Showing 21001 words to 24000 words out of 27104 words
karveta hannu bibbiyu cikin murna mai yawa.
Nan da nan ta shiga gabatar mata da abubuwan ci da na sha, ta kuma zauna kusa da ita tana qara yi mata sannu da hanya da kuma gaisawa.
A waje kuwa shima direba ya sha tarba wajen Malam Abdullahi, ganin shine mai kwashe tsarabar zuwa cikin gida a dalilin rashin yara a kusa yasa shi sa hannu wajen taya shi kwashewa saboda girmamawa.
Suna gamawa ya gabatarwa da direban abin ci da na sha, sai da ya ci ya qoshi sannan ya tafi.
Inna Habiba tana zaune gaban Abu bayan Malam Abdullahi ya shigo ya gaisheta ya fita.
“Ba ki fa ci komai ba Inna, in ban da surkin farau-farau xin surkin da kike ta kwankwaxa”.
Abu ta xan yi tsaki kaxan ta ce, “To gajiya, wannan gari da kafirin nisa yake”.
Ta ce,”Haka ne Inna, ai qasar tamu faxi ne da ita. To ya ya kika baro su?”
Abu ta ce, “Qalau, duk sun ce a gaishe ku”.
Tana maganar Inna Habiba tana kallon idonta cikin nazari da lura.
“To ai ba za ki tafi gidanki yau ba Inna tunda kin gaji da ga shi dare ya yi, kwananki huxu ne kuma da barin xakin ko don a karkaxe miki qurar ciki kafin ki shiga ai sai ki kwana a nan, ga gado can sai ki hau ki yi kwanciyar ki”.
Abu ta zuba mata ido ta ce, “Mene ne haka kuma, kwana a gidan suruki bayan ga naka a kusa?”
Inna Habiba ta yi murmushi ta ce, “Amma kuma ai na sha jinki kina cewa bakya surukuta da Malam xanki ne”.
Abu ta gyaxa kai ta ce, “Qwarai kuwa”.
Suna xan tattaunawa sai ga Malam ya shigo da qunshin tsire a cikin leda, ya miqawa Inna Habiba ya ce ba, “Gwaggo”.
Ta ce, “To, Ubangiji ya saka da alheri”.
Ya juya ya fita, ita kuma ta miqa hannu ta xauko faranti ta juye mata a ciki ta miqa mata gabanta.
Abu ta kalli naman duk da qamshin shi da tururinshi dake tashi ba ta xora hannu a kanshi ba.
“Anya zan ci nama kuwa?”
Inna Habiba ta ce, “Haba Inna, a kan me?”
Ta ce, “Gidan Mus’abu fa na fito, ai bani da kwaxayin komai”.
Inna Habiba ta sake kallonta cikin nutsuwa ta ce mata, “Duk da haka kuma bakya murna, da rama kuma kika dawo”.
Abu ta yi maza ta kalleta, ta ce, “Ke fa haka kike, za ki fara ne?”
Ta yi murmushi ta ce, “To ki yi haquri, bari in juyo miki ruwanki ki yi wanka”.
Ta ce, “To”.
Washegari da safe Malam Abdullahi ya sake shigowa wurin Abu don su qara gaisawa, suna cikin hirar tafiyar ta shiga yi mishi bayani kan ximbin tsarabar da ta zo da ita.
Ta miqa mishi kuxin da Mus’ab ya aikota dasu ya ce na Babanshi da Kawu Gixe, tare da wasiqunsu. Ya karva ya sanya musu albarka tare da addu’ar Ubangiji ya zaunar dasu lafiya. Abu ta yi maza ta ce, “Amin”.
Ya sake kallon ta cikin nutsuwa ya ce, “To ai shi kenan faxuwa ta zo daidai da zama, dama yau za ni Bauchin sai kawai in je mishi da saqon, daga nan kuma in ba shi labarin dawowarku gida lafiya”.
Ta ce, “To da kyau”. Ya tashi ya fita ya barsu nan suna ‘yar hira.
Inna Habiba ta tashi ta fita ta dawo xauke da baho mai ruwan xumi a ciki ta ajiye a gaban Abu ta ce, “Tsoma qafafuwanki cikin nan Inna in xan matsa miki su don ki ji daxinsu”.
Abu ta yi yanda aka gaya matan don ta san daxin shi tare da faxin “To, nasa”.
Inna Habiba ta zauna tana matsa mata qafafun, daxi ya kama ta har ta zurfafa cikin tunani.
Inna Habiba ta xago kai ta kalle ta, ta ce, “Me ya faru haka na ji kina ajiyar zuciya?”
