Showing 6001 words to 9000 words out of 27104 words
tsayayye kan al’amarina, na manta da cewar duk wani wanda ya tsaya min ya taimakeni ko ya soni ya yi hakan ne a dalilin ganin tsayawarka, taimakon ka da kuma soyayyar ka a gareni.
Kai ne ka tsamoni cikin halakar da na samu kaina a ciki, ka kawoni gidan nan kuka haxu kai da Inna kuka yi min gata, kuka mai dani mutum na zama cikakken xa mai cikakken ‘yanci, kuka xorani a bisa hanya ta rayuwa.
Ga shi a yau kuma ka sake yi min wani alherin na rabani da baqin cikin da ya sameni, ka ceci rayuwata daga shiga halin butulci na ganin tamkar bani da kowa, ka bani yarinyar da nake ganin tamkar ita kaxai ke gareni, in ban same ta ba kuma ba zan mallaki kaina ba, duk da kai xin ka fi kowa sanin mugayen aiyukana, ka fi kowa sanin abin da nake yi. Na roqe ka ka taimakeni ka yi min addu’a Ubangiji ya tsare min aurena da Aisha, ya kuma zaunar damu lafiya”.
Kawu Gixe ya ce mishi, “To Mus’abu zan yi maka”.
“To Kawu ka yi min addu’ar”.
Kawu Gixe ya shirya goro da minti gami da sadakin da ya biyawa Mus’ab na kuxi naira dubu uku ya tashi amininshi Malam Hadi tare da matarshi Furera da tashi matar Raliya, suka koma a cikin motar Mus’ab suka nufi Misau Adamu yana tuqa su, don suje su isar da saqon xaurin auren da ya yi tsakanin Mus’ab da Saddiqa.
Suma su Mus’ab suna ganin tafiyarsu suka bar gidan cikin motar Ishaq, su ma Misau xin suka nufa, zukatansu cike da farin ciki da annashuwa, suna tafe suna hirar Kawu Gixe da alherinshi.
GARIN MISAU
Gidan su Inna Habiba a Misau ya cika ya tumbatsa da jama’a ‘yan saka lalle, ba qaramin cika aka yi ba a gidan kasancewar Inna Habiba ta kwana biyu ba ta yi bikin ba, tun na ‘yar autar ta Hamida.
Sai dai ita kam Inna yanzu ne take faxin bikin ‘yar auta, don haka biki sosai ta shirya, ta kuma gayyaci ‘yan’uwa nesa da na kusa, ga kuma abokan arziki.
Saddiqa tana kwance a xakinta tun bayan saka lallen da aka yi mata ta kasa fahimtar halin da take ciki, ita dai kawai ta san saka lallen ya haifar mata da matsanancin baqin ciki, damuwa gami da vacin rai mai tsanani, ga shi dai ba son Mus’ab take yi ba saboda ya fita ranta kwata-kwata a dalilin munanan halayenshi da aka gaya mata na kasancewar shi fasiqi.
To amma kuma abin takaicin shine, shima Sadisun ba ta son shi shima ya fita ranta, ba ta qaunar ko sunanshi ta ji ana ambata mata. Ta fi so a barta kawai, a barta ta yi zamanta haka babu auren, shima auren ba ta son shi, in ban da kar ta yi savo ma da ta ce ta tsane shi, don daga tasowarshin ta samu kanta cikin yanayin da take ciki a yanzu na baqin ciki da qunci da tsirarar waxanda ake ganin girmansu.
Malam Abdullahi ya fito yiwa baqin shi rakiya lokacin da Adamu ya yi parking a qofar gidan cikin motar Mus’ab, da farko ya xauka Mus’ab xin ne, sai da ya ga fitowar Adamu da sauran mutanen da suke ciki nan da nan ya yi sallama da baqin nashi ya juyo tarar Malam Hadi.
“Barka da zuwa”.
Ya isa da shi xakinshi na waje. Su Baba Furera kuma suka wuce cikin gida inda su ma suka samu tarba mai gamsarwa.
Bayan sun ci sun sha an kuma gaggaisa anyi raha yaushe gamo? Inna Habiba tana tambayar Inna Raliya.
“Yanzu nan dama za ku zo amma baku iso da wuri aka yi saka lallen nan daku ba?”
Ta yi murmushi ta ce, “To ba gashi anyi ba? Ai barinki dai na yi ki yi yanda kike so, tunda ke ce uwar ke ce uban”. Mutanen dake wurin suka taya su dariyar da suke yi.
“Sallamu alaikum! Gwaggo tana ciki?”
Muryar Malam Abdullahi ne daga waje-wajen zaure saboda cikowar mutane. Da sauri Bilkisu ta iso cikin ladabi tana tambayar shi.
