Showing 15001 words to 18000 words out of 31859 words
Chapter 6 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt
sai ta ganni a yaro, in ba hakan nake yi ba zuge min ita za ayi a ce mata ni xin tsoho ne”.
Saddiqa ta ce, “Tafxijam! Ai kuwa in nice budurwar taka duk randa ka zo da askakken qasumba sai in qi yin hirar, kayi-kayi kuma in qi gaya maka abin da yasa ka ga canji”.
Leqowar Inna tana tambayar “Ke da waye”. Shi yasa hirar tasu ta katse.
Ya nufi falonta suna gaisawa, ita kuwa Saddiqa ta ci gaba da aikinta har ya fito ba ta gama ba.
“Hala askin ne ya hana ki zuwa gaisheni”.
Ta sake wata dariyar ta ce, “A’a, ban san za ka fito yanzu bane”. Ta biyo bayanshi suka fito inda ya yi parking xin motar da ya zo a ciki Bora qirar Vokewagen.
Ya buxe but xin yana cire kayan da ya zo dasu yana ajiyewa, ya xan kalle ta.
“Wato ma ni kike yiwa dariya ko Aisha?”
Ta yi murmushi ta ce, “To ka yi haquri kasa daurewa na yi, ka san ni ban tava saninka babu qasumba ba”.
Ya ce, “To na ce baki da wayo sanda Inna take nan kin ce kina da shi, ai ni qasumbata ina Italy na barta, kuma ai kin san wannan zuwan taxi na yi”.
Ta ce, “To maimakon ka je da kwarjininka sai kuma ka ragewa kanka kwarjini? Gaskiya ni ban ji daxin askin da ka yi ba”. Ta zovara baki.
“Yi haquri Aisha, nan gaba ba zan sake ba ko da kuwa ita budurwar tawa ba ta son qasumbar. Ko da yake ma ina ganin kamar ra’ayi xaya ke gareku”.
Ya gama sauke kayan ya kalle ta ya ce, “Za ki iya zuwa gidan Abu yau da yamma? Ko da yake ma yau ne ranar zuwan saurayinki”.
Ta ce, “Eh, sai dai in Inna ba ta barni ba”.
Ya ce, “Gara dai ta barki”.
Cikin sauri ta ce mishi, “Zamu wurin ta ne?”
Ya ce, “Eh, in hali ya yi sai muje xin”.
Ta ce, “To zan zo”.
A gidan Abu bayan sallar la’sar Mus’ab yana zaune a rumfarta suna hira, yaron da ya aika Bauchi ya shigo rungume da qatuwar takarda a naxe, ya zo ya ajiye musu.
Mus’ab ya sallame shi ya tafi. Abu ta jawo takardar gabanta ta buxe, cikin mamaki ta ce, “A’a-a’a, duk wannan kilishi ne haka?”
Ya ce, “Eh, ai tunda na gane da shi ake yi miki toshiyar baki, to kullum shi zan rinqa kawo miki”.
Abu ta yi dariya ta gutsiri kilishin ta saka a baka tana taunawa a hankali suna hirarsu cikin nutsuwa.
Mus’ab ya ce mata, “Abu ina so ki isar da saqona wurin Inna na riga na yi niyyar neman auren Aisha ba zan fasa ba. To amma kuma ina ganin bai kamata in yi ta yi kai tsaye ba a sanar dasu ba saboda girmamawa, don haka a sanar dasu ina cikin manema ‘yarsu don su sani a wurina girmamawa ne”.
Abu tana cin kilishinta tana korawa da ruwan lemon kwali ta ce, “Kai kam kafaffen mutum ne, in da rabon za a lissafaka cikin waxanda aka kayar ai babu makawa sai anyi hakan”.
Ya yi murmushi ya ce, “Eh, babu komai tunda ba zan zama nine na farko ba a jerin mazan da aka tava kayarwa wajen neman aure ba, ba kuma zai yiwu a ce nine zan zama na qarshe ba, a ce daga kaina an daina, ko shi gwanin da kike so xin ai an gaya min aure ya nema aka ka da shi, shine aka yi fushi aka yi nufin share mishi hawaye da Aishan”.
Abu ta qyalqyale da dariya ta ce, “Kai kuwa a ina ka samo wannan labarin?”
Ya yi shiru yana kallon ‘yan yatsun hannunshi.
“Ka kuwa san shima ya tsargu da kai?”
Mus’ab ya xago ido ya kalle ta cikin sauraro, a zuciyarshi kuwa daxi ya ji, sai dai ya voye.
