Showing 12001 words to 15000 words out of 30354 words

Chapter 5 - MASARAUTAR GOBIR Book Complete Writing by Mrs Sadauki .txt

14 Dec 2024

1377

baro asibiti,Amadi ya dawo gida ya taimaka ma Fatimah ta gyara jikinta sannan ya canza zanen gadon.
Ya rungume Fatimah a jikinsa ko zai ji sassauci,ita kuwa ta na son tambayar shi lafiya don kuwa duk ta ji koke-koken Inna sai dai yanayinsa da kuma rashin jin ƙwarin jikinta yasa ta share zancen.


Washegari duk garin Madarumfa ya ɗauka malam ya rasu,sosai Fatimah ta yi kuka musamman da ta ji an fara yada mata magana ana cewa "Amadi ya auro mai farar ƙafa,yo wa ya sani ma ko mayya ce".
Tunda aka yi rasuwar yanzu tsawon kwana uku kenan in Fatimah ta gaishe da Inna ba ta amsawa,wannan abu na damunta duk da a ɓangaren Amadi bai nuna mata canji ba sai ma ƙara nuna mata ƙauna da yake.






"Ina kwana Innarmu ya kwanan kewa?"Fatimah ta faɗa ta na mai zama kan tabarmar da Inna ke zaune a kai.Da sauri Inna ta tashi ta na cewa "tambayar mi za ki yi min bayan kin lashe kurwa mijina?Ko kuwa ni ma zowa kika yi ki lashe ni ?"Fatimah ta fashe da kuka ta na cewa "haba Inna ke ma yadda mutanen gari suka laƙa min sharri..."ko kafin ta ida Inna ta shige ɗaki ta barta nan zaune.




Jiki babu ƙwari Fatimah ta miƙe,ta saka takalmi ta nufi ƙofar fita suka yi kiciɓus da Amadi "ina za ki je?"ya tambaye ta ya na kallonta,kai tsaye tace "gidanmu, Amadi na gaji da zaman ƙunci yau kimanin sati biyu da rasuwar Baba malam amman har yanzu Inna ta ƙi fahimta ta da ba ni ce silar mutuwar sa ba,mutanen gari in sun ce yanzu ita Inna ya kamata yayi ita ma ta faɗa?"duk tana kuka ta ke yi masa wannan jawabin.
Amadi ya kama hannunta ya ja ta zuwa ɗakin Inna ,da sallama ya shiga kafin yace "Inna wannan matata ce,in har ke baki yi shedar ta ba ta yaya sauran al'umma za su yi? Sanin kan ki ne Fatimah ba wani sona ta ke ba amman nayi shige da fice har na same ta.Inna duk ɗan Adam ba zai wuce lokacinsa ba,mu ma in lokacin mu yayi doli mu tafi.Ki sa a ran ki malam ya mutu ne saboda lokacinsa da yayi sannan dan Allah ki zauna da Fatimah lafiya na roƙe ki,ita ce farin cikina,sirrina in babu ita rayuwata ragaga ce"






Tunda ya fara maganar Inna ke kuka ba tace komi ba,Amadi ya ci gaba da cewa "haba Uwata!kar fah ki manta a kullum ke ce ke faɗa min قُل لَّن يُصِيبَنَآ إِلَّا مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَنَا هُوَ مَوۡلَىٰنَاۚ babu abinda zai samu bawa baya ga abinda ga Ubangijinsa ya rubuta zai same sa,sannan وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ gare shi masu Imani ya kamata su mayar da yardarsu kenan yanzu ki na nufin ba ki yarda da Ayar ba komi?"cikin kuka Inna tace "na yarda Amadi Allah jiƙansa da rahama,Ƴata Fatimah ki yi haƙuri ruɗin sheɗan ne shiyasa sam na kasa fahimta"Fatimah ta faɗa jikin Inna ta na kuka.






Tun daga wannan rana zama mai farin ciki haɗi da zaman lafiya ya wanzu a gidansu Amadi,duk da wasu lokutan Inna ta kan ɗaure ma Fatimah fuska saboda masu zuga da kan zugata da cewa Fatimah dai ce ta kashe malam ana su tunani duk bai tashi mutuwa ba sai da Fatimah ta shigo gidan a matsayin mata?
Ita kuwa Fatimah da zarar ta ga Inna cikin wannan yanayin sai ta bar mata wajen gaba ɗaya wani sa'in ma gidan su take tafiyarta.








