Showing 9001 words to 12000 words out of 31859 words

Chapter 4 - ABU NAKA Book 1 Complete Document By SODANGI.txt

02 Dec 2024

1511

sunyi min ta’adi kuwa ni da kai ne”. ta juya ta tafi.
Har wajen qarfe goman dare abokan Mus’ab sai isowa suke yi rungume da tsarabar majinyata niqi-niqi su ajiye, su kuma miqa abin miqawa wanda Abu ke karvewa tana adana abinta.
Sadisu shima ya iso da tashi tawagar, sai dai ganin yanda Mus’ab ya kasa ya tsare ya hanashi iya zaman asibitin.
Kwana biyu da sallamar Saddiqa daga asibiti tana kwance kan katifa a falon Gwaggnta, Abu da Gwaggon suna hira bayan tafiyar Sadisu da abokanshi.
Ta ce, “Abu ba ki fa bani komai na abin da aka tara a asibiti ba”.
Ta kalleta ta ce, “Tsarabar mara lafiya biyu na raba na xauki rabi na kawo muku rabi, kuxi kuwa qwandala ba zan bayar ba na riqe su ladan kwanan asibitin da aka sani”.
Mus’ab ya yi sallama aka amsa, ya shigo cikin falon cikin shirin tafiya Ajakuta. Ya gai da mahaifiyarshi cikin girmamawa, sannan ya gai da Abu.
Saddiqa ta ce, “Yaya kar dai tafiya za ka yi?”
Ya ce, “Zan tafi Aisha yanzu cikin yardar Ubangiji”. Ya miqa hannu kusa da mahaifiyarshi ya ajiye mata envelop xin da yake sunne da shi.
Ta ce masa, “Su Hamida sun je gidanka jiya za suyi maka godiya basu same ka ba”.
Ya ce, “Eh, baba maigadi ya gaya min na kuma yi magana dasu a waya yau da safe”.
Ya zaro walet xinshi ya qirga dubu biyar ya miqawa Abu, Saddiqa ta ce, “Duk kuxin nan da aka bayar a asibiti Yaya ba ta bani qwandala ba riqesu ta yi”.
Ya ce, “Ba komai Aisha bari a qara mata”.
Abu ta galla mata harara, ya yin da bakinta ke ta faman yiwa Mus’ab addu’a. Ya miqe ya doshi qofar fita, Saddiqa tana daga kwance ta ce, “Yaya Ubangiji ya tsareka”.
Abu ta yi maza ta daka mata tsawa ta ce, “Tashi ki je ki yi mishi rakiya, ja’ira shagwavavviyar wofi, kin naxe wuri xaya kamar wata mai jinyar gaske?”
“Kar dai a ce in ban da Abu ta yi miki magana ba za ki zo mu yi sallama ba?”
Ta ce, “Uhm! Yaya Abun ce komai na yi ban fita a wurinta, in ta ga ma in zan yi rakiya ta ce ina vare-vare, in ban je ba ta ce ban san yanda ake girmama baqi ba”.
Ya yi murmushi ya ce, “To gaskiyarki gara da kike yi mata hakan, in ta ce kije-kije, in ba ta ce kije ba ki yi zaman ki”.
Ya zuba mata ido ya ce, “Amma kin san ba ki tava sha’awaa don ra’ayin kanki kin ce Yaya ga hotona na baka ba ko?”
Ta ce, “Lah! To ai ban tava sanin kana so ba, to amma tunda ahaka ne kafin ka dawo zan ajiye maka su kala-kala”.
Ya ce, “To shi kenan”.
Ya buxe aljihun motarshi ya ciro envelop mai xan nauyi ya miqa mata, tasa hannu ta karva haxe da faxin “Wa zan kai wa?”
Ya ce, “Naki ne ki qara kwalliya ki qara yin kyau Inna da Abu suyi ta ganinki suna qara jin daxi, kafin in dawo ina so ki cika min alqawarin da kika yi min”.
Ta yi maza ta ce, “Insha Allahu”.
Suka yi sallama ya tafi, ita ma ta shiga gida.

RAYUWAR MUS’AB A AJAKUTA
Gidan nashi babba ne qwarai, irin gidajen nan ne na ma’aikatan Ajakuta Star Rollin Company, yana zaune a gidan ne shi da wani tsohon abokinshi xan Bauchi da suka yi sabo tun sanda yake karatu a A.T.B.U.
Mus’ab ne ya gayyato shi ya dawo gidan, duk da shi ba ma’aikatar yake ba don ya ragewa kanshi zaman kaxaici, ga kuma yawan tafiye-tafiye da yake yi, haka nan abutar tasu ta yi dai-dai, dan kuwa halayensu xaya ne.
