Showing 21001 words to 24000 words out of 31859 words

Chapter 8 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt

02 Dec 2024

1512

ba ta labarin yanda suka yi da Saddiqa duka.
Ta ce, “To bari kawai tunda abin nata ya zama haka tun ba a ce komai ba za ta fara tsoratar da yarinyar ba za ta tsame hannunta cikin lamarin ta barta ta yiwa kanta zavi ba, to za ni gidan nasu zan gaya mata komai don ta san gaske kake yi”.
Ya ce, “Yauwa Abu, nima na c Aishan ta zo nan ta same ni ta kuma yarda”.
Ta ce, “To Ubangiji ya zava mana mafi alheri”.
Ya ce, “Ameen Abu”.
Washegari da sassafe Abu tana idar da sallar asuba ko laziminta ba ta tsaya ta yi ba ta lakato man shafawarta ta muttsuka a hannayenta da qafafuwan ta, ta miqe ta xauki carbinta da mayafinta ta yafa, ta sagala murfin qofar xakinta ta nufi gidan Malam Abdullahi, a zuciyarta tana fatan ta same shi suyi wacce za suyi don ta riga ta yi nufin taimakon Mus’ab a kan auren Saddiqa da ya yi nufin yi.
A tsakar gida ta samu Saddiqan tana yawo cikin rigar barcinta, idanuwanta a kumbure alamar daren jiya kukan da ta yi ba kaxan bane, ta yi kamar ba ta ganta ba ta nufi xakin ‘yarta tana sallama.
Da sauri Innar ta leqo ta ce, “Inna lafiya kika fito da sassafen nan?”
Ta ce, “Lafiya qalau, wurinki na zo ke da mijinki”.
Ta ce, “Ayya! Ai kuma ya fita don an sanar da rasuwa a cikin gari”.
Ta ce, “Wayyo babba ne ko yaro?”
Ta ce, “A’a, ya xan manyanta”.
Abu ta ce, “To, Allah ya ji qan musulmi”. Ta shiga ta zana suna gaisawa.
Saddiqa ta biyota da abin karyawa.
“In ce ko dai lafiya kike son ganin Malam Inna?”
Ta sake cewa “Qalau, dama qarfin zuwan nawa naki ne, don na san komai a gidinki yake Malam kam ai ba zai hana Mus’abu aure ba”.
Nan take ta shiga yi mata bayanin saqon nashi. Sai da ta ji ta yi shiru ta tabbatar ta kai qarshe sai ta xan yi murmushi.
“Uhm! Ai dama na san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, kyautar rashin hankali da yake yiwa Saddiqa shi ya qara fahimtar dani akwai yaudara a cikin lamarinshi, ko kin san tun yaushe rabon Sadisu da ya ji daxin yarinyar nan ko maganarshi ba ta son ji? To haka ake yi ba zai yi neman shi ba kawai sai ya rabata da wanda ya same ta da shi?
Sannan sau nawa ya turaki wajen nemar mishi aure Inna? Ya fito ake cewa sai ya qi zuwa ya bar yaran suna ta shirmen sonshi, haka nima yake so ya yi min?”
Abu ta yi nufin yi mata dabara ta ce, “Yauwa, to tunda an san halinshi ba sai kawai in ce mishi ya fito ba? Kinga ai sai ya yi tafiyarshi kowa ya huta”.
Inna ta ce, “A’a, a kan wannan kam kar a ce mishi ya fito tunda ko ya fiton ba bashi ita zan yi ba. Saddiqa marainiya ce, Innar kar ki shiga cikin maganar yaron nan har ya samu damar da zai cutar da ita.
Ba mijinta bane, ni dake mun san komai in har qa’idar bayar da aurenmu za a bi ai ba tarin dukiya muke dubawa ba cancanta muke bi da asali da mutunci, da sanin ya kamata. Don haka ayi mishi kashedi kawai Inna ya fita hanyarta, in ba haka ba kuma zai gamu da vacin rai mai yawa, sai in yi mishi…….”
Abu ta yi maza ta soma salati tana tafa hannu, ta ce, “Ki yi mishi me? Lallai kuwa da kin yi hauka. A kan ya ce yana son Saddiqa? Ki ce min kin yi hauka ban sani ba. To yi maza ki yi mishi baki a gabana don nima in zama shaida in qara sanin kema kin haihu.
Zancen banza zancen wofi, xanki guda xaya kin yi qememe kin qi yarda ki shirya da shi, kin takura kanki kin hana kanki sakat, kullum tsakanin ki da shi muzurai da xaure ido. Yana iyakacin bakin qoqarinshi a kanki, yana yi yana iya yinshi kina shirmenki. Sakarwa kawai ki ce min kina shirin tonawa kanki asiri don shine ke”.
