Showing 1 words to 3000 words out of 30354 words

Chapter 1 - MASARAUTAR GOBIR Book Complete Writing by Mrs Sadauki .txt

14 Dec 2024

1379

[06/09 à 07:17] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR*



LoVe and HoRoR StOrY


*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)


*Lambar waya:* +22795045822


*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.


*Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya.




_____________________


Ƙirƙirarren labari ne👌🏻




Allah ka jiƙan Sarkin Gobir duk wani mai hannu a kashe shi Allah ka tozarta shi ka toni asirin su.Wannan garkuwa da ya adabi mutane Ya Rahamu ka sa ya zama tarihi a ƙasar Nigeriya da ma duk sauran ƙasashe.


1-2
#TIBIRIN GOBIR




Wani yanki ne da ke jahar Maraɗ jamhuriyar Nijar , al'ummar yankin sun kasance Gobirawa.
TIBIRIN GOBIR ta kasance ƙaramin yanki amman mai ɗauke da ƙatuwar Masarauta wacce ta samu jagorancin wani sarki mai suna *GARBA*.Sarki Garba ya ɗale karagar mulki ne bayan Yayan mahaifiyarsa ya mutu duk da kuwa Marigayin Sarki Salis ya na da Magaji,amman kasancewar Garba ya jima ya na kwaɗayin mulki sannan al'ummar yankin na matuƙar basa girma da tsoronsa haka yasa ya hau karagar mulkin ba tare da kowa ya tuhume sa ba.








Ƴan mata ne laye kowacce sanye da zane baƙi da kuma riga fara,abinci karyawa su ke karɓa wanda dogari Ɗan Tani ke raba masu.
Tunda suka kama layin ta lula duniyar tunani,sam ba ta san layi ya kawo gare ta ba sai jin saukar dorinar ta yi tsakar kai.A mugun furgice ta ƙwala uwar ƙara wacce sai da masarautar ta amsa,wani banza kallo ya watsa mata kafin ya miƙa mata wainar fulawa wacce ta kasance abincin su a kullum.
Hannu na rawa ta karɓa ta bar gun ta na kuka,Prince Khalid wanda a gaban idonsa aka yi komai yayi saurin shan gabanta.
Cak ta tsaya ta na dubansa da idonta da suka yi ja,har ya buɗe baki zai yi mata magana ya ji murya Prince Bilal ya na cewa "ke wuce maza zuwa ɓangaren Bayi kika wani tsaya ki na sunne kai gaban Jakin dawa"
Da azama Marwa ta je wucewa Prince Khalid ya riƙo tsintsiyar hannunta,cikin sanyi murya yace "kiyi haƙuri da ƙaddarar ki,sannan in kin je part ɗin ku ki samu ruwan ɗumi ki gasa idon ki ga shi nan har ya fara kumbura"ya ida maganar ya na shafa gashin idonta,zafin da taji ne ya sa ƙwalla sake zubo mata.Kai ta gyaɗa masa alamun za ta yi yadda yace ɗin kafin ta wuce ta bar su suna ƴar kallon-kallon,Prince Khalid yayi murmurshi yace "Barka da fitowa Yarima Mai jiran gado"taɓe baki yayi a zuci kuma ya na jin haushin yadda Prince Khalid bai hassala da duk cin fuskar da yake yi masa.
Ba tare da ya amsa ba yayi gaba ya na tafiya cikin izza da taƙama,duk inda ya wuce sai kwasar gaisuwa yake daga bayi.
Direct palais ya wuce,a hakimce ya tarar da mahaifinsa yayi zaman sarakai gefe da gefe dogarai ne ke yi masa fifita duk da kuwa ɗakin na da sanyi ac.
Daga ɗan nesa ya ƙare ma mahaifin nasa kallo,sanye yake cikin ɗanyar gizner fara a sama ya ɗora alkyaba kansa kuma yane da rawani wanda bai ɓoye gobarcinsa na shidda da bakwai da kuma yetali biyun kumatunsa .Murmurshi ɗauke da fuskarsa ya ƙarasa ya zube gaban Sarki Garba ya na mai taɓa ƙafafunsa,ɗagosa yayi kafin yayi magana da muryarsa mai kama da ɓaɓarkiyar yace "Allah maka albarka yarona taso dawo nan"ya nuna masa wata kujera da ke gefensa,cike da izza ya tashi ya na mai harar dogaran kamar haɗin baki suka shiga yi masa kirari "Allah ƙara girma Yarima Mai jiran gado"






