Showing 1 words to 3000 words out of 27104 words
ABU NAKA…
2
HAFSAT C. SODANGI
Haqqin Mallaka (m) Hafsat C. Sodangi
Shekarar Bugu:
2005
An sake Bugawa A:
2015
ABU NAKA-2
M
us’ab ya wuni cikin matsanancin maye kasancewar shi kanshi ba zai iya faxin adadin kwalaben barasar da ya kwankwaxa ba.
Sani ya shigo gidan da saurinshi saboda ihun Mus’ab da yake jiwowa tun daga waje da kuma ta’adin da ya hango Mus’ab xin yana yi na jifa da duk wani abin da ke cikin falon wanda hannunshi ke iya xauka, yana tarwatsa gilasan gidan dasu.
Qarfi mai yawa Sani ya saka kafin ya iya riqe hannun Mus’ab, sunyi duru-duru suna kallon juna cikin haki, saboda wahalar da suka yi kafin suka kai ga tsayuwar.
Sani ya yi nufin jan Mus’ab zuwa cikin xakin kwananshi bai yi nasara ba, sakamakon tirjiyar da Mus’ab xin ya yi, don haka suka zube kan kujerar dake bayansu cikin haki.
“Dame wannan abin ya yi kama Mus’ab?’
Sani ne ya yi tambayar.
Mus’ab ya zuba mishi ido a gajiye, da qyar ya buxe baki ya ce mishi, “An rabani da Aisha, kuana kallo baka yi komai ba saboda kai mugu ne ko?”
Yana maganar da qyar yana zaro ido tamkar dai yanda aka san bugagge yana yi, ga kuma hannayenshi da ya damqi wuyan Sani dasu sunyi mishi kyakkyawan kamu.
Sani ya shiga kici-kicin qwatar kanshi daga hannun Mus’ab.
“Ka sato min Aisha ka kawo min ita nan gidan yanzu-yanzu nan ina son ganinta, ina son rungumarta a qirjina, ina son jin xuminta a jikina, ina son ganin no…….”
Da sauri Sani ya xoraa hannunshi a bakin Mus’ab ya toshe don rage qarfin maganar da yake yi gudun kar ma’aikatan gidan dake waje su ji.
“Mus’ab kanka xaya kuwa, duk barasar ce ta mai da kai haka?”
Mus’ab ya tunzura ya qara shaqe shi ya ce, “Nine mashayin?”
Sani ya qara tsorata da lamarin nashi ya shiga neman hanyar qwatar kanshi daga hannun shi.
Ya ce, “Ban ce maka mashayi ba Mus’ab, cewa na yi ka yi haquri ka sake ni don in samu in nemo varayin da za su sato maka Saddiqa su kawo maka ita, tunda ai ka san ni ban iya sata ba ko da ta kaya ce, balle ta mutum xungurungum!”
Mus’ab ya sake shi. Cikin sauri Sani ya miqe ya kama hanyar fita daga gidan, yana jin Mus’ab yana ihun yau xin nan nake so ka sato min ita.
Washe gari da safe Mus’ab yana zaune kan dardumar da ya idar da sallar asuba, jan carbinshi yake yi tunda ya idar da sallarshi bai tashi ba, shi da kanshi ya san rabon da ya sha barasa da ta gusar da hankalinshi irin na jiya ya yi matuqar daxewa.
Har lokacin kanshi bai bar sarawa ba, ga nauyi da yake yi mishi saboda matsanancin ciwon da yake yi, ga tunane-tunane iri-iri da mafarkai barkatai, har bai iyaa tantancewa da adadin mafarkan da ya yi a cikin daren.
Daga ciki wanda ya fi tsaya mishi a rai shine, mafarkin Hamida da ya yi cewar ta shigo gidanshi tana ba shi labari game da bikin Saddiqa da Sadisu, wanda rashin daxin labarin da take ba shi yasa ya yi ta jifanta da abubuwa har ma ya fasa mata kai.
Gabanshi ya yi mummunan faxuwa da ya qara tsunduma cikin tunanin mafarkin. Shin mafarkin ya yi ko kuwa Hamida ce ta zo gidanshi da gaske ya fasa mata kan? Wai wane irin maye ya yi ne jiya?
Ya qara zurfafa cikin tunani yana nazarin irin jifan da ya ga yana yi mata, ya zubawa wuri xaya ido yana qoqarin tunano maganganun da ta zo mishi dasu sai ga Sani ya shigo.
Mus’ab ya zuba mishi ido cikin fargaba da tsoro, cikin qarfin hali ya tambaye shi.
“Daga ina Sani?”
Sani ya kalle shi cikin nutsuwa ya ce, “Daga inda ka aike ni mana”.
