Showing 24001 words to 27000 words out of 31859 words
Chapter 9 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt
dawo mishi da xansa gida, wanda dole ta yi hakan.
Yana dawowa sai ya sanya shi a makarantar wanshi da suke uba xaya. Maimakon Mus’ab ya yi karatu sai ya zama babu abin da ya sanya a gaba sai rigima da dukan ‘ya’yan jama’a, daga nan aka mai da shi wata makarantar. Nan ma bai yiwu ba har dai Malam Abdullahi ya gaji ya dawo da shi tashi makarantar, in da ya xauki matakin horo mai tsanani a kanshi, ba shi ba, ba matarshi ba wacce babu wata mu’amala tsakaninta da shi in ban da duka, saboda vacin ranshi da take ji.
Mus’ab ya zama ko maganar iyayen nashi ya ji sai ya tsorata, maimakon al’amura su gyaru sai suka qara lalacewa, ya zama baya iya zaman gida sai bin jeji kamo tsuntsaye ko wanka a rafi tare da abokai, in kuma dare ya yi maimakon ya dawo gidansu kamar yanda sauran abokanshi ke yi, sai ya rinqa rave-rave saboda ya san akwai hukunci mai tsanani da yake jiranshi a gida.
Ana cikin haka ne aka kwana ba a ga Mus’ab ba, aka yi nema har aka gaji gaba xaya gidajen dangi babu inda ba a je ba a same shi ba, sai kawai Malam Abdullahi ya ganshi cikin kasuwa tare da abokanshi suna turaWheelbarow. Wannan shine abin da ya fusatar da shi har ya xauke shi ya kai shi qasar Bagah wurin wani malami da ya sani don ya karantar da shi Alkur’ani.
Zaman Mus’ab a Bagah sai ya samu kanshi cikin wata irin rayuwa da bai saba da ita ba, saboda a gida ko an yi mishi hukunci mai tsanani to zai kwana a wuri mai kyau mai tsabta, ya kuma ci abinci mai kyau.
Nan kuwa babu ko xaya, bai xauki wani lokaci ba sai wahala ta same shi, yunwa ta kama shi. Bai iya cin abinci in ba ya ji kamar zai galabaita ba, saboda kasancewar shi mai tsantsani da qyama, ga aikin gona in da damuna ne, don malamin ya kan ba da su suyi aikin qwadago a ba shi kuyxin, in kaka ta zo kuma ya kai su roro, ga kuma tallan da matar malam ke xora musu ranar kasuwa.
Rannan Mus’ab yaje tallan funkaso a kasuwa cinikin da ya yi ba mai yawa bane, yana cikin wannan zullumin sai kuma wani xan tasha ya kira shi ya ci mishi fankaso, sai da ya qoshi sannan ya qi biyanshi, ya yi kuka har ya gaji bai tausaya mishi ya ba shi kuxin ba, har ya gaji ya shiga tunanin yanda zai yi, don ya san in ya koma gida babu kuxin nan, to ko shakka babu a mari zai kwana.
Don haka ya gwammace gara mishi kwana a kasuwa. Tunanin da ya yi za a iya turo almajirai ‘yan’uwanshi su nemo shi yasa shi yagar takarda ya qunshe sauran fankasonshi ya maqa, ya faki idon mutane ya shige cikin wata motar katako da ake yiwa lodin buhuna ya vuya a ciki.
Ana idar da sallar isha’i direba ya tashi mota ya nufi Kano, inda zai kai kaya. Wajen asuba suka isa, cikin hikima Mus’ab ya fice ba tare da direba ko kwandasta sun ganshi ba.
Kwana biyu yana rave-rave a tasha, daga wurin mai wannan abincin ya koma wurin wancan, yana yi musu wanke-wanke suna ba shi abinci yana ci yana qoshi.
A nan wurin abincin ya gamu da wani direba wai shi Xanjuma, shine ya ce mishi “Kai wanke-wanke ai aikin mata ne, sai ko maza masu matacciyar zuciya. Me zai sa ka zauna kana yi zo muje ka rinqa bina zan koya maka tuqin mota”.
Shi kenan sai Mus’ab ya koma bin motar Xanjuma, yau suna nan gobe suna can, daga wannan garin su nufi wancan. Saboda son da Xanjuma ke yiwa Mus’ab yasa ko nawa za a biya shi ba a xaukar kayan Misau, saboda labarin da Mus’ab xin ya ba shi. Wurin Xanjuma Mus’ab ya koyi shan sigari da wiwi da kuma neman mata, a dalilin kwanan da suke yi a gidajen karuwai in sun sauka a wasu garuruwan.
A garin Bagah kuwa watanni huxu cif Malam yana neman Mus’ab babu shi babu dalilinshi, don haka ya shirya ya tafi Misau cikin qarfin hali ya sanar da iyayen Mus’ab labarin vatanxansu.
