Showing 9001 words to 12000 words out of 27104 words

Chapter 4 - ABU NAKA Book 2 Writing by SODANGI.txt

02 Dec 2024

1273

“Abu kenan, mai da wuqar ni yanzu zuwa na yi in roqeki ki taimakeni ki sa baki a bani tawa matar nima”.
Ta ce, “To zuwa yamma zan je gidan in ji abin da suke ciki”.
Abu tana zaune a falon Inna Habiba suna gaisawa, Saddiqa ta fito daga can cikin xakin ta sha kwalliya cikin sabbin kayan aurenta, ga zinare ya kama jijkinta, duk da ba a kaita gidan miji ba sheqe take yi saboda qarin kulawar da ta samu.
Abu ta harareta ta ce, “Uu-uhm! Ita kuma wannan amaryar a gidansu take kwalliyar amarcin? To wai me ya hana a kai Saddiqa gidan mijinta ne?”
Ta zubawa Inna Habiba ido tana kallon ta tare da sauraron amsar tambayar tata.
“Kin san dai baki da ikon riqe mishi mata a wannan lokacin, matarshi ce in dai ba so kike ki shiga alhakinsu ba”.
“Alhakinsu Inna?”
Ta yi tambayar cikin wani yanayi. Abu ta ce, “Eh mana, alhakinsu su duka, an ce miki ita ba ta son mijinta ne? Ko yaushe rabon da ki ganta tana kuka? Wannan kyau da sheqin da take yi an ce miki na zannuwa da zinaran da kike ba ta tana xaurawa ne? Basu bane kwanciyar hankali ta samu a dalilin an ba ta mijin da take so, da kin ba ta shima da yanzu ta fi haka, don da ta fi haka samun nutsuwa a wurinshi. In kuma kina jira ne sai ta sulale ta je ta same shi kin yi abin kunyar da gaske to”.
Saddiqa ta sawa Abu kuka cikin yanayin shagwava ta ce, “Ni bana so, bana so Abu, bana so”. Ta soma kuka har tana shure-shure.
Abu ta gallla mata harara tare da faxin,
Tafi can munafuka”.
Ta kalli Inna Habiba ta ba ta umarnin cewa, “Ki hanzarta xaukar yarinyar nan ki kaita gidan mijinta tun bamu kai ga vacin rai ba”.
A nutse cikin ladabi ta ce mata, “To Inna, to ko za ki turo min shine ya zo mu san abin da muke ciki, kin san fa duk xan tanadin nawa na kwashe na kai wa Kubrah, kuma tunda aka yi xaurin auren fa bai leqo gidan nan ba, ina ce ya dace ya zo?”
Ta ce, To bari zan turo shi tunda kuna son ganin shi”. Ta tashi ta fita ta nufi gidanta.
Mus’ab ya yi murmushin jin bayanin da Abu ta yi mishi, ai bai kamata in fiki saninta ba Abu, so take in ji gabanta ta tilastani sakin aurena, tana shawara dani ne balle aa kan wannan auren da ta riga ta qi? Bana son shirin a bani matata kawai, ai ko wani za ta aura ni mai yi mata komai ne balle kuma ta zama tawa”.
Abu ta yi kasaqe cikin yanayi na gaskata kalaman nashi, a hankali ta ce, “To kan wannan kam ai ka fini sanin nata, ina na yi wannan tunanin. Wato iya shege nima za ta yi min? To tashi ka tafi ka bar mata ita mu gani ko za ta yi ta riqe ta da auren naka a kanta”.
Mus’ab yana kwance a falonshi, sigarinshi yake zuqa yana kuma tunanin rabonshi da wurin aikinshi.
Lokacin da ya ji wayarshi ta yi qara yasa hannu ya xauka, lambobin Saddiqa ne. Ya xauka ya kai kunnen shi.
“Ran amarya ya daxe, yau kin yi sha’awar jin muryata ne kika bugo min waya?”
Shiru ta yi ta kasa amsawa. Ya ce, “In ce ko dai lafiya?” Ta sake yin shiru. Ya ce, “Ko ina son ganina ne?”
Da qyar ta iya buxa baki ta ce mishi, “Eh, ka zo”.
“In zo?”
Ya tambaye ta.
Ta ce, “Eh”.
“Kina son ganina?”
Ya sake tambayar.
Ta ce mishi, “Eh”.
Ya saki lallausan murmushi saboda abin da zuciyarshi ta raya mishi.
“To ki gayawa Inna zan turo direba ya xauke ki”.