Ya sake zubawa Sani ido yana qoqarin tunano aiken da ya yi mishi, bai tuna ba.
“Ina na aike ka Sani?”
“Sato Saddiqa mana, ba ka ce in tura varayi su shiga gida su sato ta a kawo maka ita ba?”
“Ni!”
Da qarfi ya yi tambayar tare da miqewa tsaye cikin kaxuwa. Ya sake tambayar shi “Ni? Sani na turaka ka aiki varayi su shiga cikin gidan ubana da ya haifeni su yiwo sata?”
“Ai ba sata ka ce suyi ba, Saddiqa ka ce a sato maka”.
Mus’ab ya xan yi taku biyu gaba kafin ya sake ja ya tsaya, ya sake juyowa gare shi ya ce, “To yanzu fa me ake ciki?”
Sani ya kalle shi ya ce, “Ai anyi an gama, kai kawai ake sauraro”.
Kan Mus’ab ya kama sarawa da sauri fiye da da, ya xora hannu ya dafe goshinshi cikin matsananciyar damuwa da fargabar al’amarin. Shi kam ya san babu yanda za ayi a shiga gidansu a sato Saddiqa a fito da ita alhalin Innarshi tana lafiya.
Me suka yiwa Inna? A wanne hali suka barta? Waxannan sune tambayoyin da suka tsaya mishi a rai.
Nan da nan ya juyo don Sani ya amsa su, sai dai kuma abin takaicin shine Sani ya fita ba tare da ya sanar da shi ba.
Mus’ab ya laluba kujera a hankali ya zauna, lokaci mai tsawo yana tunanin ta inda zai bi ya gyara al’amarin da ya riga ya lalace, dama an ce ba za a ba shi Aisha ba saboda shi xan iska ne, to yanzu kuma in aka gane shine yasa aka sace ta me za a kira shi?
Anya iyayenshi za su yafe mishi kuwa? Ya ya zai yi ya sake daidaitawa dasu? Shi ba abin ya xauke Aisha ya yi tafiyar shi da ita ya bar qasar yaje wani wuri suyi rayuwarsu ba, aure mai albarka yake nema a tsakaninshi da ita na raya sunnar Manzo, ban da haka ya kai munzalin shekarun da daidaituwar al’amura yake nema tsakaninshi da iyayenshi.
Tausayin kanshi ya kama shi da ya tuna in har aka gane abin da ya faru yana da hannu a ciki, to shi da Aisha sunyi bankwana kenan har abada. Amma duk da haka ya qudiri aniyar mayarwa iyayenshi da Aisha, don ba zai yarda a wannan lokacin wani abu mai tsanani ya sake shiga tsakaninshi da iyayenshi ba, musamman ma mahaifiyarshi.
Yana kwance cikin ruwan zafi da ya gauraya da turare mai matuqar qamshi cikin tunanin mafita, zai je ya ga Aisha a inda su Sani suka voye ta ya xauke ta ya mai da ita gida, maimakon ya bari sai sun bincika zai gaya musu gaskiyar lamari, iyaka dai ya san abin da yake gudu ne zai same shi.
Mus’ab ya kammala kwalliyarshi cikin fararen kaya babbar riga ‘yar ciki da wando na farin yadin boyel ne a jikinshi, hular kanshi da baqaqen takalman dake qafarshi sunyi matuqar dacewa, ga qamshin turaren shi mai sanyaya zuciya, duk da matsanancin vacin ran dake gare shi bai hana shi yin kyau ba, ga kwarjininshi na musamman a tare da shi.
Ya fito daga xakinshi zuwa falonshi ya nufi kujerar da ya hangi makullan motarshi a ajiye a kai, yana mai xaura agogonshi qirar Rolex a hannunshi. Motsin da ya ji a bayanshi ya sanya shi saurin juyawa, Sani ne a tsaye a bayanshi.
Mus’ab ya zuba mishi ido cikin nuna alamar vacin rai.
“Yanzu ina Aishan take?”
Kafin ya ba shi amsa sai Mus’ab ya ce mishi.
“Ban san baka da hankali ba Sani sai yau, wato kai duk umarnin da aka baka sai kawai ka bi Sani? Ba za ka yi la’akari da yanayin da mutum ke ciki ba a lokacin?’
Sani ya galla mishi harara ya ce, “A’a, kar ka sargeni giya hauka ne?”
Ya juya zai sake fita.
“To baka gaya min inda take ba don in san abin yi, kaima ka san yanzu ba lokacin wasa bane tunda dai komai ya riga ya lalace, ka ji tausayina mana Sani”.
Sani ya kalle shi saboda tausayin da ya bashin ya ce, “Tana gidan Innarta”.