Ta miqe ta fita ta bar Inna tana kuka saboda ganin vacin ran mahaifiyarta.
“Zan dawo in samu Malam Abdullahi in ji ko shima bakinku xaya, Saddiqan me kuma? Shima Mus’abun maganinshi kenan ja’iri mai taurin kan tsiya, ai babu abin da ban gaya mishi ba”.
Saddiqa tana xakinta adon lalle take yiwa hannayenta ta hango ficewar Abu cikin sauri, ta tabbatarwa kanta akwai wani abin da ke faruwa. Sai dai ba ta san mene ne ba, koma mene ne kuma ba ta jin daxin yanda Gwaggonta ke yiwa Yaya Mus’ab, kullum mamakinta take ji yanda ta mallaki xa jan gwarzo irin Mus’ab amma lamarinshi baya gabanta, ko tausayi kuma ba ya ba ta, kullum a cikin qoqarin kyautata mata yake, a cikin yi mata alheri yake, kusan kullum sai an zowa mahaifiyarshi godiya kan wani alherin da ya yiwa wasu amma ita ko a jikinta.
Mus’ab yana zane a xakin Abu jiran dawowarta yake yi, yana kuma sauraron zuwan Saddiqa cikin zullumu da tunanin abin da ake ciki.
Abu ta yi sallama ta shiga, ya bita da kallo gabanshi ya faxi saboda ganin yanda fuskarta ke xaure.
“Ya ya dai Abu? Ta yarda kuwa?”
Ta balbale shi da faxa ta ce, “Ta yarda dame? Tun farko mene ne ban gaya maka ba? Ban ce maka ka fita hanyar yarinyar nan ba? Ba dai kaima kafiyar tsiya ce da kai ba, in ka so abu kamar xa ya so waje. To ba ta yarda ba sai ka san yanda za ka yi”.
Ya sunkuyar da kanshi qasa ya yi shiru cikin nazarin abin yi, zuwa can ya xago ya kalli agogon hannunshi ya ce, “Goma ta wuce”. Gabanshi ya sake faxuwa.
“Kar dai ita ma ba za ta zo ba?”
Ya yi maza ya xauko wayarshi ya dana lambobinta ya ji ta xauka.
“Za ki zo kuwa Aisha?”
Muryarta tana rawa ta ce, “Gwaggo ta hanani fita, ta kuma ce wai in ka yi waya in gaya maka tana son ganinka”.
Gabanshi ya ba da ras! Ya kalli Abu ya ce mata, “Inna tana son ganina bari in je in ji”. Ta ce mishi, “To”.
Mus’ab yana zaune a gaban mahaifiyarshi cikin ladabi yana sauraron abin da take gaya mishi.
“Na ji saqonka wurin Inna, shine na ce bari in kira ka muyi magana ni da kai, abin a ce kai ne waliyinta wanda amanar al’amuranta suke hannunka, za ka bai wa mai hali irin naka ita?”
Ta zuba mishi ido tana kallon shi. Shi kuwa yana kallon qasa cikin ladabi ya ce, “Ina sonta Inna ba zan iya kwatanta muku yanda nake jinta ba in ban da hakan da ban zo gabanku neman auren nata ba, ina cikin wani irin hali ne”.
Ta katse shi ta hanyar faxin “Ai ba dogon bayani na nema ba tambaya kawai na yi maka baka bani amsa ba, cewa na yi in kai ne waliyinta za ka bai wa mai hali irin naka ita? Eh, kawai nake son ji ko kuma a’a”.
Ya sunkuyar da kanshi qasa ya ce, “A’a”. ta ce, “To shi kenan magana ta qare tashi ka tafi”.
Ya ce, “Ki yi haquri ki saurareni Inna, ni da mai hali irin nawa ba xaya bane, in a kan maganar Aisha ne Inna zan riqe miki ita fiye da duk yanda ake zato, babu wani wanda za ki baiwa ita ya fini yi mata adalci ko ya fini ganin darajarta, don ni bayan son da nake yi mata ina kallon ta a matsayin wacce zan riqe in yiwa gata don in sakawa mahaifiyarta alherinta a gare ni.
A wurinta na soma xanxanar ‘yanci, ba ta yi yawan rai ba, ba ta mori komai a cikin wahalar da ta yi a kaaina ba sai dai kullum ina yi mata addu’a. Ki taimakeni kar ki hanani ‘yarta, da tana raye na san za ta bani ita ba tare da ta tsaya kallon munin halina ba, na yarda ki bani ita bisa sharuxa da shaidun da za ki saka, zan cika duk wani alqawari da zan xauka a gabansu”.