A ɓangaren Marwa kuwa ta na shiga ta tarar da jikin Saffa ya ƙara tsananta,wainar ta aje ta nufeta da sauri.Murya na rawa ta fara kiran sunanta amman sam ta kasa amsawa,a guje ta nufo waje sai kuma ta ci karo da Prince Khalid wanda ya kasa haƙuri ya biyo bayanta.
Goshinta ta dafe wanda ya bugu da ƙirjinsa,"lafiya?ina za ki haka a guje?"ya jero mata tambayoyin,ɓarkewa tayi da kuka tace "Saffa ce babu lafiya"yadda ta ke kuka majina na yi mata zuba yasa shi dafe kai yace "ya Salam!shine kuma kike kuka ?bari na ɗauko mota a kaita asibiti"ya na gama faɗa ya wuce ba tare da ya jira cewarta ba,babu jimawa sai ga driver daga cikin dribobin masarauta.Da taimakon Marwa ta shiga mota,ya na kaita asibiti babu jimawa aka yi mata ƙarin ruwa.






"Tas,tas,tas"kake ji Sarki Garba ya ɗauke Prince Khalid da mari har uku kafin yace "cikin motar tawa za ka sa a ɗauki wata ƙaskantaciya a kai asibiti?Mi yasa ba'a kira likitan masarauta ya dubata ba?"kai kawai Prince Khalid ya sunne ya na jin zuciyarsa na ciwo.
Sarki Garba ne ya cigaba da cewa "Yarima je ka zartar mata da hukuncin da ya dace da ita,kai kuma biyo ni"kai Prince Khalid ya girgiza ya na kallon Prince Bilal wanda fuskar shi ta cika da annuri tsabar mugunta.
Babu yadda Prince Khalid ya iya haka ya bi bayan Sarki yayin da shi kuma Yarima ya fice dogarai na take masa baya.










Saffa da Marwa su na tsaka da hira wacce rabinta duk yabon Prince Khalid ne,kawai suka ga dogarai tsaye a gaban su.Babu wani jira dogari ya jawo Marwa kamar yadda Yarima yace masu farar za su ɗauko masa,kasancewar ita Saffa baƙa ce shiyasa suka gane ita ce aka basu umarnin ɗaukowa.
Saffa na kuka ta biyo bayan su amman ganin Yarima yasa ta koma ba ta shirya ba,murmushin mugunta yayi kafin yace "ku kaita kurkukun ƙasa ku yi mata horon yunwa"ya na gama faɗa ya bar gun.






Prince Khalid ya fashe da kuka ya na mai faɗawa kan Amma wacce ke zaune ta na jan casbi,ba tace da shi uffan ba har sai da ya ci kuka ya ƙoshi sannan ta fara bubuga bayan shi kamar wani ƙaramin yaro,ajiyar zuciya ya fara saukewa ya na jin wani kutulun baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi.
"Wane sharaɗi kuma ya sake gindiya maka?"ita ce tambayar da Amma tayi masa,saboda sanin cewa Prince Khalid bai kuka sai in har Sarki Garba ya zalunce sa ko ya yi masa iyaka da wani abun.
"Amma..."sai kuma yayi shiru ya haɗiye ƙodagon baƙin ciki ya cigaba da cewa "zan koma sashen Yarima na kasance mai yi masa hidima na tsawon watanni uku"
Da sauri Amma ta cije leɓenta na ƙasa ta na jin wani irin raɗaɗi na ratsa ruhinta,gashin kansa ta fara shafa masa haɗi da tofa masa addu'a cikin ikon Allah barci ya ɗauke sa.




Washegari
Kamar yadda sarki ya zartar da hukunci haka Prince Khalid ya koma sashen Yarima,tun a yau ya fara karantar waye Prince Bilal.
Rai ɓace ya ke ƙara kallon shi yadda ya murƙushe ƴar mitsitsiyar yarinyar da ba ta kai 13year ba,duk da ba sex yake yi da ita ba amman ta jigata .
Babu kunya balle tsoron Allah ya faɗa toilet,ita kuwa da sauri ta fice ta na kuka.Babu jimawa ya fito ƙugunsa ɗaure da towel,ruwan yatsunsa ya yarfa ma Prince Khalid a fuska da sauri ya dawo cikin hayyacinsa.
"Ba'a tunani sashen Yarima yin haka zai jawo tsatsauran hukunci,zo ka zaɓa min kayan da zan saka"cewar Yarima ya wani riƙe ƙugu kamar mace,wani banzar kallo Prince Khalid yayi masa har zai yi magana komi ya tuna sai kuma yayi shiru tare da miƙewa.
Har ya buɗe drawer ya tsinkayo muryar Yarima ya na cewa "je ka wanke hannun ka da sabulu"kasa daurewa yayi yace "ban gane na wanke hannuna ba cuta ka ga gare ni?to na ƙi na wanke ɗin in na fiddo ma kayan kar ka saka"ya ida maganar ya na mai baza ido domin zaɓa masa waɗanda suka fi kyau.