Tana murmushi ta xan rage murya wai za ta yi mishi tsegumi.
“Ai na je gidan su Saddiqa na samu rigima tsakaninta da Gwaggonta wai ta qi fita hira wajen Sadisu, shine na tambaye ta dalili ta ce, wai kullum ya zo sai ya yi maganar Yaya Mus’ab, ta ce mishi ya daina ya daina tunda ba alheri yake faxi a kanshi ba ya qi dainawa, don haka ta daina zuwa hirar tashi. Na ce to ta yi haquri ta je in sake yi mata maganar ka ta gaya min ni zan ce mishi ya daina don a zauna lafiya”.
Sallamar Saddiqa ta hana Mus’ab faxin komai, ta shigo cikin kwalliya sosai, wani haxaxxen leshi ne a jikinta mai ruwan bula, ga duwatsunshi sun haxu sai xaukar ido suke yi, tana tafe a yanayin takun ta mai cike da rausaya ta qaraso tana kallon Mus’ab ta saki wani lallausan murmushi.
Ya ce, “In kika sake yi min irin dariyar da kika yi min a gidan Inna ba yarda zan yi ba”.
Ta rufe baki da hannu xaya wai tana qoqarin danne dariyar, ta wuce can gefen Abu ta zauna tana gaisheta.
“Abu ke baki yiwa Yaya magana a kan askin qasumbarshi ba?”
Abu ta xago kai ta kalli Mus’ab ta kawar tana sha’aninta.
“To ni ina gamina da shi da zan tsura mishi ido sai na gane abin da qasumbar shi ke ciki, da ta fi haka kenan?”
“To ai kuwa dai da ta yi yawa”.
Saddiqa ta ce, “Ka ji Abu”.
Ita ma ta kawar da zancen.
“To wai ni ba an hana mata fita da irin wannan qamshin bane?”
Ta ce, “A’a, Abu na aure ba? Ai ni ba matar aure ba ce”.
Abu ta tave baki ta ce, “Ai sai ki yi”.
Har kusan awa guda da zuwanta hira ake yi. Ta kalli Mus’ab.
“Yaya ba zamu bane?”
Ya ce, “Zamu”.
Yasa hannu ya xauki xan makullinshi ya ce, “Abu zamu unguwa Aisha za ta rakani wajen budurwata ta ganta”.
Abu ta ce, “Sai kun dawo”.
Ya yi parking xin motarshi a harabar gidanshi.
Ta ce, “A’a, gidanka kuma muka zo?”
Ya ce, “Eh, nima zan yi wanka in yi kwalliya don kar ki fini cinyewa a wurinta, don haka fito mu shiga”.
Ta yi murmushi ta ce, “Amma sai dai ka yi sauri don kar dare ya yi”.
Da sauri ya ce, “Af! Hakaa ne fa, yau ranar taxi ne ga shi kuma da so nake ki yi min girki kafin mu tafi don yunwa nake ji, ko za ki vata kwalliyarki”.
Ta ce mishi, “A’a”.
Ya miqa hannu yana tayata zare gyalen dake jikinta tare da faxin “Kawo mayafin in ajiye miki don saurayin ki zai zo hira ai ba za ki bar yayanki da yunwa ba ko kuwa? Ban yarda na ci wani abu tunda na taso, na xauka zan zo in samu kin yi min wani tanadi”.
Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Ai ban san da zuwan naka bane”.
Ta xan kalle shi ta ce, “To yanzu me za ka ci?”
“Oho! Duk abin da kika yi kika bani zan ci, ni dai kawai in ji na qoshi buqatata ta biya kenan”.
Ta ce, “To shi kenan”.
Ta shiga kicin ta soma shirye-shiryen yin girki. Mus’ab ya biyo ta ganin yanda ta sake a ciki ya ba shi sha’awa, ina ma dai bayan aurensu ne take wannan aikin.
Ta kalle shi da gefen ido saboda ganin tsayuwar da ya yi.
“Ai na xauka wankan za ka yi akfin in gama”.
Ya xan qara matsowa ya ce, “In ina jin yunwa ai bana iya komai, har gara ma in zo nan ina taya ki wasu abubuwan don ki fi saurin gamawa”.
Ta ce, “To bari in yi maka jelof”.
Ya ce, “Babu matsala, sai dai zan sha farfesu”.
Ta ce, “To”.
Yana taya ta aikin yana yi mata hira.
