Showing 27001 words to 30000 words out of 31859 words
Chapter 10 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt
ya haqura, sai dai kuma ya qi yarda da barin karatun nashi saboda ganin yana kusa da kammala digirinshi na farko. Don haka a daddafe Mus’ab ya gama watanni biyar, bayan nan kuwa ya yi sallama da gida da dangi ya nufi qasar Italy, inda yaje ya yi digirinshi na biyu, ya karanta Archtectual Engineering, ya kuma yi zamanshi a can har tsawon shekaru bakwai.
Zaman da Mus’ab ya yi a can lokacin ne ya koma kan xabi’unshi na sigari, neman mata ya haxa har da barasa. Hakan kuma ya qara wani rashin jituwar tsakaninshi da mahaifiyar shi.
Abu ta kalle shi ta ce, “Wannan ne dalilin hana shi auren Saddiqan?”
Malam Abdullahi ya ce, “To Inna in zamu bi qa’idar da muke bi wajen ba da aure ayi bincike kamar yanda muke yiwa mazan qannen shi mata, ai ba zai ci jarrabawar ba. Don haka ki yi haquri”.
Ta ce, “To ai babu laifi”.
Ta tashi za ta fita Malam Abdullahi yana ce mata, “Ga goro”. Ta ce, “Nima ina da shi a gida”. Ta yi tafiyarta ta barsu.
Saddiqa kuma tana kwance a xakinta ta qosa ta san me ke faruwa a gidan wanda aka qi shaida mata. Tana cikin wannan tunanin yaro ya kwaxa sallama a tsakar gida ya ce, “Wai ana sallama da Saddiqa in ji Sadisu?’
Kusan minti goma da kiran nata babu alamar za ta fita. Innarta ta leqa xakin ta ga kamar Saddiqan ba ta ji ana kiranta ba.
Ta xaure fuska ta ce, “Gaskiya ni ba za ni hira yanzu ba da tsakar ranar nan”.
Inna ta tunzura ta ce, “Wacce magana ce Saddiqa ke yi? Ashe ba ina jinki ba shekaran jiya da ya zo kika ce kin daina hirar dare kamar wasu munafukai, jiya ya zo da yamma kika ce sanyi kike ji. Yanzu ya dawo da rana kin ce ba za ki yi hirar tsakar rana ba, to sai yaushe? Na ce sai yaushe zai zo ki fita?”
Ta tsare Saddiqa da idanuwanta, ita kuma ta sunkuyar da kanta qasa.
“Tashi ki fita tun muna shaida juna dake cikin mutunci”.
Ta tashi ta fita tana kuka. Inna ta koma wurin mijinta hankali a tashe ta ce, “Malam yaron nan fa zai kangarar da Saddiqa mu kasa jin daxinta”. Ta ba shi labarin canzawar da Saddiqan ta yiwa Sadisu.
Malam Abdullahi ya ce, “Bari zan tura iyayenshi su zo in sanya musu ranar biki sai ayi kowa ya huta”.
Ta ce, “To madalla, in ka yi hakan ai kuma shi kenan magana ta qare kenan”.
Abu tana isa gidan ta samu Mus’ab tare da wasu tsofaffin abokanshi da suka zo mishi hira kan qatuwar tabarmarta a qofar gida sai cin gasssun kaji suke yi ana hirar da ana dariya. Sai da ta tsaya suka gaisa sannan ta wuce cikin gida.
Kusan minti goma da shigarta kafin Mus’ab ya nemi izininsu ya shiga wajen Abu. Bayan ya bayar da kuxin qaro masu kajin saboda qaruwar ‘yan hira.
A tsakar gida ya samu Abu tana ‘yan kintse-kintse.
“Wa ya zuba min ruwa a randa ne?”
Ya ce, “Nine na kuma sa aka share miki tsakar gida”.
“Ubangiji ya yi maka albarka”.
Ya ce, “Ameen”.
Ya bi bayanta zuwa cikin xaki.
“Ya ya kuka yi dasu Baban Abu?”
Ta ce, “Dukkansu sun qi, ko da yake da na je gidanka ai a cikin maye na same ka, sai yaushe za ka kama kanka ka zama mutum na sosai ba riga ba Mus’ab? Sai yaushe. In na yi nufin taimakon ka kan auren yarinyar sai kuma tausayinta ya kama ni, ba za ta iyaka ba ka fi qarfinta, ba za ta iya da kai ba Mus’abu”.
Ya matsa kusa da ita yana kallon ta ya ce, “Haba Abu, dambe zamu rinqa yi da ita ne da za ayi ta cewa ba za ta iya dani ba? Nine fa nake sonta, kin tava sanin so kuwa? Baki san mutum bawan abin da yake so ne ba”.