Mus’ab da Sani suna zaune a falo, karan sigari ne a hannayensu, labarin tafiyar Mus’ab ke ba shi.
“Ai sa kai kawai za ka yi ka bar wani kamun qafa wurin kakarku, ka san su iyayenmu su kullum ya kamata suke basu san tuni aka bar wannan ba, ga na gida yana so yaushe za aje ana maganar na waje? Ina ce sai na gida ya qoshi ake miqawa na waje shima ya samu? Ka janyota a jikinka ka yi hikimar da za ka yi ta yanda za ka shiga tsakaninta da saurayin cikin hikima”.
Mus’ab ya zuqi sigarinshi cikin jin daxi ya fitar da hayaqin a nishaxance ta baki ta hanci, ya kalli Sani a hankali ya ce mishi, “Ba fa yarinyar nake tsoro ba, mahaifiyata nake tsoro, ita ce kuma take riqe da ita”.
Sani ya ce, “Ka dai yi qoqarin kammalawa da yarinyar tukunna”.
Ya ce, “A’a, ana ga qura kai kana ga hayaqi, in baka sani ba Aisha za ta iya cewa tana sona mahaifiyata ta ce ba ta yarda ba”.
Da sauri Sani ya tambaye shi ya ce, “A kan wane dalili?”
Ya gyara zama ya ce, “Saboda tana ganin ban dace da auren yarinya irin Aisha ba, tunda ina shan wannan”. Ya xaga karan sigarin dake hannunshi ya nuna mishi.
“Ta kuma riga ta san game dani, in na voyewa Aisha ba zan iya voyewa Inna ba. Ita kuma mai qyamar irin waxannan xabi’un ne, ina kuma tabbatar maka cewa ko cikin ‘ya’yan da ta haifa ban ga tana yiwa wani irin son da take yiwa Aisha ba”.
“To yanzu kai tunda haka ne me ka shirya?”
Mus’ab ya wurgar da guntun sigarinshi cikin ashtry ya sake xauko wani ya sake kunnawa, sai da ya yi mishi kyakkyawar zuwa ya fitar da hayaqin a hankali cikin nutsuwa, kafin ya ce mishi, “To gani nan dai Sani, ban san abin yi ba tukunna, na daia san kawai ina son Aisha, zan kuma tsaya in yi komai haar sai na ga abin da ya turewa buzu naxi”.
Jeenifer ta shigo, daga xakin shi ta fito, banbancinta da mai tsirara kaxan ne. Ta nemi wuri a gefe ta zauna, ita ma sigari take sha, sai da ta zuqa sau biyu ta nisa sannan ta ce, “Ba fa faxan ya qare bane, don kar ka xauka tilastani da ka yi na yi abin da bana so yana nufin ya qare kenan, na gaji da abin da kake yi min kullum ina tare da kai amma wai ban isa in za ka Misau ka gaya min ba, sai kawai in zo gida in samu ka tafi, ni dama ba zuwan arziki na yi ba, don kawai ka gwada min fin qarfi ne kuma ba zai hanani yin faxar da ya kawo ni ba”.
Sani ya qyalqyale da dariya ya ce, “Haba Jeenifer faxa ai ya qare tunda har aka yi haka sai dai nan gaba kar a sake tunda kin ce bakya so, nima shaida ne don haka kai Mus’ab ka ba ta haquri”.
Mus’ab ya kalle ta ya ce, “To a kan wane dalili za ayi hakan? Kar in je ganin iyayena sai na sanar na nemi izini wajen wata? Ko kuwa don an ganni a bariki? Ko na tava gayawa wani cewa daga sama na faxo ba daga jikin iyaye na fito ba?”
Sani ya ce, “Kai fa tsiyata da kai kenan, in an ce ka yi laifi ka ba da haquri sai kawai ka fi wanda ka yiwa laifin fushi”.
Mus’ab ya ce, “A’a, rainin hankali ne bana so, iyaye wasa ne? Daina xaurewa qarya gindi Sani, bariki na je? Ba za a tambaye ni lafiyar mutanen gida kafin a ce min ga abin da na yi ba sai a rinqa muzurai ana yi min barazanar tashin hankali wai za a min tsiya? To tsiyar me za ayi min? Ko na tava cewa wani ina tsoron tashin hankali ne? Ni ba rufe ni da duka za a yi ba surutu ne kawai in na ga ya ishen kuma in yi waje da mutum in rufe gidana”.