“Za ki yi kyau da karatu Aisha”.
Ta ce, “A’a, bai dame ni ba Gwaggo ba ta so”.
Ya ce, “Eh, ai daxina dake kenan biyayya, in Inna ba ta son abu shi kenan sai kema ki qishi, ina fata dai kin cika alqawarin da kika yi min na hotuna”.
Ta yi murmushi ta ce, “To me za ka yi da hotunana bayan ga sabuwar budurwarka ka samu kuma ban ganka da hotonta ba”.
A hankali ya tambaye ta ya ce, “Kina kishi ne?”
Da sauri ta juyo ta kalle shi, ya yi kamar ba daga bakinshi maganar ta fito ba, don haka ta ci gaba da aikinta, shima yana nashi na yankan albasa da tafarnuwa.
“Kishi!”
Ta faxi kalmar cikin zuciyarta.
“To a kan me za ta yi hakan?”
Nan da nan ta ji wani bayanin na daban yana zuwa mata.
“Ai kuwa Abu ta tava gaya mata cewar akwai aure tsakaninta da yayan nata, ban da haka jangwarzo ne da iya gaskiyarta kuma ta faxa kowace budurwa za ta yiwa kanta sha’awarshi”.
Ta yi maza ta tsayar da wannan tunanin ta hanyar tunawa kanta Sadisu Gwaggo take so ta aura, don haka maganar ta qare.
“Ga albasar Aisha”.
Ta juya ta karva, maimakon ya bar wurin sai ya qara matsowa ya ce, “Na ce ba Aisha”.
Ta ce, “Na’am”.
A hankali ya tambaye ta, “Kina son wannan mutumin ko son baki ne, ko kuwa dai kin yarda ne don ki farantawa Gwaggonki rai?”
Ta dakatar da abin da take yi kafin ta xago da nufin kallon shi, kallon da yake yi mata ya sata sunkuyar da kanta qasa, amma hakan bai sa ta fasa gaya mishi abin da take nufin gaya mishin ba.
“Bana son irin wannan tambayar na rufe wannan hirar a tsakaninmu, in kuma ba haka ba yanzu zan gudu in bar maka girkin…. In bar maka gidanka”.
“To a kan me za ayi hakan Aisha? Ai faxin bakya so xin ya wadatar da komai, ba zan sake ba, wannan da na yin ma na tuba”.
Nan take kuma ya canza hirar da faxin “Abu ta yi min maganar idonta, shine na ce ko za ki taimaka ne gobe mu kaita Kano ta ga likitan ido, kin san za ki yi mata amfani sosai ko a wajen layi ne”.
Ba ta ce mishi komai ba, shima bai sake maganar ba.
Ya ci abincin sosai, Saddiqa ta zuba mishi ruwan lemo a kofi, maimakon ya karva sai ya ce mata.
“Aisha sau nawa kike jin mutane suna cewa kina da kyau?”
Ta ce, “Zan gudu in barka in ka sake, don ni na tsani a sani a gaba ana cewa ina da kyau”.
Ya ce, “To ki yi haquri amma taimakeni ki yi min adalcin barina in faxi magana guda xaya”.
Ta ce, “Faxi”.
Ya ce, “Kin iya kwalliya, wani lokaci sai in ga tamkar ba a garin nan kika koyi kwalliyar ba, gaki da murya mai daxi, ga shi duk abin da kika sawa jikinki sai ya karveki, gaki da nutsuwa, gaki da girmama iyaye, ga shi kin iya girki, gaki da kamun kai. Ni gaskiya….”
Ya yi maza ya yi shiru saboda ganin hawaye sun fara cika idanuwanta, cikin hanzari ya miqe.
“Bari in watsa ruwa in fito mu tafi”.
Wani lafiyayyen Kaftani ne a jikinshi da ta yi matuqar dacewa da hular dake kanshi, ya yi matuqar yin kyau, ga qamshinshi dake iya nutsar da zuciya.
Kallo xaya ta yi mishi ta kawar da kai zuwa ga kallon agogo.
“Da alama dai ka fasa zuwa hirar nan yau tunda kalli lokaci”.
A zuciyarshi ya samu nutsuwa don ya san ita ma tata hirar babu.
Ya ce, “Eh to, sai in fasa zuwa tunda na ga kina yiwa askina dariya sai na mai da qasumbata kar in je ita ma ta ce na ragewa kaina kwarjini”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ta a kaini gida”.
Ya ce, “Yanzu kuwa”.