Abu ta yi maza ta ce, “Babu komai”.
Nan take kuma ta shigo da zancen Mus’ab don kawar da Inna Habiba daga wani zato.
“Yaron nan Mus’abu nake tunawa, ba qaramar jarumtaka ke gare shi, kin ga nisan wurin nan kuwa, amma tunda ya soma zancen auren nan bai tava rufa sati biyu bai zo garin nan ba”.
Inna Habiba ta ce, “Ai shi yasa kanshi Inna, baki ji Hausawa suna cewa, ‘wai sa kai wanda ya fi bauta ciwo ba?’ Tunda buqatarshi ta biya baki ga ya xauke qafarshi ba? Dama ai yaudara ce ya yi yanda zai samu, to ya samu ya yi dalilin da aka xauki Saddiqa aka kai mishi gari mai nisa, inda kuma ba ta da kowa sai Ubangijinta.
Dawowar nan da kika yi kuma ni na san da akwai wani abin da ya tsaya miki a rai baki faxe shi bane kawai, na kuma san da wuya in ba kan baro Saddiqa da kika yi a garin nan bane ita kaxai”.
Abu ta yi maza ta katseta da cewa, “Ke kam daa mita kike, mijinki yana haquri dake, in kika tasa magana a gaba kin rinqa yinta kenan kina nanatawa. A kan ‘yarki ne aka fara xaukar wata yarinya aka kaita nesa? ‘Yammata naw ne aure ya raba su da iyayensu da garuruwansu ya kai su inda basu da kowa? Ashe darajar aure ba zai sa ayi abin da ya fi haka ba?”
Ta ce, “Uhm! Zai yi ko in ce yana yi, amma ganewa na yi Inna farin cikinki da kuzarinki lokacin tafiyarku ya fi na yanzu da kika kai mita ita yawa, sannan ximbin tsarabar da kika taho da ita bai sa annurin fuskarki daidaituwa ba, ni na san kin fi kowa murnar ba shi ita da aka yi daren jiya, kuma duk da gajiyar dake gareki ina jin motsinki ba wani baccin kirki kika yi ba”.
Abu ta katseta, “To ya ya zan yi in yi bacci bayan kin sani na sha qwayoyin da ban san kansu ba?”
Ta yi maza ta kalleta ta ce “Panadol na baki Inna, maganin gajiya ne”.
Ta kawar da kanta ta ci gaba da cewa, “Ni ai na sanki Inna, ina ganin kamar ma babu wanda ya kai ni saninki tsawon rayuwata ina tare dake ne, bana kwana bakwai ban zo inda kike ba, babu yanda za ayi wata matsala ta voyan nan da kin yarda kin gaya min yanayin da kika barota a ciki don mu san mafita, na riga na gargaxeta in zama da shi akwai vacin rai a ciki ta yi hanzarin dawowa gida, na kuma ba ta kuxi tare da ita kar ta kuskura ta ce za ta yi haquri da shi, don kuwa ba abokin haxinta bane, ya fi qarfinta. Tana isowa kuwa zamu san abin da muke ciki ni da Yaya, don shi ya haxa ba kuma zai bari a cuci marainiya ba, na yi mata sanadin faxawa cikin baqin ciki da takaici irin na matan da basu yi sa’ar mazan aure ba”.
Abu ta zuba mata ido tana kallon ta, jimawa can ta ce, “Ai sai ki yi, ke dama ai bakya yi mishi fatan alheri sai dai tunanin abin da in ya faru ba zai zama mai daxi ba”.
Ta miqe ta kama tafiya, ta ce, “Ki xorawa yara kayana su kawo min”.
Inna Habiba ta biyota tana cewa, “To Inna ku huta gajiya sai na zo duba ku”. Ta ce, “To”.
AJAKUTA
Satin Saddiqa biyu a garin Ajakuta, tana kwance kan doguwar kujera a falonta, kallon t.v take yi, sai dai a zahiri ne kawai idonta yake kan kallon, hankalinta ba a nan yake ba, kalaman Gwaggonta take tunawa.
“Fita harkarshi Saddiqa in har kika yarda kika ruxu da shi, to wahala kawai za ki sha, ba za ki xanxani komai ba game da daxin aure. Shi farin cikin aure ba a tarin dukiya yake ba, yana tare da zaman lafiya ne da kwanciyar hankali. Ki samu mijin da zai so ki ya yi tattalinki ya tarairayeki ya kyautata miki, ya gamsar dake cewar shi xin naki ne, shi kenan magana ta qare.
