Showing 18001 words to 21000 words out of 27104 words
ne Abu?”
Abu ta nemi wuri ta zauna saboda hawayen da suka soma zubo mata tana sharewa da bakin zanin dake yafe a jikinta.
“Ban sani ba Mus’abu, ni dai na san kullum ina addu’ar Ubangiji ya shiryeka”.
Ta soma kuka sosai. Ya qara matsawa kusa da ita yana rarrashinta, har ya samu ya shawo kanta suka fita waje suna xan takawa.
“Ga gidana can Abu mu shiga ki ga irin gyaran da ake yiwa Aisha”.
Ta yi maza ta ja ta tsaya, “Kai, a’a, wannan gida naka ai ba zan sake shigarshi ba”.
“Babu komai a ciki da za ki gani ya vata miki rai, wurin da Sani ya bari nake gyara mata, shi ya koma cikin garin, dama a can yake ni na kira shi ya dawo nan saboda bana son zaman kaxaici”.
Ta ce, “A’a, hali dai da ya zo xaya, amma kai ma ai kai kaxai kake zaune ba”.
Ya yi shiru ya qi tanka maganar tata.
Da yamma suna zaune a falon da ya ce mata shine na Saddiqan, komai na wurin a kammale yake an gyara shi, an sauya duk wani abin da ya kamata a sanya, wuri ya yi matuqar yin kyau, sai mai shi ake jira ta shiga. Mus’ab xin ne yaje ya lallavo Abun ta zo nan suke hira.
“Kar ki damu da maganganunta Abu, ba ki yi komai na fifitani a kanta ba, wurin Inna kawai ta ji wannan maganar cewar kin fi sona a kan kowa. Amma in ba haka ba me kika yi mata? Ita da kike ta rarrashinta ma kina ta tarairayarta, ni kuma kina ta fushi dani kina ta zare min ido, ki kawo ta xakinta kawai Abu sai ki yi tafiyarki gida ki gayawa su Inna kin barmu lafiya, in ina tare da ita ba zan barta ta yi ta wahala ba, balle ta je tana zama da yunwa ko xurarta sai in rinqa yi”.
Abu ta yi kamar za ta yi murmushi ta kasa saboda halin da Saddiqa ke ciki na yawan kuka da qin cin abinci yasa ba ta jin daxin zuciyarta, ga kalaman da take ta furtawa na wai son da take yiwa Mus’ab ya hanata yi mata adalci, bayan su dukansu biyun jikokinta ne.
“Abu!’
Abu ta yi maza ta katse maganar ta shi ta hanyar faxin, “Ni dai abin da nake so in roqeka shine, duk abin da za ta yi maka na vata rai kar ka ce za ka buge ta”.
Ya yi maza ya ce, “Haba Abu, Abu ki daina yi min irin wannan maganar, sai in ga kamar kin xaukeni mara hankali”.
Da daddare ranar Abida ta yiwa Abu rakiya aka kai Saddiqa gidan mijinta, babu abin da bai tsaru ba, komai ya yi daxi gwanin sha’awa, ta ko’ina sai qamshi kake ji, ga kuma ni’ima.
Abida ta yi musu hira har zuwa goman dare, da za ta tafi kuma Mus’ab ya yi mata kyautar leda mai shaqe da turaruka masu tsadar gaske.
Tunda aka shigo da Saddiqa gidan ta nemi wuri ta zauna ba ta sake xaga ido ta kalli wani ba, balle ta ji wani abin gidan ya burgeta, balle ta buxe baki ta amsa wata magana da suke yi mata, balle a samu ta yarda ta ci wani abun da ya kewaye su da shi, sun yi rarrashi har sun gaji.
Mus’ab yana zaune kan kujerar roba a qofar gidan, duk da daren ya yi nisa sigarinshi yake sha lokacin da Abu ta fito ta same shi.
“Na ce ba”.
Ya xaga ido ya kalle ta bayan ya wurgar da sigarin dake hannunshi.
“Ko za ka haqura ne kawai in tafi da yarinyar nan in yaso daga baya……..”
Bai jira jin daga bayan yanda za ayi ba ya ce mata, “A’a, abu ai don kina nan ne yasa hakan, in mu biyu ne daga ni sai ita na san yanda zan yi da ita, don haka zan shirya miki jibi ki tafi gida”.
Ta yi maza ta ce, “Gobe dai, me zan zauna in yi kuma har jibi?”
Ya ce, “To shi kenan”.
Washegari sun idar da sallar asuba Mus’ab yana kicin yana qoqarin shirya musu abin karyawa, Abu ta leqo ta ganshi a hankali ta ce mishi.
