Showing 18001 words to 21000 words out of 31859 words
Chapter 7 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt
shi ya fara tafiya.
“Za ki ci xumame?”
Ya yi tambayar don ya kawar da shirun da ta yi.
Ta ce, “A’a, na qoshi, kuma ma ni bana cin abu mai nauyi da safe”.
Ya yi murmushi ya ce, “Ai kina da kyau ne”.
Ta yi maza ta vata fuska. Abu ta shigo daga wurin alwala take, sallar walaha ta soma gabatarwa.
“Siraran mutane basu cika cin abu mai nauyi ba, musamman ke gaki ‘yar gata, yanzu ni yanda nake qaton nan in ban ci abu mai nauyi ba in yi me?”
Maganar tashi ta sata murmushi, ta ce, “Kai ba wani qato bane fa Yaya, ai kai dogo ne jikinka ya dace da kai kwarjini kawai ya qara maka, in ban da haka da ka yi tsayi mai yawa”.
Ya yi murmushi ya ce, “Dame na fiki tsayin Aisha? Qafa shida ne fa dani”.
Ta ce, “Lah!”
Ya katse ta da cewa, “To bari Abu ta idar mu gwada tsayin ni dake ta gani”.
Ya kalle ta ya ce, “Bani ruwan sha”.
Da Sauri Abu ta shafa fatiha ta ce, “A’a, kar ki je min bakin randa barni in kawo mishi, haka kawai kin yi dalilin da aka sare min bishiyoyina na shekara da shekaru”.
Mus’ab ya ce, “Aka rage musu ganye dai Abu, kuma ai kema hakan ya fi miki dan za su fi ba da iska mai kyau”.
Qarfe goma da rabi suka bar Abu suka kama hanyar Kano. Mus’ab da Saddiqa suna gaban mota, ita kuwa Abu tana baya, Saddiqa tana karanta mujallun da ta samu zube a cikin motar, shi kuwa Mus’ab yana hira da Abu.
Ta xauko goron ta za ta gutsira ta ce, “Nifa wannan goron ba isana zai yi ba, in an gani a tsaya a saya min”.
Mus’ab ya ce, “Ki rinqa shan Ice-cream Abu bana sonki da cin goron nan bai da wani amfani a jiki in ban da cutar da lafiya”.
Ta harare shi ta ce, “Au haba? Na ce to da goro da taba fa?”
Ya yi shiru bai amsa mata ba. Ta sake faxin “Na ce shi da sigari fa?”
Mus’ab ya yi kamar ba da shi take yi ba. Ta ce, “Hhm! Mai sigari kuma har ya cewa mai goro wani abu? Abin da masu yinta ma kashedi suke yi muku suna faxin tana cutar da lafiya, mashayanta kuma za su iya mutuwa tun cikin quruciyarsu saboda cutar da take yiwa lafiyarsu”.
Da sauri Saddiqa ta rufe mujallar dake hannunta ta juyo ga kallon Abu ta ce, “Ya ya kike danganta shi da shan sigari?”
Gaban Abu ya faxi, ashe ba su biyu bane a motar.
“Ke tafi can shashasha”.
Ta ci gaba da cin goronta. Ta sake juyawa wajen Mus’ab ta ce, “Yaya kai kana shan sigari ne?”
Bai juyo ya kalleta ba balle ta ga yanayin fuskarshi, ya ce, “To ina na san wannan bayani Aisha, ai Abun kawai za ki tambaya ta gaya miki”.
Jin da ta yi Abu ce za ta yi mata bayani yasa ta haqura.
Tamkar Mus’ab jira yake yi a ambatar mishi sigari, nan da nan kwaxayinta ya taso mishi, sai hamma yake yi yana qarawa.
Ya gaji ya ce, “Sammin goron naki Abu in xan tauna”.
Ta ce, “Haka kuma?”
Ya ce, “A’a, bani kawai in gutsira”.
Ta ce, “To”. Ta miqa mishi yana duba goron kafin ya jefashi a baki, ya juya ya kalli Saddiqa ya ce, “Ke kam na san bakya cin goro”.
Ta ce, “A’a”.
Ya ce, “Nima yau ne saboda na ji kamar zan yi gyangyaxi”.
Abu tana daga baya ta ce, “A’a, ai haka tsiyar goro da taba yake”.
Saddiqa ta valla mata harara ta ce, “Ni bana son ana ambaton sunan taba a kusa dani”.
Abu dai suvutar baki take yi tana yin maganar, ta yi nufin kame bakinta daga hirar shima Mus’ab ya yi nufin daina jan Abu da hira don gudun kar ta yi mishi tonon asiri.
