Showing 12001 words to 15000 words out of 27104 words
zama xan kallo in ta same mu, ban tava ganin…..”
Abu ta yi maza ta katseta ta hanyar jawo qaton zaninta mai girman yadi uku dake rataye ta lulluvawa Saddiqa ta kama hannunta tana ja ta yi waje da ita.
Kawu Gixe dake tsaye yana jiran fitowarsu yana ganinsu ya sanya su cikin motar, ya kuma sallami direban suka kama hanyar tafiya suka tafi.
Kusan awa uku da soma tafiyar tasu Saddiqa ba ta daina kuka ba, tun kukan bai damu Abu ba tana goga goronta tana watsawa a baki tana taunawa cikin nishaxi, har dai abin ya gundureta ta shiga yi mata faxa, har ta gaji da faxan ba ta daina kukan ba, sai kuma ta shiga rarrashinta.
Babu abin da ya fi komai vatawa Saddiqa rai irin ranar xaurin aurenta aka sa Gwaggonta kuka, yau ma da za a kaita gidan miji akaa fito da ita aka barta tana kuka. To ita kuwa wane daxi auren Yaya Mus’ab zai yi mata?
Abu ta shiga hira da direban motar.
“Kai wannan gari da nisa yake”.
Ya ce, “Eh, Baba ai Nigeria qasa ce mai faxin gaske, ga albarka da Ubangiji ya zuba a cikinta na arzikin qasa, illa iyaka dai bamu yi dacen shugabanni masu tausayin talakawansu ba”.
Abu ta ce, “Shugabannin yanzu kam ai sai sha’ani, tausayin talakawa sai su Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, su kam duk abin da suka yi don talaka suka yi shi, Ubangiji ya gafarta musu”.
Direba ya ce, “Amin Baba”.
Suna cikin hirar ta waiwaya wai ta ga halin da Saddiqa ke ciki don ta ji ta yi shiru, sai kawai ta ga bacci ya xauke ta. Ta cewa direban “Tunda wannan ta yi bacci, to bari nima in tava, in lokacin sallah ya yi dai sai ka tsaya muyi”. Ya ce, “To”.
Wajen sha xaya da rabi na dare suka shiga garin Ajakuta, a lokacin nan daga Abu tsohuwa har Saddiqa mai quruciyar babu wanda bai galabaita ba.
Kasancewar direban tsohon direba da ya saba zuwa Ajakuta, basu wahala ba wajen neman unguwa da gidan da Mus’ab yake ba, saboda gamsasshen kwatance da kuma kajin da Kawu Gixe ya ba shi.
Suna tsaye a qofar gidan dai-dai lokacin da Abu ke magana kan hadarin da ya taso.
“Nan ne Baba, ina ganin ga gidan can”.
Ta bi can xin da kallo tare da faxin, “To ai gara ka je ka qwanqwasa musu qofar tun ruwan nan bai sauko ya tsinke ba”.
Ya ce, “To”.
Ya fita daga cikin motar riqe da katin a hannunshi don qara tantancewa. Sai da ya qara tabbatar da lambon sannan ya shiga qwanqwasa gidan har aka fito, sai dai savanin yanda ya yi zato maimakon ganin namiji tunda a hirar da suka yi da Abu ta gaya mishi jikanta ne da ya tsufa bai yi aure ba yau za ta kai mishi matarshi.
Mace ya gani a tsaye cikin shigar mutanen garin.
“To, bana jin Turanci, amma bari in kira su ko su suna ji ku yi dasu”.
Ya gayawa matar da ta fito xin bai kuma tsaya ba ya juya ya nufo wurin su. Abu ita kuma ta bishi da kallo ba tare da ta san abin da ya gaya mata ba.
Ya isa jikin motar dai-dai lokacin da iska ta taso mai haxe da ruwan sama da feshi a ciki.
“Ai sai ku fito”.
Su Abu suk biyo bayanshi har suka haura barandar gidan tana tsaye tana kallon su.
“Ke Saddiqa yi mata Turanci ki tambayeta ina yake?”
Abu ce mai wannan umarnin. Saddiqa ta ji kamar ba ta ji ba, cikin zuciyarta tana tunanin maganar Gwaggo, ta tabbagar manemin mata ne na qarshe, ina jiye miki ranar da za ki ganshi da wata!’
Kalmar Gwaggonta ta tuna. Nan take wasu sabbin hawayen suka soma zubo mata.
