Showing 3001 words to 6000 words out of 30354 words
Chapter 2 - MASARAUTAR GOBIR Book Complete Writing by Mrs Sadauki .txt
yanzu ba ta warware daga sumen da ta yi ba"
'Suma?'Marwa ta maimaita kalmar cikin ranta,cinkayo muryar Amma tayi ta na cewa "ƙila turaren nan da na saka ne ya juya mata kai,ka san kwanaki ma haka ya sumar da jakadiya" Prince Khalid ya kai dubansa ga Marwa wacce ta sunne kai sannan yace "ya kamata ki bar kunna sa kar ya zo ya hana surukar shigowa nan sashen"
Da sauri Amma tace "wane shigowa kuma?ai ta shigo kenan daga yau nan sashen za ta ci gaba da zama"cike da firgici Marwa ta ɗago ta kalli Amma,wata uwar harara ta aika mata babu shiri ta mayar da kanta yadda yake wato ƙasa.
Ɓangaren Yarima kuwa ba ƙaramin jin zafin bugun da Prince Khalid ya yi masa,dauriya ya aro ya fice.
Direct sashensa ya nufa,zarya ya fara yi ya na tunanin mafita dan sam bai so Sarki ya san da maganar.
Wani murmurshin mugunta yayi bayan ya hango hanyar ɓullewa ta har abada wacce zai yanke farin cikin Prince Khalid ga baki ɗaya.
Toilet ya shiga yayi wanka,kayan shan iska ya saka bayan ya fito kafin ya ɗauki waya ya kira wata lamba "a kawo min ita"kawai ya faɗa bayan an ɗaga kiran.
Babu jimawa jakadiya ta shigo yayin da a bayanta matar mutumen nan ce wanda Yarima ya yi masu Shari'a.
"Ranka shi daɗe ga ta nan na kawo,an yi komi kamar yadda ka buƙata fatan komi yayi yadda kake so?"Jakadiya ta tambaya ta na wani yin ƙasa da kai kamar tantabarar da hauka ya kama.
Tun daga ƙafafunta wanda suka sha lallen Hausa ya fara bi da ido har izuwa fuskarta wacce aka yi ma simple kwalliya,kai ya fara gyaɗawa kamar wani ƙadangare kafin ya yiwa Jakadiya alamu da ido ta fita.
Fitar ta ke da wuya Yarima ya miƙa ma Maryam hannu alamun ta tawo,jikinta ne ya fara rawa duk da cewa tun kafin su shigo an yi mata bayanin komi.
Wani irin fizgota yayi ta faɗa jikinsa ya lumshe ido ya na shaƙar ƙamshin turarenta wanda ya san aikin Jakadiya ne,shafar ta ya fara yi gami da aika mata saƙonni a ɓangarori mafi daraja a jikin mace.
★★★ MADARUMFA
Kwalokwalo(jirgin ruwa) ya gyara ma zama kafin mutane su fara shiga shi kuwa gefe ya koma ya na kallon wata bafulatana ta kasa shiga tsabar tsoro.
Ya gyara tsayuwa ya na ƙara kallon ikon Allah yadda bafulatanar nan ta ke shiga jirgi sai ta zauna sai kuma ta fito ta na zarar ido, murmurshi yayi a zuci yace "ashe dai dagaske ne Fulani sokwaye ne,yanzu miye a cikin jirgin ruwa da har ta ke tsoro?"
Maganar waɗanda suke tare da ita ne ta katse zancen zucin Amadi, "Fatimah ki shigo ki zauna kin ga saura mutum biyu kawai jirgin ya cika kuma in wasu suka zo shikenan za mu bar ki a nan"Lauriya ke faɗa yayin da sauran suke kallon wacce aka kira da Fatimah suna masu haɗin baki wajen cewa "ki shigo dan Allah"
Fatima ta maƙe kafaɗa tace "aradun Allah ba zan higa ba,wannan ai mun yi mashi yawa sai ya nutse da mu cikin ruwan"
Dariya Amadi ya ɓarke da ita yace "halan daga ƙauye kike?" Fatimah ta waigo bayanta ta na mai dubansa wanda shi ɗin ma ita ya ke kallo.
"Daga ƙarƙashin ƙasa na ke"ta bashi amsa cikin jin haushi kafin ta daure ta shiga jirgin,duk da maganar ta yi ma Amadi zafi hakan bai sa ya fusata ba sai ma cewa yayi "to madallah zan tabbatar"ya na gama faɗa shi ma ya shiga jirgin ya na mai tsoma muciyar da suke tuƙi da ita cikin ruwa .