“Ban fa san yanda aka yi ba sai na ga yarinyar nan ta gaji ta kwanta har bacci ya xauke ta”.
A hankali ya ce mata, “Ta wahala da yawa”.
Ta tave baki ta ce, “To ni dai zan tafi duk da zuciyata ta qi yarda ta ji daxin barin yarinyar da zan yi, na kuma kasa yin jarumtakar xaukanta in tafi da ita ba tare da yardarka ba, ko kuma zargin da ta yi min xin ne yake nema ya zama gaskiya a kaina na fifitakan oho!”
“Ba ni kika fifita ba Abu, aure kika girmama. In ban da darajar tashin ai ba za a baki ita a ce ki kawo min ba. Amma da yardar Ubangiji ba za ki yi nadamar bar min ita da za ki yi ba, saboda ba zan barta ta shaidi komai daga gareni ba sai alheri”.
Ta ce, “To, Ubangiji ya shiryaku”.
Ya ce, “Amin”.
Saddiqa tana ta sharar barcinta lokacin da Mus’ab ya gama shiryawa Abu tafiyarta zuwa gida, tsaraba mai ximbin yawa ya yi mata, ga maqudan kuxaxe da ya ba ta gami da wasiqu zuwa wurin Kawu Gixe da kuma Baban shi.
Qarfe bakwai da minti arba’in dai-dai direban ma’aikatarsu ya iso qofr gidan kamar yanda Mus’abu ya yi mishi umarni, su Abida da Idris suka zowa Abu sallama, suna nan ma motar ta tashi ta tafi.
Mus’ab ya koma cikin gida ya yi shirye-shiryen da zai yi na kintsi, ya yi wanka ya shirya cikin qananan kaya coporet wears. Ya shiga wurin Saddiqa daidai lokacin da ta buxe ido.
“Kin tashi Aisha?”
Ba ta yi mishi magana ba. Ya zauna a bakin gadon yana kallon ta, kanta a sunkuye ba ta xaga ta kalle shi ba, sai dai ta shaqi daddaxan kamshin shi.
“Kin rame da yawa Aisha, ga wahalar tafiya, ga shi kin zo kin ga abin da bai kamata ki gani ba, ga kuma zama da yunwa da kike ta yi. Na roqeki ki yi haquri ki mai da komai ba komai ba mu fuskanci abin da ke gabanmu na zaman aure mai daxi. Mu biyu ne dake yanzu a gidan nan, in ban da abubuwa marasa daxi da suka faru da wannan lokacin shine lokaci mafi soyuwa da zaquwar zuwanshi a gareni na ganina tare dake mu biyu kina matsayin matata”.
Ta xaga ido ta kalle shi saboda nanata kalmar mu biyun da yake ta yi, idanuwansu suka haxu daidai lokacin da ya furta mata kalmar “Abu ta tafi”.
Kurma mishi ihu ta yi, nan take ta mimmiqe ta soma shessheqa tana qoqarin sandarewa tamkar wacce take shirin suma.
Dr. Usman ya iso gidan saboda kiran da Mus’ab ya yi mishi, yana tsaye a kanshi ya gama yi mata komai.
“Za ta daxe tana baccin, ina kyautata zaton ruwan zai qare kafin ta tashi, za ta xan samu kuzari saboda akwai duk wani abin da take buqata a ciki mun saka”.
“To Doctor na gode”.
Sai cikin dare ta farka, yana kwance a gefenta. Yana ganin ta tashi zaune shima ya miqe ya zauna yana kallon ta, ya yin da ita kuma ta sunkuyr da kanta qasa hawaye suka soma zuba.
Ya yi maza ya ce mata, “Look Aisha, ba fa irin zaman da zamu yi dake ba kenan, don kuwa ba auren qiyayya aka yi mana ba, ina sonki ne kina sona kafin Inna ta gaya miki halina kyakkyawar mu’amala ce a tsakaninmu, zuwan da kika yi kika ga wata a gidana kuma ba yana nufin kin kamani da wani mugun abu bane. Zaman da zamu yi dake ne nan gaba zai zama in kin kama ni da laifi kin kama ni, amma abin da aka gaya miki a kaina na hali ko kika ga na aikata wannan abin da ya shafeni ne ni kaxai, yanzu ne kike da haqqi a kaina, kamar yanda nima nake da shi a kanki, don haka ki yi haquri abin da ya faru a baya ya wuce mu fuskanci wanda yake gabanmu kawai”.
