Showing 15001 words to 18000 words out of 27104 words

Chapter 6 - ABU NAKA Book 2 Writing by SODANGI.txt

02 Dec 2024

1272

ko baka jin yunwa sha’awa zai sa ka ci. To balle su Abu da suka wahala wajen tafiya suka iso ba su ci komai ba, suka kuma kwana suna kwara amai.
Sai da suka ci suka qoshi har Abu tana cewa a kunna mata fanka sai ga Abida ta sake shigowa da wani kwanon abincin za ta ajiye kusa da Abun, ta yi maza ta ce mata.
“Ke ‘yar nan in dai ba so kike mu ci sai mun kasa tashi ba gara ki barmu haka”.
Abida ta yi murmushi ta ce, “Ba za ku kasa tashi ba ai babu wani abu mai nauyi cikin abin da kuka cin”.
Abu ta ce, “Ba zamu sake cin komai ba”.
An xan jima kaxan Abida ta ce, “To ai sai muje ku kwanta ku huta”.
Abu ta ce, “A’a, mu yanzu mota kawai za a kawo mana ta xebe mu ta mai damu inda muka fito”.
Idris da tuni ya gane akwai matsala tsakaninsu da Mus’ab, ya ce mata, “To ku xan miqe mana kafin in je in zo muku da motar”.
Ta ce mishi, “To”. Saboda mutuncinshi da na matarshi da ta gani.
Suna kwanciya kuwa bacci ya yi maza ya xauke su, basu sake sanin abin da ake yi ba.
Mus’ab yana tare da Idris yana ba shi labarin abin da ya faru, bai voye mishi komai ba. Idris ya kalle shi cikin vacin rai da nadama ya ce, “Yanzu wannan abin da me ya yi kama? Ni dama ina kallonka ne tare da mamakin wannan rayuwar da kake yi, saboda daga ganinka sai a gane kai xin mutum ne mai asali da ya fito daga wuri na mutunci, amma ka zo ka biyewa wannan sharholiya. Yanzu ina alherin wannan abin da ya faru? Me za ka cewa wannan yarinyar?”
Suka xan yi shiru. Jimawa kaxan ya yi tsaki ya ce, “Kai da aka yiwa gata da irin wannan lafiyayyar yarinyar me za ka yi da waxannan da kake kwasa masu gashin doki a ka?”
Mus’ab ya ce, “Uhm! Don ma baka san artabun da aka yi da mahaifiyata ba kafin aka bani ita”.
Idris ya sake wnai tsakin ya kawar da maganar ta hanyar qwalawa matarshi kira.
Ta amsa da “Na’am, gani nan zuwa, minti biyu.
Ta iso kafin cikar minti biyun da ta ambata cikin kwalliya da qamsohi, tana goye da xansu dake ta miqe-miqe nuna alamar bai son goyon. Hannunta kuma xauke da tiren abincin da ta shiryo musu ta ajiye a gabanshi.
“In zanin ya kwance ya faxi fa Abida?”
Ta ce, “Sai ya ji da shi”. Ta faxa daidai ta kwanto shi za ta ajiye mishi shi, ganin irin kallon da ya yi mata yasa ta yin murmushi tare da faxin “To ka yi haquri”. Ta samu wuri ta xan zauna tare da sauraron abin da yake gaya mata.
“Babu zuwa cikin gari yau”.
Ta yi murmushi ta ce, “Na sani ai tunda muna da baqi”.
Ya sake cewa, “To muna da ‘yar matsala tare da baqin namu”.
Ta sake cewa “Na gane, don na ji Abu tana cewa Aisha gaskiyar uwarta ne da ta cewa fitina kawai aka xauko mata, don haka ba za ta barta cikin fitinar ba za ta tasa ta a gaba ta mayarwa uwarta da ita”.
Gaban Mus’ab ya sake faxuwa. Idris ya cewa matarshi “To a irin hikimarku ta mata ki san yanda za ki yi ki rarrasar mana su mana, musamman Abu ta yi haquri”.
Ya miqa hannu ya jawo musu tiren abinci ita kuma ta miqe ta shiga ciki.
Wajen sha biyu da rabi na ranar ne Abu ta farka cikin salati da miqa, tana buxe ido ta xaxawa Saddiqa duka.
“Ke tashi sakarya mara zuciya, kin kwanta kin saki jiki kin hangame baki kina ta yin bacci sai ka ce ba da vacin rai kika kwanta ba”.
Saddiqa ta ce, “Kai Avbu kenan, sai ka ce ba tare muka yi baccin ba”.
