Showing 30001 words to 31859 words out of 31859 words
Chapter 11 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt
ki taimakeni kamar yanda Innata ta taimake ni a farko, ai ita ta haifeki Aisha, taimakeni ki yi min kwatankwacin gatan da ta yi min a farko”.
“In ma ban yi ba, ba laifina bane kai ne tsoro ya hanaka yin abin da ya dace ka yi”.
“Ai tsoron ni kar a rabani dake ne Aisha, Inna ta ce in na ce ina sonki za ta baki labarin mugun halina, tana qina dake ne wai a dalilin tana tsoron kar in cutar dake. Na rantsre miki ba zan iya cutar da ke ba Aisha, don haka ki toshe kunnuwan ki a kan abin da za ki ji an gaya miki a kaina”.
Ta kalle shi cikin nutsuwa ta ce, “Kana nufin ba gaskiya bane?”
Da sauri ya ce mata, “Gaskiya ne Aisha, gaskiya za ta gaya miki, ni ban tava jin wata magana ta fito bakin Inna ba sai gaskiya, don haka gaskiya kawai za ta faxa, ni xin ne ita ta haifaeni ta fi kowa sanina, tana qina dake saboda wasu halaye nawa da take ganin basu yi mata ba.
To amma kar ki manta na zauna gaban Innata ta tausaya min ta taimakeni ta rabani da duk wani abin da nake yi a wancan lokacin, don haka na roqe ki duk abin da za ki yi a kaina ki tausaya min kar ki juya min baya”.
Saddiqa ta miqe da nufin tafiya gida Mus’ab ya biyota.
“In kin je gidan za ki yiwa Inna maganar ne?”
Ta ce, “Ai nima tsoro nake ji”.
“Haba Aisha, ki taimakeni mana kar ki bari su aurar dake ga wannan mutumin na fishi dacewa dake, na fishi sanin darajarki, zan fishi girmamaki in kika daure kika toshe kunnuwanki kan abin da za ki ji a kaina kika amince kika aureni. To ni kuwa ba zan tava baki kunya ba”.
Suna isowa qofar gidan ta shige ciki ta barshi nan a tsaye.
Innarta tana ta aikin qunshe goron da take aikewa da shi na gaiyatar mutane biki, ta kalli Saddiqa yanda fuskarta ta canza.
“Hala daga wurin yayanki kike?”
Ta koma gefe xaya ta tsuguna alamar tana son yin magana, sai dai ta kasa, ta rasa ta inda za ta faro zancen.
Ta kalli Inna cikin rawar jiki da rawar murya ta ce mata, “Inna mene ne?” Ta yi shiru saboda yanda jikinta da muryarta suke rawa.
Inna Habiba ta zubawa Saddiqa ido cikin tausayi, zuciyarta ta tabbatar mata da cewar son Mus’ab take yi, sai dai ba za ta barshi ya yi nasara a kan yarinyar ba.
“Me ya faru Saddiqa? Me kike son gaya min? Tambayi duk abin da kike son sani zan gaya miki ba tare da raina ya vaci ba, ba zan yi fushi dake ba balle in je ina yi miki faxa, ai baki da wata uwar da ta wuceni, nice uwarki. Yayanki ya gaya miki wata magana ne?”
Saddiqa ta soma kuka, ta ce, “Yana sona, Inna ya ce kece kika hanashi ya gaya min yana sona bayan kuma shine xan’uwana”.
Gwaggo ta yi murmushi ta ce, “Ke yarinya ce Saddiqa shi yasa baki gane dalili ba, ke da yayanki ‘yan’uwa ne da zumunci ya haxaku, sai dai halayenku da xabi’unku ba xaya bane, shi ba abokin haxinki bane, hanyar jirgi daban ta mota daban, ba zamu iya dashi ba halayensa sun fi qarfinmu”.
Ta ce, “A’a, Gwaggo ni zan iya da shi, ni shi nake so ba Sadisu ba, dama na yi shiru ne kawai don bai riga ya furta min ba, amma yanzu tunda ya gaya min ya yi min rantsuwar bai da wata budurwa a Misau in ba ni ba. To ki taimakeni ki yafe min kar ki baiwa Sadisu ni, Yaya Mus’ab nake so”. Ta kai gwiwpyinta qasa ta durqusa a kansu alamar roqo cikin kuma kuka mai tsanani.
Inna Habiba ta zuba mata ido tana kallon ta, ta ce, “To Saddiqa ni dama ai ba wai bana sonki da shi bane, savanin dake tsakaninku ne na ga ya yi yawa na ce gara miki inda za ki samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Amma tunda haka ne ai shi kenan, ni na gane ke ko warin sigari baki so a kusa dake, to shi kuwa na ji labari an ce lokacin da kamfanin sigarin da yake sha na Rothmans suka yi bikinsu har kyautar girmamawa suka yi mishi saboda cinikin da yake yi musu.
To wannan ma da xan sauqi a awurina da ya tsaya a haka nan, inda kike ganinshi mashayin barasa ne na qarshe”.
Saddiqa ta qwalla qara da iyakacin qarfinta tare da kama kanta da hannayenta duka biyu.
“Wayyo Inna! Wayyo Allah!!”
Inna ta samu damar xora bayaninta da cewa, “To shi nake jiye miki, kin san halin mashayi bai da wata amana, ga shi manemin mata. A nan garin ne kawai baya yi, amma an tabbatar min da cewar duk inda yake in ba a nan bane bai rabo da matan banza suna biye da shi, shi yasa nake tausayin quruciyarki.