To ba za ki samu hakan ba wurin wannan yaron, don ba zai tava mallaka miki kanshi ke kaxai ba, ba za ki samu wannan daxin ba a wurinshi, manemin mata ne. ina jiye miki randa za ki ganshi da wata a irin kishin dake gare ki, ga ki da kishin matsananci”.
Ta tuna irin murmushin da ta yi a lokacin da Gwaggon nata take jaddada mata kishin nata, “Ni kishi ne dani Gwaggo?” Ta yi maza ta ce mata, “Qwarai kuwa, ai mu muka haifeki mu kuwa kishi wahalar damu yake yi”. Hawaye masu yawa suka zubo daga idanunta.
Abida ta yi sallama rungume da xanta a qirji, da sauri Saddiqa ta miqe tare da amsa sallamar, hannu biyu ta saka ta karvi yaron.
“Cavxijan! Ga wuri ga wuri amma sai yau kuka zo duba mu?”
Abida ta yi murmushi ta ce, “Yau xin ma nice na matsawa Baban Umar da qyar ya bari”.
Ta tave baki tare da zubawa Umar xin ido tana kallon shi cikin nazari, cikin nutsuwa ta ce, “Lah! Kinga xan sati biyun da na yi ban ga yaron nan ba har ya qara qiba”.
Abida ta yi murmushi ta ce, “Ni da babanshi ne gayawa maigidan ana sallama da shi a waje”.
Fara’ar Saddiqa ta ragu, ta yi maza ta mane kai da kafaxa nuna alamar qi kafin ta ce, “A’a, ni bana magana da shi”.
Abida ta zuba mata ido ta ce, “Bakya magana da shi wane irin zama kuke yi? Ya yi miki wani abu ne?’
Ta yi shiru hawaye suka soma zubo mata shar-shar-shar! Ta ce, “Ni na fi so ya kaini gida ne”.
Ta sake kallonta, ta xan yi murmushi ta ce, “To kawo min ruwa in sha ko baki da komai ne a gidan?”
Ta yi maza ta miqe sbaoda tunawar da ta yi ashe ba ta gabatar mata da komai ba. Maimakon taa ajiye mata yaron sai ta sanya shi a bayanta ta xaure shi da zanin dake jikinta, qafafuwanta suka fito har sharabarta ta bayyana.
Abida ta bita da kallo sai da ta shige cikin kicin xin dake wurin sannan ta mai da kallon nata cikin falon, tuni ta gano canjin da falon ya samu a sati biyun da ta shigo cikinshi ba ta dawo ba.
Saddiqa ta fito riqe da tire mai xauke da abubuwan marmari na kayan itace, inibi, tuffa, ayaba, gwaba har da su ube ta ajiye mata.
Ta koma gefe ta zauna. Abida ta ce, “Ya ya za ki ajiye min ki koma gefe? Ai in kina so in ci to ki matso mu ci tare muna hirarmu”.
Ta yi yanda Abidan ta ce saboda tana girmama karva da xawainiyarsu da ta yi ta yi a gidanta, sai take ganinta kamar ‘yar’uwarta, hira ta yi daxi a tsakaninsu, duk da dai yau ma Abidan ce mai ba da labarin.
Sai ga Mus’ab ya shigo yana murmushi, ya ce, “Sai yau su Umar suka zo duba amarya?”
Ta yi murmushi ta ce, “A to, maigidan ne ya ce wai ba kowanne lokaci ake zuwa gidan amare ba, musamman ma da yake ya ga ba fita kake yi ba, wai ko ofis baka zuwa”.
Mus’ab ya yi murmushi daidai lokacin da ya kama Umar ya zare a bayan Saddiqa, ya ce, “Kin kama yaro kin xaure kina zaune?”
Sai da ya xan yi wasa da shi kafin ya kalli Abida ya ce mata, “Gidan ne babu kowa in na fita sai ta zama ita kaxai, ba ta kuma saba da hakan ba, sannan ni ke yi mana girki ba ta yarda ta fara shiga kicin ba wai tana amarci”.
Abida ta riqe baki tana dariya ta ce, “Ai kuwa in dai haka ne to lallai kuna buqatar mai taya aiki, za ta yi muku girki in baka nan, kuma za ta taya Aisha zaman gidan, in yaso randa ta wattsake sai ta karvi girkinta ita ta rinqa wanke-wanke da shara, tunda ni dai ban ga amfanin a barwa mai aiki girkin gida ba matuqar ba yawan nashi ya kai yawa bane”.
Ya yi murmushi ya ce, “Ita ma amarci ne bari ta wattsake ki gani, gwanar girki ce amma a yanzu dai kam taimaka ki samar mana mai aikin”.