Jennifer ta zovara baki. Sani ya ce, “Gaskiya kema baki kyauta ba, da kika san gida yaje ai da sai ki tambaye shi mutanen gidan kafin ki yi maganar da za ki yi daga baya, don haka a dai yi haquri kawai maganar ta qare”.
Ta zauna nan suna hira da Sani, Mus’ab ya kalle ta ya ce, “Zan fa ci abinci”.
Cikin hanzari ta miqe ta shiga kicin ta soma aikin abincin da za su ci.
Tana cikin shiryawa a falo bayan ta kammala ya yin da shi kuma Mus’ab yake tsaye yana gyara hannun rigarshi da ya naxe saboda alwalar da ya xauro, sai ga wata sisin ta shigo gidan tana takun qwas-qwas, tun daga bakin qofa ta sakar mishi murmushi.
Ya ce, “Welcome Blessing”.
Ta iso gare shi, kafin ya ankara har tasa hannayenta biyu ta rungumoshi tare da sumbatar kumatunshi, da sauri ya ture ta cikin takaici.
“What nonsese is this Blesssing? Kina ganin ruwa a jikina ke baki san in anyi alwala ba a irin waxannan abubuwan ba?”
Bai saurari maganarta ba ya fice cikin sauri don ya sake wata alwalar don kar ya rasa jam’in masallacin unguwar.
Mus’ab ya dawo ya samu Sani a tsakiyarsu yana ba da haquri, ya kalles hi bayan ya wurga carbinshi kan kujera.
“Kar dai yau ma baka je masallaci ka samu jam’I ba?”
Sani ya ce, “Ai inda na tafin kuwa da ba ta yi kyau ba, don dambe suke yi mana a gida”.
Mus’ab ya harari Sani ya ce, “Suyi mana dambe a gida hauka suke yi? Wace ce matata a cikinsu? To ko matan aure ai huxu aka bani ikon yi balle haka kawai daga ana zaman cin arziki sai kuma wata ta ce ba ta yarda a ci da wata ba. Ni duk matar da ta shigo gidana saboda ni sonta nake yi, in na ga dama in haxa biyu ko uku a kan gadona duk zan iya daku, gadon kuma mai faxi ne kar wata ta ce za ta tayar min da hankali”.
Ya xebi abincinshi ya soma ci hankalinshi a kwance, ko kallon inda suke ba ya yi.
Jenifer za ta yi magana ya katse ta.
“Look, I want peace? Kin gane?”
Ya tsareta da ido. Ta tsuke baki, ya tashi ya shiga xakinshi ya fito kowacce ya ajiye mata dubu goma a jikinta ya ce, “A gai da gida, in na yi marmarin ganinku zan nemo ku”.
Jennifer ta watsa mishi kuxin da ya ajiye mata ta ce, “Azzalumi”. Ta wuce ta yi tafiyar ta. Ya bi bayanta da kallo tare da faxin “Kin huta”.
Kwana biyu da dawowar Mus’ab yana kwance cikin kujerar kwando a harabar gidanshi da yamma yana shan iska, ya danna lambobin Saddiqa yana jin muryarta ya yi ajiyar zuciya a hankali.
“Ya ya jikin naki Aisha?”
Ta amsa da cewa, “Abu fa ta ce lafiyata qalau wai shagwava ce kawai”.
Ya ce, “To ai ta dace dake, kin san ba duka mata ne suke kyau da yin shagwavar ba, amma ke kam taki tana bani sha’awa, sai in ji tamkar ina ma dai nima budurwata haka take kamar ki, da sai in rinqa barin komai in yi ta lalacewa wajen tarairayarta. Shagwava tana cikin abubuwan da suke burgeni, ban sani ba ko don ni xin ban tava samun damar da na yi ta bane”.
Ta yi murmushi ta ce, “Yanzu nan kana nufin ko cikin quruciyarka baka yi shagwava ba?”
Ya ce, “To wa zan yiwa Aisha? Inna dai kema kin san ban yi mata ba, dama a gaban Abu ne na xan fara aka kuma yi maza aka rabani da ita, ita kuma Innata da ya kamata in yi mata tunda ita ce ta jani a jikinta ta yi min duk wani abin da uwa ke yiwa xa na zo wurinta ne da wayona, ban kuma ma riga na saba da shagwavar ba.
A lokacin nan qoqarina kawai bai wuce in jiyar da ita daxi ta hanyar yin abin da ta ce min in yi ba, in kuma bar abin da ta ce min in bari, wanda gaba xaya abubuwan da za su taimaki rayuwata ne, ban kuma gama mallakar hankalina ba sai kawai na rasata kwatsam, wanda ban tava zaton zan rasata ba”.