Kina da sha takwas ne yana da talatin da biyar, ina tausayin ki zama matar mashayi ko manemin mata, shi yasa na zava miki Sadisu yaro qarami, bai girmeki da wasu shekaru masu tsanani ba, za ku yi quruciyarku tare ne ku girma tare, a kan idonmu aka haife shi har ya girma, bai da wani halin assha, shi yasa na zava miki shi ku biyun dukanku yaran kirki ne masu biyayya masu ganin girman na gaba. Ko kuwa har yanzu kin fi son auren yayanki a kan Sadisu?”
Cikin kuka ta ce, “Na haqura Gwaggo, na yarda da zavin da kika yi min na auren Sadisu”.
Daxi ya kama Inna Habiba, ta shiga sanyawa Saddiqa albarka, cikin zuciyarta kuwa faxi take yi ja’irin yaro kawai, ba zan barka ka yi galaba a kanta ba balle ka sanyani in ji kunya, bayan na riga na yi alqawarin baiwa xan aminiyata ita za ka zo ka bijirar min da ita.
Mus’ab kuwa yana can gidanshi tare da Sani suna tattaunawa kan yanda za ayi, sai dai maganar kawai yake yi amma hankalinshi yana can wajen sauraron wayar Saddiqa, don ta gaya mishi yanda suka yi da Gwaggonta shiru babu wayar.
Hankalin Mus’ab ya kai matuqa wajen tashi. Sani ya kalle shi cikin raxa ya ce, “Ina ganin tunda ni a gida ba a san na zo ba, tunda da sauran duhu muka iso muka kuma taho nan kai tsaye, ko in ka ga da matsala abin zai mana gardama in xauke maka yarinyar mana in tafi da ita sai kai ka yi zaman ka, ka yi ta taimakawa wajen neman ta, ka ga babu mai gane kana da hannu cikin vacewar tata, in yaso daga baya in hankula suka kwanta sai a dawo da ita sai a xaura muku aurenku”.
Mus’ab ya zuba mishi ido cikin nazari ya ce, “Da zan yi jarumtakar yin hakan to da na ji daxin shawarar taka, to ba zan iya ba saboda dalilai guda biyu.
Na farko bana so wani savani ya sake shiga tsakanina da iyayena, a yanzu mun shirya ni da babana, ni da shi muna da fahimtar juna, zamu zauna tare mu yi hira, zai bani shawara zai yi min nasiha har muna zuwa unguwa tare. Inna ce bani da wannan fahimtar da ita, ina kuma qoqarin ganin mun samu daidaituwa sai kuma in zo in tafka musu irin wannan laifin? Bana zaton in ya bayyana zamu sake samun wata fahimta dasu.
Na biyu duk matsanancin son da nake yiwa Aisha ina son mallakarta ne ta hanyar aure, in babu auren to bani da wata buqata irin wannan a tare da ita, don ba zan iya keta haddinta ba, don haka na fi so iyayenmu su yarda su bani ita in mallaketa ta zama matata da izininsu don mu samu albarka, in kuma yi qoqarin gyara abin da na riga na vata a baya.
Yanzu fatana bai wuce komai za a gayawa Aisha ta yarda ta daure ta bani haxin kai ba, in har ta yi min haka, to komai zai zo min da sauqi. Don in har ta dage ta ce ni take so, ina ganin kamar Innar za ta yi sassauci”.
Gajiya ya yi ya xauki wayarshi ya danna lambobin Saddiqa, kwance take a xakinta har lokacin kuka take yi ba ta daina ba.
Kamar kar ta xauki wayar sai kuma wata zuciyar ta ce ta xauka.
“Na ji shiru ne Aisha shine na ce bari in bugo in ji me kike ciki? Sai dai na ji kamar kina kuka, me ya same ki?”
Ta ce, “Kukan baqin ciki nake yi”.
Gaban Mus’ab ya faxi ras! Ya daure ya tambaye ta.
“Baqin cikin me kike yi Aisha?”
Ta ce, “Baqin cikin da ka yi min dalilin shi”.
Ya sake wani mummunan faxuwar gaban mai qarfi.
“Ki taimakeni Aisha ki tausaya min ke kaxai nake dake, Aisha in kin barni za ki barni cikin qunci da wahala, taimakeni ki bani haxin kai ki zama matata”.
Ta yi maza ta katse shi da cewa, “Kana nufin in zama matar mashayi?”
Ya ji tamkar guduma ta buga mishi. Ya yi qarfin hali ya ce, “Ba haka nake nufi ba”.
Ta ce, “To abin da Gwaggo ta gaya min kenan game da kai, ko kuwa me ka ce game da maganganun da ka ce za ta gaya min?”
Ya ce, “Na ce miki gaskiya ne ban tava ji ta faxi wata magana ba sai gaskiya, ita ta haifeni ta fi kowa sanina. Sai dai komai ta gaya miki ki daure ki taimakeni…….”
Kafin ya qarasa ta katse shi da cewa, “Ba zan iya ba, tunda ban ga alamar kaima kana taimakon kanka ba, don haka ka yi haquri ka taimakeni ka fita hanyata, ka taimakeni kar ka sake shiga al’amurana ka barni in yiwa iyayena biyayya. Dama ni abin da na saba kenan, don haka daga yau bani ba kai……”
Ta katse layin ta bar Mus’ab riqe da kan wayarshi a hannu cikin kaxuwa da firgita, a zuciyarshi kuwa cewa yake yi “Wayyo Aisha! Za ta tilastani yin abin da bani da niyyar yi a kanta!”
Mu haxu a littafi na biyu.
ABU NAKA wai maganin a kwaveka.
Taku;
Aunty Hafsat.