Showing 3001 words to 6000 words out of 31859 words

Chapter 2 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt

02 Dec 2024

1510

“Ita Innar ta sake sauraronka kan irin wannan zancen?”
Mus’ab ya xan yi murmushi a yanayi na ladabi.
“Yanzu dai ta ce babu ruwanta sai dai ko a gaba”.
Malam Abdullahi ya ce, “Ai in ban da ba a shiga tsakaninku da ko ni sai in ce mata kar ta sake shiga harkarka”.
Mus’ab ya qara sunkuyar da kanshi qasa yana sauraro, a hankali ya ce, “Na ba ta haquri”.
A gidan Abu bayan sallar isha’I Mus’ab yana zaune a tsakar gidan shi da ita saboda wadataccen hasken farin watan da ake da shi, wanda ya haskaka sararin subhana. Mus’ab yana rungume da gwiwoyinsa saboda kasancewarsu tsaye.
Abu ta kalle shi ta ce, “Ka miqe qafafunka mana ka ji daxin zama, ga abincinka”.
Ya ce, “Gaskiya ba zan iya miqe qafa a nan ba tsoron damatsiri nake ji”.
Cikin sauri Abu ta kalle shi ta ce, “A ina ka ga damatsirin?”
“To ko ban gansu ba Abu ai na san suna nan tunda ga bishiyoyin Aduruku duk inda suke kuma ai ana samun su, don haka ni gara mu shiga ciki”.
Ya shiga tayata kwashe kayan dake wajen yana qoqarin xaukar tallan mijiya ta ce, “A’a, xauki tabarma ni zan xauko miyata kar ka yi min varinta”.
Sun gama cin abinci Mus’ab ya kalli hannunshi ya ce, “Abincin ya yi daxi, sai dai farfesun ya ji daddawa”.
Ta ce, “Eh, a haka aka cinye aka kuma shanye romon ba”.
Ya yi murmushi ya je ya wanke hannunshi da sabulu mai qamshi, ya dawo ya zauna suka shiga hira.
Sai ya ce mata, “Mu yi maganar gaskiya mana Abu ina fa son Aisha, ko kuwa kina son sai ciwon so ya kamani?” Yana kallon ta yana murmushi.
“Ai ni iya shegenka ne yake haxani da kai, ciwon so ya kamaka a kan Saddiqan?”
Mus’ab ya gyara zama ya ce, “Mu bar maganar wasa Abu, ki taimakeni a kan maganar yarinyar ina sonta ban qara sanin hakan ba irin da na ganta tare da Sadisu a qofar gida xazu suna hira, sai na ji har ina buga tuntuve.
Ko na yi miki laifi a baya, ai kuma ba za ki bari alhe ri ya wuceni ba, aurena da Aisha kuma kin san alheri ne, ni da ita duka naki ne. Abu in kika taimaka xin kuma sai ya zame miki kin yi tuwonki ne manki”.
Ta ce, “Ai duk daxin bakinka wannan karon haka za ka yi ka barni, ko dama ka xauko abin a inda ya dace balle haka kawai, ban da haka kaima ka san bamu da fada wurin mai abin”.
Washegari da safe Saddiqa tana aikace-aikacen gida, Mus’ab ya shiga gidan.
“Sannu da aiki Aisha”.
Ta yi maza ta xan tsuguna nuna alamar girmamawa.
“Sannu da zuwa Yaya”.
Bai tsaya ba ya wuce zuwa xakin mahaifiyarshi wacce gaisuwa ce kaxai take haxa shi da ita, bayan wannan ba ta sake sauraron komai daga gare shi, sai ma in ta ga zai daxe a zaune a xaki ta fita ta ba shi wuri.
Sanin da Saddiqa ta yi Mus’ab bai cika zama cikin gidan ya daxe ba in har mahaifinshi ba ya nan, ya sanyata barin abin da take yi ta bi bayanshi don ta gaishe shi.
“Yaya na ga tsaraba na gode, Ubangiji ya qara girma”.
Ta faxi bayan sun gama gaisawar.
A hankali ya ce, “Babu damuwa, ina Baba ya je?”
Ta ce, “Anyi rasuwa a cikin gari yana wurin karvar gaisuwa”.
Ya juya wajen mahaifiyarshi cikin nutsuwa ya tambayeta wa ya rasu Inna?
Ta gaya mishi gidan da aka yi rasuwar, ya yi addu’a Ubangiji ya ji qan musulmi suka ce amin.
“To bari in je in yi musu ta’aziyya daga nan sai in samu baban”.