Harara ta galla mishi kafin ta ja tsaki.
“To gaskiya zan gaya miki Abu, in na rasa Aisha kema za ki rasani, don tafiyata Italy zan yi in yi zamana ba zan sake dawowa ba”.
Ta sake jan wani tsakin ta ce, “Uhm! Sai me in ka yi hakan?”
Ya yi murmushi ya sake matsawa kusa da ita ya ce, “Taimake ni Abu ki rufa min asiri kar ki bari su rabani da yarinyar nan, taimake ni ki gaya min abin da kike ganin ya dace in yi”.
Ta ce, “Ka tafi ka koma wurin aikinka ka ga yau kwananka uku, zan yi nazarin abin yi ai ba bikin suka sanya ba”.
Ya ce, “To Abu”. Ya ciro kuxi masu yawa ya ajiye mata ya ce, “In kin yi min addu’a ki rinqa haxawa da sadaka”. Ta ce mishi, “To”.
A waje ya yi bankwana da baqinshi bayan su ma ya yi musu alheri, sannan ya nufi gidan iyayenshi.
A waje ya samu Saddiqa tana sharar qofar gida, ya ce, “Yauwa Aisha, ai gara ki shareni kinga shi kenan sai a bar mikini”.
Ta xago ta kalle shi fara’ar dake fuskarshi ta kau, cikin sanyin jiki ya isa gareta.
“Kuka kika yi haka? Me ya same ki?”
Ta soma wani kukan.
“Anyi miki wani abu ne?”
Ta yi shiru. Ya ce, “Gaya min mana, ko kuwa nine na ja Inna ta yi miki faxa?”
Ta ce, “A’a”.
“To mene ne?”
Tana kuka take gaya mishi “Bana jin daxi, ban san abin da ya same ni ba, qirjina yana yi min nauyi”.
Ya qara matsawa kusa da ita ya ce, “Yi haquri Aisha, don wannan kar ki rinqa kuka, yawanci haka mutum ke yi in zai girma. Yanzu na zo ne mu yi sallama zan koma Ajakuta”.
Da sauri ta kalle shi ta ce, “Yanzu?”
Ya ce, “Eh, ki yi min addu’a kawai bari in shiga gida in yi musu sallama, ki jira ni a nan”.
Ta ce mishi, “To”.
Da sauri ya shiga ya fito ya sameta a inda ya barta, ya xauko zoben da yake sanye da shi ya matsa kusa da ita ya ce, “Kin gani Aisha zobe ne ya yi min kyau, sai na yiwa yatsanki sha’awarshi, yngo saka mu gani”.
Ba ta yi musu ba. Ya yi mata dai-dai, ya kuma dace da yatsun nata.
Ta xago yatsun tana nuna mishi, “Ka gani”.
Ya yi murmushi ya ce, “Dama yatsun masu kyau ne Aisha, taimakeni ki yi min alqawari ba za ki cire zoben a jikinsu ba”.
A hankali ta buxe baki ta tambaye shi, “Babu wani abin da yake faruwa kuwa?”
Da sauri ya ce mata, “Akwai, sai dai tunda su Innan basu gaya miki ba to ki yi haquri lokaci zai yi da za ki ji komai, kin gane?”
Ta ce mishi, “To”.
“In gaya miki wata magana?”
Ta yi maza ta ce mishi, “Eh”.
A hankali ya ce mata, “Kina da kyau Aisha, kul kika yarda wani abu ya dameki, ni zan tafi na roqeki ki rinqa yawan tunawa dani kina tausayina saboda bani da kowa babu wani wanda yake sona, Inna ce kawai dama to na riga kuma na rasata, kin gane?”
Ta ce mishi, “To”.
Kwana uku da isar Mus’ab Ajakuta yana kwance tamkar mara lafiya, wurin aikinshi ma ranar Mondy bai iya zuwa ba, yana gida abin da ya yi matuqar tayarwa Jennifer hankali duk da ba kula juna suke yi ba.
Mus’ab yana kwance Sani yana zaune a gefenshi ya ce, “Wai ni ciwon gaske kake yi ne ko damuwa ce ta yi maka yawa?”
“Gani nan ne kawai Sani, ka duba ka gani wai ‘yar wayar da nake samu muna ‘yar hirar ma ina tahowa sai Inna ta karve”.
Sani ya ce, “Nifa inda nine kai da tuni na tafi wurin Kawu Gixe na gaya mishi komai”.
