Showing 6001 words to 9000 words out of 31859 words
Chapter 3 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt
miqa mata, ta zuba mishi ido nuna alamar ba za ta karva ba.
“Gaskiya kyautukan da kake yi min sun yi yawa, ni wani lokacin ma har tsoro suke bani”.
Ya tsareta da idanuwanshi ya ce, “Wace irin magana Aisha ke gaya min? Nine mai yi miki kyautar da take baki tsoro? Kina nufin su Bilki sun fi kusa dani ne? Don dai baki da wayo ne sanda Inna take raye ko? Ina ganin da ba sai na tsaya ina gaya miki muhimmancinki a wurina ba, ba sai na tsaya ina gaya miki cewar bani da wata wacce zan yiwa alherin da zai sani jin daxi fiye dake ba. Ni dama na daxe na gane yanda nake jinki ba haka kike jina ba”.
Da sauri ta ce mishi, “Ba haka bane Yaya”.
“To in ba haka bane ya ya ne? Yanzu da kin mai dani nine na fi kowa kusa dake kamar yanda kike a wurina kya gaya min wannan maganar don kawai na ce ga waya, ko gaisuwar safe ma rinqa yi da safe”.
Tasa hannu biyu ta karva tare da yin godiya. Ya miqa hannu ya xauko xan makullin motarshi dake ajiye ya ce, “Muje in kai ki gida”.
Ta ce, “To”.
Sun fito harabar gidan kenan su kai kicivis da wata mota qirar Honda mai nambar Azare tana shigowa.
Mus’ab ya kalle shi ya ce, “Sai dai ka jira ni in je in dawo don ba zan fasa mai da yarinyar nan gida ba”.
Mutumin ya fito yana murmushi, ya ce, “To ka tsaya in zo mu gaisa mana don mu san juna ko kuwa?”
Ya ce, “A’a, ba sai kun san juna ba qanwata ce wannan, don na ga kana wani murmushi”.
Ya ce, “Eh, in dai gantan a haka tunda ku dama Fulani ai qannenku ne suke rikixewa su zama matanku”.
Mus’ab ya ja mota ya tafi, sai da suka hau hanya sosai sannan ya ce mata, “Aisha”.
Ta yi maza ta juyo gare shi. Ya ce, “Wannan fa shine Sham’unu abokina da nake zuwa wurin shi a Azare”.
A nutse ta ce mishi, “Na gane shi, watannin baya ka zo bikin shi”.
Ya ce, “Haka ne baki manta ba”.
Qofar wani hamshaqin kanti ya tsaya, fuskarshi a xaure ya kalli Saddiqa a yanayi na rashin wasa ya ce mata, “Muje ki duba man shafawa”.
Ta xan yi shiru. Ya fita ya rufe motar. Ya kusan minti talatin kafin ya fito, ana biye da shi da manyan ledojin sayayyar kantin guda biyu. Ya sake tsayawa a wani wurin ya sayi gasassun kaji sannan suka tafi gida.
A qofar gidan ya sauke ta da kayan ya juya ya tafi.
Cikin dare tana kwance a xakinta Mus’ab ya yi mata waya.
“Tun xazu na so na bugo in tambaye ki wani abu sai na fasa don tsoron in bugo in sameki kina taxi”.
Ta ce, “Taxi kuma Yaya? Ba ka ce in na gaya maka magana za ka gaskatani ba don ka san ba zan yi maka qarya ba?”
Ya ce, “Qwarai kuwa Aisha, ai na yarda dake da kuma zan samu yanda nake so da kema sai ki yarda dani mu yarda da juna”.
Ta ce, “To ai na ce maka sau xaya nake hira a sati, kuma xazu ka ce min in na zo gidanka za ka gaya min laifin da na yi maka na zo baka ce min komai ba”.
“Dama maganar karatunki zan yi miki, to kuma na gane bake ce bakya son yi ba Inna ce ta ce ya isa haka ki yi aure. To ai ba zan ce kar ki yi ba Aisha, tunda na san alheri ne nima da kika ganni ina zaune haka tuzuru don tawa uwar ta rasu ne da ban kawo yanzu a hakan ba”.
Ta kawar da zancen nashi ta hanyar tambayarshi, “Me kake son tambayata?”
Ya ce, “Lokacin da nake yaro na san Inna da yawan nafilfilin dare, har nima ta kan tasheni ta ce wai in yi sallah in roqi Ubangiji ya shiryar dani, kema tana yi miki haka?”
Ta ce, “Ai na riga na saba yanzu ba ma sai ta tashe ni ba da kaina nake tashi”.
