Showing 3001 words to 6000 words out of 27104 words
su tsaya ayi hidimar auren Saddiqa dasu.
‘Yar’uwarku ce, hanaka aurenta da aka yi ba zai sa ku yanke zumuncin dake tsakaninku ba, tana da haqqin ku yi zumunci da ita. Kune ‘yan’uwanta da ta fi sani ta fi so, ta kuma fi shaquwa dasu, tunda ba ta da abin da take so take kuma girmamawa irin uwarku.
Raina ya yi matuqar vaci sanda Bilki ta zo min da bayanin shirin da ake yi a kan hanaka aure, na kuma yi nufin zuwa gidan naku in samu shi Malam Abdullahi tunda da yardar shi ake yin komai.
To amma da Bilki ta aiki ita Hamida gidanka don ta je ta gaya maka abin da ake ciki, saboda ka hanzarta zuwa ku tattauna ku san abin da za ku yi ta dawo. A yanayin da ta dawo na kuma kalle ta na tabbatar ba kukan fasa mata kan da ka yi take yi ba, tana kukan baqin ciki ne na yanayin da ta same ka a ciki. Sai na gane ba komai yasa iyayenku hanaka auren Saddiqa da suka yi ba illa kawai su xin mutanen kirki ne masu gaskiya da riqon amana, Ubangiji kuma zai yi musu kyakkyawan sakamako a kan zumuncinsu.
Gaskiyarsu ne, Saddiqa ba matarka ba ce, kai daban ita daban, ka fi qarfinta ba za ta iya rayuwarka ba, kowace qwarya ai da abokin burmin ta. Ka girma ne baka san ka girma ba, in an ganka a tsaye cikin sutura abin gwanin sha’awa, amma hali babu. Da girman nan naka da gwarjinin naka giya kake sha, in ka sha kuma ka yi hauka, qannen ka ma basu tsira ba, to wa zai tsira?
A wannan halin naka kuma wane mutumin kirki ne zai xauki ‘yarshi ya baka in dai ba a kan rashin sani ba, ko kuma yana kwaxayin abin hannunka?”
Wasu hawayen masu yawa suka sake zubowa daga idanun nata, dai-dai lokacin da ta xago idanuwanta ta kalli Mus’ab ta ce mishi.
“Iyayenka mutanen kirki ne, nima rashin adalci ne ya sani vacin ran abin da aka yi makan, in ban da haka ai dukanku xaya ne a wurina, kai da Saddiqa xaya kuke, ita gaskiya kuma ai guda xaya ce daga kauce mata kuma sai a shiga vata, bai kuma dace in yi hakan ba”.
Mus’ab yana zaune ya rasa yanda zai yi, ya rasa inda zai sa ranshi ya ji daxi, ga Abu da Bilki sun qi daina kukan da suke yi, ga shi nashi hawayen sun qi yarda su zubo balle su haxu su duka ukun suyi kukan.
Sai dai zuciyarshi ta kai matuqa wajen quntata, zafin da take yi ya wuce duk yanda za a yiwa kwatance, ya rasa me zai yi. A hankali ya miqa hannu ya xauki xan makullin motarshi dake ajiye kan tabarma ya miqe ya fita ba tare da ya san inda zai tafi ba.
Tuqin kawai yake yi bai san inda ya dosa ba, zuciyarshi cike da baqin ciki da nadama, da dai da hali to da ya ce daga yau ba zai sake tava barasa da hannunshi ba, saboda baqin ciki da qasqanci ga abin da kunyar da ta ja mishi, a dalilinta ya rasa yarinyar da yake ganin tamkar don shi aka haife ta Aisha saboda tsananin son da yake yi mata.
Ga kuma qasqanci da kunyar da ta ja mishi wurin ‘yar qanqanuwar qanwar shi ‘yar autan xakinsu Hamida, wacce ya tabbatar kafin zuwan nata gidanshi ta same shi a halin da ta same shi ba za ta gaskata komai game da labarin da take ji a kanshi ba, da wuya ma ta saurari irin waxannan maganganun saboda tsananin girmamawar da take yi mishi.
To wai ya fasa mata goshi da kwalbar giya ya yi mata rotse saboda wai ya bugu, wace irin giya ce wannan? To wai tunda yake shan barasa ma shi wane alheri ta tava haifar mishi ne in ban da sharri. Ya yi nisa cikin tunanin sharrin barasa.
Sai kuma ya ji wata zuciyar tana ce mishi, babu ruwan barasa, ba ma laifinta bane, gata ne kawai ba shi da shi, rashin tsayayye a kan al’amari ne kawai ya ja mishi, da yana da tsayayye da ba a jefa shi ba ma cikin damuwa da vacin ran da zai samu kanshi cikin wannan halin ba. Inna ce ta rasu ba ta nan ne, da tana raye da ban ma samu kaina a irin wannan yanayin ba.