Da sauri ta ce mishi, “A’a, kai ka zo”.
“To shi kenan ki fito mu haxu a gidan Abu”.
Ta yi maza ta ce, “A’a, sai dai ka zo nan gidan”.
Ya ce, “A’a, Aisha in zo wurinki kina cikin gidanku ai ba zan iya ba, wai ba ki san ko ban yi surukuta da kowa ba dole in yi da Inna, ai in ba ita ce ta ce ki kira mata ni ba a yanzu babu abin da zai sa in shigo muku gidanku saboda kunya da girmamawa irin ta surukuta”.
Da sauri Saddiqa ta ce, “Ai ita xin ce ta ce in yi kiranka”.
Ya ce, “A’a, ban yarda ba wayo kawai kike son yi min”.
Ta kama rantsuwa ta ce, “Ita ce ta ce na kira ka amma kar in ce in jita ne in ce in jini wai za ka fi saurin zuwa”.
Ya ce, “Naqi yarda da wannan maganar taki, saboda a bakinki na saba jin kina cewa, wai maganar fari ita sarki yake karva, don haka sai anjima”.
Ya ajiye wayar cikin nazarin abin yi tunda ya gane Innarshi ta matsu tana son ganinshi. Nan take ya qara sanin akwai abin da take shiryawa a kanshi.
Yana zaune cikin ladabi a gaban Kawu Gixe bayan ya gama mayar mishi da bayanin halin da ake ciki.
“To kai me ya hanaka zuwa ka ji kiran da take yi makan?”
“Tsoro nake Kawu kar in je ta bani umarnin da zan kasa cika mata, har yanzu auren bai kwanta mata ba, sai nake ganin kamar so take in je ta titsiyeni ta tilastani yin abin da ba zai yi min daxi ba a kan auren”.
Kawu Gixe ya xan yi shiru zuwa wani lokaci kaxan kafin ya dawo da nutsuwarshi gare shi.
“To wai kai me ma ya zaunar da kai ne? Ka baro wurin aikinka kusan sati uku tuni abokanka sun koma kai kana zaune kana zirga-zirga a hanya, ka kama hanya ka yi tafiyarka ka koma wurin aikinka”.
Mus’ab ya sake kallon shi cikin ladabi ya ce, “To Kawu Aishan fa?”
“Ka yi tafiyarka ka barta mana ba taka ba ce? Ko za ta sake xaura mata wani auren ne a kan naka? Tunda zamanta da ita bai isheta ba ta je ta yi ta yi, kana can wurin aikinka ma in ka yi haquri za ka ga ta turo maka ita, ai matarka ce”.
Mus’ab ya yi kamar ya ce ba za ta turo ba Kawu. Sai kuma ya haqura ya amsa umarnin da yake ba shi na kar ya yarda ko aike ya ji shi yana yi musu.
Ya ce, “To”. Ya yi mishi sallama ya fita, maimakon ya nufi Ajakuta sai ya koma Misau don yin shirin tafiya Ajakuta.
Mus’ab yana zaune gaban Abu suna magana kan tafiyar da zai yin, ya fiddo kuxin da ya sunne cikin babbar rigar shi ya ajiye a gefen Abun.
“Ki kaiwa Inna”.
Ta kalli tudun kuxin kafin ta mai da kallon nata gare shi ta ce, “Ba ka ce Kawun ka ya hanaka yi musu aike ba?”
Bai amsa ba. Ta buxe ledar da kuxin ke ciki ta ce, “To na mene ne, me za ta yi da shi? Ko kuwa na sayayyar ne?”
“Bana son sayayya Abu, ki kai mata ki kuma ba ta haquri kan rashin zuwana, na roqeta ta yafe min”.
Tausayinshi ya kamata. Ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ubangiji ya yi maka albarka, ya rufa maka asiri ya kuma azurtaku kai da ita da samun zuriya xayyaba”.
Daxi ya kama Mus’ab, sai dai bai ya cewa komai ba, sai a zuciyarshi ne ya amsa amin xin. Ya sake miqa mata wasu.
“Na waye su kuma?”
Ya ce, “Naki ne Abu, ki sha fura”.
Ta yi murmushi ta ce, “Har da zuma da kaji. To ina na baban ka?”
“Sai da na je wajen shi a kasuwa kafin na zo nan”.
Ta ce, “To madalla”. Ta shiga qara yi mishi addu’o’in da ta saba yana cewa “Amin”.
Ta biyo shi don rakiya tana cewa, “To baka faxi yaushe zamu sa rai da kai ba”.
