Showing 24001 words to 27000 words out of 27104 words
vata muku rai a cikin gidan nan bai zamo hujja a wurinki ba da za ki yi ta bijire mishi, ba a kan idonki ya kawota ba, a yanzu in har kuka shirya ke da shi zai yi matuqar kiyaye abin da bakya so, ba ma sai kin tsaya kina ce mishi ga abin da bakya son ba, ai shima ya xanxana wahalar wannan dogon fushin da aka yi mishi”.
Har suka gama girkin nasu suna hirarsu, suka gama suka shirya komai tsaf. Abida ta kalli Saddiqa ta ce mata, “To sai ki xauka ki kai musu”.
Ta ce, “A’a, ke daai ki kai tunda ni kam ai ban tava leqa wannan falon nashi ba”.
Abida ta ce, “A’a, ai yanzu suna tare da abokinshi don kin kai ba wani abu bane, sia ma ya ji daxi ya kuma san kina shirye da a shirya”.
Ta yi maza ta ce, “Tafxijam! Wato ma nice mai neman shirin? Lallai ba za a shirya ba, ajiye musu nan in ya zo wucewa ya gani zai xaukar musu”.
Abida ta qyalqyale da dariya ta ce, “Kin gani kuwa da yake na san daxin nawa auren bana yarda maigida ya yi fushi dani, ina ganin alamar vacin rai a tare da shi nake yin maza in shawo kan abina don bani da jarumtakar irin wannan zaman da shi”.
Hira sosai ta yi mata, sai wajen yamma suka tafi gida.
Washegari kuwa da yamma sai ga Abidan ta dawo tare da wata lafiyayyar yarinya budurwa, ta shigo falon Saddiqa, Mus’ab yana ciki yana nazarin wata mujalla, ya yin da Saddiqan ke cikin xakin a kwance. Sun gaisa ta soma yi mishi bayani.
Saddiqa ta fito tana mata sannu da zuwa, “Ku shigo”. Mus’ab ya bi bayan kyakkyawar yarinyar da kallo, ya yi kamar ya tambayi sunanta sai kuma ya fasa saboda kar Saddiqa ta ji shi yana maganar.
“Aisha ga qanwata na kawo miki Zainab, ‘yar Kawuna ce kwanan nan ta gama karatunta na sakandire, baban Umar ne ya bani shawarar kawo miki ita ta xebe miki kewa kafin a samo miki mai aikin”.
Wannan shine bayanin da Mus’ab ya jita tana yiwa Saddiqa.
Tun zuwan Zainab gidan al’amura suka soma daidaita, Mus’ab ya smau damar komawa kan aikinshi, sai dai kullum in zai fita zai kukkule ko’ina na gidan, ta yanda wani ba zai shigo ba na ciki kuma ba zai fita ba sai in ya dawo ne yake barin ko’ina a buxe.
Saddiqa kuwa tana tare da Zainab a gida ta mai da ita tamkar ‘yar’uwarta saboda yanda take jin daxin zama da ita, zuwanta ya rage mata kewa da damuwa, ta fidda ita daga zaman shiru da take ciki, matuqar suna tare zai jisu suna ta raha da dariyarsu.
Cikin qanqanin lokaci suka shaqu da juna, har girkin ma in za suyi tare suke shiga kiin xin suna aikinsu suna hirarsu, tamkar sun daxe da sanin juna.
Shima Mus’ab ganin yanda ta saki jiki da Zainab xin yasa shi samun nutsuwa da kwanciyar hankali, saboda ya lura Saddiqa ta samu sassaucin damuwa.
Ganin haka sai ya fara tunanin hanyoyin da zai bi wajen ganin al’amura sun daidaita tsakaninshi da ita, ya shiga qoqarin keveta ita kaxai ya xan yi mata kalamai masu nutsar da zuciya, duk da dai ba wani amsa mishi take yi ba.
Haka nan yana kiyaye lokacin dawowar shi gida, yana tasowa daga ofis bai yarda ya tsaya ko’ina sai gida, ga kuma hidimomi iri-iri don dai ya faranta mata rai.
GARIN MISAU
Abu tana kwance a xakinta cikin dare iska sai faman kaxawa take yi, kasancewar lokacin kaka ne. Abu ta miqe zaune a tsakiyar gado ta yi tagumi zugum, tunanin yanda ta baro Saddiqa take yi a gidan Mus’ab. Mafarkinta na daren jiya ne ya fi tsaya mata a rai, ta tuna yanda ta ga Saddiqa a mafarkin, bayanin dukan da Mus’ab ya yi mata take yi, tana nuna mata raunukan da ya yi mata.