A kwana a tashi asarar mai rai,yau auren su Amadi ya cika shekara guda cur amman shiru kake ji Fatima ko tsallaken wata ba ta taɓa yi ba balle a sa ran ciki.
Wannan batu shi ya dagula lissafin Amadi,tun ya na haƙuri har ya kasa ya ƙara aure inda ya auro wata mata mai suna Hassia.
A budurwa ya aureta, duka-duka ba za ta wuce sa'ar Fatimah ba.Tsohon ɗakin malam ta tare,watan farko Hassia ta fara amai isar su asibiti aka tabbatar da ta na da shigar ciki.Murna gun Amadi ai ba a faɗa,uwa uba Inna wacce duk duniya ba ta da maƙiyiya kamar Fatimah.
Tunda Hassia ta samu cikin nan kullum cikin gori take yi ma Fatimah,ita kuwa baiwar Allah sai dai ta yi kuka ta rarrashi kanta sauƙin abun ma dai dan Amadi na haukan sonta har yanzu.
A wani yammacin juma'a Hassia ta fara naƙuda,Inna ta kaita asibiti babu jimawa Allah ya sauketa lafiya ta haifo ɗanta namiji.Amadi yayi masa huɗuba da sunan Yakubu wato sunan Marigayin malam,har washegari Fatimah ba ta san an yi haihuwar ba saboda ciwon mara da ta tashi.
Kwaramniyan ƴan Barka yasa ta farga da haihuwar,da jan ƙafafu ta isa banɗaki dan watsa ruwa amman kafin ta kai ga shiga jiri ya kwasheta ta faɗi.Amadi wanda tunda aka sallamo su daga asibiti bai fita ba ya yo kanta,da taimakonsa ta miƙe ta na cewa "jiri nake gani ka riƙe ni"Amadi ya ƙwala ma wata yarinya kira yace "je ki taro min taxi"da to ta amsa kafin ta fita,zuwa can ta dawo ta shaida ga mai taxi nan ƙofar gida.






Tambayoyi likita ya fara yi mata kafin a sa mata ledar ruwa,a kwance ta ke Amadi na gefenta fuskar nan fal farin ciki sakamakon albishir ɗin da likita yayi masa Fatimah na ɗauke da ciki.
Lokacin da ta farka Amadi ya shaida mata har da kuka tsabar murna,Innaro wacce ke gefe ma murnar take ita ma za ta ga jikanta.
Amadi ya koma gida ya bar Innaro tayi jinyar ƴarta saboda likita yace sai ta yi traitement na 6days kafin a sallame su duba da yadda jininta ya hau saboda damuwa.


Bayan kwana shidda aka sallamo su,a cike suka tarar da gidan da ƴan biki.
Innaro ta ɗauki robar da kayansu suke ciki yayinda Fatimah ta shige gaba,ta buɗe ɗakinta wanda Amadi ya share sa tsaf ya saka turare.
"Fatimah ki kula da shan magani banda saka damuwa a rai,ki kula da kyau ni zan wuce gida"Innaro ta faɗa kafin tayi ma Fatimah sallama.




Da rana bayan Fatimah ta tashi daga barcin da ya zame mata jiki tayi wanka ta saka sabbin kaya,kuɗi ta ɗauka kafin ta fita zuwa ɗakin Hassia.
Da sallama ta shiga dagin Hassia ne suka amsa ita baya da cije fuska babu abinda ta yi saboda haushin Fatimah da ya ƙaru a zuciyarta jin tana da ciki.
"Ashe Allah ya sauke ki lafiya? To Allah raya kan sunnah ga shi a saya ma baby kwalli "ta miƙa kuɗi yayar Hassia ta karɓa ta yi godiya.
Fatimah ta yi tsaye tana kallon Hassia na shayar da kyakkyawan yaronta,a zuci tace 'Allah sa ni ma yarona yayi kyau kamar wannan,ji yadda yake da kyau kamar aljani'
Jin sallamar Lauriya ya saka Fatimah fitowa suka taɓa kafin su tafi ɓangaren ta,su na tsaka da hira suka jiyo kururuwa Hassia "wayyo Allah na shiga uku na lalace mayya ta lashe min yaro sai bulle-bulle yake wayyo jama'a ku taimaka min"zuciyar Fatimah ce ta fara dakan uku-uku tuni suka fito ita da Lauriya,jariri kuwa sai canyara kuka yake kamar ransa zai fita kafin wani lokaci duk ya wahala jikinsa yayi jajur duk ko ina burdi ne...