Ta ce, “To”.
Ya tashi ya fita, Saddiqa ta bi bayanshi tana tambayarshi cewa, “Za ka dawo tana nan ne?”
Ya buxe motarshi ya zauna a ciki kafin ya juyo ya kalleta a yanayinshi na kowanne lokaci.
“Mene ne in zan dawo ta nan xin?”
Ta ce, “Akwai xanyen kifi ne masu kyau na san kana son farfesunshi sai in yi maka kafin ka dawo”.
Ya juyar da kanshi ga kallon sitiyarin motarshi.
“Ai ni na riga na yi fushi dake Aisha”.
Cikin sauri ta tambaye shi, “Me na yi maka Yaya?”
Ya ce, “Ai suna da yawa ba zan iya faxarsu a yanzu ba tunda sauri nake yi za ni wurin ta’aziyya, ina kuma son ganin Baba”.
“To in yi farfesun kenan za ka dawo?”
Ya ce, “In kina so insha farfesunki ki kawo min gidana, daga nan sai in samu damar gaya miki laifukan da kika yi min xin a nutse”.
Ta ce mishi, “To”.
Ya ja motarshi ya tafi, ita kuma ta koma cikin gidan.
Gidan Mus’ab hamshaqin gida ne qwarai da ya gina shi a unguwar G.R.A, wato unguwar Turawa na garin Misau.
Mafi yawancin gidajen dake wurin gidaje ne na ma’aikatan gwamnati, ko kuma dai masu hannu da shuni da suke sha’awar keve kansu daga hayaniyar cikin gari.
Mus’ab ya gina gidan ne shekara guda bayan dawowar shi daga qasar Italy, inda yaje ya yi zama na shekaru bakwai bayan kammala karatun da ya kai shi. Ya gina gidan ne a Misau don cika burin da ya dawo a kai na kyautata mu’amala tsakaninshi da mahaifinshi, wacce ta gurvace tun zamanin quruciyarshi.
Gidan Mus’am gida ne da ya amsa sunanshi, a garin Misau kawai ba har a garuruwa dake kusa duka kwatancenshi ake yi, shi da kanshi kuma ba zai iya faxin ga iyakacin dukiyar da ya kashe ba wajen gina gidan.
Tun dawowarshi daga wurin ta’aziyyar zaune yake shi kaxai a cikin falon, zuciyarshi sai kai kawo take yi kan shirmen da ya yi na cewa Saddiqa ta kawo mishi farfesun gidanshi bai ce mata zai turo direbanshi ya xauke ta ba.
To in ba ta zo ba fa? Ya tambayi kanshi. Dai-dai lokacin da ya sake mai da idanuwanshi kan agogo don ya qara ganin lokaci, qarfe uku ne da minti biyu, wajen awarshi biyu uku kenan rabonshi da ita. To farfesun kifi wani daxewa yake yi?
Maigadin gidan ya yi sallama Mus’ab ya amsa da fitan isowar Saddiqa zai gaya mishi. Sai ya je ya ce mishi “Wasu mutane ne suke son ganin ka ranka ya daxe”.
Takaici ya kama shi, ya ce, “Basu haquri Baba ka ce musu sai gobe su dawo”.
Baba ya xan rusuna kafin ya ce mishi, “Masu lalura ne na kuma ji ka ce lalura ta ciwo in aka zo da ita……”
Bai qarasa ba ya sake kallon Mus’ab a yanayin girmamawa ya ce, “Taimako suka zo nema suna mara lafiya ke garesu a asibiti”.
Mus’ab ya miqe tsaye ya ce, “Jira ni”. Ya shiga xakinshi ya fito ya miqa mishi bandir xin dubu ashirin.
“Ungo ka basu”.
Baba maigadi yasa hannu biyu ya karva tare da yi mishi addu’a.
“Yallavai Ubangiji ya saka maka da alheri, ya baka abin da kake nema na alheri duniya da lahira”.
Addu’ar ta yi mishi daxi. Ya ce, “Amin Baba”.
Huxu ta wuce Mus’ab yana zaune wurin da ya idar da sallar la’asar, har ya soma fidda rai game da zuwan Saddiqa, ya mai da hankali wurin jan carbinshi, lazimin yamma yake yi.
Sai da ya gama ya yi addu’o’inshi ya shafa ya tashi, juyowar da zai yi sai ya ganta a zaun, cikin zuciyarshi daxi ne ya kama shi, amma bai yarda ya nuna ba.
Sai ya ce mata, “Ke Aisha kin shigo min gida babu sallama, ya ya aka yi haka?”