Ya xan yi shiru kaxan, kafin ya ci gaba da cewa, “A kullum na tuna rayuwata a gaban Inna na kan tambayi kaina, ko inda na gama girma na gama mallakar hankalina a gabanta da wane irin mutum na zama?”
“Irin yanda ka zama a yanzu mana Yaya, rayuwarka ai rayuwa ce da ta yi nasara…”
Ya yi maza ya ce, “A’a, Aisha bar wannan maganar kawai, ni dai na sani ni da Kawuna muka fi kowa rashinta, don kullum na tuna ta tausayin kaina yana kamani, in kuma ji tausayin Kawu, mune har yanzu muke fama da maraicinta, ke kam kin daxe da mancewa da ita. Ko da yake dai dama can ba wani saninta kika yi ba”.
A hankali ta ce, “Na santa mana”.
Mus’ab ya ce, “Aisha wani saninta kika yi? Lokacin da ta rasu ai baki da wayo”.
Ta ce, “Tafxijam! Shekarata fa bakwai ne”.
Ya ce, “To na ji gaya min me kike tunawa da shi game da ita?”
Ta ce,”Tana aikena in kai sadakar qosai wurin yara”.
Mus’ab ya yi ajiyar zuciya ya ce, “Eh, xabi’arta ce yin hakan”. Ya sake yin ajiyar zuciya a hankali.
“Kullum a cikin kewarta nake, na sani da tana nan da ban samu kaina a cikin halin da nake ciki ba a yanzu”.
Ta ce, “Kai Yaya kullum sai ka ce matsaloli ni kuma bana ganar maka su”.
Ya ce, “Uhm! Don ke yarinya ce da kin san ina dasu da yawa, yanzu misali zan miki ina da budurwa a nan Misau wacce nake so kamar raina, amma na kasa fitowa in nuna ina sonta saboda tsoron rashin samun goyon bayan iyayenta, da Innata tana raye da ba sai na buxe baki na ce ina son yarinyar ba za ta bani ita. To balle in ce mata ina so, ai da iyakar abin da zan yi kenan sai kawai ta gama min komai. To yanzu fa?”
Ta ce, “Yanzu ma ai kana da yanda za ka yi Yaya, bana ganin kamar tsoro ko rashin samun goyon baya daga wurin wasu zai hanaka samun matar da kake so”.
“To bani shawara mana Aisha na yanda zan yi in same tan”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ai ba sai na koya maka ba, hikimar samun macen da namiji ke so irin ganin xabi’arshi ne ba koya mishi ake yi ba. To balle ma kai ka girmeni nesa ba kusa ba, Inna ma cewa ta yi wai xan qiris ya rage shekarunka su wuce nawa”.
Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “Yawan shekaru ba shine hikima ba Aisha, yanzu ni xin nan da kike gani da qasumbar nan tawa da yawan shekarun nan nawa da Inna take gaya miki, da hali zai yi mu zauna wuni xaya ni dake da kin gane shekarun ne kawai da qasumbar amma bani da wata dabara”.
Ta yi dariya mai qarfi ta ce, “Haba, haba ai kuwa da sai ayi mamaki”.
Ya ce, “To shi kenan, amma ai kin san dama can dabarar maza ba ta kai ta mata ba”.
Ta ce, “Haka nake ji wai”.
Ya ce, “To madalla na yi sa’a da ba a bakina kika fara ji ba. To mazan da suka samu damar kusantar iyayensu mata ma kenan a shekarunsu na quruciya, to balle ni da ban samu hakan ba. Shi yasa nake jin wani lokaci zuciyata tana raya min to ko dai zan qulla abota ne ni dake”.
“Abota kamar ya ya?”
Da sauri ta yi tambayar. Ya ce, “Kamar ta baiwa juna shawara in ina da matsalar da ta shafi budurwar tawa in gaya miki komai, in kina tare dani xin za ki qarfafa min, kin sani ko cikin ‘yan’uwa Aisha akan samu wanda ya fi kwanciya maka a rai, sai ki ga bayan qaunar zumunci dake tsakaninku sai ki ga kuma akwai wata fahimta ta daban da take haddasa musu shaquwa.
Yanzu in da za a tambaye ni a ce Mus’ab cikin ‘yan’uwanka duka wa ka fi so? Ai in aka barni sai in ce kece, in aka sake tambayata shaquwa fa? In sake cewa Aisha, kamar yandaa na san kema za ki ce nine”.
Ta yi maza ta ce, “A’a, ya ya ka yi ka sani bayan ga ‘yan’uwa da yawa ina tare dasu a Misau?”
Ya ce, “To

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login