A sannu suka fara tafiya cikin tabkeken tabkin,ba ka jin komi sai kukan tsuntsaye da ƙwari,iska mai haɗe da sanyi da ƙamshin ruwa sai kaɗawa ta ke.
Sun zo daidai tsakiya Fatima ta ji tamkar ana yafito ta,cike da tsoro ta buɗe idonta wanda ta rufe tun farkon soma tafiyar su ai kuwa kamar walƙiya haka ta ga wani abu "wuuul!"ta cikin ruwa babu zato ba tsammani sai jinta tayi ta faɗa canɓal cikin ruwan.
Ihu su Lauriya suka fara yayin da Amadi ke gumtse dariyarsa,can kuma ya tsayar da jirgin haɗi da ce ma wani namiji "ka ida fitar da ku,ni zan shiga na cirota"ba tare da wani jinkiri ba ya faɗa "tsumbul".
Ko da suka isa gaɓar ruwa duk cirko-cirko suka yi su na kuka ganin har yanzu babu labarin Amadi balle Fatimah.
Tsawon lokaci kafin su tsinkayi Amadi saɓe da Fatimah a hannu kamar wata jaririya,a ƙasa ya kwantar da ita dogon gashinta wanda ya warware ya baje a ƙasa yayin da kayan Fulanin ta suka jiƙe sharkaf.
Cikinta ya shiga dannawa ruwa na ta ɓulbulowa daga hancinta,bakinsa ya sa a nata bayan ya matse hancinta ya hura iska.
Da sauri ya janye jin ruwan da ta sha sun shiga bakin sa,tari ta soma sosai ta lumsar ido kamar wacce ta yi maye gabanin ta fara kallon mutanen gun da suka taru su na yi mata sannu.
"Sannu Fatimah,ya kike jin kan ki yanzu?"Lauriya ta tambaya cike da tausayi,kawar da kai ta yi gefe ta na mai tashi tsaye ta na son tuna abin da ya faru da ita lokacin da ta faɗa cikin ruwan.
Amadi yayi murmurshi yace "ƴar fullo ko zaki koma inda kika baro ne"da sauri ta kalle sa nan take jikinta ya hau tsuma a guje ta arta da gudu ƴan uwanta suka shiga kiranta Amadi kuwa sai dariyar ƙeta ya ke kwasa.
Fatimah ba ta zarce ko ina ba sai gidan Abdu wanda dama can sukan je kafin zuwan gulbi,Nana matar Abdu ta fito jin an shigo a guje.
"Fatimah?lafiya daga ina kike?waye ya biyo ki haka a guje?"Nana ta jera mata tambayoyin,Lauriya ce ta bata amsa "ruwa ta faɗa sai da mai jirgin ya shiga ya tsamota,shine fah mafarin gudun"Hannuwa Nana ta fara taɓawa ta na salalami kafin ta yi masu iso zuwa cikin ɗaki.
Sai yamma lis sannan su Fatimah suka baro gidan Nana,wannan karon zagaye suka yi ba su bi ta gulbi ba dan kuwa aradun Allah wacce Fatimah ta ja a kan ba za ta shiga jirgin ruwa ba ta cika buhu.
Amadi bawon Allah tun ya na zuba ido ya ga dawowar su Fatima har ya haƙura ya nufi gida.
Tun a bakin ƙofa ya ke jin ihun wani ƙaton saurayi,tsuki yayi a fili ya furta "aikin kenan kullum cikin ihu kamar gidan mahaukata mtws...kawai an mayar mana da gida faɗar cirar aljanu"
"Amadi tare min shi kar ya fice"cewar Malam mahaifi ga Amadi,babu yadda ya iya haka ya tare saurayin ya riƙe sa tamau kamar ɗaurin goro.Har cikin ɗakin da Malam ke Ruƙiya Amadi ya kai wannan saurayi,cikin daka tsawa yace "zauna nan kuma in ka saki ka fita sai na gundile ma kai,bari ganin ka na da Jinnu to na bisa kaina sun fi ƙarfin naka"abu kamar almara haka saurayin nan ya lafe waje guda ya na kallon Amadi fuskarsa ƙarara tsoro.