Shiru Yarima yayi ya na tunanin muguntar da zai yi ma Prince Khalid,can yayi ƙyaci kafin ya fara shafa lotion.
"Ka saka waɗannan tabbas za su yi machin da fatar jikin ka"Prince Khalid ya faɗa ya na fiddo wasu kaya kalar zaiba sai ƙyalli su ke.
Ba tare da yace komi ba ya ci gaba da gyara gashin shi,Prince Khalid kuwa haushi ya ji kawai sai ya aje kayan kan bed ya nufi ƙofar fita.
"Zo taimaka min na saka kayan"Muryar Yarima ta daki dodon kunnensa,sai da yayi ɗan jimmm kafin ya juyo ya na masa kallon ƙasa-ƙasa.




Da taimakon Prince Khalid Yarima ya shirya tsaf cikin kayan sarauta,babu ko godiya haka ya fice ya na baza ƙamshi.
Prince Khalid kuwa direct sashen bayi ya nufa,a zaune ya tarar da Saffa ta rabka uban tagumi.Sallama yayi amman shiru hakan ya sa ya ɗan taɓa hannunta figigit ta zabura tare da dawowa hayyacinta,gaishesa ta yi ba tare da ya amsa ba yace "ina take?"sai da ta goge ƙwalla tace "har yanzu ba su dawo da ita ba"Prince Khalid ya cije leɓensa na ƙasa ya na jin wani zafi kafin ya fice ita kuwa ta bi bayansa da kallo ta na jin wani yanayi a tattare da shi wanda ta kasa gane na miye.






Palais ya nufa,a zaune ya tarar da Yarima kan kujerar sarauta da alamu yau shi ya maye gurbin mahaifinsa kamar yadda yake yi wasu lokuta in zai yin Shari'a .
Gefen sa Prince Khalid ya zauna bayan ya amsa gaisuwar da fadawan suka yi masa,a nutse ya ke kallon yadda Yarima ke gudanar da shari'ar wasu ma'aurata da suka kawo ƙarar junan su.




"Na baka zaɓi biyu ka rubuta mata takardar saki ko kuma ka rinƙa turo ta nan ta na yi ma masarauta hidima dan samun abincin da za ta ci"cewar Yarima ya na shafa jan gemunsa wanda ya shafa ma colorant,mijin matar wanda ba zai haura shekaru arba'in a duniya ba ya ɗago kai ya dubi Yarima wanda yin haka kuma ya saɓa ma dokar masarauta tuni Dogari ya zabga masa bulala ya na cewa "yi ƙasa da kan ka matsiyaci,ragon namiji wanda ya kasa ciyar da matarsa ƙaryar idon ka su kalli mai girma Yarima Sarkin gobe"
Murmurshi Yarima yayi da alamu kirarin ya yi masa daɗi,ya miƙe tsaye ya na mai tattare alkyabbarsa sannan yace "ku shiga da ita daga ciki ta fara aikatau"dogarai biyu suka yi ma Karime jagoranci zuwa can cikin Masarauta yayin da Prince Khalid ya take ma Yarima baya ya na yi kiran sunansa amman ya ƙi tsayawa.






Gabansa ya sha kafin ya haɗe girar ƙasa da ta bisa yace "haba Yarima ba girman ka ba ne,ta yaya ka na shugaban gobe amman ace za ka yanke ɗanyen hukunci irin wannan?sannan sabida Allah miye laifin Marwa da za ka hukuntata ta wannan sigar?"
Kallon tsaf Yarima ya yi masa nan ya hango tsantsar son da Prince Khalid ke yiwa Marwa,cike da isa yace "wace amsa kake son na baka?ta farkon ko ta biyun?"
"Ta biyun"Prince Khalid ya bashi amsa cikin dakewa,kallon masheƙan aya ya yi masa kafin yace "ko za ka hukunta ni ne a kan mace?"kai ya girgiza yace "banda wannan ikon domin kuwa da ina da shi da ko kallonta ba zan bari ka yi ba balle har ka hukunta ta"cike da mamakin lafazinsa Yarima ya matso kusa da shi haɗi da ɗora hannun kan kafaɗarsa yace "kai haba?to ina tabbatar maka ba wai iya kallo ba har taɓata sai na yi in ya so ka haɗiye zuciya ka mutu"ya na gama faɗa ya ture Prince Khalid ya wuce ya na jin zuciyarsa na yi masa ƙuna.