“To ai Kawu Gixin ne ya ce ita ce wuqa da nama a kan maganar yarinyar”.
Sani ya ce, “Duk da haka tsananin ai ya yi yawa, ita yarinyar da alama ai in ta samu an ci za ta ce ba ta son wancan mutumin, sai kawai ka yi qoqari ta amsa da bakinta tana sonka”.
Da daddare suna hirarsu a falo bayan sallar isha’I sai ga Jennifer ta shigo, ganin Mus’ab a zaune riqe da karan sigari ya sata tambayar abin da ta fara gamuwa da shi.
“Wannan kuma wace ce na gamu da ita yanzu?”
Ya yi murmushi ya ce, “Gaisheni ta zo yi mene ne?”
Ta tave baki ta harare shi ta ce, “Ka dai ji kunya, yarinyar cikinka ka koma nema, wanan ai ba ta fi sha takwas ba, in ta yi qoqari ashirin”.
Ya ce, “Jennifer kenan, to ni xin dame na fi haka, ai nima yaro ne ba shi yasa kema kike biye dani ba”.
Jennifer ta zo har wuya ganin Sani yana dariya. Ta ce, “Ba laifinka bane ni na zo gidanka. Uhm! Tun farkon mu’amalata da kai da ka nuna kana sona sai da Felicia ta yi min kashedi a kanka ta ce kar in yarda za ka yi amfani dani ne kawai ka awurgar a lokacin da ka ga dama, bayan ka rabani da samarina na gaskiya”.
Mus’ab ya yi dariya bayan ya fitar da hayaqin sigarin, a hankali ya miqa hannu ya kaxe tokar kafin ya kalle ta cikin murmushi ya ce, “Sai dai baki ji kashedin da qawar taki ta yi miki ba, saboda kin mato a kaina, kinga santalelen yaro. Haka nan ita ma qawar taki da take yi miki kashedi, kashedin nata bai hanata amsa kiran da na yi mata ba sai da na gaji da ita na watsar don kaina”.
Ta yi magana cikin yanayin xaci, “Babu laifi, wata rana ba za ka yi ba, don wata matar ma dole ka ganta ka qyaleta”.
Ya ce, “Ehm, babu matsala tunda dai na samu na bi ta kanki ke da qawar taki ai ni shi kenan buqatata ta biya”.
Sani yana danne dariyar shi yana faxin, “Kai ku kam kuna da abin mamaki, in baku ga juna ba babu zaman lafiya, in kun haxu kuma sai kunyi faxa. Wace irin soyayya ce wannan? Kai Mus’ab ko gaishe ka aka zo yi wai sai anyi faxa da kai a baka da lafiyar ma?”
“A’a, to in an zo gaishe ni sai a zageni in qyale? Ta zo gaishe ni ta coge a nan?”
Sani yana murmushi ya ce, “Kema Jennifer har dake, mara lafiya ai kusa da shi ake zuwa. Dawo ta nan ki ji damuwar shi”.
Ya miqe ya fita ya basu wuri yana faxin “Dawo ta nan Jennifer in dai dubiyar kika zo yi da gaske ba qarasa shi kike son yi da baqaqen maganganunki ba”.
Mus’ab ya fara nishi “Wash! Ya kalle ta cikin murmushi, kafin ta ce za ta yi wata magana tuni yasa hannu ya cafkota ya shiga sumbatarta.
Sani ya shigo ya gansu ya yi kamar bai ga abin da suke yi ba, ya wuce ya yi tafiyarshi.
Saddiqa tana Misau ta rasa inda za ta sa ranta ta ji daxi, an sanya bikinsu da Sadisu sati biyu kawai aka xiba. Qunci da takaici ne suka gallabeta, sai dai in an tambayeta ba za ta ce ga taqamaiman abin da ya haddasa mata hakan ba.
Tana kwance cikin kasala da rashin sanin abin yi, wayarta ta yi motsi alamar saqo ya shigo a cikinta. Duk da ta daxe ba ta samu wayar Mus’ab ba saboda daxewar da ta yi ba ta riqe wayar ba, miqa hannu ta yi ta xauko wayar, ga abin da ya ce mata.
Aisha!
Mutane suna rayuwa, mutane suna mutuwa, wasu su ce sai anjima, wasu za su iya mantowa amma ni kam har abada kina cikin zuciyata.
Mus’ab Abdullahi!
Ta sake kallon kalmomin cikin tunani, ba ta gane komai game da kalamanshi ba. Ya ji labarin bikin ne? Ta tambayi kanta. Ta yi kamar ta kira ta tambaye shi sai kuma ta fasa.