Malam yayi murmushi yace "yawwa Amadina gwara da ka gargaɗe sa na san kuwa in ba ni nace ya fita ba to fah babu inda zai je"Amadi yace "to Malam in ba abun ka ba waye bai tsoron Tabarno,su kansu aljanun yanzu tsorona suke"cike da murna Malam ya kuma cewa "shi yasa nake ma kwaɗayin shiga sahun maluman Ruƙiya"ɗif fara'ar fuskar Amadi ta ɗauke yace "haba Malam sai kace dan aljanu mu ka zo duniya?a bar ni da iya sarautar Sarkin ruwa"Malam bai ce komi ba saboda haushi dan ya jima ya na son saka yaron nasa harakar cire ma mutane Jinnu duba da yadda ya ke da ilimi sosai ga kuma wata baiwa da aljanun ruwa suka bashi.
Alwala sallar magrib Amadi yayi kafin ya wuce masjid,ko da ya dawo ya tarar da Inna ta zuba masa abinci.
Kan tabarmar kaba ya zauna ya tanƙwashe ƙafafunsa kafin ya jawo langar tuwon dawa, Bismillah yayi ya ɗibi abinci zai kai baki kwatsam sai Fatimah ta faɗo masa a rai.
Lomar tuwon ya mayar ya na mai sakin murmushi ya dubi Inna wacce ita ma shi ta ke kallo "Inna albishirin ki?"
"Goro"cewar Inna, Amadi yace "na samu matar aurena, bafulatanar da na ke baki labari ta na zo min cikin mafarki to yau dai kam na gan ta a zahiri"
Inna tace "Amadi ban son shirmen banza,ta ya aka yi ka gane ita ce ?"ya ɓata fuska yace "Allah Inna ita ce,dan tabbatarwa har masarauta na kai ta" "wace masarauta?"Inna ta tambaya ta na mai ƙure sa da ido,ƙeya ya sosa da alamu yayi suɓul da baka kawai sai ya jawo abinci ya fara ci.
Sai da ya ci ya ƙoshi sannan ya miƙe,hannu ya wanke ya cika moɗa da ruwa ya shanye kafin ya shiga ɗakinsa.
Wata ƙwarya ya fiddo daga ƙarƙashin gado mai cike da ruwa,iskan bakinsa ya hura ruwan suka rausaya kafin hoton fuskarta ya bayyana a ciki ƙwaryar na ɗaukar wani irin haske kamar an saka fitila.
Kwance take sanye da kayan Fulani farfaru,gashin kanta a warware duk ya zuba kan jikin Innaro wacce ke shafa mata ɗanyen man shanu a kai.
Murmurshi Amadi ya saki daga nan ya hura iska gashin kanta wanda ya rufe gefen fuskarta ya ɗan tashi sama,wata zabura ta yi ta tashi zaune Amadi kuwa kallonta kawai ya ke.
Ɗif hasken ya mutu sakamakon shigowa da Inna ta yi,da sauri ya mayar da ƙwaryar kafin ya maido hankalinsa ga Inna wacce ke yi masa kallon tuhuma.
"Amadi tsafi kake?kenan har yanzu ba ka bar wannan rufa idon ba?"Inna ta tambaya murya na ɗan rawa.
Cikin alamu na maras gaskiya yace "a'a fah Inna kawai baiwa ce Allah ya bani,kuma ke da kan ki kin faɗa kin ce tun ina ɗan yaro nake abubuwan mamaki"Inna ba ta sake cewa komi ba ta fice daga ɗakin.
★★★ MARADI
"Wai Marwa gaske ne can sashen su Prince Khalid za ki koma da zama?"Saffa ke tambaya ta na kallon Marwa wacce ta zube ƙasa ta na zaɓen kayan da za ta tafi kamar yadda umarnin Amma ya bada.
"Ki na fah ji na shine kika yi banza da ni ?"
Marwa ta ɗago ido taf hawaye tace "ya zan yi Saffa?ban san mi yasa ta ke son na koma can ba,tun jiya zuciyata ta kasa nutsuwa dakyat fah barci ya ɗauke ni a can sashen"
Cikin jin haushi Saffa ta mayar mata da "babu wani ba ki ji daɗi ba,ina ce can da AC sannan a bed kika kwana amman da yake baki son ki nuna min shine kike zancen wahala.Marwa ki je ki sha daɗi ke ɗaya na ji na gode da haka,dama tunda na ga wannan jararababen ya lanƙame maki na san da sai ya raba zumuncin mu"
Marwa ta tashi tsaye ta na ma ƴar uwarta duban mamaki,ko kafin tace wani abu sallamar Jakadiya haɗi da kirarin ta ya iso gare su.