Asibitin ido na Niger Optical Service suka je, sun ga kan lokaci da aka yi alqawari, an kuma sallame su da magunguna bayan an tabbatar musu da cewar idon bai da wata matsalar da ta wuce shekaru ke haddasawa.
Daga can Mus’ab ya zarce dasu Cort Road gidan abokinshi na makaranta Ishak, suna yin parking maigidan ya fito, yana ganin baqin ya buxe baki yana faxin, “Amma yau ka burgeni, ai ban san ka da irin wannan kirkin ba, ko da yake ga waxanda suka kawo ka, uwargida ne da amarya ko?”
Ya shiga yiwa Abu da Saddiqa sannu da zuwa. Ya matsa kusa da Abu saboda ganin fitowar matarshi Atika don tarar Saddiqa.
“Ai ni yau shar dani tunda ga amaryata ta zo”.
Abu ta yi murmushi tare da faxin “Yi dai a hankali kar matar gidan ta ji ta qi yi min malmala mai auki”.
Gaba xaya suka yi dariya. Atika ta wuce gaba tana yiwa Saddiqa jagora zuwa saman gidan, ita kam Abu wurinsu Mus’ab ta yi zamanta.
Nan da nan Atika ta zagayesu da kayayyakin lashe-lashe da tanxe-tanxe. Ta kalli Abu ta ce, “A’a, ke kuma a nan za ki hakimce wurin maigidan?”
Ta ce, “A’a, ni bana zama xakin kishiya”.
Suka yi dariya. Atika ta zauna suka gaisa, sannan ta xebowa Abu nata plate xin ta kawo mata kusa da ita, sannan ta juya da sauri ta haura sama inda ta bar Saddiqa tana jiran dawowarta.
Mus’ab ya kunna sigarinshi ya sanya a baki bai cewa kowa komai ba, sai da ya zuqe kara biyu.
Ishak ya kalle shi ya ce, “Yallavai wannan shirun duk a daxin yake?”
Mus’ab ya kalle shi ya ce, “Yau ai ba qaramin wahala na sha ba”.
Ya kwashe bayanin duka ya yi mishi na yanda suka yi a mota. Ishak ya yi murmushi ya ce, “Ai in har ka saba shan sigari bayan ka ci abinci, to bari cin abincin ka zauna da yunwarka ya fi sauqi, ko kuma in ka ci ka san yanda ka yi ka yi dabarar da ka xan xorata, amma kai a ina ake yin haka?”
Yana tambayar yana dariya ya ce, “Har sigarin ba ta san kana sha ba? Tafxijam! Ai za ka wahala, ka voye wuta ka voye hayaqinta? Ai in aka voye wasu abubuwan shi sigarin sai kawai a nuna mata ana sha, in yaso sai a roqeta ta ba da lokaci za a daina kafin nan ta shiga gida shi kenan”.
Abu ta qyalqyale da dariya tana kallon su, ya sake wani murmushin ya zubawa Mus’ab ido ya ce, “Ai haka ake yi, amma ka tattara komai ka voye, ni da ban voye duka ba ma ai da aka gano abin da ake ciki ba qaramin bori aka yi ba”.
Mus’ab ya gyara zama ya ce, “Ni neman auren nawa ne babu gata a ciki, nan inda kake ganin Abu ma ba ta tare dani, shi yasa ta yi ta qoqarin tona min asiri a gabanta”.
Abu ta yi dariya ta ce, “Ubangiji ya shiryeku yaran nan”.
Suka ce, “Amin”.
Ita kam Saddiqa tana can suna shan hira da Atika tamkar sun daxe da sanin juna, rayuwar da Atika ke ciki ta ba ta sha’awa, saboda ganin da ta yi tamkar komai nata ya yi dai-dai.
“Ya ya ban ga yara ba a gidan?”
Ta yi murmushi ta ce, “Yanzu ne fa nake da cikin bai ma fi wata uku ba, Mus’ab bai baki labarin wahalar da muka yi wurin neman haihuwa ba?”
Saddiqa ta yi murmushi ta ce, “Kun daxe da auren?”
Ta yi maza ta ce, “Shekara uku fa, abokan aurenmu wasu ma sunyi biyu”.
Saddiqa ta yi dariya ta ce, “Yanzu nan in an shekara uku ba a haihu ba sai hankali ya tashi? Ai bai wuce amarci ba”.
Atika ta zaro ido tare da faxin, “Tafxijan! To bari mu ga ku yanda za ku yi naku amarcin, in baki sani ba in gaya miki, Mus’ab yana ganin kin wuce wata uku za ki ga ya fara…..”