Kalaman da suka rinqa kai kawo a zuciyarshi kenan, bai kuma ankara ba saia ganin shi kawai ya yi yana shiga cikin unguwarsu ta Tudun Alqali dake cikin garin Bauchi.
Ya yi parkinga a qofar gidansu wanda a yanzu ya mai da shi ginin zamani saboda rushe tsohon ginin da ya yi ya yi sabo. Kawu Gixe yana zaune cikin falon shi ya yi sallama ya shiga ya tsuguna.
Da sauri Kawu Gixe ya soma tambayar shi.
“Me ya same ka Mus’abu? Me ya sameka kake wannan baqin cikin?”
Mus’ab ya matse idonshi hawayen da suka taru suka xiga, abin da ya yi dalilin miqewar Kawu Gixe tsaye saboda tashin hankali.
“Me ya sameka?”
Ya sake yi mishi tambayar bayan ya kafa idanuwanshi a kanshi.
“Maraici ne kawai ya dame ni Kawu, tunda Inna ta rasu ta barni na koma watangaririya a tsakanin mutane, bani da wani tsayayye a kan al’amarina, rashinta yasa na samu kaina cikin baqin ciki da vacin rai, da tana raye da ban samu kaina cikin qasqancin da nake ciki ba a yau. Bani da uwa bani da mai tausayina balle ta rufa min asiri, bani da kowa, bani da inda za ni in faxi damuwata.
Shi yasa na zo gabanka in yi kuka don ka qara sanin har abada ba zan daina kukan mutuwar Inna ba, inda tana raye a duniya da babu mai yi min irin tonon asirin da aka yi min a Misau, an taro an nuna min fin qarfi an hanani auren Aisha saboda wai ni xin mashayi ne, da tana nan a raye Kawu da tasa an bani auren duk da ita xin ta fi kowa sanin mugun halayena, da ba za ta hanani auren ba, saboda ta san rabani da ita zai iya haddasa min vacin rai na samu kaina a yau cikin baqin ciki da qunci da ciwon zuciya, amma wai a hakan Abu ta sani a gaba tana yiwa waxanda suka hanani auren addu’ar Ubangiji ya saka musu da alheri, don wai gaskiya da adalcin sune yasa suka hanani auren da suka yi”.
Kawu Gixe ya koma kan kujerar shi ya zauna ya zubuawa Mus’ab ido, cikin nutsuwa ya tambaye shi.
“Dama kai kana son Saddiqa ne baka yi magana ba?”
Ya ce, “Eh, Kawu hanani yin maganar aka yi ta hanyar tsoratar dani wai idan na ce ina sonta za a gaya mata halina, to ga shi ban tsira ba, abin da na guda shine ya sameni. Inna ce jagorar rabani da Aisha, su Baba da su Abu suka mara mata baya. Ni ban ma qara sanin da hannun Abu a ciki ba sai da na jita ta dage tana ta yi musu addu……”
“Kai tafi can ka rufe min baki, kai ka jawa kanka komai, yanzu ka zo kana wannan surutun da in ba sa a ba zai tashi a shirme da surutu, bayani nake so na yanda aka yi hakan”.
Mus’ab ya shiga yi mishi bayani dalla-dalla tun farkon yanda ya faro maganar a gaban Abu, har kawo lokacin da Innarshi ta yiwa Saddiqa bayanin komai, al’amuran da suka biyo bayan hakan da suka yi dalilin bikin gaggawa da suka tayar, har rotsen da ya yiwa Hamida da ya zama hujjar Abu ta fita cikin lamarinshi, da addu’ar da take yiwa iyayenshi bai voye komai ba.
Kawu Gixe ya sunkuyar da kai qasa cikin tunanin mafita. Mus’ab ya yi matuqar razana, don tunanin ko shima zai yi fushi da shi ne. nan da nan ya shiga ba shi haquri yana magiya.
“Ka taimakeni kasa baki cikin lamarin Kawu ka hana su xaurin auren da suke shirin yi jibi, ka tura shi zuwa wani lokaci dan in samu damar da zan ga Aisha in san yanda na yi-na yi mata bayanin da za ta fahimceni, zan gaya mata irin son da nake yi mata, zan yi qoqari in fahimtar da ita al’amura masu yawa da ke tsakanina da ita a baya, ban samu damar gaya mata abin da ya kamata in gaya mata ba saboda ina tsoron kar a tona min asiri a wurinta, to yanzu kuma tsoron ya qare zan nuna mata……”
“Kai rufe min baki mashirmancin banza!”