Ta yi shiru cikin tunani mai zurfi tare da tuna irin dukan da ya yiwa Jennifer a kan idonta, jikinta ya xauki rawa saboda tabbatarwar da ta yi in har ya ce zai yiwa Saddiqa irin wannan dukan to ba za a haifi xa mai ido ba.
Dare ya yi nisa Abu tana zaune a bakin gadonta taqi yarda ta kwanta balle ta samu ta yi barci, saboda babu halin ta rufe ido ko gyangyaxi ya xan xauke ta sai ta ga Saddiqa tana tsaye gabanta tana kuka tana faxin “Ke kika ja min wannan musibar Abu da kika qi yarda ki tahowa Gwaggona dani kika barni wurin Yaya Mus’ab, saboda kin fifita sonshi a kaina, bayan kuma Gwaggona ta roqeki ki tausayawa maraicina in kinga ba daidai ba ki dawo mata dani gabanta”.
Abu ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji daxi, ita da kanta ta zargi kanta da rashin iya tsai da adalci a tsakanin Mus’ab da sauran jikokinta a ko’ina, ba ta iya voye shi daban ne, ba ta iya voye sonshi a zuciyarta, ba ta barwa kanta wannan sirrin.
To wai ma mene ne dalilin da yasa ta fi sauraranshi a kan sauran? Ta fi tattalin farin cikinshi a kan kowa? Ta fi son ganin ya samu abin da yake so a kan kowa? Me yasa take yi mishi irin wannan son?
Mus’ab ne ya fi kowa biyayya a cikin jikokinta ko kuwa ba haka bane, shine ya fi kowa jawo musu magana, shi ya fi kowa taqadaranci, ya fi kowa rashin tsoro, ya fi kowa yin yanda ya so. Amma ta je ta kasa hana shi Saddiqa saboda ta gane babu abin da yake so irin a bar mishi ita.
Nan take ta soma kuka tana faxin bai cancanci abin da take yi mishi ba, ba ta yiwa kanta adalci ba da ta bari sonshi ya rinjayeta. Ta miqe ta yi alwala ta dawo ta soma gabatar da addu’o’i na Ubangiji ya kare Saddiqa daga dukkan sharri.
Nan take ta qudurawa ranta gari na wayewa za ta je gidan Malam Abdullahi ta gayawa Inna Habiba halin da ta baro mata ‘yarta na gaskiya, don ta san abin da za ta yi ta taimaketa ta san matakin da za ta xauka.
Saddiqa tana kwance kan doguwar kujera tana nazari da tunanin al’amuranta da Mus’ab kan irin kai kawon da yake yi da yanda yake nuna qauna da kulawa a gareta, yanda yake qoqari da tattalin ganin sun shirya shi da ita. Duk da har yanzu ba wani amsa maganarshi take yi ba, ba ya fushi ko nuna vacin rai game da abubuwan da take yi.
Kalaman Abida kashedin da ta rinqa yi mata kan haqqin aure suka dawo mata.
“Ki fa yi hankali Aisha kar ki yarda ki shiga haqqin mijinki. Wannan bijirewar taki tana nema ta wuce gona da iri, don kun same shi da wata a gida bai zama miki dalili ba fa, don kuwa samun ta kika yi ba ita ta zo ta same ki ba”.
Ta yi ajiyar zuciya daidai lokacin da Mus’ab ya shigo falon.
“Ajiyar zuciyar me kike yi? Ko kina jin yunwa ne?”
Ta xaga ido ta kalle shi, kwalliyarshi ta qananan kaya ta burgeta, ga qamshinshi mai daxi, in a Misau da Bauchi kaxai ka san shi ba za ka tava sanin yana amfani da qananan kaya ba. Zuciyarta ce ta raya mata hakan.
“Bari in shiryo miki abincinki”.
Ya juya zai shiga kicin. Da sauri ta ce mishi, “Ni babu halin in yi wani motsi sai a ce yunwa nake ji?”
Ya yi maza yaja ya tsaya nan take, ya juyo ya fuskanceta can cikin zuciyarshi daxi ne ya kama shi, bai tava jin ta yi mishi wata magana da jimlarta ta yi tsawo kamar wannan ba.
“Za ta fara magana dani kwanan nan”.
Tunanin da ya zo mishi a ranshi kenan.
“To in ba yunwa ba ce mene ne Aisha?’
Ya yi tambayar daidai isowarshi kan kujerar da take zaune. Maimakon ta zabura ta miqe kamar yanda ta saba yi mishi sai ya kamota, sai ya ga ba ta motsa ba.