Kan Mus’ab ya xaure, ya sake tambayar shi.
“Wacce Innar tata?’
Ya ce, “A’a, gidan Inna mana, ai ban aiki wani sato ta ba”.
Ya kalli Sani ya yi tsaki.
“Wato kai duk halin da mutum yake ciki sai ka zolye shi ka qara mishi damuwa saboda tsabar rashin tausayi, to ka zu muje saboda mu san abin da suke ciki tunda duk wayoyi da na yi ta yi mata ta qi xauka”.
Sani ya kalli agogon hannunshi ya ce, “Gaskiya sai dai ka yi haquri ka je kawai, Ishaq ya yi waya kana wanka ya ce yana bisa hanya, ina ganin in jira shi ya zo ya fi in bika ya zo ya smau gida babu kowa. Ko me ka gani?”
Ya fita ya tafi ba tare da ya amsa ba. Mus’ab yana tafiya cikin motarshi Marsandi qirar 190, zuciyarshi sai faman shirya mishi kalmomi masu daxi take yi da zai yi amfani dasu wajen shawo kan Aisha don ta sassauto daga tsattsauran ra’ayin da ta xauka a kanshi saboda abin da Gwaggonta ta gaya mata game da shi.
Ya yi parking a qofar gidan cikin matsanancin fargaba da tsoro, nan take ya ji zuciyarshi ta shiga dakan uku-uku saboda cincirindon yaran da ya gani a qofar gidan suna wasanninsu alamar akwai taro a cikin gidan.
A saninshi yau saura kwana tara ayi xaurin auren Aishaa, to me ya kawo taron jama’a tun a yau? Yana gama yiwa kanshi tambayar mafarkin Hamida da abin da take gaya mishi ya faxo mishi cikin ranshi.
“Yaya zuwa na yi in shaida maka cewar Baba da Inna sun dawo da xaurin auren Saddiqa da Sadisu wannan Juma’ar, wai za suyi hakan ne don su shammaceka da jama’ar da za su iya cewa wani abu game da hanaka da suka yi, baka ankara ba sai kawai ka ji an kaita gidan mijinta”.
Waxannan sune kalaman da ya tuna Hamida ta gaya mishi a cikin barcin shi. Ya fito daga cikin motarshi cikin sanyin jiki da matsanancin fargaba ya wuce yaran ba tare da ya kula su ba alhalin yin hakan ba xabi’arshi ba ce.
Yana shiga zauren gidan hayaniyar muryoyin jama’a mata da ya jiyo daga cikin gidan ya dakatar da shi daga shiga.
“Ku miqo min kwandon tsaman can wannan ya cika”.
Muryar da ya jiwo kenan wacce ya fahimci mai ita. Cikin sauri ya juya ya fita, ya samu yaro mai hankali cikin yaran dake wasa a qofar gidan ya ce mishi.
“Maza shiga cikin gida ka cewa Bilkisu wai ta samu yayanta a gidan Abu”.
Ya ce, “To”. Ya shiga cikin gida da gudu, shima Mus’ab ya yi maza ya bar qofar gidan.
Mus’ab yana zaune kan tabarma cikin matsananciyar damuwa, ya qosa qwarai ya ga shigowar Bilkisu.
Ita kuwa Abu sai qoqarin qarasa kwalliyarta take yi, atamfar ‘yar Ingila ce a jikinta sabuwa dal, ga ‘yan kunne da sarqar zinare da Mus’ab ya saya mata sun kama wuyanta, su ma ranar ta fara sanyasu. Qafarta ta yi shar gwanin sha’awa da lalle, duk da dai ba ta gama yin baqi ba tana riqe da mashayin kwallinta a hannunta tana zizirawa a idonta.
“Ni kwalliyar me Abu take yi ne haka?”
Cikin qarfin hali Mus’ab ya kawar da shirun dake xakin ta hanyar yi mata tambayar. Ta dakatar da girgiza tandun nata ta shiga qoqarin fito da mashayin nata don ta zizarawa xaya idon nata. Ta zuba mishi ido kafin ta ce mishi.
“Yaushe ne ka tava zuwa gidana baka sameni cikin kwalliya ba?”
Ya xan qara kallon ta kafin ya ce, “A’a, Abu ba dai irin wannan kwalliyar taki ta yau ba, kwalliyarki ta yau ai ta fi kama da so kike ki cinye wata gasa. Ba don na san tsofaffi basa zuwa gasar sarauniyar kyau ba da sai in yi zaton can za ki tafi”.
Abu ta yi murmushi ta ce, “Ko ba za ni cin gasa ba ai na yi kwalliya yau kam ta cinyewa, tunda yau ne saka lallen Saddiqa. Sa’a ma ka ci ka sameni a gida don can gidan nasu za ni yanzu”.