“Tashi ni mu shirya mu tafi”.
Saddiqa ta yi maza ta miqe.
“Fita ki tambayi matar gidan ko an kawo mana motar?”
Ta fita tana magana da Abida, ita kuwa sai kallon Saddiqa take yi cikin sha’awa.
Gasu nan dai a falo yanzu suka dawo bari in tambayesu.
Ta ce, “To”.
Ta koma xaki tana yiwa Abu bayani, ita kuma Abida ta nufi falon mijinta ta gaya musu tambayar da Abu ke yi.
A hankali Mus’ab ya buxaa baki ya ce, “Xan kira mana ita Abun”.
Ta ce, “To”. Ta tafi.
Idris da Sani suka gaisheta ta amsa, ta qi amsa ta Mus’ab.
“Haba Abu, ai tamu dake ba ta vaci, muna ‘yar haka dake ne? Ai Aisha ce ya kamata ta yi fushi dani, ke kuma sai ki haxamu ki yi mana faxa ki sasantamu ki ce mu zauna lafiya, tunda na saba jinki kina cewa shi aure sasanta shi ake yi ba lalatawa ba”.
Da sauri ta ce, “Ba irin naka auren ba, ai kaimaa baka nufin yinshi, mai nufin yin aure ba zai yi wannan abin da kake yi ba, tunda dai duniya ka tasa a gaba ai sai ka je ka yi ta yi, amma Saddiqa kam zan mayarwa uwarta da ita, don suna kuka aka raba su ta kuma roqeni in har na ga ba daidai ba kar in bar Saddiqa don ba za ta iya da kai ba”.
Sani ya yi murmushi ya ce, “Haba Abu…..”
Kan ya yi maganar da zai yi ta yi maza ta kwave shi, ta ce, “Kul! Kar ka ce za ka ce min komai, ina ce ku dukanku iya shegen kuka tasa a gaba, ai ina ganin lokacin da ka dawo. To ko varawo ne ya dawo gidanshi a wannan lokacin ai yaa isa lalaataccen varawo”.
Idris ya ce, “Gaskiyaa ne Abu, ita wannan rayuwar ai ba rayuwa ba ce, yaushe za a haxa matan bariki da matan da kuka bamu?”
Abu ta ji daxin zancen shi, ta saki jiki suka yi ta hira. Ta kwashe bayani duk ta yi mishi, tun daga ranar da Mus’ab ya zo gidanta da zancen neman auren Saddiqa, har kawo barowarsu gida jiya da abin da ta zo ta tarar a nashi gidan, wanda idonsu ya ganar musu ba ta rage komai ba sai da ta gaya mishi.
Cikin nutsuwaa ya ce mata, “Ya gayaa min Abu, saboda shima ya san bai kyauta a. to amma kuma abin da ya yin bai kai na ki tafi mishi da maatarshi ba, ki yi haquri”.
Ta yi maza ta ce, “A’a, abin da ya kamaceni kenan in yi adalci a tsakaninsu, ba za ta iya da shi ba ya fi qarfinta, baqin ciki kawai zai yi ta qunsa mata, yarinya ce ‘yar qarama”.
Idris ya ce, “Na ganta ai”.
Ta yi maza ta ce, “Yauwa, to wannan randa ya ce zai yi mata irin dukan da na ga ya yiwa wata jiya ai falle-falle za a xauke ta. Amma da yake ita wancan xin mai qoqari ce sai na ga ta fito da qafarta tinqis-tinqis har tana iya magana”.
“To amma Abu”…….
Abun ta yi maza ta kalli Mus’ab ta ce, “Kai kar fa ka ce za ka rinqa tsoma min baki”.
Ya yi maza ya yi shiru. Idris ya ce, “To ki yi min wata alfarmaa mana”.
Abu ta ce, “Ta mene ne in ji in zan iya”.
A hankali ya ce, “Za ki iya, so nake ki bar maganar tafiya a yau ki haqura har zuwa jibi, ke da kanki kin ce yarinyar nan a jigace take, ke kanki ba ta fiki jigata ba. To ku xan hutaa mana kafin ku tafi”.
Ta ce, “To sai dai gobe, amma jibi kam ya yi yawa”.
Ya ce, “To na gode, Ubangiji ya saka da alheri”.
Ta ce, “Amin”.
Da yamma Abida tana aikin abincin dare, ta bari ta leqa xakin da su Abu suke ta kira Saddiqa.
“Aisha ko za ki fito ki xan taimaka min ne?”