Ta katseta da cewa, “Lah, Yaya Mus’ab fa Yayana ne ba saurayina bane”.
Atika ta zaro ido haxe da cewa, “Kina nufin ba kece nake jin suna labarinki da Ishak ba?”
Ta ce, “A’a, bani ba ce”.
Ta yi maza ta miqe ta nufi matattala inda za ta hango mijin nata a falo, “Na ce ba”. Ya ce, “Na’am”. Ta ce, “Ba wannan ce yarinyar nan ba?” Ya yi maza ya ce, “A’a, ba ita ba ce, wannan ai qanwarshi ce”. Ta juyo tana faxin “Ai ashe kuwa ba ke ba ce”.
Sai da suka yi sallar la’asar sannan suka yi sallama, Ishak ya kawo turamen holland guda biyu tare da wani rantsattsen leshi ya bai wa Saddiqa, ita ma Abu ya ba ta turame biyu tare da dubu biyar wai ta ci goro kafin ya zo. Suka yi godiya suka tafi.
Mus’ab yana barin gidan bai zarce ko’ina ba sai shagon Alhaji Ibrahim Umar a cikin kasuwar Sabon Garin Kano.
Saddiqa tana zaune kan kujerar da aka ba ta, mamaki take yi na yanda aka maqare shagon da zinare Gold qirar daban-daban, cikin fara’a da iya karvar baqi Alhaji Ibrahim ya ce, “Barka da zuwa ranki ya daxe, hala amare ne suka zo ziyara?”
Mus’ab ya ce, “Babbar ta fara zaven abin da take so”.
Alhaji Ibrahim ya bi Abu yana nuna mata don ya tayata zave, shi kuma ya yi amfani da hakan ya matsa kusa da Saddiqa ya ce, “Aisha misali a ce kece budurwar da nake shirin ki rakani wurinta taxi na kawo ki nan me da me za ki zava?”
Ta yi shiru cikin tunanin maganar tashi, sai ya yi maza ya ce, “Taimakeni ki tashi ki duba mata sarqoqi don ina ganin kamar ra’ayinku kusan xaya ne”.
Ta yi murmushi ta ce, “To”. Ta miqe ta soma duba sarqoqin dake rataye cikin kabet-kabet, ta nuna wasu guda biyu aka ciro su aka xora kan sikeli ana gwada nauyi.
Alhaji Ibrahim da kanshi ya jinjina zaven da ta yi, ya yiwa Mus’ab kuxin. Ya kalli Saddiqa ya ce, “In an haxa da abin hannu bai fi ba?”
Ta ce, “Ya fi”. Ya ce, “To zavo kamar na hannunki kala biyu”. Ta ce, “To”.
Nan ma ta zuba ido ta zavo abin da take ganin in ita ce abin da za ta xaukawa kanta kenan. Ya biya suka fito suka shiga mota suka xauki hanyar komawa Misau.
Abu tana kwance a baya barcinta take yi, ita kuwa tana jingine sai dai can cikin zuciyarta Yaya Mus’ab da budurwarshi take tunawa, irin sayayyar da ya yi mata bayan ko fara zuwa wurinta bai yi ba. Wannan ranar da ya fara zuwa ko me zai yi oho. Ta yi maza ta kawar da tunanin ta hanyar tunawa kanta shi xin mai alheri ne ga kowa.
Shi kuwa Mus’ab yana tuqi ne tare da tunanin abin da ke tsakanin shi da Saddiqa wanda ba ta ma sani ba, sai dai zuwa yanzu kam yana ganin Innar shi ta soma sansano wani abu.
Sai da suka isa qofar gidan Abu ya sauke ta ya rakata ta shiga ciki, sannan ya dawo da nufin kai Saddiqa gida.
Saddiqa ta buxe qofar motar ta fita tare da faxin “Yaya ka huta gajiya”. Ya ce, “Amin, to zo mana”. Ta juyo tana kallon shi.
“Ai kin yi mantuwa”.
Ya xauko ledar dake xauke da sarqoqin ya miqa mata. Ta yi saroro tana kallon shi.
“Karvi mana Aisha”.
Ta ce, “A’a, ai budurwarka ka sayawa”.
Ya zuba mata ido ya ce, “Kin tava ganinta ne? To karvi mana”. Ta sake cewa, “A’a”. Da sauri ta juya ta nufi gida za ta tafi ta barshi dasu.
Ya yi maza ya tare ta a zauren gidan ya ce, “Haba Aisha, ni dake ai abotarmu ta hana mu yiwa juna haka”.
Ta maqure kanta jikin bango, shima ya mamayeta ta ko’ina ta zama ba ta shaqan komai sai qamshin jikinshi.