Hankula suka tashi aka shiga neman Mus’ab ta ko’ina, ta inda ake zato da ta inda ba a zato. Shekara guda ana abu xaya har dai aka gaji aka haqura aka dangana aka barwa Ubangiji lamarin aka koma roqonshi ya dawo da Mus’ab lafiya.
Shekaru uku Mus’ab yana tare da Xanjuma, a lokacin nan babu wani shaqiyanci da bai gama qwarewa a kai ba. Suna yaba a can a Lagos cikin tasha suna sauke cittar da suka tafi da ita daga arewa, shi kuma Malam Gixe wan Habiba ya je saro kaya kamar yanda ya saba, sai kawai suka yi kicivis da Mus’ab a cikin tashar.
Nan Mus’ab ya yi qoqarin vace mishi amma ina? Ya riga ya ganshi ya kuma gane shi. Ganin haka yasa ya haqura ya kama shi.
“Kai ni wurin wanda kake tare da shi”.
Ya ce, “Ni kaxai ne Kawu”.
Babu yanda bai yi da shi ba amma ya qi nuna Xanjuma, saboda yana tsoron abin da zai samu Xanjuman. Don haka sai ya taso shi suka dawo Misau ya dawo da shi gaban iyayenshi, shi kuma ya koma Bauchi inda yake da zama.
Dawowar Mus’ab gida gaban iyayenshi maimakon su daidaita sai al’amura suka qara lalacewa, tun kafin ya zama taqadarin gaske iyaye da sauran dangi sun ce ya fi kowa, to balle yanzu da ya je ya koyi taqadaranci a yawon duniya.
Duk da mahaifinshi ya yi ta yi mishi taimako don ganin ya nutsu ya zauna a gida, ya mai da hankalinshi da nutsuwarshi kan karatu da son karatun, cikin ‘yan makonnni kaxan ne sai ya dangana ya haqura da son zaman nashi, saboda ganin irin halayen da ya dawo dasu.
Labari ya watsu cikin dangi cewar har sigari Mus’ab yake sha, a wancan lokacin kuwa kusan sai a ce shi kaxai ne yake shan sigarin. Ba a yi nisa ba sai aka kama shi yana koyawa yara sa’o’insa shan sigarin, dama waxanda basu kai shi ba.
Inna Habiba wacce take ganin Mus’ab ba komai bane face jarrabawa ga zuriyarsu, saboda abin kunyar da yake ja musu ta rinqa fatan ganin ya koma inda ya fito, ta qauracewa magana da shi, ko ya yi mata ba ta amsawa, ta qauracewa duk wata mu’amala da shi.
Ran nan Malam Abdullahi yana makarantarshi yana ba da karatu wani mutum ya zo mishi, tun dagaa nesa yake aiko mishi da maganganu.
Almajirai suka miqe da nufin su tare shi don jin kalaman da yake yiwa malaminsu, ya yi maza ya dakatar dasu cikin zuciyarshi dai ya san Mus’ab ne ya je mishi, addu’a yake yi kar ya zama ko ya lalata musu wata yarinya ne, don abin da bai bayyana nashi ba kenan.
A nutse ya tambaye shi dalilin cin zarafin. Sai ya ce mishi, “Xan isakn xaanka da ka haifa ka kasa yiwa tarbiyya ka barshi yaa lalace yake kuma nema ya lalatawa wasu nasu, yana nema ya mayar mana da ‘ya’ya mashaya sigari, kai ba ita kaxai ba har da qwaya”.
Malam Abdullahi wanda bai tava ganin qwaya ko saninta ba sai ko yanzu, ya yi shiru sai da mutumin nan ya gama bambamin shi ya yi shiru don kanshi, sannan ya xago ya kalle shi ya ce mishi, “Ka yi haquri kan laifin da aka yi maka, zan kuma xauki matakin da hakan ba zai sake faruwa ba, amma ba don ni ba don gaba zan baka shawara, kar ka sake yiwa wani uban gori kan lalacewar xanshi, ba abun ne da yake samun iyaye a kan suna so ba, musifa ce da ya kamata a tausaya musu a kai.
In ka lura da rayuwar Mus’ab sai ka ga tun farko makaranta na kai shi, da yanda na so na samu da ba haka ba. To amma har yanzu ban fidda rai ba a kanshi, don babu mai fidda rai ga samun rahamar Ubangiji sai tavavve”.
Mutumin yana tafiya Malam Abdullahi ya suri takalmanshi ya shiga gida, ya shiga xakin da Mus’ab ke kwance yana ta bacci, yasa hannu ya tashe shi ya tashi ya zauna suna kallon juna.