“Baba Abu za a kira maka?”
Ya ce, “Eh, maza kira min ita”.
Ta yi maza ta nufi xakin da Abu ke ciki tare da ‘yan tsofaffi aminanta suna hirarsu. Tana jin kiran ta yi maza ta fita ta nufi inda Malam Abdullahi ke sauraron zuwan nata.
Sai da ta gama sauraron bayanin nashi sannan ta shigo gida tana salati.
“Iko sai Ubangiji, wani baya auren matar wani. Shi aure dama ya gaji haka, koma in ce abin da ya fi haka, dama kuma an ce matar mutum kabarinsa”.
Gaba xaya wuri ya yi tsit! Ana sauraron kalaman nata.
Ta leqa falon Inna Habiba inda jama’a ke cike ta ce, “A’a, ke Furera ashe kun baiwa xanku auren shine da kuka zo baki gaya mana ba?”
Inna Habiba ta zuba musu ido tana kallo cikin yanayi na rashin fahimta da son jin bayani.
Inna Furera ta ce, “Eh, Gwaggo gani na yi mun zo da amininshi”.
Ta ce, “Haka ne ta xaga ido ta kalli taron jama’ar dake wurin, ta ce, “Jama’a aure fa ya zama a kan Mus’abu yake, don xazu da yamma Kawunshi ya xaura mishi aure da Saddiqa, ga goro nan da minti da kuma sadakinta dubu uku ya bayar ya ce a kawowa uwarta”.
Kukan da Inna Habiba ta saka shine ya taqaita farin cikin su Bilkisu da ‘yan’uwanta, gaba xaya aka taru a kan Inna Habiban ana ta faman ba ta haquri.
Baba Furera kuwa cewa take yi, “Babu wata kunya da aka baki tunda ya ce a gaya miki ki sa a xaurawa Sadisu aure da Kubra, ba shi kenan ba magana ta qare”.
Ita kuwa Saddiqa tana kwance a xakinta ta yi kasaqe tana sauraro tare da tambayar kanta me yasa Gwaggonta kuka haka a cikin taron mutanen da ta tara?
A daidai lokacin ta ji wayarta tana qara, rabon da ta ji qaarar an daxe, don haka ta miqa hannu ta xauka don ta ga waye.
Duk da ta daina amsa wayarshi sai ta yi nufin amsawa, wai ta ji me zai ce mata. Yana jin ta xauka bai jira ta ce komai ba ya soma ce mata.
“Ina miki barka tare da albishir na zama amarya ta har abada, Aisha ina tabbatar miki da cewar daga yau kin shiga amarcin da ba zai tava qarewa ba har abada, dama can ni dake abu xaya ne Aisha, za kuma mu ci gaba da zama abu xaya”.
Saddiqa ta rasa me za ta ce mishi tunda ba ta gane me yake nufi da kalaman nashi ba balle ta gane inda ya dosa.
Abin mamakin dai shine, muryarshi ba ta cikin yanayi na tashin hankalin da ya kirata a baya, ba ta san yanda aka yi ba sai kawai ta ji ta fashe mishi da kuka. Ya yi maza ya katse layin.
Qawarta da ta fita tsakar gida don wanke hannu ita ce ta shigo tana ce mata, “Na fa ji kamar ana cewa wai yau a Bauchi an xaura aurenki da Yaya Mus’abunki, shi kuma Sadisu wai an ce a bashi ‘yar’uwarki Kubra”.
“Yaya Mus’ab?”
Da qarfi Saddiqa ta yi tambayar. Nan take kuma ta sake fashewa da wani sabon kuka mai tsanani.
Su Bilkisu da ‘yan’uwanta suka yi maza suka fice daga gidan saboda ganin an samu an shawo kan mahaifiyarsu ta daina kukan da take yi. Kasancewar dare ya riga ya fara yi bai hanasu nufar gidan Mus’ab ba dake can bayan gari don su taya juna murna.
Qwayayen fitilu sun haske ko’ina na harabar gidan, tun kafin ka qaraso kuma kana jiyo sautin jama’a, ga kuma motoci a tsaitsaye a harabar gidan alamar tuni har abokanshi dake kurkusa sun fara isowa.
A haka suka qarasa shiga gidan, daga nesa suka hangoshi riqe da sigarinshi a hannu yana kuma amsa waya.
“Yaya Mus’ab ashe kuma sai zama ango?”
Ya yi murmushi ya ce, “Eh, Bilkisu abin kamar babu wuya amma mu kam ai mun san mun ji jiki, ko kuwa?”