Ta ce mishi, “To, yarinya kake so ko babba?”
Ya yi kamar zai faxa sai kuma ya fasa, ya ce, “Da yake bani za a kawowa ita ba, ita matar gidan ta gaya miki wacce iri take so kawai, ni a wurina in dai ta yi aikinta shi kenan”.
Yana jin ta soma tambayar Saddiqa ra’ayinta ya miqe rungume rungume da Umar a qirjinshi ya tafi wurinshi. Yana barin wurin suka shiga hirarsu mai daxi suna dariya.
Mus’ab da Idris suna tasu hirar a nashi wurin.
“Kai angwaye suna qibar jin daxi kai kana zubewa?”
Mus’ab ya yi tsaki ya ce, “Wane angwanci nake yi ni da amarya ba ta magana dani, ba ta ma yarda ta ci abinci sai in ta ga zan danneta in xura mata”.
Idris ya qyalqyale da dariya ya ce, “Borin nata har ya kai haka?”
Ya yi tsaki tare da sosa gefen fuskarshi da yatsanshi.
“To amma wannan borin ai ya yi yawa, in da nine kai sai in kawo qarshen abin gaba xaya, in yaso in yi ta yin rarrashin mai dalili”.
Mus’ab ya yi shiru kamar bai gane abin da yake nufi ba, ya sako musu wani zancen, suna hira Mus’ab yana kallon agogo, a zuciyarshi yana tunanin lokacin xora girki ya yi, sai dai ya ya zai yi ya yiwa Idris wannan maganar. Tashi zai yi cikin hikima ko kuwa shiru kawai zai yi?
Saddiqa tana tare da Abida suna hira, ganewar da Abida ta yi maigidan ne mai girkin gidan ya sata kallon Saddiqa ta ce mata, “To muje kicin mana muna hirarmu muna aikin abinci sai mu yi mu gama kafin baban Umar ya ce mu tafi”. Ta ce mata, “To”.
Suna girkin suna zancensu, mafi yawancin maganar Abida ce take yi mata, nasiha ne kuma kan ta daina fushin da take yi ta yarda ta zauna lafiya da mijinta.
Saddiqa ta ce, “Uhm!” A zuciyarta kuwa tunani take yi, wannan ba ta san halin Yaya Mus’ab ba. Kalaman Gwaggonta suka sake zuwa mata.
“Zamanki da shi wahala ne saboda kishinki”. Ta xan rage fara’a kafin ta ce, “Gwaggo kullum sai ki rinqa dangantani da kishi bayan na ji an ce bai da kyau”.
Gwaggo ta ce, “Eh, to ya dai wahalar da mace mai shi kam, musamman a ce ba ta yi dacen mijin da zai tausaya mata ba, tausayinki ba zai sa wannan yaron ya haqura da son ranshi ya barki ki mallake shi ke kaxai ba”. Ta girgiza kai don qara tabbatar mata da abin da ta gaya matan.
Abida ta katse tunanin nata ta hanyar tambayarta cewa, “Kin san daxin amarci kuwa?”
Ta xan yi murmushi kaxan da nufin zolayarta, ta ce, “Da kin san yanda abin yake da baki tsya kina yi muku wannan takurar ba, kin qi ki kwantar da hankalinki balle ku ji daxin zaman naku, kin tsangwameku gaba xaya kun zube kun rame, ban ga abin da kika rasa a wurin mijinki ba, a shirye yake ya kyautata miki. Dubi yanda ya qara qayatar miki da wurinki a sati biyunki na zaman wurin kawai, in kika saki jiki da shi kina zaton akwai wani abin da ba zai yi miki ba”.
Ga mamakinta sabodaa ta saba yin magana Saddiqan tana shiru, sai dai ta saurareta kawai sai ta ji ta ce mata, “Ai ni ba abinshi nake so ba”.
Da sauri Abida ta kalleta cikin nutsuwa ta tambayeta, “Me kike so nashi?”
Ta yi shiru ta sunkuyar da kanta qasa nuna alamar jin nauyi.
“Ni yarki ce Aisha, in baki yi magana dani ba da wa za ki yi? Randa Abu za ta tafi da na zo mata sallama kuka ta rinqa yi tana cewa, in riqe ki amana.
Jin hakan yasa ita ma Saddiqan ta soma yi mata kukan, ba ta hanata ba sai ta ci gaba da yi mata magana.
“Ni dake dukkanmu jirgi xaya ne ya xauko mu, auren zumunci aka yi mana, yanda na san ba zan ce auren dole aka yi min ba, haka kema na san bana dolen bane. Don kun zo kun samu abin da ya