“Yau saka lallen Saddiqa?”
Ya yi tambayar a firgice cikin faxuwar gaba da razana tamkar Abu ba ta gane yanayin da ya samu kanshi a ciki ba. Sai ta ci gaba da magana.
“Iyayen Saddiqa sun matso da xaurin auren zuwa jibi, sun ce ka xaga musu hankalin yarinya kana nema ka sata ta bijire musu bayan ita ba bijirarriyar ba ce, tunda uwarta ta bayyana mata halayenka babu abin da take yi in ban da kuka, ko abinci ta qi ci. Don haka gara suyi maza su kaiwa mijinta ita tun baka yi dalilin da suka kunyata ba, don haka yau ne ake aikin kayan tsarabar biki su cincin, lkaki, nakiya da dubulan. Yanzu haka ma ai ina jin gidan a ciki yake”.
Bilkisu ta yi sallama Abu ta amsa mata, ta shigo ta durqusa ta gai da Abu sannan ta juya wajen Mus’ab, bai saurari gaisuwarta ba ya balbale ta da faxa.
“Har daku Bilki cikin bukin da su Inna ke shirin yi? Na ce har daku? ‘Yan ina da buki? Ko ba a gayyacesu ba sai sun je? Yanzu ashe har daku cikin wannan bukin?”
Abu ta bar abin da take yi ta zuba mishi ido tana kallon shi. Bilkisu kuwa kuka take ta yi, ya yin da shi kuma yake ta faxa.
“In ban da rashin hankali da rashin sanin ciwon kai me ya shigar daku cikin wannan bukin? Na ga hanaku auren aka yi aka bai wa wasu, ko kuwa kuma kuna cikin masu marawa Sadisu ne? Ko har daku aka haxu aka yi min taron dangin da aka yi aka hanani auren ne? Ta hanyar gwada min fin qarfi, kuma kun biyewa Abu ne?
To ita murna take yi da abin da aka yi min tana farin ciki, kin ganta ai gayenta take yi, yaushe rabonki da ganinta riqe da madubi tana qalqale fuska in ban da yau? Murna take yi tana farin ciki an hanani auren Aisha an qwace min ita, bayan kuma tawa ce saboda kawai bani da gata dama kuma tun farko sai da ita Abun ta sarawa neman auren nawa baki”.
Abu ta katse maganganun nashi ta hanyar qyalqyalewa da dariya. Sai da ta yi shiru sai ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce mishi.
“Sambatun kayan ne haka ko kuwa har yanzu a buge kake maye ne ya saka waxannan maganganun?”
Ya yi maza ya qara xaure fuska ya ce, “Wane irin maye?”
Ta ce, “To in ban da haka ka ce don an hanaka auren Saddiqa kar su Bilki suje bikin? Kanka xaya? Saddiqa ba qanwarka ba ce? Ko kuwa barasar ce ta mai da kai haka baka san ya kamata ba sai kanka kaxai ka sani?”
“Bana son kina yi min irin waxannan maganganun a gaban qannena”.
Ta ce, “Kai tafi can ka bani wuri, mene ne basu sani ba a halayen naka? Mene ne qannen naka basu sani ba game da kai? Ni abin kunyar da ka yi ma da Bilkin ka yiwa zai xaga min hankali ne har ya dame ni ya tayar min da hankali? Ita Bilki ai ta san komai naka tunda tare kuka taso shekaru uku ne a tsakaninku, tun ba ta isa komai ba kuma take cikin lamarinka, babu wani abu naka da ba ta sani ba.
Amma Hamida fa? ‘Yar qanqanuwa cikin qannenka, yarinyar da in da kai mace ne ka haifeta da girmanka fa aka haifeta, ba ta san komai game da halayenka ba, in dai ba ta ji a labari ba in wani ya gaya mata”.
Mus’ab ya shiga tsoro da fargaba, ya qosa qwarai Abu ta kai qarshen maganar tata ko kuma ta katse dogon bayanin ta gaya mishi me ya yiwa Hamidan? Kar dai fa mafarkinshi ya zama gaskiya? Kar dai fa da gaske ne Hamida ta je gidanshi ya jefe ta ya fasa mata kai? Tambayoyin da suke kai kawo cikin zuciyarshi kenan.
Abu ta shiga kuka sai dai ba ta bar magana ba.
“Haba Mus’ab, sai yaushe ne za ka bar wannan mummunan halin naka? Duk yanda qannenka suka kai da baqin cikin hanaka auren da aka yi ya ya za suyi? Me za suyi wanda ya wuce abin da suka yi? Dole ne