Abu ta gaji da jiran Saddiqa ta yiwa Jennifer magana ta juya ta kalleta ta soma yi mata magana tare da kwatancen Mus’abu muke nema, nice kakarshi Abu. Ta nuna qirjinta da hannunta, kafin ta nuna Saddiqa ta ce, “Wannan kuma matarsa ce, an ce nan ne gidanshi, ina yaje na ganki a ciki?’
Ko da Jennifer ba ta jin Hausa ta gane wannan matsanancin kwatance da Abu ta yi mata. Nan take zuciyarta ta hautsine kishi mai tsanani ya lulluve ta, ta yi matuqar kaxuwa da ganin Saddiqa, wannan ce yarinyar da ya aura? Cikin ranta ta tabbatar ta haife ta, in za ta yiwa kanta adalci ma ta san ta haifi wacce ta fita.
“Wurin Mus’abu muka zo”.
Abu ta sake nanata mata.
“Come in”.
Ta faxi dai-dai lokacin da ta ja baya don basu hanyar shiga, suna shirin shiga direba ya fara yi musu sallama.
“To da safe za ka zo ne”.
Ya ce, “A’a, ai an riga an biyani zan yi sammako kawai in xauki hanyar komawa gida, Ubangiji ya sanya alheri”.
Ta ce, “Amin”. Suka yi sallama ya tafi.
Abu da Saddiqa suna zaune cikin haxaxxun falon gidan sai rarraba ido Abu ke yi, cikin hanzari ta cewa Saddiqa.
“Ba shakka gidan ne, don ga hoton shi can”.
Saddiqa ta yi kamar ba ta jita ba, a zuciyarta ta ce, “Sai yanzu kika gani kenan”.
Abu ta saake buxa baki, “Wai ina Mus’abun yaake ne?”
Ta sake yin wata tambayar saboda ganin Jennifer da ta yi ta fito za ta shiga wani wurin.
Jennifer ta fahimci tambayar ta juya tana yi mata bayani cikin Turanci tare da nuna mata agogo.
“Yanzu sha biyu da rabi ne na dare lokacin dawowar shi gida bai yi ba tukunna yana can club inda zai sha barasarshi, wataqila in kun yi sa’a ya dawo zuwa ukun dare, in kuma ya gaamu da wata ‘yar iskar a can to sai gobe in ya taso daga office ya dawo gida”.
Ta wuce ta shiga xakin da take nufin shigar. Abu ta kalli Saddiqa da tuni hawaye ke zuba a idonta ta ce, “Me kenan ta ce?”
Ta yi shiru ba ta tanka ba. Haushinta ya kama ta, ta ce, “In dai kin kasa jin wannan cakwalkwalallen Turancin da matar nan ke yi to zirga-zirgar bokon naki bai magunta ba, don ko ni xin nan inda zan kasa kunne da kyau zan ji abin da take faxi. Me ta ce?”
Ta qi tankawa. Ta vata rai ta ce, “Ai sai ki yi ta yi, ana tambayarki kin yi shiru kin qi ki cewa mutaane komai”.
Jennifer ta dawo falon xauke da tiren gasassun kaji guda biyu, sai kuma manyan dogayen kwalabe su ma guda biyu, ga kuma kofunan tangaran masu dogayen mariqai su ma guda biyu.
Abu ta miqa hannu ta sunkuto kwalbar ta miqawa Saddiqa ta ce, “Sa qarfin quruciyarki ki buxe kwalbar da mai ruwa-ruwa zan fara”.
Saddiqa tana kallon kwalbar ta qwala ihu ta ce, “Yarda kwalbar Abu barasa ce”.
Abu ta kixime, maimakon ta yar sai ta jefar, kwalbar ta daki teburin gilashin da ke falon ta fashe. Nan take warinta ya mamaye ko ina, da gudu Saddiqa da Abu suka yi waje suna faman kwara amai.
Sunyi tsumu sun takura waje xaya jikin bango saboda matsanancin ruwan saman da ake kwarawa kamar da bakin kwarya.
Jimawa can suka hango fitilar wata mota ta haske gidan, ta kuma nufo su. Sai da ta zo jikin matakalar hawa barandar sannan ta ja ta tsaya.
Mus’ab ya fito daga cikin motar da karan sigarinshi a bakinshi, cikin sauri ya hayo matakalar zuwa barandar alamar shima bai son ruwan ya jiqa shi. Walqiya ta haske wurin dai-dai lokacin da tsawa gami da aradu suka mamaye duniya.
Hankalinshi ya kawo kan tsugunon da ya hanga, hakan ya sa shi jin maqyarqyatar da ake yi.
“Su waye a nan?”
Ya yi tambayar daidai lokacin da ya kai hannu ya kunna fitilar da ya tarar a kashe haske ya bayyana. Abu ce mai maqyarqyatar, rawar sanyi take yi.