Cikin sauri ta tashi ta fito suka shiga kicin xin tare suna aikin tare da hirar da Abida ce mai kawo zancen, ita amsa ne kawai nata shima a taqaice.
Zirga-zirgar Umar ta dame su, Saddiqa tasa hannu ta xauke shi ta goya shi suka ci gaba da aikinsu.
Idris ya shigo kicin xin riqe da ledar yankakkun kaji, Abida ta karva tana yi mishi sannu. Ya yi murmushi ya ce, “Amaryar kike sawa aiki? To bari in kira angonta ya ganta”.
Saddiqa tana jin haka ta yi maza ta bar kicin xin ta xauka da gaske kiran nashi zai yi.
Abida ta ce, “To ai sai ka shigo ka tayani tunda ka korar min ita”.
“Haba Abida, ai sai Abu ta ce yanda kika ga damaa kike juyani”.
Abu dake kusa bai sani ba ta yi maza ta ce, “Ai gara maka haka, a juya kan da wannan tanbaxa da su Mus’ab suke yi”.
Da daddare bayan cin abinci Mus’ab da Idris suna tare da Abu, saqarta take yi tare da sauraron bayanin nasu.
“Haba Abu, ki taimaakeni mana irin taimakon da na saba ganin kina yi min, kar ki tafi min da Aisha ki yi haquri ki samu kwanaki biyar zuwa bakwai don ki rarrasar min ita. Shi Kawuna da ya ce zai kawo min ita ai bai ce miki in kinga ba daidai baa ki mai da ita, ke kin san ba zan cuceta ba, don kin fi kowa sanin ina sonta, don haka ki taimakeni ki rufa min asiri”.
Ta harare shi ta ce, “In yi qarya kenan?”
Idris ya karve da cewa, “Ba qarya bane Abu gyara ne, ai kinga ni bana goyon bayan abin da yake yi, zan sa miki ido a kan zaman ina ganin ba daidai ba ko somi-somin wulaqanci zan sata a mota in kawo miki ita har gida Misau, don ba ta cancanci ganin irin wannan baqin cikin ba”.
Abu ta yi shiru cikin nazari, zuwa can ta ce mishi, “Kai a’a, ba zan iya barinta ba, na kuma roqeka kaima kamar yanda ka ce min in yi maka alfarma in qara kwana, to nima ka yi min alfarma ka kawo min motar da za ta mai damu gida gobe”.
Da sauri ya ce mata, “Cikin yardar Ubangiji zan kawo muku”.
Ta ce, “To, na gode”.
Ta miqe ta shiga ciki ta barsu a nan. Ya kalli Mus’ab cikin nutsuwa ya ce mishi, “In har baka samu wata hanya ta hanasu tafiya ba zan ba da motar da za ta mai dasu, saboda ba zan yarda in vata mata ba, saboda tsohuwa ce mai mutunci da addini”.
Mus’ab ya yi shiru sai dai hakan bai hanasu ci gaba da tattaunawa ba.
Washe gari da asuba daga fitowarsu daga masallaci ya bar unguwar a cikin motarshi, daga Idris har matarshi dama Abun sunyi zaton bai son ganin tafiyarsu ne yasa ya yi hakan.
Suna ciki suna shirye-shiryensu na lodin tsarabar da Idris ya yi musu, ga kuma Abida da take ta yi musu girke-girken da wai za su riqe su ci a hanya.
Qarfe bakwai da rabi daidai motar da za ta xauke su ta iso aka shiga fitar musu da kaya saboda ba qaramar tsaraba Idris ya yi musu ba.
Suna cikin haka sai ga Mus’ab ya iso gidan xauke da limamin babban masallacin garin cikin motarshi, wanda kuma shine kakan Idris. Dattijo mai kimanin shekaru tamanin a duniya, yana riqe da sanda a hannunshi saboda matsalar qafa da yake da ita.
Gaba xaya su Idris suka iso wurinshi suna yi mishi sannu da zuwa.
“Har baqin namu sunyi harama ne?”
Idris ya amsa “Eh, malam ai har sun kammala shiri”.
Ya ce, “To ai sai mu xan shiga daga ciki don mu gaisa”.
Ya ce, “To”.
Ya gayawa Abu ta amince da hakan cikin yanayi na girmamawa.
Liman ne kaxai zaune a kan kujera, sauran duka a qasa suke har da Abu suna sauraron shi bayan an gama gaisawar.