★★★ TIBIRIN GOBIR 👑






Duk wani tsarin masarauta Yarima wanda ya kansace sarki a yanzu ya canza su ya ɗora jadawalin rashin mutumcinsa.Kwana uku kacal da hawansa kan karagar mulki al'ummar yankin Tibiri suka gane ashe gata ne Sarki Garba yayi masu,saboda yadda Yarima ya tara mutanen gari ya ɗora dokoki wanda ko a mulkin mallaka sai haka.
Dogari Ɗan Tani wanda ya kasance mai kula da abincin bayi gaba ɗaya na masarauta ba ƙaramin haushi ya ji ba,dama can Sarki Garba ya sakar masa ragamar store tsabar ƙeta ya sa shi rinƙa yiwa bayi wainar fulawa a kullum sai ya na yin ƙasa da faɗi wajen kwashe kayan masarufi.To yanzu kam Sarki Bilal ya ɗora sabon jadawali inda ya zartar da hukunci bayi za'a rinƙa yi masu tuwon jar masara a duk daren Allah,da rana a jiƙa masu kwakwi a barbaɗa ɗan gishi.






Waziri wanda ya kasance aboki ga tsohon Sarki,ya shigo palais ya na mai rusunawa ya kwashi gaisuwa ya na mai cewa "Allah ja da zamanin mai martaba,al'ummar ka na son ganin ka su na can a waje su na ƙus-ƙus akan hukuncin da ka yanke na duk kowane magidanci zai biya kuɗin lanwo ko wacce safiya,su na son a sassauta a mayar da shi ko da duk bayan sati ne "
Sarki Bilal ya miƙe cike da ƙasaita dogarai na take masa baya,waje ya fito inda mutane suka yi cincirindo.
Duk tashi suka yi domin girmamawa ga shugaba,ya gyara tsayuwa haɗi da gyaran murya yace "Sultan ke magana,na ji koken ku sannan na karɓa sai dai ku sani da sharaɗi guda duk wani mutum da ke nan yanki zai bayar da yaro guda domin yin hidima ga masarauta.Abu na gaba da zan shaida maku shine ban yarda wani ko wata ya ɗaga kansa sama ba balle har na ji wani sabon ƙorafi,dogarai ku bi gida-gida ku fito min da yaro ɗaya-ɗaya ku tabbatar kun shiga gidan kowa da ke wannan yankin"ya na gama faɗa ya juya izuwa ciki,jama'ar gari kuwa kamar ruwa ya ci su haka duk suka fita jiki duk a mace yayin da dogarai suka fara aikin da Sultan ya saka su.








A ɓangaren Sarki kuwa banda rikicewa babu abinda ciwonsa ke yi,sai allurai ake yi masa amman ga banza.
Ranar da Prince Khalid ya dawo normal ne ya koma sashen da aka kai Sarki,kallon tsaf yayi masa kafin daga bisani yace "shi yasa ake so a ko wane lokaci mutum ya kasance na ƙwarai,miye ribar ka a yanzu ? Ka raini yaron da ba naka ba ka nuna masa ƙauna ka susuta shi amman yanzu daga ƙarshe ga yadda ya mayar da kai nan"ya tsagaita ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ci gaba "ba zan ce ban sonka ba,saboda kai mahaifina ne sai dai ka sani ka zalunce ni tunda har ka raba ni da abar ƙaunata."
Idon sarki suka ciko taf da ruwa ya na son yin magana sai dai bai iyawa,aka turo ƙofa aka shigo wani dogari ne riƙe da ƙaton gora mai cike da ruwan zam-zam.
Prince Khalid ya karɓa sannan ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya shimfiɗa tapis ya zuba ruwan zam-zam ɗin a kofi ya ɗago kofin kusa da bakinsa.




Da Bismillah ya fara sannan ya karanta wannan surorin:
Alfatiha⁷
Falaq³
An Nas³
Al kafirun ³
Ayattul ƙursiyu¹
Amanar Rasuluh²


Ya na gamawa ya je ya buɗe bakin Sarki ya fara ɗiga masa ruwan,har zai aje sauran ruwan kawai sai kuma ya shiga yayafa masa su a jiki.Nan take jikin Sarki ya fara rawa ya na mai jin sassaucin azabar da yake ji,ganin haka ya sa Prince Khalid ɗaura niyyar zuwa maraice zai yi masa ruwan wanka.Waje ya fita ya bai wa wani bawa ƙaton buhu yace ya figo masa ganyen magarya.