Ya zuba musu ido yana kallon su tamkar bai taba ganinsu ba, cikin wani irin yanayi na tsoro, fargaba gami da razana mai tsanani. Ina ma dai a ce mafarki yake yi.
Da qyar ya iya buxa baki ya ce, “Abu ce?”
Cikin rawar sanyi ta ce mishi, “Eh, sannu”.
Kamar a ce yana da layar zana ya vace, ko kuma ya yanka da gudu ya shiga jerin dake bayansu ya yi tafiyarshi. Babu hali sun rigaa sun ganshi ba kuma zai yiwu ya gudu ya barsu cikin halin da ya same sun ba.
Ya daure ya ce, “Ya ya za ku zo ku tsuguna a nan Abu, ku tashi mu shiga cikin gida mana”.
Abu ta ce, “A’a”.
“Haba Abu, ku yi haquri”.
Ya sunkuyo tare da matsowa ya tsuguna a kusa dasu yana rarrashi, hayaqin sigarin dake hannunshi da hatsaniyar barasar da ya kwankwaxa da ba ta rabu da shi ba suka haxu suka tayar da hankalin Saddiqa, ta sake kwaro wani aman.
Ya yi maza ya ja da baya tare da wurgar da guntun sigarin dake haannunshi. Ya miqe ya shiga cikin gidan, karon da ya yi da kwalbar barasa a fashe ga kuma kaji a kan tire ya qara faxar mishi da gaba.
“Kar dai barasa Jennifer ta basu?”
Ya yiwa kanshi tambayar cikin rawar jiki. Da sauri ya nufi cikin xakin nashi, tana kwance tsirara daga ita sai xan kamfai wai tana shan iska.
“Wane ne ya yi ta’adin da na gani a falo Jennifer?’
Ta yi kamar ba ta jishi ba, ta yi lamo tamkar tana barci. Sai da ta ji ya xaxa mata duka ya shige ta sannan ta yi zumbur ta miqe zaune.
“Ina jin wannan tsohuwar ce”.
Jikinshi ya kamarawa.
“Kakata kika kaiwa giya ta sha Jennifer?’
Ya zuba mata ido cikin matsanancin baqin ciki. A yatsine ta ce mishi, “To mene ne, ba da shi kake saukar baqinka ba a gidanka?”
Yasa hannu ya xauke ta da mari yana zaton zai kwashe qalau kamar yanda ya saba kwashewa, har ma a ba shi haquri.
Sai kawai ya ga tasa hannu biyu ta cakumoshi alamar dama ta shirya mishi, abin da ya haddasa Mus’ab rufe ta da duka mai tsanani ta shiga ihu tana kururuwa tare da ruwan ashar, a hakan kuma duk abin da ta raruma sai ta yi wurgi da shi wai ta same shi ko ta yi mishi wani ta’adin.
Rigima mai tsanani ya kaure, ihunta ya qara tsananta. Su Abu suka yi matuqar tsorata, maimakon tsuguno suka koma tsayawa suna tunanin inda za su nufa cikin tsohon daren da ake tsuga ruwan sama kamar da bakin qwarya.
Sani ma ya iso ya yi parking a qofar gidan da sauri ya fito ya nufi shiga cikin gidan don yin rabo.
“Kai Mus’ab baya jin shawara ya sake kawowa matar naan wata matar kenan”.
Ya yi kamar ya haxiye maganar tashi da ya yi a bayyane ya mai da ita cikinshi ta zama bai yi ba, saboda ganin da ya yiwa su Abu a tsaitsaye.
“Abu! Abin mamaki, kune a gidan namu? Ai sai ku zo mu shiga wancan sashin”.
Ta ce, “A’a, shiga dai nan ka yi rabo don kar ayi kisan kai”.
Da gudu ya shige ciki gidan, sai ga shi ya fito da Jennifer daga ita sai tawul xin da shine ya xaura mata. Ya yi maza ya jefata a motar da ya zo a ciki ya juya ya koma inda ya fito.
‘Yan mintina kaxan sai ga Mus’ab ya fito daga cikin gidan tsab da shi, kuma cikin nutsuwa tamkar dai ba da shi aka yi wannaan ba ta kashin ba”.
“Ku shigo daga ciki Abu”.
“Kul! Kar ka sake cewa in shiga gidanka”.
Tana magana tana vari saboda sanyin dake kaxata.
“To muje in samar muku hotel don ku samu wurin kwanciya”.
Kalmar sama musu hotel xin ta sata fashewa da kuka tare da salati.