Ta kalle shi a lalace ta ce, “Saboda yanzu kana cikin natsuwarka ne yasa kake tuna alherin mahaifiyar Saddiqa, haka nan yanzu ne za ka iya shaida alqawari da cikawa, amma in ka shawo barasa ta yi maka karo fa? Kana nufin zan yarda Saddiqa ta zama matar mashayi ko manemin mata? Yarinya ce da ba ta san komai ba sai ladabi da biyayya.
Me kake so in ce mata randa ta gane na san komai game da halayenka amma na xauke ta na baka don kawai ka yi min alqawarin da na san ba za ka cika ba, ba zan fifita sonka a kan nata ba, in na yi haka ban yi mata adalci ba, alhakin zumunci kuma ba zai barni ba, don haka fita hanyarta kawai don ba zan baka ita ba”.
A kixime ya ce, “A’a, Inna kar ki hanani ita, na rantse miki ina sonta, ki taimaki rayuwata ba zan iya haqura da aurenta ba”.
Ta ce, “Za ka yaudari kanka ne kawai in ka yi mata irin wannan son, don babu gami tsakaninka da ita, in dai ka kuma in alhakin wasu da suka rinqa binka kana wulaqantawa ne ya kama ka”.
Mus’ab yasa hankicif ya share gumin dake feso masa a goshi.
“Ki taimakeni Inna na tuba kar ki kamani da laifukan da na yi miki a baya ki hukuntani ta hanyar hanani samun matar da nake so”.
Ta ce, “Ba ni na hanaka ita ba Shari’a ce ta hanaka ita, da ta ce mazinaci matarshi mazinaciya, don haka zan qara yi maka kashedi ka fita harkar yarinyar nan kar ka yarda ka ce mata kana sonta, in kuwa ka yi hakan to ni kuwa zan rabaka da ita ta hanyar gaya mata halayenka, sigari, giya, neman mata, babu abin da zan rage a ciki don ta san ban cuceta ba”.
Tsawon lokaci suna zaune shiru, da qyar Mus’ab ya iya yunqurawa saboda sarawa da kanshi yake yi ya ce, “Inna ni zan koma”. Ta ce, “To, Ubangiji ya kiyaye”. Ya ce, “To, amin”.
Mus’ab yana fita gidanshi ya nufa, kai tsaye ya wuce xakin kwanciyarshi. Wunin ranar bai yarda ya ga kowa ba, babu abin da yake yi in ban da nazarin hanyoyin da zai bi.
Ya riga ya san Innarshi za ta raba shi da Saddiqa ta hanyar gaya mata halayenshi, to in har ta yi hakan wace hanya shi kuma zai bi don ya mallaketa?
Abu kuwa tana gidanta hankalinta yana wajen sauraron dawowar Mus’ab don ta ji bayanin da zai yi mata, shiru babu shi babu dalilinshi har yamma, har dare.
Abu ta tabbatar babu lafiya, domin qa’idarshi ne in dai yana garin to zai ci abincin dare a wurinta.
Gari yana wayewa ta yi sammakon tafiya gidanshi don ta ga halin da yake ciki. Muryarta da ya jiyo tana qwala sallama cikin falon ne ya yi dalilin fitowar shi sanye da doguwar jallabiya,
Ta zuba mishi ido tana nazarin canzawar da ya yi a ‘yan awowin da ba ta ganshi ba.
“Ba ka zo ka ci abincin dare ba lafiya?”
Ya ce, “Inna ce ta ce in fitar hanyar Aisha, Abu ya ya zan yi? Tana da haqqin in yi mata biyayya ita ce ta haifeni ko ba shi kenan ba”.
Abu ta zuba mishi ido tana nazarinshi.
“Amma ai kin san Aisha matata ce ko? Ko baki sani ba?”
Bai jira amsarta ba ya ci gaba da cewa, “To na rantse miki zan yi ta’adi, zan yi varna”.
Abu ta katse shi da cewa, “Kai Mus’ab hala maye kake yi na ga alamar baka cikin hankalainka, ina jin jiya kwana ka yi kana sha, wato ba za ka daina wannan halin naka da yake ja maka tsana a wurin su ba ko?”
Ya ce, “A’a, Abu so nake in gaya miki gaskiya cikin biyu ki zavi xaya, wanne ya fi?”
Ya tsareta da idanuwanshi da suka riga suka kaxa.
“Da in vatar da Sadisu da in sato Aisha in kawota gadona in voye ayi ta nemanta ba a gani ba wanne ya fi miki? Ki faxa”.
Ta yi tsaki cikin takaici ta juya za ta bar falon, ta ce, “In ka wattsake dagaa shirmen naka sai ka zo gida ka same ni”. Tana tafiya cikin ranta tana addu’ar Ubangiji ka shiryar da wannan yaro. Ta fita ta barshi a zaune.