Sun fito harabar tsakar gida take tambayar shi cewa, “Yaya ni su waye suke sha maka sigari ne a gida?’
Ya taya ta kallon guntayen sigarin da take magana a kai ya ce, “To ya ya zan yi Aisha gida na jama’a? Wani abin ai dole sai ka yi haquri, kema bakya son shi ko?”
Ta yamutsa fuska ta ce, “Ai ni warin taba amai yake sani”.
Bai yi mamakin yanayinta da ya gani ba, saboda ya san sanda yake yaro ya san Innarshi kan ware abin amfani na daban saboda baqin da ta san mashaya sigari ne.
Wani hamshaqin kanti suka je ya tsaya yana kallon ta ya ce, “Muje ki zavi abin da kike so”.
Ta xaure fuska ta ce, “Bayan tsarabar da ka zo min da ita?”
Ya yi shiru ya tsareta da idanuwanshi ya ce, “Kin dai koyi yin jayayya dani”.
Ta yi maza ta ce, “Ba haka bane”.
Ya ce, “To ya ya ne? Sai kuma ki zo gidana ki tafi haka ko ‘yar tsarabar ‘yan oyoyo babu. Shiga ki duba wani abu”.
Suna cikin kantin wanda babu komai a ciki in ban da kayayyakin mata, yana cikin tayata zaven takalma sai ga Sadisu ya shigo cikin kantin.
Mus’ab ya yi kamar bai ganshi ba ya ci gaba da abin da yake yi. Ya iso wurin da suke ya ce, “Barka dai”. Ya cewa Mus’ab.
Ya yi kamar bai ji shi ba sai da Saddiqa ta ce mishi, “Yaya ana magana”.
Ya xaga ya ce mishi, “Barka”.
Vacin ran Sadisu ya qara bayyana, ya ce, “Saddiqa me kike yi a nan yanzu?”
Ta kalle shi cikin sakin fuska ta ce mishi, “Sayayya”.
Ya ce, “To ina son ganinki a waje”.
Ya yi maza ya juya. Ta xaga ido ta kalli Mus’ab a hankali. Ya ce mata “Jeki mana”. Ta bi bayan Sadisu.
Shi kuwa ya ci gaba da tsintsintar abubuwan da yake ganin za su yi mata kyau, har minti goma sha biyar ba ta shigo ba. Ya fara tunanin me suke faxa haka? Ko dai sun wuce ne suka tafi suka barshi a nan? To ko dai ya leqa ne ya ganewa kanshi? Kai a’a, gara dai ya qara haquri kar yaje leqawa Sadisu ya ganshi.
Ya koma wajen zaven agigona sai ga Saddiqa ta shigo. Da sauri ya yi kamar bai samu wata matsala ba, haka nan bai gane yanayin da ta shigo a ciki ba.
Ya ce mata, “Mu ga xan hannun ki ko wannan zai yi miki?”
Ta ce, “A’a, ni ka kaini gida kawai”.
Ya ce, “To”. Ya mayar ya ajiye. Ya rungumo ledojin ya zo ya biya kuxin suka shiga mota, ko tsayawa wurin sayen kaji bai yi ba ya kaita gida ba tare da ya ce mata komai ba.
Washe gari da safe tun tara Saddiqa ta isa gidan Abu cikin kwalliyar wani lallausan voil mai ruwan madara, ta yi kyau sai qamshi take yi.
Tana sallama a qofar xakin Abu Mus’ab ta fara gani yana zaune kan tabarma yana cin ximamen da Abun ta yi mishi.
Ya kalle ta cikin nutsuwa ya ce, “Ni dai sai dai duk yanda za ki yi dani ki yi, amma ba zan daina cewa kina da kyau ba”.
Abu ta ja tsaki ta ce “Matsa ni ka gani in wuce, in dai Saddiqa ce mai kyau a wurinka ai baka more ba, tunda baka san kyan ba kenan”.
Ta fice ta barsu. Ya xaga ido yana kallon ta cikin nutsuwa, ya ce mata, “Zolayar ki fa take yi don kuwa ta fini sanin kina da kyau, sbaoda ta fini sanin da su wa kike kama”.
Ta xaure fuska tare da juyar da idanuwa nuna maganar ba ta dame ta ba. Hakan da ta yi yasa shi bin idanuwan nata da kallo, zuciyarshi ta raya mishi kuka ta yi. Kamar ya tambaye ta abin da yasa ta yin kukan, sai kuma ya ga to a na me? Alama ne dai na wata qila saqon