"Taka ranki lafiya gimbiya sarauniya uwa ga Prince Khalid,gafara dai masu abu da abunsu kura da kallabin tumbi ,gafara dai masu sarauta za su shigo"
Amma ta fara shigowa Jakadiya na take mata baya,sanye take cikin kayan sarauta kai kace ita ce matar sarkin.Lokaci ɗaya zuciyar Marwa da ta Saffa suka buga yayin da kuma jikin Marwa ya ɗauki wata irin rawa ita kuwa Saffa ƙuri ta yi ma Amma ta na yi mata kallon ido cikin ido.
Ba Amma ba hatta Jakadiya ta ɗan razana ganin yadda idon Saffa ke fitar da wani hayaƙi ya ɗauki kalar kore,a hankali Amma ta fara taka ƙafa zuwa gunta sai dai ko kafin ta kai hannu ta dafata abun cikin idon Saffah ya ɗauke cak.
Girgizata Amma ta yi amman tsit ba ta ji komi ba,da sauri ta yi ƙasa ta na kwasar gaisuwa ita kuwa Amma ɗago Saffa ta yi ta haɗeta da jikinta ta na cewa "tashi Ƴata gaisuwar ta isa haka"sannan ta juyo gun Marwa wacce jikinta yayi sanyi laƙas duk wata laka ta jikinta ta mutu murus.
"Kin gama kimtsawa ne?"ita ce tambayar da Amma ta yi mata,kai ta girgiza alamun a'a ta sakar mata murmushi ta na mai kuma cewa "ok toh in kin gama ki jira za'a zo a tafi da ke,zan wuce palais dan isar da saƙon mallakar ki"ba tace komi ba a haka Amma ta fita Jakadiya ta take mata baya.
"Ban yarda da wannan matar ba,sam ba ta yi kama da mutumniyar kirki ba amman ban san mi yasa kuma na ji zuciyata ta kamu da sonta farat ɗaya"Saffa ke magana ta na wani jujuya ido,Marwa kuwa kallon sabon al'amarin da ke tattare da ƴar uwarta kawai take.
Saffa ta girgiza ta tace "ko baki ji abin da nace ba?"Marwa ta nisa tace "na ji mana,amman ki iya bakin ki nan masarauta ce fah za'a iya yi maki hukunci mai tsauri"Saffa ba ta iya cewa komi ba sakamakon wani abu da take ji ya na yawo a kwanyarta doli ta kwanta nan ta ɓingire da barci.
A can ɓangaren Amma kuwa su na isa palais dogarai suka fara yi mata kirari,duk da kasancewar ba kasafai take zuwa nan ɗin ba sai ta na da wata muhimmiyar magana.
"Ran sarki ya daɗe Sarauniya Amina na son ganawa da kai akwai Magana a bakinta,a bani izini dan sallamar dogarai"Jakadiya ke wannan maganar bayan ta yi gurhano a gaban sarki,cike da izza yace "na baki dama"Jakadiya ta miƙe ta na yi ma dogarai alama da su fice ita ma fita ta yi ta tsaya bakin ƙofa.
Bayan fitarsu ne Amma ta yi wani murmurshi mai ɗauke da ma'anoni dayawa,duk da kasancewar Sarki Garba na da iko sosai amman sam bai san mi yasa ya ke shakkar Amma ba kusan ma ta zame masa ƙarfen ƙafa.
Zagaye ta fara ta na magana "babu shakka ƙarfin mulki ya ratsa jikinka sosai,dukiya na ta ƙara hauhawa amman har yanzu ban ga alamun za'a baiwa Prince Khalid gadon mahaifinsa ba"
Cike da dakiya Sarki ya miƙe tsaye yace "Amina ki yi maganar da ta kawo ki,banda isasshen lokaci"
Amma ta juyo ta ɗan taɓe baki tace "dama maganar *Tawaye* ne ina son ɗaya ta koma sashena " Sarki ya murmusa har gemunsa ya motsa kafin yace "a kan wane dalili ne za ta koma part ɗin ki?"sai da Amma ta ƙanƙance ido sannan tace "kar da ace Sarki ya mance da sharuɗan masarauta?"ya girgiza kai yace "ban mance ba,sai dai ina son sanin dalilin ne"kai tsaye ta basa amsa da "Prince Khalid ke sonta kuma sai na ga bai dace ba ta ci gaba da yin bauta a matsayin ta na sarauniyar gobe"
Sarki ya tako har izuwa inda Amma take yace "Dama bauta ce suke?tun yaushe aka yi jera su cikin jerin bayi alhalin sashen su daban yake da na sauran sannan kuma in ban manta ba babu wani aiki da suke yi"
Amma tace "ko cin abincin bayi da suke shi ma bauta ne,balle kuma wani sa'in sukan ɗebo ruwa"
Sarki yace "ya isa haka nan,ki je ki tafi da ita sai mi kuma?"Amma ta yi ƙofar fita ba tare da tace komi ba nan suka yi karo ita da Yarima wani kallon ƙasƙanci ya yi mata,kafin ita kuma ta kafesa da ido na wani ɗan lokaci ta yi murmushin da ita kaɗai ta san ma'anarsa.