“To in roqe ki mana Aisha”.
Da sauri ta ce mishi, “To”.
“Ki rinqa yi min addu’a”.
Ba ta ja maganar ba ta ce, “To zan yi”.
Ya ce, “To sai da safe”.
Saddiqa ta ajiye wayar tana tunanin tsakaninta da Yaya Mus’ab, a saninta dai tun tana ‘yar qanqanuwarta yana cikin mutanen da suke da muhimmanci a wurinta, saboda xinbin kulawarshi a gareta. Shi mai sonta ne, mai kula da ita, mai yawan alheri a gareta, a dalilin hakan ne ma ta fi kowa farin cikin dawowar shi.
To amma a yanzu halin da take ciki, tana cikin ruxani ba ta fahimtar al’amuran, varin dukiyar da yake yi mata bai yi mata daxi, a ganinta ko ‘yan’uwanshi da suke ciki xaya ba ya yi musu haka.
Washegari da safe ta idar da sallar asuba kenan ta ji qarar wayarta, ta sa hannu ta xauka.
“Ina kwana Aisha?”
Ta amsa, “Lafiya lau Yaya, ya ya gidan?”
Ya ce, “Lafiya, sai dai ban yi bacci ba jiya”.
Da sauri ta mishi, “Nima haka?”
“Me ya hana ki bacci Aisha?”
Ta yi shiru. Sai ta ji ya soma yin bayanin cewa, “Ni kin san ban iya voye-voye ba, tunanin aure ne ya hanani bacci, Aisha sai na ga ke gaki yarinya ‘yar qarama don sanda aka haifeki ina ganin kamar in ban yi sha bakwai ba na kusa, amma ga shi iyayenki sun tsaya suna son ganin sun aurar dake, ni kuma ina zaune a haka.
Sai na ga to ai dama an ce wai in ka rasa uban da zai yi maka faxa sai ka ga wani yana yiwa xanshi faxa. To sai ka rava kusa ka ji abin da yake gayawa xan nashi, don kai ma ka amfana da kalaman nashi. Shi yasa na ce to bari nima dai in hankalta da abin da ake shirin xora ki a kai in yiwa kaina qiyamullaili, ko kuwa?”
Cikin nutsuwa ta ce mishi, “ Haka ne”. Ta ja bakinta ta yi shiru.
“To ni na gaya miki abin da ya hanani bacci ke fa? Me ya hanaki yin bacci?”
A hankali ta ce mishi, “Anti Kuluwa ce ta zo gida jiya da daddare suna rikici da mijinta, ka san zai yi aure?”
Mus’ab ya ce, “A’a, wa zai gaya min Aisha in ba ke ba? Inna ba ta hira dani, Baba kuwa cewa zai yi nima ba auren gare ni ba balle aje ana tsomani cikin lamarin rikicin aure, amma in zai yi aure Aisha sai ta je tana rikici da shi?”
Ta ce, “Ai shi ya ja bai biyo ta hanyar son a zauna lafiya ba, lokacin da ya zo gaya mata zancen auren shi sai ya yi mata alqawarin canza mata kayan xaki, yanzu kuma bikin ya zo ya ce mata wai hidima ta yi mishi yawa bayan da can ba roqon shi ta yi ba. Shine abin ya tsaya min a rai, na ce to dama haka ake yi ne in za a kawo sabuwa sai ayi kamar ta gida ba sonta ake yi ba?”
Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “To ni kam ina zan sani tunda ani ko xayar ma ban yi ba. Ai shi yasa na tsarawa kaina tunda dai ni na san kaina ni ba wani jarumi bane fitina tsoro take bani, don haka na ce to in dai har na samu na auri matata guda xaya in dai har na samu wacce nake so xin to ta isheni”.
“Ai nima shine na ce ko randa za a yi min tawa amaryar ya ya zan ji oho”.
Mus’ab ya qyalqyale da dariya ya ce, “Ya ya za ki ji kuwa ban da yanda sauran mata suke ji, ga dukkan alamu dai ina jin kishi za ki yi Saddiqa?”
Ta ce, “To a yanzu dai kam ban sani ba tukunna sai a nan gaba”.
Ya ce, “To da na y niyyar sai na dawo daga Kano in zo gidan, amma ina ganin zan zo yanzu kafin in tafi”.
Ta ce, “To, sai ka zo”. Ta ajiye wayar.
Mus’ab yana zaune a falon baban shi bayan fitar Malam Abdullahi jiran shigowar Saddiqa yake yi.
“Wa alaikumus salam”.