“Zan iya zama kenan?”
Zuciyarshi ta sake raya mishi, don haka ya smau wuri a gefenta ya zauna, ita ma ta miqe daga kwance ta zauna cikin nutsuwa kanta a sunkuye.
“Kina son wani abu ne ko kina da wata damuwa ne?”
Ta girgiza kai tare da faxin “A’a”.
“To in baki da ita ni ina da ita Aisha, ko baki da damuwa da abin da ya dame ni?”
Ba ta tanka mishi ba, sai dai ganin ba ta yi yunqurin tafiya ta bar mishi wurin ba yasa shi jin daxi, nan take kuma ya yi nufin amfani da damar da ya samu wajen yi mata magana.
“Ban tava tunanin don an gaya miki mugun halina ko kin kama ni da wani laifi za ki nuna min qiyayya da tsana irin wacce kike yi min ba, saboda ni na san waxannan abubuwan guda biyu ba sune matakan da ake xauka wajen gyara mutumin da ake ganin yana buqatar gyara ba. Sanda Abu ta kaiwa Kawu Gixe ni shi kuma ya damqa al’amurana a hannun Mama, ko in ce Innata, ni da kaina qyamar kaina nake ji, zuciyata ta yarda da cewar ni xin ba komai bane face wata jarrabawa da aka jarrabi iyayena da ita, saboda kullum abin da ake gaya min kenan.
Don haka sai na zama a takure bana ko iya sakewa in shiga mutane balle in yi mu’amala dasu, saboda ko da na kasa barin abin da ake so in barin to kuma bana jin daxin vata musu ran da nake yi, da yanda nake ja musu magana. Tunda a gabana an yiwa babana gori a kaina, ba sau xaya ba, ba sau biyu ba.
Don haka ko da aka kawowa Kawu Gixe ni na bi umarnin Abu ne kawai na biyota, amma cikin zuciyata na yi niyyar fakon idonsu in yi tafiyata don kar suma in ja musu irin abin da na jawa iyayena a Misau.
Sai dai ban iya tafiya na barsun ba Aisha, saboda cikin xan qanqanin lokaci ne na fahimci su basu xaukeni abin kunya ba balle su kalleni a matsayin jarrabawar rayuwarsu, ban tava sani ko tunanin ina da wani alheri a tare dani ba sai da na ji Mama tana rama gorin da aka yi mata a kaina da wasu kalamai da ba zan furta miki su ba.
Amma bayan lokacin ne ni da kaina na gane ashe duk abin da na yi a rayuwata ban tava xaukan abin wani ba, haka nan na kan faxi laifina ni da kaina, ko kuma in faxi gaskiya kan abin da aka tambaye ni. Sai da na ji wannan shaidar a bakin Mama kafin ni kaina na san eh, ashe haka xin nake.
Da na zauna da ita sai da ta yi min wani irin riqo, ta yi mu’amala dani wata irin mu’amala da ta tilastani jin kunyarta, na zama mai gudun vacin ranta, na zama ban da abin da nake so irin na burgeta, in sata ta ji daxi, in jita dai tana sanya min albarka tana roqon Ubangiji ya shiryar mata dani.
Ba duka ta rinqa yi min ba, ba zagi ba, kalamai ne kawai masu sauqi da suka fi kama da nasiha. Yanzu mene ne amfanin yaro kamarka a same shi yana irin waxannan abubuwan da kake yi? Yanzu ko don in ji daxin zuciyata ba za ka daina ba? Ba za ka bar abin da nake cewa ka bari ba? Don Inna ta ji daxi, don in sata ta yi farin ciki. Sai na wayi gari na daina abubuwan da take faxin in daina, duk da wuyar barinsu”.
Ya xan yi shiru kaxan kafin ya buxe baki cikin nutsuwa ya ce mata, “Na xauka tunda ita ta haifeki halayenki za su zamo masu sauqi irin nata”.
Duk da kalaman da ya yi mata sun ba ta tausayi, sun kuma kashe mata jiki hakan bai hanata xagowa ta kalle shi ba, kan ta gama tunanin dake zuciyarta sai ta ji ya ce.
“Ko da yake dama an ce wai a kan haifi xa ne ba a haihuwar halinshi”.
Ta yi maza ta gyaxa kai. Ya yi murmushi ya ce, “Nima da halin Inna ne dani ai da bamu samu matsala dake ba ko?”
Ta sake sunkuyar da kanta qasa.
