataye a katangar banɗaki.
Fatimah ta saki murmushi ta nufi ɗakin Amadi domin jiransa,ba ta wani daɗe da zama ba ya shigo.Kanta sunne a ƙasa ba tare da gaisuwa ba tace "Innaro ta amince da aurenmu shine nace bari na zo na faɗa ma"
Amadi yayi murmushi yace "ai na sani,yanzu haka wankan zuwa gidan ku ne na yi amman tunda ga ki kin zo mu je kawai gaɓar ruwa"
Babu wani muso ta miƙe tsaye ta bi bayansa,su na tafe su na hirar soyayya har suka kawo gaɓar ruwa.
Amadi ya ɗauki ƙanƙara ya jefa a ciki ta bada sautin "tsulum"can sai ga kifi ya fito daidai inda babu ruwa ya na motsi,Amadi ya duƙa ya ɗauki ƙaton kifin kafin ya koma gefe ya cire masa wuya.Wuta ya hura ya fara gasa kifin,ita dai Fatimah na gefe ta na kallon siddabarun Amadi kala-kala.
Cike da burgewa ta ƙaraso gun sa,cikin muryata ta Fulani tace "yanzu in nace sai ka mayar da kifin nan ɗanye ya za ka yi?"Amadi wanda ke ƙoƙarin juya kifin dan ya fara gasuwa ya ɗago ya dubeta yace "tsaf zan maidosa ɗanye kuma da ransa"Fatimah ta waro ido tace "da gaske?"ya jinjina mata kai.Ta rufe baki da dukan hannuwanta kafin tace "to mayar na gani"wata formula Amadi ya faɗa nan take kifin da ke kan wuta yayi tsul ya faɗi a ƙasa ya dawo ɗanye har ya na motsi.Fatimah ta waro ido tace "to mayar da shi gasashe"ko ida rufe bakinta ba ta yi ba kifin ya koma yadda ya