Ya amsa. Ta shiga ta zauna ta ce,
“Ga ni Yaya”.
Ya xauki rubutaccen chaque xin dake ajiye a gabanshi ya miqa mata ya ce, “Ki kai wa Kuluwa wannan chaque xin ta karvi kuxin ta yi hidimomin gabanta, ki gaya mata kar ta sake yiwa mijinta wata magana su zauna lafiya kawai”.
Daxi ya kama Saddiqa ganin kuxin dake rubuce.
“Yaya Ubangiji ya qara maka arzikinka”.
Ya sake miqa mata envelop guda uku, “Ki kawai Bilkisu xaya, Hamida xaya, kema xaya, na san in za su sayayyar bikin za ki raka su”.
“Mun gode Ubangiji ya dawo da kai lafiya”.
Ya ce, “Ameen”.
Da yamma Mus’ab yana gidan Abu, hirarsu suke yi irin wacce suka saba, yana kuma cin dambun zogalen da ta yi mishi.
Saddiqa ta yi sallama ta shigo cikin kwalliya sosai mai ban sha’awa, ga yafen lafayan da ta yiwa jikinta ya yi matuqar karvarta. Rungume take da leda a hannunta, tana ganin Mus’ab ta qara fara’arta.
“Ashe har ka dawo?”
Ya ce, “Eh, tun la’asar nake nan gidan”.
Ta tsuguna ta gaisheshi shi da Abu. Ta miqawa Abu ledar dake hannunta ta karva tare da faxin “Tsaraba aka kawo min?”
Ta ciro ta, atamfar Diamond ce mai kyau, tare da kwalbar turare.
“Atamfa na samu? To Allah ya yi albarka, hala yau ma zannuwan kika saya?”
“Ka ji Abu, me zan saya? Su Yaya Hamida ne suka yi sayayyar kayan xaki, ni kuwa na sayi kayan ado. Yaya Kuluwa kuwa…. Ta qyalqyale da dariya kan ta yi bayani.
Tsakin da Abu ta ja ya katseta. Abu ta ce, “Sakarya, ‘yammata suna tari ran bikinsu ka ga sun fito da kaya gwanin sha’awa amma ke kullum kuxinki a zannuwa kina tsoma su a ruwa shi kenan kin wanke kuxinki”.
Ta yi dariya ta ce, “Amma ai kuma kwalliyar tawa tana burge ki ko. Tunda na sha jinki kina cewa daxin ki dani akwai ni da kwalliya, shi yasa ma duk tsiyata ba ta dame ki ba”.
Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “Aisha wani iya tsiya ne dake?”
Abu ta yi maza ta riqe baki ta ce,”Wuuu! Ai ko sarkin fawa ya san da ita”.
Mus’ab ya yi dariya ya ce, “Mahauta su ji abin da kike gayawa sarkinsu”. Ya yi dariya yana kallon Saddiqa ya ce, “Bani ruwa mai sanyi a randar Abu”.
Ta miqe ta fita ta bar Abun tana cewa, “Kai kam tunda tana ganin girmanka ai ba za ka san iya shegenta ba”.
Suna jiran dawowar Saddiqa yana yiwa Abu mitar “Kin bani dambu baki bani ruwa ba”.
Ihunta suka jiwo ta qwalla qara mai firgitarwa, da gudu suka isa inda take tsugune a bakin randa, kuka take yi da iyakacin qoqarinta tana kuma riqe da qafarta da iya qarfinta da hannayenta duka biyu.
“Mene ne? Me ya same ki?”
Mus’ab ya tambaye ta. Ba ta yi magana ba kuka take yi sosai tana faxin, “Wayyo! Wayyo Gwaggona, a kira min Gwaggona”.
“Me ya same ki Aisha?”
Ya sake tambayarta a yanayin tashin hankali.
“Gwaggo nake son gani”.
“Me za ta yi miki in an kira miki itra?”
Ta qara tsananta kukan tana faxin, “Zan gaya mata ne maciji ya sare ni”.
“Maciji?”
Da qarfi Mus’ab ya yi tambayar. Bai saurari amsarta ba ya sureta ya nufi waje da gudu da ita, ya bar Abu tana faxin “Babu maciji fa a gidan nan sai dai ko damatsiri”.
Tana kwance shame-shame a motar tana ta faman kuka, sai salati Mus’ab yake yi, babu fa maciji a gidan nan damatsiri ne.
Mus’ab ya dafe kai da hannu xaya saboda takaici. Haba Abu da kin bar wannan maganar, mene ne damatsiri mene ne maciji? Kina jin yarinyaa har ta fara sambatu.