Gaba xaya suka yi murmushi. Nan take kuma suka shiga gaishe shi da yi mishi murna a yanayi na girmamawa.
“To ya ya Inna ta karvi labarin?”
Cikin nutsuwa ya yi musu tambayar. Suka gaya mishi komai. Ya yi ajiyar zuciya a hankali ya furta kalmar.
“Ta yi haquri, ku taimake ni ku ba ta haquri, ku ba ta haquri Aisha matata ce ta yi haquri ta karvi hakan, Kawu ya riga ya bani ita, qaddara ce hakan don haka ta yi haquri”.
Sun xan fara yin magana sai ya xaga ido ya kalli Hamida a wani yanayi da ya fi kama da kunya ko nadama tare da shan mur!
“Ba ki dai gayawa mijinki abin da ya sameki a goshin ba ko?”
Ta yi maza ta sunkuyar da kanta qasa tare da jan gyalenta ta qara rufe fuskarta dake goshin nata ta yi shiru saboda jin nauyinshi.
Suna cikin zancen da suke yi Bilkisu ta ce, “Shi kenan ‘yan ina da biki, biki ya zama nasu sai ya ya kenan?”
Ya yi murmushi ya ce, “Sai ku yi sabon shiri Balki, sabon biki sabon komai”.
Su Ishaq suka shigo, Sani ya wuce kicin Ishaq ya tsaya wurinsu yana faxin “Qannen ango ne a daren nan?”
Suna gamawa gaisawa Sani ya sake shigowa cikin falon da abubuwan ci da na sha yana ajiye musu, yana yiwa Mus’ab bayani.
Ishaq ya katse shi ya ce, “Bilkisu ku fita a mai daku gida mu zamu koma Bauchi yancu zamu je musa ango a lalle, a can zamu yi hidimar bikinmu, zamu xora muku nauyin haxa mana kayan aure duk da mun san kuma hidimar taku tana da yawa, don haka mota za ta zo ta xauke ku gobe, sai ku samu Atika a Kano ku haxu ku yi sayayyar ko kuwa?” Suka amsa “To”.
Mus’ab ya miqe ya shiga xakinshi ya fito rungume da wasu lesuna ya zube, ya sake komawa ya fito riqe da akwatin matafiya ya zo ya miqa musu suka buxe suna dubawa. Sarqoqi ne masu asalin kyau haar kala uku, kowanne kuma yana haxe da wara-waran da suka dace da shi.
Mus’ab da Ishaq suka yi singing xin cek guda biyu suka miqa musu.
“Ga shi nan in kun je yin sayayyar kar ku mance da kawunanku”.
Suka sa hannu biyu suka karva tare da godiya gami da fatan alheri.
Biki sosai su Mus’ab suka yi a Bauchi, don can suka yi hidimar tasu a gidan Kawu Gixe.
Ko ita ma kuwa Inna Habiba duk da vacin ran dake cikin ranta voyewa ta yi, hidima sosai irin wacce ba ta tava yi ba, ga kuma su Bilki da suka qara qayatar da bikin ta hanyar sakar mishi kuxi sosai.
Anyi xaurin auren Kubrah da Sadisu, an kuma kaita gidan mijinta duk wani shiri da Inna Habiba ta yiwa Saddiqa ta kwashe ta bayar an kai wa Kubrah gidan Sadisu.
‘Yan biki sun watse an bar Saddiqa da Innarta a gida kamar yanda dama suke.
Suna zaune a falon Innar suna hira, akwatinan auren Mus’ab ne a gabansu suna qara dubawa.
“Ai zan yi maganinshi, wai shi ya iya shege ko? Ya za ga yaje ya kaiwa Yaya maganar shi kuma Yaya da yake bai ganin laifinshi duk da ya fi kowa sanin shi, ya xauki auren ya ba shi. To ai zan ga mai kai mishi ke, kar ki yarda zuciyarki ta karyo a kan qiyayyar da kike yi mishi, don wannan aure da Yaya ya xaura ba komai bane illa fitina, ba zamu iya shi ba don haka bake ba shi, kar ma ki yarda ki saurare shi, don ba za ki tare a gidanshi ba ma, kuma nan ina jiran randa zai shigo gidan nan titsiye shi zan yi sai ya rubuta takardar sakin auren ya bani sannan ya fita”.
Saddiqa ta kalleta cikin nutsuwa ta ce, “To amma Gwaggo kin san da haka kike ta bani kayanshi ina xaurawa? Ko jiya fa tirmi goma kika bayar a xinko min?”
“Ai ba zan mayar mishi da kayana ba har zinaran sun zo kenan ladan kukan da ya sani na yi a cikin mutanen da na tara ana kallona ina sharvar majinar baqin ciki”.