Kawu Gixe ya yi maganar a yanayi na vacin rai. Ya yi maza ya ja bakinshi ya yi shiru.
“Kira min Malam Hadi”.
Ya tashi cikin nutsuwa ya fita don cika umarnin da Kawun ya ba shi, ya nufi unguwar Railway don isar da saqon.
Malam Hadi shine amini na qut da qut a wurin Kawu Gixe. Bai yi qasa a gwiwa ba ya biyo shi suka taho tare, ya wuce cikin gida ya barsu nan suna tattaunawa.
Mus’ab yana zaune a wani xaki da ya barwa kanshi a cikin gidan, wanda yake ganin tamkar shine a gurbin na Innarshi da ta rayu a ciki, inda tana nan da ita ce za ta bani Aisha, ba tare da ta damu da cewar ni xin mashayi ne ko manemin mata ba, inda tana nan ma wataqila da ban samu kaina a wannan halin da nake ciki ba.
Ya xan yi ajiyar zuciya kafin ya sake ya sake tsunduma cikin tunanin rayuwarshi a gaban Innar tashi, yanda ya zo mata da yanda ta tafi ta barshi.
“Wayyo Inna!”
Ya yi shiru zuwa wani lokaci kafin daga bisani ya shiga gabatar mata da addu’o’i, tsawon lokaci yana cikin wannan yanayin kafin ya koma kan tunanin Aisha da kalamanta na ba ita ba shi, bayan kuma sun yiwa juna alqawarin kasancewa tare, sai da taimekon shi kan maganar neman auren shi, sai ga shi da abin ya bayyana a kana ta bijire mishi, saboda an gaya mata halayenshi.
Sannu a hankali ya sake tambayar kanshi.
“Ko meye alherin barasa? Ko ya ya zai yi ya daina shanta? Anya in har ya rasa auren Aisha zai iya daina shan barasa a rayuwarshi? Ina ma dai a ce duk mutanen duniya irin Innarshi ne masu qoqarin taimakon mutum, gyara halinshi da mugayen xabi’unshi ta hanyar janshi a ciki, taimakon shi ta hanyar qarfafawa, mutunta shi da nuna mishi munin abin da yake yin a nutse, maimakon a qyamace shi ko a guje shi”.
Kawu Gixe suna tare da amininshi Malam Hadi, kusan minti talatin suna tattaunawa kan hanyar da za su bi su fitowa lamarin. Daga qarshe suka yankewa kansu abin da ya dace suyi, wanda ya sanya Kawu Gixe cikin sauri ya shiga cikin gida ya kira babban xanshi Adamu ya aike shi cikin motar Mus’ab ya zo da ita.
Sani da Ishaq suka iso falon Kawu Gixe cikin ladabi suka gaishe shi.
“Kawu mun zo wajenka neman taimako ka sanya baki cikin maganar auren da ake shirin xaurawa Saddiqa a Misau jibi”.
Ya kalle su ya ce, “Yau ne ya kamata ku sanar dani?”
Sani ya gyara zama cikin nutsuwa ya ce, “Kawu ka yi haquri, muma yau ne da muka bi bayan Mus’ab zuwa gidan Abu muka ji cewar jibin za a xaura aure, mun kuma nemi Mus’ab a waya ya rufe, Abu kuma ta gaya mana cewar ta gaya mishi komai, bai kuma ce mata ga inda za shi ba don haka muka ce bari mu zo gabanka mu roqi wannan alfarmar, don mun san duk inda yake in ya samu labarin an xaga xin zai samu sassauci”.
Malam Hadi ya shigo tare da wasu dattawa su uku, don haka su Sani suka ja gefe suka takure suna jiran su gama abin da suke yi kafin su sake matsawa gaban Kawu Gixe su qara roqon shi ya yi wani abu kan al’amarin.
Suna zaman jiran sai ga Adamu ya shigo da manyan qunshin goro guda biyu.
“To ai ma shi kenan mun isa Allah gafarta malam ko kuwa?”
Kawu Gixe ne ya yi tambayar.
Malamin dake zaune a gefenshi cikin rawani ya ce mishi, “Eh, mun isa ai shaidu ma su kan gamsar wajen xuarin aure, balle mu a nan mu shida ne”.
Da sauri Malam Hadi ya ce, “Ai ga su Malam Isa ma sun dawo”.
Ya yi maza ya leqa ya kirasu suka shigo, su ma su uku. Nan take Kawu Gixe yasa aka xaura auren Mus’ab da Aishatu, abin da ya yi matuqar baiwa Sani da Ishaq mamaki.