“In kika qi karva wa zan kai wa? Ki karva ki yi kwalliya in na gani a jikinki zan ji daxi, bani da wata budurwa tunda na kasa yin jarumtakar gayawa wacce nake so xin. Karvi kawai ki yi amfani dasu”.
“Ni da Gwaggo dukanmu bama son kyaututtukan da kake yi min, in jita wai akwai abin da zai biyo baya, kuma in yi hankali da kai”.
Ta soma kuka ya rasa yanda zai yi da ita, shi ba abin ya sake ficewa da ita zuwa wani wurin ba, ya san Innar tana jin isowarsu.
“Ni bani da abin da zan ce miki a yanzu illa in roqe ki duk abin da za ki ji a kaina ki taimake ni ki yi min adalci, ki bani damar da zan yi magana dake kullum ina gaya miki kina ganin kamar wasa nake yi bani da wani gata, in har ba ke ce kika tsaya min ba to zan shiga matsalar da ban san qarshenta ba.
Na dogara dake ne saboda qarfin zumuncin dake tsakaninmu da mutumta juna da muke yi, ni dai na san ko baki yi hankali dani ba, ba zan iya cutar dake ba, ke ce baki san yanda kike ba a wurina, nine nake rayuwa ni kaxai a wurin Innata sai ga shi kin shigo cikinmu, ina murnar nima na samu qanwa wacce zan yi ta tarairaya, wacce zan yi ta so ina tausayawa kamar yanda Inna ta yi min, sai kuma ta tafi ta barmu, sai kuma in rasa wacce zan cutar sai ke.
Ke kaxai fa ta bari a duniya sai in cutar da ke? Ai ni tunanina da burina da sha’awata bai wuce mu dunqule ni dake mu zama abu xaya ba, da tana nan a raye kuma ina tabbatar miki da abin da za ta yi mana kenan”.
Saddiqa ta xago ta kalle shi cikin kuka mai yawa, ta ce mishi, “Ba na gane abin da kake nufi da irin maganganun da kake yi min ban san me kake nufi ba”.
Ya ce, “To ki yi huquri ki karvi waxannan sarqoqin tunda na riga na saya sai ki yi min ado da guda xayan zan ji daxi sosai, gobe ki zo gidana don mu warware al’amuran dake tsakanin mu”.
Ta ce mishi, “Inna ta yi min kashedin zuwa gidanka, sai dai ko gidan Abu”.
Ya zuba mata ido yana kallon ta ya ce, “Haka ne?”
Ta gyaxa kai nuna alamar eh. Ya ce, “To kin gani Aisha karvi sarqoqin ki kai mata, gaya mata kawai ni na sai miki ita ta san abin da nake nufi”.
Tana sa hannu ta karva ya yi maza ya fice daga zauren don ya ji motsin fitowar Innarshi tsakar gidan.
Saddiqa na tsaye a zauren ta shigo riqe da tochlight xinta tana haskata.
“Me ya faru Saddiqa? Kukan me kike yi? Ya tava ki ko? Ya yi miki wani abu ne?”
Ta shiga haskata ta ko’ina, ta ce, “Nifa dama can ban yarda da kusantar juna da kuke yi ba”.
Cikin kuka Saddiqa ta ce mata, “Haba Gwaggo, Yaya Mus’ab ba xan’uwana bane?”
Maganar ta zo mata a bazata, ta tsaya tana kallon Saddiqa, matsanancin kukan da take yi ya qara mata tausayinta. Cikin zuciyarta ta ce, “Uh-uhum! Shi kenan wannan yaron ya gama da Saddiqa, don kuwa matsanancin kukan da ta yi jiya da wannan da take yi a yau ba komai bane illa SO, wanda ya san shi ya san abin da yake sanya zubar hawaye”.
Tausayin ta ya sake kamata da ta qara taabbatarwa kanta da cewar, “Wanda bai kamata a so bane Saddiqa ta kamu da sonshi”. Ta miqa hannu ta riqo nata ta jata suka shiga gida tana rarrashinta.
Shi kuwa Mus’ab yana barin gidan bai nufi gidanshi ba wurin Abu ya koma, har ta kwanta ta ji shigar shi cikin xakin nata, ta fito tana haskashi da fitilarta.
“Lafiya? Me ya faru ka dawo cikin wannan tsohon daren?”
“Abu ki ji Inna wai Aisha ta yi hankali dani”.
“Hankali da kai kamar ya ya?”
Ya ce, “To ina na sani Abu? Tana son rabani da Aisha, za ta rabani da ita”. Cikin matsanancin yanayi yake maganar. Ya