"Ya mahaifina miye dalilin da kake barin wannan matar na shigowa palais mi yasa ba ka yi mata iyaka ba?"Yarima ke faɗar haka sa'ilin da ya isa gun Sarki.
Sumar kansa ya shafa kafin yace "har yanzu kai yaro ne,da sannu za ka gane taƙon saƙar.Wannan masarauta na da rikici sosai babu wanda ya isa ya san inda ta dosa sai Allah amman da sannu komi zai warware"
Yarima ya sauke ajiyar zuciya yace "to amman miye ta faɗa ma?" "Ɗaya daga cikin tawayen masarauta za ta koma sashen ta saboda Prince Khalid na sonta"a hasale Yarima yace "in dai har ina da rai ba zan taɓa bari ya aureta ba saboda ni ma sonta nake"Sarki ya girgiza kai yace "tabbas alƙalumana sun daɗe da nuna min Prince Khalid zai aureta sai dai ban san wacce ce a cikin su ba har yanzu sai in Amina ta kaita sashenta zan tabbatar,maganar kuma ka na sonta wannan ƙarya ne sha'awarta ce kake"
Da sauri Yarima ya kalli mahaifinsa ya na mamakin ya aka yi ya san sha'awarta kawai ya ke?bai tsinke da lamarin ba ya ji muryar sarki na cewa "in kuma tunanina ya zamana haka ne to kai ne namiji na farko da za zai kusanceta kafin shi wanda zai auren nata ya same ta "tsabar farin ciki ya saka Yarima rungume Sarki yace "na gode mahaifina dama kamar ka san plan ɗina haka na tsara"Sarki ya murmusa yace "wani hanzari ba gudu ba,ƙa'idar ita ce sai ta sha wasu ruwa kafin ka kusanceta"Yarima ya ɓata fuska tare da tambaya "wane irin ruwa kuma?akan wane dalili?"
Sarki yace "saboda muddin ta na cikin hayyacinta aljanin da ke jikinta ba zai taɓa barin hakan ta faru ba"
Jikin Yarima yayi sanyi yace "to in kuma na bata ruwan ta ƙi sha fah?" Sarki ya nufi kujerarsa ya na mai cewa "ba kai za ka bata ba ƴar uwar tawaicinta za ta bata su,sannan ta hanyar lalama za ka nemi wannan alfarma muddin ka tursasata gari zai kwaɓe ma saboda ita ma ta nada nata aljanun"
Cike da ƙosawa Yarima yace "wai ni kam su Tawayen nan ba mutane ba ne ko mi? Naji sai wasu sharudda kake gindiya min akan bayi"Sarki yayi murmushi yace "mutane ne sai dai ba kamar kowa suke ba,su ɗin *Tawayen* masarauta ne" Yarima kai ya dafe saboda caji da ya ɗauka sam ya kasa fahimtar komi.
Bayan kwana biyu
Tunda Marwa ta koma sashen Amma sam barcin dare ya ƙaurace ma idonta,a ko wane dare cikin dararen biyu da irin masifar da ta fuskanta.
Daren farko barci na fara ɗokarta , ta fara ganin wata ƙatuwar halitta tamkar za ta cika ɗakin,dare na biyu kuwa gawar Prince Khalid ta ke gani akan makara yayin da wata murya cikin siririn amo ke gargaɗarta a kan ta fita harakar Prince Khalid.
A mugun furgice ta farka ta na dafe da saitin zuciyarta,a hankali ta saukar da ƙafafunta daga makeken gadon.Ta kama ƙofa za ta buɗe kenan Saffa ta shigo hannunta riƙe da kofi,Marwa za ta tambaye ta kawai ta kafa mata kofin ruwan ta na cewa "sha wannan sai mu yi magana"sai da Marwa