Ya ce, “Abu kenan, mata fa zan tafi in bari ai kema kin san ba wani daxewa zan yi ba”.
“To ba Kawunka ya ce ka tafi ka mance dasu ba?”
Ya yi murmushi ya ce, “To zan iya ne?’

MUS’AB YA ISA AJAKUTA
Mus’ab ya koma Ajakuta, bayan komawar Sani da daxewa, don haka tuni labarin yin auren nashi ya bazu a ko’ina. Tarba mai yawa da girmamawa ya samu a wurin abokan harkoki daban-daban, abokan arziki na wurin aiki, da na sha’anin gari sun shirya mishi liyafar taya shi murnar auren nashi. Su ma abokan bariki ba a barsu a baya ba, sunyi mishi irin nasu shirin.
Kwananshi uku da komawa Jennifer ta isa gidan nashi a dalilin labarin dawowar shi da ta ji.
“Oh Darling!”
Ya faxi hakan dai-dai lokacin da suka haxa ido. Ta qara xaure fuska sosai nuna alamar ba wasa ya kaita ba.
“Kar ka sake Darling ya fita daga bakinka, kar kaa nemi ka mai dani qaramar yarinya, maciyin amana kawai”.
Ta ja tsaki ta sake galla mishi harara kafin ta ce, “Wai ka yi aure? Imgine. Uh-uhm! Ko wace ‘yar iskar ka samu ka aura?”
Mus’ab ya kalleta cikin murmushi da nutsuwa ya ce mata, “Ba ‘yar iska ba ce, Jennifer da za iya auren ‘yar iska ai da ke na aura. Yarinya ce mai asali da tarbiya wacce mutunci, zumunci da kawaici irin na iyayenmu yasa na sameta, in ban da haka da iya shegen da kuka koya min a bariki yasa na rasata.
To sai na yi sa’a iyayenmu mutanen kirki ne, zumuncinsu ya kan fiye musu komai, shi yasa na sameta. Yarinya ce ‘yar qarama, don ba ta fi sha bakwai ba”.
Ta ja tsaki ta ce, “Mai abin kunya, kai kuma irin lalacewar da ta same ka kenan bin yara ‘yan qanana sa’o’in ‘ya’yan cikinka? Ina tausayin wannan yarinyar da ka je ka baiwa ubanta kuxi ya baka ita”.
Ya yi kamar maganar tata ba ta soke shi ba, ya daure ya haxiye sai ya ce mata, “To, quruciya ai ba qarya bane Jennifer, in ka bi mai ita kuma baka yi laifi ba, ba ga shi nima kin manne min ba, ni ina bin wasu ne ai kema kina bina kina dangwala tunda ni dai na san ni ba sa’anki bane kin girmeni”.
A fusace qwarai ta ce mishi, “Haihuwar ka na yi ba girma ba”.
Sani dake gefe yana jinsu ya yi qoqarin danne dariyarshi, ya yin da Mus’ab ya ci gaba da magana.
“Ai ya riga ya bayyana kin san in ya riga ya zo shaf-shaf bai voye shi”.
Ta ce, “Eh, ai na ce kai na haifa”.
“A’a, ni kam ai kin yi kaxan ko in ce baki isa ba, ni ai masu mutunci ne suka haifan, gamuwa daku ne ya yi sanadin da na zama haka. Amma mai shekaru irin nawa dai kam talatin da biyar na san ba za ki rasa shi ba a qauye an barwa iyaye”.
“Kai Mus’ab wai meye haka ne? Ina laifin Jennifer da ta zo gidan nan ta nuna kishinta kan auren da ka yi, ai qauna ce ta kawo hakan. Maimakon kawai ka ba ta haquri ka yi mata alqawarin auren naka ba zai kawo qarshen mu’amalar dake tsakaninku ba?”
Ta yi maza ta ce, “Qyale shi kawai Sani, laifina ne da na zo gidanshi, ba ya yi aure ba? Ai gara ya wulaqantani, ni dai na san auren shirme ya yi don babu inda zai je, biki ne kawai don ba za ka tava daina neman mata ba ya riga ya zama jinin jikinka haka za ka mutu”.
“A’a-a’a!”
Sani ya tsoma baki.
“Ke Jennifer…..”
Kafin ya yi magana sai Mus’ab ya ce mata, “Eh, na ji ba zan daina neman mata ba, to amma ai zan iya daina neman tsofaffi ko in koma neman yara sa’o’in matata, ai na samu ci gaba idan na yi hakan”.