Direct sashen da aka kai Marwa ya nufa,umarta masu gadin wurin ya yi da su fiddota haɗi da canza mata waje.
Cikin izzar mulki ya shigo ya na ƙare mata kallo,fara ce kyakkyawa son kowa ta na da masifar kyau mai ɗaukar hankali.
A zuci Yarima yace ‘ƙila saboda kyawunta ya ke son ta' a zahiri kuma takawa yayi kusa da ita yasa hannu zai gyara mata gashin da ya rufe rabin fuskarta,da sauri ta buge masa hannu ta na mai ja da baya ta na hararsa.
Yarima ya waro ido waje yace "iyeee!Ni kike harara da wannan ƙwala-ƙwalan idon kamar kwalshi?"kafin ta samu damar yin magana ya shaƙota tuni ta fara kakarin wahala,da sauri Yarima ya sake ta jin wani azababen zafi a kwanyarsa.


Prince Khalid ya jawo Marwa ya mannata a jikinsa murya a matuƙar ɓace yace "zan iya jure dukkanin launukan azabar da za ka min amman kar ka kuskura ka taɓa wannan domin ita ɗin rayuwata ce zan iya yin komi a kanta"ya na gama faɗar haka ya ja Marwa suka fito.






Sai da suka zo daidai sashen su sannan ya saki hannunta yace "ki shiga ki yi wanka zan kawo maki abinci sai na kai ki gun Amma"ido Marwa ta zuba masa ta na jin wani irin sonsa ya shigeta ba ta yi aune ba,ba ta san lokacin da hawaye suka shiga zubo mata ba.
Bayan hannunsa ya saka ya fara goge mata hawayen haɗi da hura mata iskar bakinsa,sai ta lumshe ido "ina son ki"muryarsa ta daki dodon kunnenta kafin ta yi magana suka ji ƙarar rufe ƙofa "gam"
Da sauri Marwa ta ruga ciki dan kuwa ta ga Saffa lokacin da take tsaye, a bisa tabarma ta tarar da ita ta na goge ƙwalla.




Marwa ta dafata tace "amadadin farin ciki mi zai kai ki zubda ƙwalla?koko ba ki ji daɗin gani na ba?" Saffa ta waske tare da aro jarumta tace "tsabar farin ciki ne yasa ni kuka" "to amman kamar fuskar ki ba ta nuna alamun farin ciki ba"cewar Marwa ta na ƙara kallon Saffa dan tantance gaskiyar lamarin.
Saffa ta haɗiye mugun kishin da take ji game da ƴar uwarta ta miƙe tsaye haɗi da cewa "eh yanayin da na ganku ke da Prince ne ya kawar min da farin cikin,sam hakan da kuka yi bai dace ba kuma ba zan ɓoye maki ba na ji haushi sosai"
Marwa ta sauke ajiyar zuciya tace "yi haƙuri ƴar uwata ni ma ban san ya haka ta faru ba amman in shaa Allah zan kiyaye" jikin Saffa duk sai yayi sanyi hakan yasa ta kwantar da murya tace "ba fa da wata niyya na faɗa ba,kawai dai ina son ki tuna matsayin ki ke baiwa ce shi kuma ɗan sarki ne"
Marwa ta saki murmurshi tace "kuma fah a hakan wai yake sona" duk da Saffa ta ji ta amman sai ta share ta ma shiga aikin gyaran ɗakin su ganin haka yasa Marwa shiga toilet bayan ta ɗauki kayan da za ta sa.






Gabanta ne ya faɗi jin muryarsa daga bisa,ta kafesa da ido ta na jin kamar ta je ta rungume sa tsabar ƙauna.
Prince Khalid ya kawar da kai jin Saffa ta ƙi amsa masa tambayar da yayi sai ma ƙure sa da ido da ta yi,ajiyar zuciya ta sauke tace "My prince !"shaye da mamaki Prince Khalid ya juyo ya na kallonta.
Marwa ta fito daga toilet sanye da wasu kaya daban,sunne kai ta yi ganin Prince Khalid a tsaye hannunsa ɗauke da kwano ga kuma Saffa ta tsare sa da kallo.
Zuciyar Marwa banda dukan uku-uku babu abinda take,a zuciya kuwa addu'a take Allah sa ba wata baƙar magana Saffa ta faɗa masa ba.