Ta ce, “Na yi hankalinka yana wurin sallar da kake yi shi yasa baka ji ba”.
Ya ce, “To na yarda”.
Ya zauna can gefe kan wata kujera suna fuskantar juna.
“Ina jin dai da an fasa kawo min farfesun nan ne ko? Ko kuma an gama samari suka zo taxi aka mance da Yaya”.
Cikin nutsuwa da girmamawa ta ce mishi, “Ka yi haquri, cewa na yi tunda zan kawo maka to bari in yi maka abincin dare”.
Ya kalle ta ya ce, “Ke, ki ce min hankali ne dake ban sani ba”.
Cikin zuciyarshi kuwa yanayin girmamawar da Saddiqa ke yi mishi ne ya fi tsaya mishi, so yake ta rinqa sakewa sosai don ya ji daxin jawota a jikinshi ta yanda zai canza yanayin shaquwar dake tsakaninsu daga yanayin shaquwa irin na qaunar zumunci da girmamawa, zuwa shaquwa ta mu’amala mai sauqi.
“To me kika girka min?”
Ya yi tambayar cikin sakin fuska sosai. Ta tashi ta xebi kwanukan ta kawo gabanshi tana buxewa. Ya zubawa abincin ido yana kallo cikin sha’awa.
“Ashe dai aiki kika yi sosai, Ubangiji ya baki miji na kirki mai sonki ya sha lagwada a wurinki”.
Ya tsareta da ido don ganin yanayinta.
“Ba fa wannan saurayin naki nake yiwa wannan addu’ar ba, wani daban don ni bai kwanta min a zuciyata ba, sai nake ganin kamar akwai wanda ya fishi cancantar samun ki. Amma fa in maganar tawa ba ta yi miki daxi ba to ki yi haquri”.
Bai kawar da kai daga gareta ba, ita ma tana nan a yanayinta na sunkuyar da kai qasa.
“Kinga Baba maigadi da za ki shigo?”
Canzawar yanayin maganar tashi ya ba ta damar da ita ma ta canza.
Ta ce, “Eh, har ma ya tayani shigo da kwanuka”.
Ya ce, “To dama shi nake so ki xibarwa abincin nan, bi ta can za ki ga qofa kicin ne, ki buxe ta ki shiga ki xebo plate nawa da naki da na Baba maigadi”.
Ta ce, “Ai ni na qoshi”.
“A’a, to a ina ake yin haka Aisha za a kawowa mutane abincin da kai ba za ka ci ba”.
Ta sake cewa, “Na riga na ci a gida”.
Ya ce, “To shi kenan, kawo mu ci zubana”.
Ta tashi ta nufi inda ya yi mata kwatance, kicin xin da Saddiqa ta gani irin wanda take gani ne a mujallun Turawa da take karantawa, ko kuma a finafinan Indiya da take kallo, kusan mancewa ta yi da aiken da Mus’ab ya yi mata ta lalace wajen kallon tsarin kicin xin, bai da mace a gida amma ya yiwa kicin…..
Kiran da ta ji ya yi mata ya dawo da ita cikin yanayinta, ta yi maza tasa hannu ta xebi plate xin da duk wani abin da ta san za ta buqata ta fita.
“Hala kin tsaya kallon kyanki ne a madubi”.
Maganar tashi ta sata jin kunya, ta sunkuyar da kanta.
“Ai ba sai kin kalli mudubi za ki gane hakan ba, Aisha ke mai kyau ce, ko kina so ne ki nuna min cewar shi wannan saurayin naki bai gaya miki irin kyan dake gare ki ba?”
Shiru ta yi ba ta tanka mishi ba, sai dai kuma ta kasa zuba abincin a sunkuye kawai take.
“Ai in nine saurayinki kullum sai na gaya miki kina da kyau Ai…..”
Yanayin da ya gani a fuskarta ya sa shi hanzarin canza maganar tashi.
“To zuba mana abincin mana”.
Ta zuba ta haxa a kan madaidaicin tire da nufin ta kai wa Baba maigadi, ya yi maza ya miqe ya xauka.
“Yi zamanki bari ni in kai mishi”.
Ya gama cin abincinshi ya qoshi ya xan kishingixa suna hira bayan ta kawar da komai daga wurin ta gyara ta mai dasu mazauninsu.
“Hala Abu ke koya miki girki?”
Ta yi murmushi ta ce, “Gwaggona fa?”
Ya ce, “Uhm! Kin san ni ban cika sanin daxin abincin Inna ba, saboda sanda nake yaro sau da yawa na kan ci abincin ne bayan an yi min duka, ina kuka kuwa ai ba zan ji wani xanxano ba ko kuwa?”