Ba ta tanka ba shima bai sake mata magana ba, ya miqe ya nufi banxaki ya haxa ruwan wanka ya gaurayashi da turare mai qamshi, ya fito ya ce mata “Kina da haqqi a kaina, na yarda zan tsare miki shi ko wane iri ne, na yi miki alqawari zan kiyaye. Amma nima zan tsaya in ga kin kiyaye nawa haqqin ko da ba duka ba. Ga ruwan zafi can na zuba miki ki je ki yi wanka”.
Shiru ta yi ba ta tanka ba, ba ta kuma nuna alamar za ta yi abin da ya ce ba. Don haka ya naxe hannun riga sai kwai ta ji ya sureta yaje ya tsomata cikin ruwan har da rigar dake jikinta. Ya kama zai tuveta ta qanqame jikinta wuri xaya. Ta ga dai hakan ba zi mata ba, ta yi maza ta qwallara mishi ihu.
“Zan yi”.
Ya sake ta tare da faxin ya fi sauqi hakan. Ya fita ya barta.
Ta gama sanya kayan da ta samu ya ajiye mata ba tare da ta tsaya shafa mai ba, ya shigo ya kalle ta ya ce, “Ga abincin ki na kawo miki falo zai fiye mana sauqi ki yi haquri ki ci da kanki, don ba zai yiwu in yi ta zuba miki ido kina wuni da yunwa kina kwana da ita ba. Kina jin bayanin da likita ya yi cewar ba wani abu ne ya sae ki ba illa yunwa, kin kuma san mijin kirki ba zai juri ganin matarshi cikin yunwa ba. Muje wurin abincin”.
Ya fita ya dawo ya samu ba ta motsa ba, ya ce, “Baki gane irin zaman da nake so mu yi ba, ni don bakya magana dani zan jure, don na tava zama da wani bebe a Italy, zama mai daxi kuma muka yi, yana sha’anin shi ina nawa. Sai mun ga dama mu yiwa juna magana, don haka ki ci abincinki kawai sai in qyaleki ki yi sha’aninki nim in yi nawa”.
Ya fita ya nufi masallaci saboda kiran sallar asuba da aka yi. Har ya yi sallar ya dawo ba ta ci ba, sai ma ta sake miqewa bayan ta idar da tata sallar.
“Zaman namu zai koma irin zaman tabbataru kenan, kin san shi tabbatara kullum xura yake yiwa matarshi a baki, ina ganin cikin tsuntsye babu wanda ya kai shi yiwa matarshi hidima, ya kuma yi mata kirri da wasannin bajinta da kwarkwasa don ta ji tamkar babu kamarta a duniya. In hakan kika zava ai sai in yi miki don kin cancanci ayi miki komai”.
Hannu ya miqa ya surota ya xora kan cinyarshi, ya ce, “Ni inda kike ganina xin nan babu abin da ban iya ba na reno, sanda nake yaro har xura nake yiwa qannena dama ‘ya’yan malamina can inda aka kai ni almajiranci, saboda barni da halina amma ban son ganin xan Adam yana jin yunwa”.
Kwantar da ita ya yi kan cinyarshi duk da mutsu-mutsun tirjiyar da take yi yasa hannunta na hagu qarqashin qafarsa ta dama ya matse, zafin matsin gami da takaicin cin zarafin da yake mata yasa ta soma kuka sosai, ya yi amfani da hakan wajen xura mata kunun gyaxa dake wurin, ta yi maza ta haxiye gami da qwarewa, wani kuma ya zube a jikinta. Ya sake surarta ya nufi byan gida da ita yana faxin “Wannan wankan ai dama ba wanka bane, tunda ba a yi mishi shafa ba balle kwalliya”.
Dolen Saddiqa ta yarda da bin umarnin wanka da na cin abinci, in ya ce ta yi ta yi, ko da kuwa ba ta son yin hakan. Kuma qa’ida ne in ta yi wankan ta yi shafa ta yi kwalliya, ta kuma sanya kayan da ya ajiye mata.
Rannan ta shiga wanka saboda umrnin da ya ba ta na ta yi wankan, yana zaune yana tunanin abin da zai yi ya kawo qarshen wannan zman nasu, don ya fara isarshi.
Tunaninshi ya kai kan faxaxa mu’amalar ta hanyar shigo da wasu abubuwan da yake ganin tamkar za su taimaka mishi, yana tashe da sabbin zannuwan da ya karvo mata daga wurin xinki, ta fito tana goge gashin kanta da xan qaramin tawul xin dake hannunta.