“Ni da nake neman cikawa da imani me zai kai ni kwana a hotel”.
Nan take ya gane kuskuren da ya yi wajen faxin hakan da ya yi, ya koma ba ta haquri.
“To faxi inda kuke so in kai ku Abu, amma saboda girman Ubangiji kar ki ce za ku kwana a nan a wannan halin da kike ciki”.
Magiyar da ya yi ta sanyata buxe baki ta ce mishi, “Kai mu gidan liman”.
Ya xan yi nazari kaxan kafin ya ce mata, “Nan inda muke muna wajen gari ne Abu, liman kuma yana zaune cikin gari, don haka ki yi haquri ga jikan liman ina maqwabtaka da shi mutumin kirki ne yana kuma tare da iyalinshi, muje in kai ku can gidanshi”.
Ta ce, “To”.
Gidan Idris gida ne da komai nashi irin na Mus’ab ne, kasancewar su dukansu ma’aikatan Steel Rolling xin ne, bai da nisa sun kuma daxe suna maqwabtaka mai daxi.
Sai da suka buga qofar gidan sosai kafin aka zo aka buxe. Yana ganinsu ya basu izinin shiga falon.
“Sannun ku da zuwa”.
Sai da ya yi gaisuwar kafin ya waiwaya ya kalli Mus’ab.
“Kar dai a ce baqin amare muka yi cikin daren nan?”
Ya ce, “Eh, sune”.
Ya sake wani murmushin.
“Hala uwargida ce da amarya?”
“Eh, sune”.
Mus’ab ya sake amsawa. Sai dai qarfin hali kawai yake yi yake ba shi amsar, shi kaxai ya san yanda zuciyarshi take.
“Abida ai sai ki fito ga baqin amare kin yi”.
“Ayya! Da ka barta ta yi baccinta wuri kawai za ka bamu mu xan miqe, don jikinmu ya yi tsami da yawa”.
In ji Abu. Bai saurara ba ya shiga ya tasota suka fito tare. Kyakkyawar yarinya mai matsakaicin tsawo wankan tarwaxa, mai yalwataccen gashin kai. Sanye da kayan bacci tana muttsuke ido tana fara’a saboda ganin baqi.
“Sannunku da zuwa”.
Ta faxi cikin murmushi.
“A’a, lallai amarya ce ta yi mana saukar dare cikin ruwa?”
Abu ta ce, “Cikin ruwa fa kam gamu nan jage-jage”.
Daga cikin xakin da ta fito yaro ya qwalla qara ta yi maza ta shiga ta xauko shi za ta baiwa Idris shi, Abu tasa hannu ta karve shi tana cewa, “Dama da babban mutum ne a gidan?”
Mus’ab ya ce, “Eh, mai sunan liman ne Umar”.
Ta yamutsa fuska jin ya tsoma baki cikin maganarta.
Abida ta sake fitowa tana murmushi.
“To ga gajiya ga yunwa da wanne za a fara, wanka ko cin abinci?”
Abu ta ce, “Da wurin kwanciya kika bamu muka kwanta kawai”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ai yanzu huxu da rabi ne na asuba, gara kawai ku yi haquri in mun yi sallar asuba sai ku kwanta ku huta”.
“To bamu ruwan mu yi wanka don yarinyar nan ma ta xan ji daxin jikinta, ta wahala ta yi amai yau har ta gaji, a jigace take, ga shi ko kaya ba ayi dabara an zo mata da shi ba, to ba a san abin da za a zo a tarar ba kenan na vacin rai da tashin hankali, yanda mace ba ta yi sa’ar miji ba ta gamu da matsala”.
Abida ta bita da kallo ta ce, “Amma a haka Baba ai kin fita alamar jigatar”.
Mus’ab da ya san da shi Abu take yi ya cewa Idris, “Bari in shiga gida ina zuwa”. Ya ce mishi, “To, a fito lafiya”. Da sauri ya fita
Kafin Saddiqa ta fito daga wanka har ya dawo, ya zo ya miqawa Idris leda mai xauke da sabbin riguna guda biyu dogaye da aka yiwa xinki mai kyau a jikin asalin galila, ga ‘yan kwalayensu da gyalensu, under wear da qananan ‘yan kunnaye.
Ya miqawa matarshi ita ma ta kai wa Saddiqa dake shafa, tasa hannu biyu ta karva ta saka cikin murna da farin ciki, saboda ba ta san daga inda suke ba.
Ana idar da sallar asuba Abida ta kewaye su Abu da nau’’o’in abinci iri-iri na ci da na sha, ga shi dama ta iya girki, ta tsara su ta tsara shi ta yanda