A hankali ta xago ta kalle shi a yanayin muryarta mai cike da nutsuwa ta tambaye shi, “Dama Gwaggo tana duka ne?”
“Saboda bakya gagara shi yasa ba za ki san hakan ba, amma ni sanda nake yaro rigama ce dani, kina nufin baki tava jin labarin gagarata ba?”
Ya yi tambayar yana mai kallon ta.
“Uhm! Ai ba ta yin hirarka”.
Suka xan yi shiru, jimawa kaxan sai ya sake shigo da wani zancen.
“Wato kenan tunda kika gama sakandire shi kenan kin gama karatu ko? Kin dena neman ilimi kin fi so ayi miki aure ko?”
Ta ce, “A’a”.
Ya ce, “A’a, ya ya ne?”
“Gwaggo ce ta ce ya isa haka”.
“Shi yasa kike hira da samari? Kullum na zo garin nan sai na ganki kina hira da saurayi ko kunyata bakya ji ko?”
Ta sunkuyar da kanta qasa.
“Wai jiya ma har na shiga gidan na fito ko zuwa mu gaisa baki samu damar yi ba don kina tsoron kar ya yi fushi ko?”
Ta ce, “A’a, ba zai yi fushi ba, ai shima ya ce wai zai zo ya gaishe ka kafin ka koma”.
Mus’ab ya ce, “A’a, ya sha zamanshi bana son gaisuwarshi”.
Ta xago ta kalle shi saboda maganar tashi, idanuwansu suka haxu ta yi hanzarin kawar da nata.
“To meye gamina da shi da zai zo gaisheni? Ba yana zuwa gai da su Abu ba? Ki gaya mishi ni na ce bana son gaisuwar shi don ba zan yi surukuta da shi ba, ya rinqa zuwa gidan su Inna da su Abu da suka san da zaman shi suke kuma xaure mishi gindi, sai ko ke da na ji an ce wai kina mutuwar son shi”.
Ta sake xagowa ta sake kallon shi a wani yanayi. Bai kawar da kai daga gareta ba ya ce, “A to, nima a bakin Abu na ji, abin da ta gaya min kenan wai kuna mutuwar son juna”.
Ta sake kallonshi, “In ji Abu?”
Ya ce, “Eh, ko ba haka bane?”
Ta yi shiru. Ya ce, “In ba haka bane ai sai ki gaya min in ji”.
Ta ce, “Ai ni na daina yin wannan maganar alqawarin da na yiwa Gwaggo kenan”.
“To na ji kin yi alqawari, amma kina son shi ko bakya son shi?”
Ta ce, “Ina son shi”.
Falon ya yi shiru na wani tsawon lokaci saboda faxuwar gaban da Mus’ab ya samu.
Ya yi qoqarin kawar da damuwar ta hanyar yin jarumtakar faxin “To ko kina sonshi ai yin karatu ba laifi bane”.
Ta langavar da kai kafin ta ce, “Tunda Gwaggo ba ta so shi kenan na haqura”.
Ya ce, “Haka ne Aisha, ga dukkan alamu dai kirki ne dake, don waxannan kalaman naki alama ne na zurfin nazari”.
Ta ce, “Zan tafi, don Gwaggo ta ce kar in daxe”.
Ya ce, “To Aisha, ai na gode miki kin yi min abinci mai daxi na ci na qoshi, ban da haka kuma kin yi min hira, iya kai dai hirar taki ba ta ishe ni ba, na kuma san in na ce zan biyoki gida mu qara ba yarda za ki yi ba, za ki ce saurayinki zai zo kar in zo in yi muku buqulu in hanaki hirar soyayya”.
Ya zuba mata ido a yanayin zolaya, “Ga kuma irin toshin nan da samari ke yiwa ‘yammata in sun zo hira”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ba fa kullum nake hira ba Yaya, sau xaya nake yi a sati Juma’a, dace kake yi kana samuna ina hirar saboda qarshen sati kake zuwa”.
Ya ce, “Ai shi kenan Aisha, zan iya yarda dake a kan komai tunda na san ba za ki yi min qarya ba”. Ya ce, “To yanzu tunda nima kin zo min hira me kika gani ya baki sha’awa a gidan nan?’
Ta yi murmushi ta ce, “Komai na gidanka ya bani sha’awa, musamman kicin xin. Sai dai ban buqatar ka bani komai na gode”.
Ya tashi ya shiga xakinshi ya fito da kwalin handset ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login