"Princesse ga abinci nan na kawo maki,ki tabbatar kin ƙoshi Amma na can na jiran zuwan ki"cewar Prince Khalid ya na sakin murmushi mai sauti haɗi da ƙarasawa inda take.






Jin hucinsa kusa da ita yasa tayi saurin ɗagowa kafin ta waiga da sauri ta kalli Saffa,uwar hararar da ta jefo mata yasa tayi saurin sunne kai idonta suna masu cika da hawaye.


"Ɗas !"hawayenta suka ɗiga a babban farcen ƙafarsa,kamar ɗigar dalma haka ya ji su ya rumtse ido da ƙarfi yayinda zuciyar
sa ta shiga girgiza jin shashekar kukan ta.
Bai san ya aka yi ba ko kuma abin da ya ja ra'ayinsa da yin haka,kawai samun kansa ya yi da kama hannunta suka fice suka bar Saffa cikin ƙunci.






Part ɗin Amma suka shigo,sanyin AC da na turaren wuta suka bugar mata hanci a doli ta ji wata irin nutsuwa ta saukar mata.
Amma wacce ke zaune ta na jan casbin da ya zame mata jiki,ta miƙe murmurshi kan fuskarta.Kafaɗun Marwa ta dafa lokaci guda suka ji wani girrr kamar lantarki amman hakan bai sa Amma janye hannuwanta daga gare ta ba.
Marwa ta ɗago kai ta kalli Amma,sai kawai tayi luuu za ta faɗi da sauri Prince Khalid ya tareta ta faɗa kan ƙirjinsa....
[06/09 à 08:18] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MASARAUTAR GOBIR*



LoVe and HoRoR StOrY


*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)


*Lambar waya:* +22795045822


*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.


*Sadaukar wa:* Ga duk Gobirawan duniya.




_____________________


3-4








Wata irin zufa ce ke tsatsafowa daga goshin Marwa,a zahiri za ka ɗauka barci take amman a baɗini farke take mai haɗi da fitar hayyaci dan ba komi take fahimta ba.
Prince Khalid ya goge mata zufa a karo na ba adadi,kafin ya dubi mahaifiyar ta sa yace "Amma kin ga fah kamar idonta sun juye babu baƙi sai fari" cikin son kwantar masa da hankali Amma tace "barci ne take,dayawan mutane za ka same su a ido buɗe kamar ita dai a yanzu"
Prince Khalid ya sauke gwabron numfashi ya na jin mamakin faɗuwar Marwa har yanzu bai fita daga zuciyarsa ba.






```Gefen fuskarta ya shafa ya na wangale mata bakinsa mai ɗauke da haure ƙwaya ɗaya tal,halshensa ya ziro mai kama da maciji ya saka sa kunnenta ya na zuba mata yawunsa,ido ta rumtse jin wata irin azaba na ɗigar mata a kunne ya na shigewa cikin kwanyar ta.Ihu ta fara yi amman alamu sun nuna sam babu mai jin ta dan kuwa Prince Khalid da ke tsaye kanta bai nuna alamar ya fahimci halin da ta ke ba balle kuma wasu jama'a da ke waje.Tsawon lokaci kafin ya zare halshensa daga cikin kunnenta wanda kuma ya yi daidai da ɓacewar hallitar,atishawa ta yi kafin ta miƙe zaune.```






"Kin tashi?"ita ce tambayar da Prince Khalid ya yi mata,kai kawai ta gyaɗa ta na jin wuyanta ya ƙage ga wani irin sarawa da ɗaya-wajen kanta ke yi mata.
Amma ta yi murmurshi tace "Barka da zuwa Princesse" da sauri Marwa ta dafe kai jin muryar ta ruɓayan gida biyu inda ta ji wata tace ```"ki fita daga harakar Prince Khalid"``` kai ta ɗago ta dubi Amma wacce a zahiri murmurshi ne kan fuskarta amman a wajen Marwa wata fuska ta ke gani kamar dodanniya.
Da sauri ta sunne kai zuciyarta na halbawa,Prince Khalid ne yace "Amma ina ga surukar nan ta ki har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login