Saddiqa ta vata ido ta ce, “Dama an bar mishi kayanshi kawai Gwaggo, da wanne zai ji?”
Ta yi maza ta ce, “Kul! Na sake jin wannan maganar a bakinki, kwalliyarki za ki yi ta yi dasu”.
Da daddare misalin sha biyu da rabi Mus’ab yana kwance a xakinshi dake gidanshi na Misau, ya yi sha’awar a ce shima an kawo mishi Aishanshi kamar yanda aka yiwa Sadisu tashi matar, ina ma dai a ce a gefenshi take yana a kwance, ga shi kuma daren mai cike da iska ne mai xauke da saqon sanyi a cikin shi.
Ko sai yaushe ne haqqina da damuwa ta za su zamo abin dubawa wajen Inna? Shima Baba ya yi shiru ya zuba ido yana kallon abin da ake yi min xin bai tanka ba.
Ya xan yi tsaki mara sauti, a dai-dai lokacin da ya miqa hannu ya xauko wayarshi dake gefenshi a ajiye ya soma dannaa lambobinta. Ko ba ta amsa maganar da nake yi mata ai tana jina, bari in gaya mata abin da zan gaya mata. Tunanin dake zuciyar shi kenan.
Saddiqa wacce Gwaggonta ta dawo da ita kwana a xakinta, a nan gadonta suke kwana tare tun bayan watsewar ‘yan baki, saboda tsoron da take yi na kar Mus’ab ya shigo cikin gidan ba ta sani ba.
“Xauki mana ki ji abin da zai ce miki”.
Don haka ta miqa hannu ta xauka.
“Aisha!”
Ya kira sunan a hankali cikin jan hankali da nutsuwa.
“Wai ni me yasa haqqi in nawa ne taka shi bai da wuya wurin Inna? An fi sati guda yau tunda Kawuna ya bani aurenki amma har yanzu ba a ce min ga lokacin da za a kawo ki ba, an xaura auren Kubrah da Sadisu ne bayan nawa xaurin auren, amma tuni da yake shi xan gata ne an kai mishi tashi matar.
Ki taimaka ki yiwa Inna magana mana tunda ke ‘yar lelenta ce ki gaya mata kema kina buqatar mijinki, na rantse miki zama dani zai fiye miki na zaman gidan daxi, ba zan rinqa barinki kina kwanciya a kan kafita ba kan qirjina zan rinqa shimfixe ki, kin san kuwa xuminshi ba zai tava yin daidai da na katifa ba. Zan jiyar dake daxin da baki tava xanxana ba, zan yi miki tausa da sumba….”
Ya yi maza ya katse layin saboda kukan da ta soma yi mishi.
“Uh-uhm! Abin da ya iya kenan”.
Mus’ab yana zaune gaban Abu, hira suke yi mai daxi, sai qamshi yake yi yana kuma cin dambun zogalen da Abun ta yi musu.
“Ai na zo ranar talata bakya nan Abu, za ki ce wai angwanci ya voye ni. Kuma ni wane angwanci zan yi tunda an qi a bani matata”.
Abu ta qyalqyale da dariya ta ce, “To ba dai zamanka take yi ba? Ko ba daxe ko ba jima ai za ta baka ita”.
“A’a, Abu ni kawai a bani matata babu maganar ko ba daxe ko ba jima, ni na xauka ma za ki je wajen ta maganar a bani itan”.
Ta ce, “A’a, ranar talata gidan Kubra na je saboda ‘yan’uwan mijinta sun zo nan sun kawo kaya na abin arzikin da taje musu da shi, suka ce a shaidawa iyayenta cewar ‘yarsu ta kai ‘yancinta, don haka na je don ba ta daga can kuma na je na gayawa Innarku na kuma kai mata abin da suka zo da shi”.
Mus’ab ya ce, “Kai wannan al’ada taku Abu sai yaushe za ku barta?”
“Mu barta a kan me?”
A hankali ya yi tsaki, ya ce, “Haba, abin da ya kamata ya zamo sirri tsakanin miji da mata wai sai ayi ta bi ana yayatawa, ai ni ba zan yarda ayi min irin wannan bankaxar ba”.
Ta galla mishi harara ta ce, “Eh, ai ku dama ‘ya’yan zamani ko in ce yanzu duk wani abu na al’ada dake taimakawa wajen kame mutunci da gudun abin kunya bakwa son shi, faxin budurwa ta kai budurci bankaxa ne amma neman matan banza ayi ta lalacewa dasu wannan ba bankaxa bane?”
Ya yi murmushi don ya san inda ta dosa.