An gama xaurin aure an raba goro, jama’a suna watse kowa ya nufi gidanshi, Sani da Ishaq suna durqushe gaban Kawu Gixe sun rasa kalmar da za suyi amfani da ita wajen yi mishi godiya. Sai ga Mus’ab xin ya shigo saboda kiran da Kawu Gixe yasa aka yi mishi.
“Ku gama kafin in fito”.
Kalmar da Mus’ab ya riska kenan na maganar Kawu Gixe. Ya kuma kalli Mus’ab xin bayan ya nuna su Sani da hannunshi.
“Ga masu neman ka can”.
Ya wuce ya yi tafiyarshi. Ishaq ya qanqame Mus’ab a yanayi na tsananin farin ciki.
“Na rantse yau ne na tabbatar da kalmar da Hausawa ke furtawa ta ABU NAKA…. Wai maganin a kwaveka. Kawu Gixe ya xaura auren ka Mus’ab”.
Mus’ab yasa hannu biyu ya hankaxe shi.
“Kai bana son irin zolayar da kuke yi min yau? Haka Sani ya ce min wai sun sato Aisha ashe qarya yake yi min, zuciyata a quntace take ina cikin wani al’amari da ban san shi ba……..”
Kan ya qarasa maganar tashi Ishaq ya yi mishi rantsuwa.
“Yanzun nan muka gama xaurin auren ka Mus’ab, Kawu Gixe ya baka auren, ga goro ga minti ga takardunsu kana kallo”.
Sai a lokacin ne hankalinshi ya kai garesu, gabanshi ya yanke ya faxi, cikin fargaba da tsoro kar dai shima Kawu Gixen irin auren da Abu take so ta yi ya yi mishi, auren huce fushi.
Hannu ya xora kan qirjinshi saboda harbawar da takeyi.
“Kawu Gixe ya xaura min aure?”
Da qyar ya iya buxe baki ya sake tambayar su.
“To wa ya bani?”
Sani yana murmushi ya ce, “Saddiqa”.
Mus’ab ya kalle shi haushin zolayar da suke yi mishi ya qara kama shi, me suke nufi dani waxannan? Basa tausayina ne? Ko so suke su mai dani tamkar mahaukaci? Ya juya ya fita wajen Kawu Gixen ya tafi.
“Ka taimakeni Kawu kar ka bani auren da ba shi nake so ba, Aisha kaxai nake so in ba ita ba ce gara a barni haka kar a xora min nauyin kowa a kaina, a barni kawai in yi zamana a haka”.
Kawu Gixe ya zuba mishi ido.
“Me abokan naka suka gaya maka?”
Ya buqaci sani.
“Kawu rabu dasu, su basa tausayina zolayata suke yi. Sun ce min wai da Aisha ka xaura min auren, amma na san qarya suke yi so kawai suke yi wai su ga na samu nutsuwa, bayan kuma baqin ciki ya sameni”.
Cikin nutsuwa Kawu Gixen ya ce mishi, “Ita na baka Mus’abu, da ita na xaura maka aure, ai taka ce. ABU NAKA…. Maganin a kwave ka. Gaskiya ne da ka ce inda uwarku tana raye za ta baka ita ba tare da ta xaga ido ta yi duba kan irin laifuffukanka ba, ba ta nan, to ni ina nan, nima kuma ba zan iya barinsu su rabaka da ita ba. Don haka a zaman da kake yi a yanzu Aisha matarka ce, na baka ita ta hanyar xaura auren sunna a tsakaninku, mallakinka ce tana qarqashin hukuncinka, yanda ka so haka za ka yi da ita a yau”.
Mus’ab ya sunkuyar da kai a gaban Kawu Gixe tsawon lokaci bai ita ce mishi komai ba. Sai Kawu Gixen ne yake magana mafi yawancin nasiha shan giya da neman mata.
“Manyan musibu ne Mus’abu, aiyukan savo ne masu girma, kai ka sani irin waxannan aiyukan kuma xabi’u ne na mutanen banza, mutanen da basa tsoron Ubangiji, kai ba mutumin banza bane, domin mutanen kirki ne suka haifeka, iyayenka mutanen kirki ne, ka fita cikin wannan rayuwar ko kaxan ba ta dace da kai ba, ba kuma ina yi maka wannan maganar bane a yau wai ko saboda Aisha ta zama matarka, a’a, sai dai don a zuciyata ina burin ganin ka zama cikakken mutumin kirki ba mai yawan cuxanya da zunubai ba”.
Cikin ladabi Mus’ab ya ce mishi, “Na sani Kawu, na roqeka ka yafe min rashin kawo maganar da ban yi ba tun farko na rinqa ganin kamar bani da wani