Suna isa asibitin ya sake surarta ya rungume a qirjinshi da gudu ya haura da ita saman benen ya shimfixe kan gadon da ba marasa lafiya.
“Cizon maciji ne, likita cizon maciji ne”.
Bayanin da yake yi kenan.
Nan da nan aka shiga gwaje-gwaje da bincke don gano inda cizon macijin yake babu, sai kuma ya shiga gwajin dafi tsawon lokaci yana aikin.
Ita kuwa Saddiqa ba ta ko buxe ido sai faman salati take yi Mus’ab yana taya ta tare da yi mata bayani, babu fa abin da zai same ki Aisha, ai ba za ki mutu ke kaxai ki barni ba, ai sai maraicin ya yi min yawa ni dake ai….”
Tsakin Abu ya katse shi, ya yi maza ya koma inda take, ashe ma ta daxe tana harararshi bai lura. Haushi da takaicin Abu suka tarar mishi, ga shi babu halin ya ce ta koma gida saboda shakkar barin ta da yake yi.
“Yallavai bana jin akwai dafin maciji a jikin yarinyar nan”.
Tsit! Gaba xaya xakin ya yi har ita ma Saddiqan. Nan take ta tsai da kukan nata.
“Babu dafin maciji, bamu samu wani dafi a jikinta ba”.
Mus’ab ya juya ya fuskanceshi yana share gumin fuskarshi da hankicif.
“Ban gane ba likita”.
Likita ya yi cikakken bayani, ya ce, “Babu dafin maciji babu ma alamar cizon sa a nan, wannan kuwa ai bai wuce cizon kwarkwasa ba zo ki gani babu”.
Ya juya yana kallon Abu. Abu tana matsowa a hankali tana faxin “Ni kam ai na santa likita, ai wannan ma ba komai bane cikin irin tsiyar da ta iya, babu shakka ita ce”.
Mus’ab ya matsa jikin Saddiqa ya ce, “Aisha kin ga macijin da ya cije ki ne da idonki?”
Ta ce, “A’a, amma dai na ga shukar bayan randar tana motsi”.
Abu ta galla musu harara su dukansu, bayan ta ja tsaki mai qarfi haxe da faxin, “Aikin banza kawai har da na wofi”.
Su Gaggo suka turo qofa hankal a tashe, da sauri Abu ta ce musu, “Duk ku kwantar da hankalinku, iya shegenta ne kawai ya motsa ta yi sha’awar ta-ta da hankalin mutane, gata nan ita ma ta amsa ba ta ga maciji da idonta ba, shukar bayan randa ta gani tana motsi”.
“Sannu Saddiqa”.
Gwaggo ta faxa tana mai kallon ta.
“Yauwa Gwaggo”.
Ta amsa cikin shagwava. Likita ya shigo da takarda yana nufin yin sallama, “Babu cizon maciji sallama zamu ba ta……”
Mus’ab ya ce, “Ina ganin a barta a nan zuwa gobe ta qara samun nutsuwa”.
Ya ce, “To, babu laifi, bari mu ba ta xaki”.
Abu ta ce, “Ashe ba gara mu koma gida ba tunda dai yarinyar nan lafiyarta qalau?”
Ya ce, “A’a, gara dai tana kusa zuwa goben in an qara tabbatarwa sai a tafi”.
Suka koma xakin da aka basu, Abu tana mitar yanda Saddiqan ta kaxa musu ciki babu gaira babu dalili.
Kafin yamma asibiti ya cika da jama’a, sai shiga suke yi suna fita, duk masu dubiya ne. Abokan Mus’ab ma suka yi ta kaiwa da kawowa.
Gwaggo kam tuni ta bar wurin saboda ganin Mus’ab ya qi barin asibitin, sai Abu ce a zaune. Ita kuma tuni ta kawo Mus’ab iya wuya saboda yanda take yiwa masu zuwa dubiya bayani lafiyarta qalau iya shegenta ne dai da ta saba ya motsa, ana ta kwashewa da dariya.
Mus’ab ya gaji ya kirata gefe ya ce, “Abu so nake…”
Gane abin da yake nufi yasa ta galla mishi harara ta ce, “Yanzu ashe samarin nan da na ga kana tura min cikin gida sare min bishiyoyin gidan kasa suke yi?”
Mus’sab ya ce, “A’a Abu, ni cewa na yi nemo macijin da ya sari Aisha su kashe shi a biyomu da shi asibiti, ina jin gurin neaman shi ne suka sare miki bishiyoyin”.
“To in