Mus’ab yana kwance a xakinshi wasanni suke yi da Jennifer lokacin da wayarshi ta yi qara, a haka ya miqa hannu ya xauki wayar cikin sauri ya kaita kunnen shi.
“Hello Ishaq”.
Qoqarin faxin hakan ya yi saboda yanda Jennifer ke sarrafa shi.
“Yaushe rabonka da Misau?’
Cikin hanzari ya bar komai ya miqe zaune.
“Me ya faru?’
Ishaq ya ce, “Na fa ji kamar sun sanya bikin yarinyar nan, don shekaranjiya na je gai da Abu ita take bani labari”.
Mus’ab ya zama tamkar mutum-mutumi a zaune a kan gadon, ya rasa me zai ce in ban da gumi babu abin da ke keto mishi a jikinshi.
Jennifer ta kixime tana faxin “Me ya faru? Anyi mutuwa ne?” Tana qoqarin qanqame shi take faxin “Maman ka ce ta mutu”.
“Shut up Jennifer!”
Ya faxi da qarfi tare da yin jifa da ita ta faxa can gefe. Banxaki ya shiga ya yi wanka ya fito ya kama shirin tafiya ba tare da ya jira wayewar gari ba.
Sani ya shigo xakin saboda kiran da Jennifer ta je ta yi mishi saboda tsoratar da ta yi da yanayin Mus’ab da ta gani.
Cikin harshen Hausa yake yiwa Sanin bayani za su kasheni ne Sani, za su aurar da yarinyar nan Aisha suna son ganin na yi mutuwar tsaye.
Ita kuwa Jennifer sai faman sorry take cewa tana qoqarin rarrashi da kwantar da hankali.
“Bari in fito mu tafi tare kawai don bai kamata ka yi wannan doguwar tafiyar a wannan tsohon daren kai kaxai ba kana kuma tuqi”.
Tare suka fito da ‘yammatansu su biyu da dama suka kawo don su taya su kwana, suka sauke su a hanya suka wuce suka kama hanyar Misau.
Qarfe shida da rabi na safe Mus’ab da Sani suna zaune a falon Mus’ab xin a gidanshi na Misau, yana yiwa Saddiqa waya lokacin ta idar da sallar asuba.
“Me yasa za ki yi min haka Aisha? Me yasa?”
A kixime ta tambaye shi cewa, “Me na yi maka kuma daga ina kake maganar?”
A hankali ya ce mata, “Gani nan a gidana Aisha na zo Misau yau kuma maganar aurenki ya kawo ni, ina son ganin ki yanzu, ina so mu tattauna al’amuran dake tsakaninmu, mu gamu yanzu a gidan Abua ina son sanin abin da ake ciki”.
Mus’ab yana zaune gaban Abu yana kallon agogon hannunshi yana kuma kallon hanyar da Saddiqa za ta vullo.
Ita kam Abu haquri take ba shi tana kuma gaya mishi wai har ta samar mishi wata yarinyar da take shirin sawa ayi xaurin auren rana xaya da na Saddiqan sai gata ta shigo.
Ramar da ya gani a tare da ita, ita ce ta fara sanyaya mishi jiki. Mus’ab ya kalle ta cikin nutsuwa.
“Kin yi ciwo ne Aisha?”
Ta sunkuyar da kanta qasa hawaye suka soma zuba daga idanunta.
“Daina kuka ki gaya min Aisha kina sona?”
Da sauri ta xago ta kalle shi idanuwansu suka haxu, ta yi maza ta sake sunkuyawa.
“Gaya min kawai Aisha, ai ni na daxe ina sonki, na daxe ina burin mallakar ki a matsayin matata, na daxe ina buri da fatan in samu damar da na sanyaki a gabana na gaya miki wannan kalmar ina sonki Aisha, ai bani da wata budurwa a Misau in bake ba, kece yarinyar da nake so ban samu damar da muka zauna muka tattauna matsalolin da masoya ke fuskanta ba saboda tsoro”.
“Tsoro kuma?”
Ta yi tambayar cikin wani yanayi.
“Yanzu tsoro ne ya hanaka gaya min abin da ya kamata a ce tuntuni ka gaya min?”
Ya yi maza ya ce, “Eh, Aisha tsoro ne, in ban da haka ai da tuni na gaya miki cewar duk duniya bani da abin da nake so kamar ki”.
Ta miqe da niyyar tafiya ta barshi. Ya yi maza ya kama hannunta ya riqe.
“Kar ki tafi ki barni Aisha, kar ki yi fushi dani taimakeni ki rufa min asiri,