Ya ce, “Saurareni da kyau Mus’abu, ka ga garin nan garin iyayenmu da kakanni, yanda duk nake da son zaman ka kusa dani dole ne in haqura, don ba zan barka ka zamewa zuriyarmu abin gori ba.
Saboda haka ina so ka tashi ka xauki qunshin kayanka ka bar garin yau, yanzu kuma ka tafi duk inda ka ga dama. Na roqe ka kar ka sake dawowa matuqar baka shirya barin abin da kake yi ba, don haka tashi muje ungo kuxin mota”. Ya ajiye mishi ya juya ya fita ya bar gidan.
Bilkisu wacce ita ke bin Mus’ab tana jin abin da mahaifinsu ke gaya mishi, ta ruga da gudu ta nufi gidan Abu tana kuka ta kai mata labarin abin da ke faruwa.
Cikin sauri suka taho tare, ta samu Mus’ab a tsugune gaban babanshi a zaure riqe da qullin kayanshi.
“Me ke fa ruwa Malam?”
Ya ba ta labari. Ta ce, “Ka yi haquri?” Ya yi maza ya ce, “A’a, Inna da kamar shi kaxai yake yin abinshi da sai in qyale shi, tunda na san ana yi mishi addu’a. amma tunda har zai koyawa wasu ai gara ya tafi kawai”.
Kafiyar Malam Abdullahi kan lallai sai Mus’ab ya tafi ya sanya Abu shiryawa ta tasa shi a gaba ta nufi Bauchi da shi gidan xanta na fari wanda yake shine wan Habiba wato Malam Gixe.
Zuwanta na farko gidan shi ba ta kuma kwana ba. Malam Gixe yana da matanshi na aure guda biyu. Mama wacce take matarshi ce ta zumunci abokiyar wasanshi, kuma Innar Mus’ab saboda abokiyar wasan Habiba ce, ga shi kuma wabin ‘ya’yanta take yi, ita ya baiwa Mus’ab. Sai amaryarshi Raliya wacce a lokacin ‘ya’ya uku ne da ita.
Yana zaune tare da matarshi a xakinta, ya kalle ta cikin nutsuwa ya ce mata, “Mama ga fa yaron nan an kawo shi wurinmu, ba sai na ce miki komai a kanshi ba xanki ne, ba kuma a kanshi kika fara riqe ‘ya’ya ba balle in ce wani sabon abu naa kawo miki, taimakeni a kanshi kamar yanda kika saba taimakona a baya”.
Ta ce, “Babu komai Malam, Ubangiji dai ya shirya mana”. Ya ce, “Amin”.
Mama mace ce mai haqurin gaske, gata da juriya da kuma iya zama daa jama’a.
Cikin xan lokaci kaxan na zaman Mus’ab a wurinta sai ta gano yanda yake, saboda sa ido da ta yi a kanshi. Naan da nan sai ta gane hanyar tafiyar da shi, ganewar da ta yi babu abin da yake irin ayi mishi faxa yasa ta yi qoqarin janshi a jikinta suka yi matuqar shaquwa, ta yi hira da shi ta yi mu’amala kullum za ta nuna mishi muhimmancinshi.
Shekarunka shaa biyar ne fa amma har ka iya shan sigari, ni kunya nake ji a ce qannenka sun gane abin da kake ciki, kar hakan ya jawo zubewar girmanka a wurinsu, tunda kai ne ya kamata suyi koyi da kai, in suka yi kuskure a gaya maka don ka gyara musu. To sun gani a wurinka ya ya kenan?
Da irin waxannan kalaman da nasihohi da ja a jiki, maimakon gidansu da ba a hulxa da shi sai ya ga a nan kullum tare da Kawu Gixe yake cin abinci, duk da sun san halin da yake ciki.
A haka sai Mus’ab ya soma jin kunyar halayenshi, ya soma voyewa don kunya ba don tsoro ba, a haka sai ya zama mai ganin girma, daraja da kuma qaunar iyayenshi, musamman Mama, bai son ganin ranta a vace ta ce laifinshi ne ya vata mata rai, sai ya zama ya yi watsi da shaye-shaye.
Sallah kuwa ba sai an ce mishi tashi ka yi ba, shi kuma dama jarumi ne mai aiki saboda ya riga ya saba da wahalar rayuwa. A haka sai ya samu farin jini har wurin manyan unguwa, saboda aikin da aka sa shi da ma wanda ba a sa shi ba shi yi yake yi.
Kawu Gixe ya sanya shi makarantar boko, inda ya fara daga sakandire aji biyu a dalilin a yawace-yawacen shi ya xan koyi wasu abubuwa.
Mus’ab ya kama karatu cikin hazaqa da basira, ga karatun addini da dama tun farkon zuwan shi gidan ya kama a wurin Kawun da Mama, da kuma makarantar Allon dake unguwar.