Bayan an kawo masa ne ya ta saɓa sa a turmi kafin ya samu bokitin ruwa ya fara karanto surorin da ke karye sihiri kamar haka:




Suratul Fatiha¹¹
Falaq¹¹,Nas¹¹,Kafirun ¹¹
Ayattul ƙursiyu¹¹
Shafin suratul Safat na farko
Suratul Yaseen¹


*Ayoyi daga cikin wasu surori*


Alhqaf Aya ta 31
Al isra Aya ta 82
An nisa Aya ta 54
Ashu'ara Aya ta 80
At tauba Aya ta 14
Fusilat 44
Al hashir Aya ta 21
Al Mulk Aya ta 3
Al Qalam Aya ta 51
Al'araf Aya ta 117 zuwa 199
At tauba Aya ta 26 da kuma ta 40
Al fatahi Aya ta 26, 18,da kuma ta 4


Bayan ya gama karanta wannan ayoyi sai kuma ya ƙara da:


_As'alullahu azhim,rabbal arshil azhim an yashfiyak⁷
_A'uzhu bikalmatillahi tammati min kulli shaitanin wa hammat wa min kulli ainin lammah ³
_Allahumma Rabban nas,adbihil ba'asa ishfi anta ash'shfi laa shifa'ia illa shifa'uka,shifa'an laa yugadiru saqama³
_Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa aleyhi tawali'u wa huwa Rabbul arshil azhim ⁷
_Bisimillahi³
_A'uzhu bi'izzatillahi wa ƙudiratihi min sharri ma'ajidu wa'uhazhir




Tsawon lokaci Prince Khalid ya ɗauka ya karance duk wannan ayoyin kafin ya zuba saura a cikin flask na ruwa,sauran kuma wanka ya yiwa sarki a nan inda ya ke kwance kamar yadda aka haramta yin wanka da ruwan da aka yi ma ruƙiya a banɗaki.
Wani irin siraci ke fita daga jikin Sarki kamar tukunyar da aka ɗora kan ruwa,tuni jikinsa ya fara saɓewa daga kumburin da yayi.
"Alhamdullah , Sarki ka ga ikon Allah ko? To ina so daga yau ka cire hannun ka da dukan wasu saɓon Allah ka tuba ka koma garesa shi ɗin mai yafiya ne kuma mai jinƙai"murmushi kan fuskar sarki ya jinjina kai.






Tun daga wannan lokaci Prince Khalid ke kula da mahaifinsa,sosai kuma suke ganin sauƙi dan yanzu sarki ya na iya tashi da kansa haka ya na yin magana saɓanin da.






*BAYAN WANI DOGON ZANGO*


★★★ DUNIYAR IFIRITU




Marwa ce duƙushe cikin jini Maa na gefe ta na ƙoƙarin yanke ma jinjirin cibi,shi kuwa sai canyara kuka yake.
Cikin zane ta naɗe yaron kafin ta fara kimtsa Marwa,ta na gamawa ta miƙa mata yaron wanda kamar an tsaka kara shi da mahaifinsa.
Da sauri ta kawar da kai zuciyarta na halbawa,Maa tace "ki shayar da shi kafin isowar Maheer"idonta na ɗigar ruwa ta shayar da shi.




Guguwa ta taso kamar daga bisa,can sai ga shi ya bayyana cikin fararen kaya "Assalamu alaikum, Marhaban bika Ɗana Mahadee!!!"....








A nan na kawo ƙarshen free page wato na kyauta,yanzu duk mai son ci gaba za ta tura 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 .Labarin fa yanzu ne zai fara sai yanzu aka haifi jarumin littafin fatan kun fahimci haka? Wannan duk shimfiɗa ce💃🏻💃🏻💃🏻ƴan Nijar carte moov za ku turo ta 500f.




NB: Kawai ki tura kuɗin ki ga detail can a sama ki turo min evidence sai na saka ki group,wacce ta san ba ta shirya ba ta yi wa girman Allah kar ta min magana
[09/09 à 10:39] MRS SADAUKI 👑M~SHURAIM🤍: *MAITAR IDO*👁️
👁️👁️👁️👁️👁️
HoRrOR story☠️


Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI💫✍️


*FCWA ☀️*




1-2


“ Gulbi ya zo” Laila ta faɗa ta na mai ajiye hullar gashin dokin da na bata ta sharce mini.


“Za mu je mu yi wanka da zarar mun gama” Farida ta ɗora.


“Ni dai ba zan je ba,ina da aiki sosai” na faɗa ina mai ci gaba da saƙa sabuwar hullar gashin doki.


Duk suka matso kusa da ni kowacce da nata kalaman har suka ci galaba kaina na yarda ba tare da na san abin da ke jirana can gulbin ba.
Na ce “ amma za ku taya ni sayar da abinci ”
“Mun yarda” suka haɗa baki wurin faɗa .