“To amma ko baki yi min yanda Inna ta yi min ba tunda Kawuna ya riga ya bani ke duk da ya fi kowa sanin yanda nake xin, ai ina ganin ba irin wannan zaman ya kamata mu yi ta yi ba, ya kamata ne mu yiwa juna adalci ni in rage wasu abubuwan ke kuma ki yi haquri da wasu, sai mu haxu a wata matsaya da zamu ragewa kanmu damuwowin da muke ciki ko kuwa?”
Kan ta yi magana sai ga Zainab ta shigo cikin falon xauke da tiren abincinsu.
“Yaya za a kawo maka naka nan ne ko falonka za a kai?”
Ya ce, “A’a, bar shi a kicin xin in ina buqata zan xauka”.
Ta ce, “To”. Ta juya ta fita.
“Aisha!”
Yana nufin ci gaba da maganar ta hanyar ba ta umarni ta kai mishi nashi abincin wurinshi, sai qarar wayar landline ta katse shi. Ya yi maza ya miqe ya nufi falonshi don amsa wayar a can, zuciyarshi cike da farin cikin damar da ya samu tare da Saddiqa.
“Kwanan nan zan shawo kanta ta yanda al’amura za su daidaita a tsakaninmu”.
Kalaman zuciyarshi kenan.
Ita ma Saddiqa ta miqa hannu cikin dabara ta xauki kan wayar dake ajiye kusa da ita a tata zuciyar tana tunanin, “Ai ko za ta saki jiki da shi kyakkyawar mu’amala ta shiga tsakaninsu to sai ta tabbatar ya rabu da ‘yan iskan ‘yammatanshi tukunna”.
Tana jona wayar da jikin kunnenta sai ta jishi yana cewa, “Zan amsa gaisuwar nan kuwa Sarah? Aui na yi zaton kin riga kin share sunana a dairy xinki”.
Ta yi ‘yar dariya ta ce, “A’a, sai dai in kai ne ka yi hakan, tunda baka tava nemana ba gara ni ai na je ofis xinka aka ce min kana gida kana hutun angwanci, shine na ce to ango kuwa ai bai da lokacin sauraron abin da ke waje, musamman ma a ce bai danganci amarya ba. Shi yasa na ce bari in saurara sai ka fito tukunna, yanzu ma dai na bugo ne in ce maka congratulation, ina tayaka murna”.
Ya yi dariyar jin daxi ya ce, “To na gode Sarah, sai dai ko ina angwanci ai bai kamata in rasa lokacinki ba, kina gida ne?”
Ya ce, “Eh, to yanzu dai bana gida amma zuwa awa xaya xan isa gidan”.
Ya ce, “To sai na zo”.
Ya ajiye wayar, ita ma Saddiqa ta mai da tata ta ajiye.
“Aunty kin gama wayar ne?”
Saddiqa ta xago ido ta kalle ta jikinta sai rawa yake yi, zuciyarta tana raya mata zai fita ya barni ya tafi wurin ‘yammatanshi na banza saboda na tsare mishi inda zai kawo su. Gara in ba shi wuri, bari kawai in tafi in bar mishi gidanshi ya sake ya yi abin da ya so, dama abin da ya saba yi kenan.
“Mu ci abinci mana”.
Zainab ce take yi mata magana saboda ganin halin da ta shiga shirunta ya yi yawa.
“Ci ki bar min Zainab, kinga ai xazun nan na karya”.
Ta miqe ta shiga xakinta ta shafa jikinta ta ji lalitar kuxinta da Gwaggonta ta ba ta, ta duba kuxin suna nan a ciki. Ta yi saxaf-saxaf cikin sanxa ta wuce Zainab a kicin tana gyare-gyare tana tsaftace wuri ta fita harabar gidan dake buxe, cikin sa’a babu kowa balle ya ganta. Tana baro gidajen nasu da kaxan ta yi sa’a ta samu mashin ta xane zuwa tashar motar garin dake kusa.
Shigarsu tashar ta ji ana Kano ciko mutum xaya a tasi. Tana jin haka ta faxa ciki a zuciyarta tana tunanin daga can sai ta shiga mai zuwa Misau ya fi mata ta zauna jiran ta Bauchi ta cika don kar ya gane ta fita ya biyo bayanta ya sameta.
Nan da nan aka gama haxa kuxin fasinja aka sallami direba yaja mota suka soma tafiya.
Saddiqa tana zaune cikin mota sai faman sharara gudu take yi, zuciyarta cike da farin ciki yau kam za ta koma Misau gaban Gwaggonta. Ta tuna Gwaggon nata da irin kalamanta da ta sha gaya mata a kan Mus’ab.
“Halin wannan yaron sai shi babu mai iya mishi sai mace ‘yar bariki irinshi, amma bake ba