Cikin xan taqaitaccen lokaci sai ya zama har malamai sun san shi, a wannan lokacin ba a cewa ga farin cikin Kawu Gixe da Mama.
Mus’ab yana aji uku a makarantar sakandire Innarshi ta haifi ‘ya mace, babu mai kwatanta farin cikin Kawu Gixe kan wannan haihuwa da aka yi mishi, to balle kuma Mus’ab da bai tava so ko jin wani a matsayin da yake jin Mama a rayuwarshi ba.
Sai ya xauki son duniya ya xora a kan yarinyar, duk wata hidima ta Aisha ko Saddiqa yanda Mama ke kiranta shi yake yi, har wankinta kan ya tafi makaranta ya gama komai. Wankin Mama da na Saddiqa, share-share da zuba ruwa a randuna. In ya dawo kuma ya yi reno, duk inda za shi yana maqale da ita, ko wace qwandala ya samu ita yake kashewa, suka yi matuqar shaquwa.
Saddiqa ta taso cikin kulawa, tsabta da kuma tarbiya. Har Mus’ab ya gama karatunshi na sakandire ya samu shiga A.T.B.U labarin da Innarshi ke ba shi na yanda take fama da rikicinta in baya nan yasa shi xaukar matakin ya rinqa zuwa gida duk qarshen mako, wato juma’a da yamma, lahadi da safe ya koma. In ya zo xin kuwa zai yiwa Innarshi da Saddiqa, da ma Kawu Gixe wankin kayansu ya goge.
Suna nan a haka Mus’ab yana karatun shi, shekara ta uku a jami’a aka zo kiran shi ranar wata talata da yamma. Ya hanzarta tahowa gida saboda a zaton shi jikin Saddiqa ne ya tashi, saboda ranar lahadin da ya koma ya barta tana zazzavin baqon dauro.
Yana isa gida ya samu ana zaman makoki, ya yi zaton Saddiqa ce ta rasu, sai daga baya ya gane Innarshi ta rasu a sanadin ciwon cikin da ta tashi da shi a ranar, wanda bai wani xauki lokaci mai tsawo ba.
Mus’ab ya kixime ya yi kuka har ya ji tamkar bai da sauran hawaye, ya samu kanshi cikin wani matsayi da ba zai kwatanta ba.
Da aka yi kwana bakwai Kawu Gixe ya zaunar da Mus’ab a xakinshi yana yi mishi nasiha.
“Ai haka rayuwa take Mus’ab, Mama kwananta ya qare bamu da abin yi sai haquri da bin bayanta da addu’a, sai ka shirya in anjima da yamma sai ka koma wajen karatunka, ita ma Habiba na gaya mata in za ta koma Misau ta tafi da Saddiqa ta koma can wajenta da zama”.
Mus’ab bai iya ce mishi komai ba in ban da kukan da yake ta yi. A haka ya fita ya je ya yi mata sayayyar ‘yar tsarabe-tsaraben yara ya kawo mata, shima ya shirya ya koma wajen karatunshi.
Sati biyu a jere Mus’ab yana zuwa gida kamar yanda ya saba, daga nan ya xauke qafa ya yi zamanshi a makaranta har tsawon wata guda.
Ran nan Kawu Gixe da kanshi ya je ya same shi, Mus’ab yana isowa inda Kawu Gixe yake ya tsuguna gabanshi ya kama kuka.
“Haba Mus’ab, in babu Mama ba za ka zo gida ba? To ni fa? Kuma ai akwai wata uwar taka a gidan, ga kuma sauran ‘yan’uwanka. Ba za ka tausaya min ba? Na rasa Mama kuma in rasaku ‘ya’yanta duka? Babu Saddiqa babu kai, to da wanne zan ji?”
“Ka yi haquri Kawu, na so zuwa wannan satin sai na ce bari in je Misau in dubo Aisha, amma zan zo gida sati mai zuwa”.
Suka xan tattauna yaa kawo bain da ya zo mishi da shi ya ba shi sannan ya tafi.
Tunda Mama ta rasu sai Mus’ab ya rasa farin ciki, kewa ya addabe shi, ya rasa yanda zai yi ya ji daxin zuciyarshi. Sai ya shiga tunanin yin nesa da gida, nesa da dangi, nesa da mutanen da ya sani. A ganin shi har da mu’amalarshi da sune ya hana shi mancewa da rashin da aka yi mishin.
Sau biyu yana roqon Kawu Gixe ya amince mishi neman tafiya qasar waje don ci gaba da neman iliminshi. Bai yarda ba saboda a ganin shi a hali da shekarun da Mus’ab ke ciki kusan ashirin daa biyu zuwa da uku, ba wani wuri ya kamata ya tafi ba, qarasa karatun shi ya kamata ya yi, ya yi aure shima ya samu nutsuwa tare da iyalinshi.
Kafewar Mus’ab tasa Kawu