Sunana Sarah ,Laila da Farida ƙawayena dukkanmu ba za mu wuce shekara sha uku-uku ba.Muna da ra'ayi kusan duk ɗaya,ciki kuwa har son wasar ruwa ko ruwan sama ake yi sai mun san yadda muka yi muka fito muka yi wanka.
Ƴar talakawa ce ni,boyi-boyi shi ne aikina ina taya wata mai gidan gyaran gashi aiki da kuma mai sayar da abinci aiki duk don na samu abin da za mu rufawa kanmu asiri ni da Kakata.


Fitowa muka yi mu duka ukun na rufe salon ɗin kafin mu kama hanyar da za ta kai mu wajen magudanar ruwa.Tun a hanya muke ta zancen har muka iso,duk tsaye muka yi muna kallon yadda ruwan ke ta zubowa daga wani dogon tsauni su na cika makeken wurin da muke kira Gulbi .


Tuni sun shige sun fara wanka,ƙafa ta ɗaya na saka da niyyar isa wurin su sai na ji kamar an riƙe ni.
“Sarah ki shigo mana” shine abin da suke faɗa ,na amsa da “ tooo” ina mai ɗora ɗayar ƙafar tawa ta dama a can gaba.
Dodon kunnena na ji ya tsira kamar wacce aka cakawa allura,kafin kuma na fara jin wani irin zafi daidai saitin zuciyata yayin da wani abu ke min yawo a maƙogoro kamar wacce ta ci yaji.




Na ɗaga idona na kalli sararin samaniya sai na ga hadari baƙi ƙirin ya na haɗuwa ,ya na yo ƙasa kamar zai rubto cikin ruwan gulbin.Wani tsoro ne ya ziyarce ni nan take, kwacaaaa na faɗi rub da ciki cikin ruwan “Saraaaaah!” na ji muryar ƙawayena wacce ita ce ta ƙarshe daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai tashi na yi na gan ni kwance kan yamutsatsar katifar mu.


A hankali na tashi zaune ina mai dafe gaban goshina da ke yi min mugun ciwo.
“Kin tashi?” Kaka ta tambaye ni ta na tsure ni da ido.
Na ce “ eh! Amma....” sai kuma na yi shiru.




“Ki kwanta ki sake hutawa na san kin galabaita ” ta faɗa tare da miƙo min wata ƴar madaidaiciyar ƙwarya,na karɓa da niyyar shan ruwan da nake kyautata zaton magani ne sai kuma na tsaya cak ina kallon can ƙasan ƙwaryar da nake hango wasu halittu masu motsin rai.


“Kaka mine ne nan kika bani?” na yi tambayar ina mai maido dubana gare ta.
“Ruwan floris ne” ta bani amsa, floris wata itaciya ce mai warkar da dukkan wata cuta musamman wacce ta shafi mugaye,na sha jin masana na faɗar ta don ba zan manta har a cikin wani littafin Mrs Sadauki na RUHIN ALJAN na ta taɓa jin an yi amfani da ita.Sai dai sam wannan launin ruwan ba su yi kama da waɗanda aka yi siffanta na floris ɗin ba,duk da hakan dai bai hana ni na sha su ba.
Ƙwaryar na ajiye ko minti biyar ba a yi ba na soma jin goshina na yin wata ƙara kamar irin ana son ɓara shi gida biyu.Dunƙulallar kwanyata ce ta fara motsi a cikin ƙoƙon kaina,yayin da hasken abin da ya faru da ni a cikin ruwan ya dawo min.
Kifaye ne irin masu rabi mutum suka tarbe ni a ƙarƙashin ruwan ,tamkar wata sarauniya haka aka dinga yi mini wanka da wasu ruwa sannan aka shafa min wani abu cikin tafin ƙafa ,mundun wuyana wani matashin saurayi mai hatsabin kyawu ya cire ya saka a wuyansa kafin ya cillo ni gaɓar ruwa.Na ja wani dogon numfashi bayan na gama samun flashback ɗin da aka gama yi min,wuyana na shafa tabbas babu sarƙar munduwar (irin sarƙar nan da ake yi da kuɗi mai tambarin kan mutum....)




Kaka ta matso kusa da ni ta na cewa “Sarah faɗa mini mi kika gani?” shiru na yi na ƙo bata amsa sai ma kwanciyata da na koma na juya mata baya.


Ta yi wani “hum!” kafin ta fice,ganin haka yasa ni kuma na tashi da sauri na jawo wani tsohon akwatin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login