Ya bita da kallo ya ce, “Yau kam bari in shafa miki man nan Aisha”.
Ta yi maza ta kalle shi, shima ya tsareta da idanuwanshi ya qara cewa, “Bari in shafa miki man”.
Qarar da waya ta yi ya katse shi, ya yi maza ya xauki kan wayar dake xakin.
“Hello!”
Nan take ya mai da kan ya nufi wurinshi cikin sauri. Ganin yanda ya yin ya sanyata matsawa kusa da wayar a hankali tasa hannu ta kai kunnenta. Ko shakka ba ta yi ba matar da ta samua a gidan ne, ga abin da ta ji tana cewa.
“Na bugo ne in ji yanda kuke ciki kai da amaryar taka”.
“To ina gaminki da ita da za ki so jin abin da muke ciki?”
“Saboda ka wulaqantani a kanta ka ci mutuncina saboda ita”.
“Ai baki da wani mutunci da za a ci Jennifer”.
“Da ka yi a hankali Mus’ab ka daina cin zarafin mutane a kan ‘yar wannan yarinyar da ba wani abin arziki za ta iya tsinana mka ba, ni na san nan ba da daxewa ba za ka zo nemana da abinka a wandonka kana tuba kana in yi haquri”.
Saddiqa ta rintse ido jin kalaman nasu, a hankali ta mai da kan wayar ta ajiye kamar yanda ta same ta, ta koma wurin shafarta ta yi abin da za ta yi na gyaran jikinta, ta gama ta xauki xaya daga cikin atamfofin da ya ajiye a wurin ta saka. Kwalliya sosai ta yi, atamfar kuma ta yi matuqar karvarta, ta fesa turare ta ji ni’ima cikin ranta, ta koma gefen gado ta zauna tana tuna Gwaggonta da halayenta na faxin gaskiya a kan koma waye.
Sai ga shi ya shigo yana murmushi, ya ce, “Kinga yanda kika yi kyau kuwa? Kin kalli kanki a madubi?”
Ba ta tanka mishi ba kallon shi kawai take yi, a zuciyarta tana mamakin al’amarinshi, ko ya ya aka yi ya zama haka oho! Tamkar dai a ce ba Gwaggonta ce ta haife shi ba, mutumin da ta rinqa ganin tamkar ya fi kowa kirki da kyawawan xabi’u, take yi mishi kallon kamammen mutum mai tsabta, take ganin tamkar duk macen da ta same shi a matsayin mijinta na aure ta morewa rayuwarta. Sai ga hi a yau ya zube mata ta kuma gane matarshi ba komai za ta sadu da shi ba a rayuwarta illa baqin ciki da vacin rai mai tsanani.
Ta sake tunawa da Gwaggon nata da irin halayenta, nan take ta sake fahimtar bai zama lallai ba ashe a ce dole sai xa ya yi hali irin na iyayen shi. Gwaggo halinta daban na xanta daban, haka na Abu ma daban, don da Gwaggo ce ta ga abin da Abu ta gani da babu yanda za a yi ta sulale mata ta gudu ta barta cikin halin da ta barta.
“Aisha yanzu in ina so in tsotsi bakinki ya ya za ayi?”
Ya yi tambayar a yanayin dake nuna yana son yin abin da ya ambata. Tana xaga ido ta kalle shi takaicin shi ya qara kama ta, ta soma yi mishi kuka.
Ya yi maza ya juya ya nufi kicin ya shiryo abinci a tire ya shigo yana faxin, “Gaskiya ai dole ki yi min kuka, ban baki abinci kin ci kin qoshi ba ina yi miki maganar tsotson baki, da wanne za ki ji?”
Ya ajiye tiren a gabanta ya ce, “Za ki ci da kanki ne ko in baki?”
Ya jawo hankicif ya riqe alamar wai zai iya bayarwar, gudun kar ya yi mata abin da ya saba yi matan yasa tasa hannu ta xauki cokali ta soma ci da kanta, shi kuma yana kallon ta.
“Haba, to ko ke fa Aisha, me ya fi haka daxi? Bari in zauna ina zuba miki”.
ABU TA ISA GARIN MISAU
Wajen qarfe takwas na dare motar dake xauke da Abu ta yi parking a qofar gidan Malam Abdullahi a cikin garin Misau.
Malam Abdullahi da kanshi ya fito yiwa Abu oyoyo tare da sannu da zuwa, tana amsawa tare da xan xingisa qafa, cikin tafiyar tata ta wuce ta shiga cikin gida, inda nan ma Inna Habiba ta