“Ki yi haquri, ki yi haquri da duk abin da ya yi, mu yi ta addu’a muna roqon Ubangiji ya shirya mana su. Ai abin da ya saura tsakaninmu dasu kenan a yanzu, don haka kar ki tafi mishi da matarshi na roqi wannan alfarmar ina fata za ki yi min ita”.
Abu ta gyaxa kai nuna alamar za ta yi tare da faxin “To Allah gafarta malam Ubangiji ya yiwa zuriyarta albarka, ya kuma sa ta gama da duniya lafiya”.
Aka ce “Amin”. Sai ya yi tambayar cewa, “Ina yarinyar take?” Abida ta yi maza ta miqe ta shiga ciki ta fito tare da Saddiqa, ta zo ta durqusa ta gaishe shi ya amsa tare da sa mata albarka.
Da aka sake nutsuwa sai ya kalli Abu cikin fara’a ya ce, “Kin kawo mishi alheri irin wannan kuma ki ce za ki tafi da shi? Bar mishi ita ai tashi ce, Ubangiji zai daidaita tsakaninsu, mu dai mu yi ta addu’a. in kinga ka dage a kan roqon abu, to kuwa Ubangiji ya yi nufin biya maka buqatarka ne, in ba haka ba, ba ma zai baka ikon ka roqa ba”. Ta sake cewa, “Haka ne”.
“Mu yi sallati ga manzon rahama”
Liman ya ba da umarni. Nan da nan aka shiga yi, liman ya yi addu’o’i ga ma’auratan dama sauran jama’ar musulmi baki xaya aka shafa. Ya miqe nuna alamar tafiya, Mus’ab ya yi maza ya bishi suka tafi ya mai da shi gida.
Abu ta bi bayan Saddiqa zuwa xakin da aka sauke su.
“To haka kuma abu ya kasance, wannan dattijo bawan Allah ya zo ya xaure ni da jijiyoyin jikina babu yanda zan yi in yi musu da shi, da dai na san wani yaje xaukowa ai da sammako muka yi muka tafi”.
Saddiqa tasa hannu ta share hawayen kukan da take yi. Ta kalli Abu cikin nutsuwa ta ce mata, “Dama shi kike jira, ai tunda kike cewa ya gudu don bai son ganin tafiyarmu na ce miki ba zai gudu ba wani abin yaje yi mu hanzarta tafiya kawai kika qi, kika ce mu tsaya jiran girke-girken da ba ci kike ba. Dama ni Gwaggona ta gaya min cewa babu wanda kike so a cikin jikokinki sai shi”. Ta kama kuka sosai.
Abu ta kama salati tana faxin “Ka ji ja’irar yarinya, kamun bakin da za ki yi min kenan? Yanzu a wannan zuwan da na yi me na yi na son Mus’abu? To ban fi son shi ba, gaya min yanda kike so in yi yau na ji”.
Ta juya ta fita ta je ta yi alwala ta soma gabatar da sallar walaha saboda sallamar da Idris ya ce mata ya yiwa mai motar a qara natsuwa kafin ta tafi.
Ta daxe a zaune tana addu’o’o ya yin da Saddiqa ke kwance lamo a kan shimfixarsu, sai aka leqo aka cewa Abu Idris yana son ganin ta a falo. Ta shafa fatiha ta shiga falon, maimakon Idris Mus’ab ta gani a zaune.
Yana ganinta ya yi murmushi alamar samun nutsuwa, ita kuma ta yi maza ta tsuke tata fuskar.
“Wane ne mai kiran?”
A hankali ya ce mata, “Nini Abu”.
Kan ta yi magana ya yi maza ya kai gwiwoyinshi qasa ya durqusa a kansu.
“Ki yafe min abin da na yi na laifi kike fushi dani, Abu ban saba irin wannan mu’amalar dake ba. Na yi baqin ciki tare da nadamar al’amurana da na sameki a wurin nan, da kuma na gane fushin da kika yi dani mai yawa ne sai na ji tamkar na tozarta kaina ne, na wulaqanta saboda na gane na qure haqurinki a kaina.
Sanina dake tun ina yaro duk wanda ya faxi laifina a gabanki korarshi kike yi, ki ce sharri ake yi min aniyar kowa kuma za ta bishi, in kuma iyayena ne suka faxi laifin nawa tunda su kin san ba masu yin sharri bane a gare ni, sai ki shiga yi musu faxa kina faxin wai komai qanqantar abin da na yi ba za su zauna suyi ta yi min addu’a ba, sai su rinqa taya masu neman vatani su yayata qarya a kaina. To amma wai a irin wannan haqurin naki da qaunarki a gareni na qureki, ni wane irin mutum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login