Malam Abdullahi yana zaune kan tabarma a xakinshi shi kaxai, karatun Alkur’ani mai girma yake yi, matarshi ta yi sallama a bakin qofa har sau uku kafin ya dakatar da karatun ya amsa sallamar.
Ta shiga ta tsuguna a gefe ta ce, “Ina kwana Malam?”
Ya amsa. Suka gaisa sannan ta ce mishi, “Inna ce ta zo tana son ganinka”.
Ya ce, “To gani nan zuwa”.
Ya mai da Alkur’ani wurin zaman shi ya ajiye, sannan ya shiga falon matarshi inda ya san a nan take jiran nashi.
“Lafiya dai ko Inna?”
Ta ce, “Lafiya wurinka na zo kai da matarka kan maganar Mus’abu”.
Da sauri ya kira matar tashi, “Ke Habiba!” Ta amsa ta shigo ta ce, “Gani”. Ya ce, “To zauna mana”. Ya ba ta umarni. Don haka ta koma gefe ta zauna cikin sauraro.
Abu taa gyara zama ta ce, “Wurinka na zo Malam in ji wai da gaske kuke yi ne ba za ku ba Mus’abu yarinyar nan ba?”
Malam Abdullahi ya sunkuyar da kai qasa ya ce, “Inna da baku shiga maganar nan ba, ai kun san komai, wani abin ma ni kun fini sani. Ba muna son yin jayayya daku bane a kan maganar maraicin yarinyar muke dubawa, nutsuwarta da irin halayenta da irin xabi’unta, kun santa kun san Mus’ab.
Inna kun san komai. don haka na roqe ki in kin kalli vangarenshi kin tausaya mishi saboda son da kike yi mishi, to ita ma ki kalli nata vangaren ki tausayawa rayuwarta kar ki fifita wani kan wani, dukkansu naki ne ki yi hukunci kawai na adalci a tsakaninsu”.
Ya xago a hankali ya kalli Abu, ya ce, “Qila dai Inna ta fara mancewa da shine ko?”

ASALIN RAYUWAR MUS’AB DA IYAYENSHI
Iyayen Mus’ab fulani ne na asali waxanda suka taso suka samu kansu zaune cikin garin Misau, a dalilin zaman iyayensu a wuri xaya a cikin gari suka koma neman ilimin addinin musulunci.
Malam Abdullahi da Habiba sune mahaifan Mus’ab, su kuma ‘ya’ya maza suke aka haxasu aure na zumunci. Mus’ab shine babba cikin ‘ya’yan da suka haifa guda huxu, mata uku namiji xaya, matan gaba xaya anyi aurensu suna gidajen auren su tare da ‘ya’yansu.
Gidan su Malam Abdullahi gida ne na malanta, gudun duniya, sanin ya kamata da gudun abin kunya. Kusan kowa a zuriyarsu in dai namiji ne to alaramma ne, mata ma basa aurar dasu sai sun yi sauka. Yaro bai fi sha biyu sha uku ba sai ka ga tilawa yake yi yana kuma neman sanin litattafan addini, kusan a ce a zuriyarsu basu tava ganin taqadari ba.
Mus’ab ya fara yarintarshi ne a gaban Abu, ita ta xauke shi yaye, ko da yake tun yana qarami gagararre ne, sai kuma ya samu shagwava wurin kaka, saboda dalilai da yawa.
Na farko dai ita Habiba ita kaxai ce ‘ya mace wurin Abu, na biyu Malam Abdullahi xan lelenta ne, ita ce ma ta sa aka ba shi Inna Habiba. Na uku Mus’ab tun yana xan qaramin shi kyakakyawan yaro ne, waxannan dalilai sai suka sa Abu ta zama quda ba ta son ganin ya sauka a kan Mus’ab balle ta samu lokacin kwavar shi, har da ya kai munzalin zuwa makaranta in ta tura shi ya qi zuwa saia ta ce mishi yi zaman ka karatu in ana gadonshi ai ka gaje shi, in kuwa ba a gadon shi, to randa ka koma gidanku ka yi naka tunda na san ba bar min kai za suyi ba.
Mu’amalarshi da gagararrun yara da basu san mene ne bari ba, sai ya taimaka qwarai ya zamo gagararren sosai, tunda shima ba barin ake yi mishi ba.
Nan da nan sai labarinshi ya bazu cikin dangi, kowa yana faxin albarkacin bakinshi kan gagarar tashi da irin riqon da aka gane Abun tana yi mishi, kan wannan dalili ne Malam Abdullahi ya tafi wurin Abu ya roqeta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login