Mus’ab ya ci gaba da harkokinshi na sharholiya kamar yanda dama ya saba. ‘Yammata sai wacce ya zava, ita kanta Jennifer da suka yiwa juna cin mutunci sun sake shiryawa, suka mannewa juna har ta dawo gidaan shi da kwana. Sai dai hakan bai hana shi yin wasu ‘yammatan baa, sai dai baya kawo su gida ya kan yi harkokinshi ne in ya fita yawon shi na qa’ida.
A garin Misau kuwa, fiye da wata guda ne da tafiyar Mus’ab ko waya baya yiwa Saddiqa balle wani aike.
Inna Habiba ta rasa inda za ta vullowa al’amarin.
“An xauki auren yarinya an ba shi ya tafi ya yi banza da ita, rabon da ya xauke qafa zuwa gida haka ai an daxe. To ya samu yanda yake so an damqa mishi auren da bai san darajarshi ba, shi yasaa na yi ta fatan ya zo gabana in titsiyeshi ya saki auren don kar ya tafi ya barta da auren shi a kanta hakan bai yiwo ba, ba kuma wani ne yaja min wannan vacin ran ba illa Yaya Gixe, ya kuma zuba ido yana kallo ba zai neme shi don a sana bin da ake ciki ba, babu kuma wanda ya san ranar dawowar shi”.
“Assalamu alaikum”.
Muryar da ta yi sallama daga cikin zauren ita ce ta yi dalilin katsewar tunanin zucin nata tare da haifar mata da faxuwar gaba.
Cikin nutsuwa ta kalli Saddiqa da suke zaune tare tana zanen lallenta, ta ce, “Kamar muryar Yaaya Gixe?”
Da sauri Saddiqa ta miqe ta fita, ta dawo ta ce, “Ai kuwa dai shine Gwaggo”.
Ta yi maza ta shuri tabarma ta nufi zauren don yi mishi shimfixa tana faxin “Yaya sannu da zuwa”. Sai ga Abu ta shigo da xan qunshinta a hannu.
Inna Habiba tana gaisheta tana kallon qunshin nata. Ta wuce ta barsu tare da xan’waunta.
“Yanzu nan Habiba har yanzu zaman yarinyar nan a gabanki bai isheki ba, kwana wajen arba’in da tafiyar yaron nan amma baki yi tunanin bari ki tura mishi matarshi ba?”
“Bai fa damu da auren ba Yaya, don bai san darajarshi ba, dama duk kai kawon da yake yi na a bashin ne kawai, amma tunda aka ba shi ya sake nuna damuwarshi a kanta ne? Sau nawa ina cewa ya zo ya qi?”
“Ai ya san halinki ne, ya san in ya zo gabanki ba za ki yi mishi adalci ba. Yanzu zuwa na yi ki gaya min me kike ciki?”
“To yanzu dai ina wani adashi ne nake son in xauka sai in yi mata tata sayayyar”.
“To gaskiya sai dai in kin xaukan ki aike musu da abin da za ki aike musu, amma yau za ta kwana gidan Mus’abu da yardar Ubangiji”.
Kafin ta san abin da za ta ce mishi sai ga mota peogeout ta yi parking a qofar gidan. Adamu ya fito daga ciki alamar shi ya zo da direban.
“Shiga ki fito da ita ga mota nan da na tura Adamu ya yiwo shatarta don ta kai su ita da Inna ta yi mata rakiya”.
Nan take ta soma kuka tana faxin “Wannan haxi da ka yi fa bai haxu ba, kai ma ka san wannan yaron kama fi kowa sanin shi, ka kuma fi kowa sanin bai bar komai ba cikin halayenshi sai ma abin da ya qaru kan abin da ka sani”.
“Ni ban san wani hali nashi ba ke kika snai, ki ba da matarshi a kai mishi kawai”.
Ta ce, “To gaskiya a bari ya zo nan tukunna don a sa shi yaje ya yi irin gwajin nan da ake yi na zamani a tabbatar da lafiyar shi”.
Kawu Gixe ya miqe tsaye yaa ce, “Haba Habiba kar ki vata min rai mana, kina kallo mutane suna tsaye suna jira, wurin nan kuma ba nan kusa bane”.
Inna Habiba ta shiga cikin gida, Saddiqa da take zaune tana adon lallentaa ba ta san me ke faruwa ba, ta ga Gwaggonta tana kuka, ta yi maza ta ture abin lallen ta shiga tambayarta menene ya faru Gwaggo?
Abu ta ce, “To in kina da abin da za ki yi gaya mata”.
“Fitina ce kawai Yaya yake nema ya jefamu a ciki ya kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login