Showing 30001 words to 30354 words out of 30354 words
Chapter 11 - MASARAUTAR GOBIR Book Complete Writing by Mrs Sadauki .txt
adon wato gashin kaina ya koma mai yawa.Shafar shi na soma yi ina jin tsantsar farin ciki tare da tambayar kaina ‘ shin gaske mafarki ne na yi ko kuwa rayuwar zahiri ce na je can ɗin a gaske?’ banda amsa,kawai sai na je na ɓoye Kambu sarautar cikin kayana tuni kuma haskensa ya ɗauke yayin da kuma na lantarki ya dawo.
Gashina na harɗe wuri guda da abun ɗaurewar da ni kaina ban san inda na same shi ba,sai kuma na laulaye gashin yayi tudu kamar na sa a cuci maza sannan na ɗaura kallabi.
Fita na yi na je na yi fitsari tare da wanke jiki na dawo na kwanta,sai dai sam na kasa komawa bacci har rana ta fito wantsar na fita na yi shara na wanke kwanuka a ƙarshe kuma na yi wanka na zo na canza kaya .
Sai na tsurawa Kambun ido ina kallo ina murmushi tuna wai mahaifina ya bani shi,
“ Ke lafiyar ki?” na ji muryar anty Sailuba.Da sauri na rufe kayan na ce “ babu komai ina kwana anty?”
“Lafiya lau,ungo ga makullin shago ki je ki share shi ki goge komai sannan a cika manyan bokitan ruwa yadda ba mu yi aiki ba jiya ai na san yau aiki sai mun ture wa buzu naɗi wasu ma har sun fara kirana ”
Makullin na karɓa,har zan fita ta ce “zo ki karɓi kuɗin da za ki ci abincin kari,don mayun jiya duka suka cinye komai mtswww” ta ja tsuki.
Na dube ta da kyau na ce “kenan kin san Mayu ne su?”
Yadda ta tsure ni da ido yasa na yi saurin canza tambayar “ina nufin kenan Mayu ne?”
“Hum! Ungo dai ban iya surutun ki da kika iya ba” kuɗin na karɓa na fice,maimakon na je shagon a'a sai na wuce gidan anty Hinda don ina son ganin yadda suka kwana tun a hanya nake tuntsira dariya har na isa....
Littafin kuɗi ne Hajiya domin samunsa tun daga farkonsa har zuwa ƙarshensa ki yi payment ɗin 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 Ni kuma sai na saka ki paid group inda nake posting.